Showing 186001 words to 189000 words out of 259198 words
Chapter 63 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
magana, ta tattara Farhan ta watsar ko kallon in da take Umma ba ta yi.
Ga mutane da suke ta shigowa, wai yiwa Umma jaje da yawa ba jajen ne ke kawo su ba, zunzurutun gulma ce ke kawo su.
Haka a waje ma, Abba tararsa ake da maganganu daban daban, wasu na masa jaje wasu kuma na gulma, nan fa abun duniya ya kuma tsayewa Farhan, kullum cikin wunin ɗaki take, in ta fito banɗaki za taje.
Abun duniya ya sake sakota a gaba, ta rasa abunda yake mata daɗi, har ɗaki taje ta samu Abba ta durƙusa akan gwiwowinta tace "Abba, dan Allah dan Annabi kayi haƙuri, nasan nayi kuskure amma ku yafemin dan Allah"
"A'a Farhan, karki sake cewa kuskure, ganganci dai da son zuciya, Farhan 'ya'ya na maza ba suyi shaye shaye ba, ki barni inji da alhinin abunda ya sameki, na fasa Aurenki, amma dan ki kunya tani a idon duniya, Ranar ɗaurin Auren ki ita ce zaki sha abun maye?"
"Abba, maganin ciwon kai na siyo, ban san abun maye bane wallahi, na zaci maganin ciwon ka ne kawai, dan Allah Abba ka yafe min"
Abba yace "Ai dama bance miki komai ba, tashi kije"
Jiki a sanyaye Farhan ta bar ɗakin Abba, tana zubda hawaye, tana kallon yadda Umma ke wurga mata wani irin mugun kallo, amma Farhan ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta wuce ɗakinta.
Sedai fa maganin nan da ta sha, ta ji sauƙin nauyin da kanta ke mata, ta ɗorawa kanta laifi ne saboda rabi aka ce ta sha, amma ta sha fiye da haka, sedai tunda maganin ya saketa, take jin kanta ya cigaba da nauyi, zuciyarta na mata wani irin zafi.
Washegari da safe, Umma ta ga Farhan ta shiryo cikin Uniform, ta kalli Farhan tace "ina zaki?"
"Umma makaranta zan koma"
"Wallahi baki isa ba, bayan abun kunyar da kika janyo mana, ki wanke ƙafa kice zaki wata makaranta, me karatun naki ya amfana mana, kik biyewa saurayi ya hure miki kunne, kinyi kutungwilar da aka fasa Aurenki"
Mamaki ya cika Farhan, meye laifinta a cikin fasa Aurenta da a kai, ita wace gudunmuwar ta bayar na fasa Auren.
"Umma dan Allah ki barni in cigaba da zuwa makaranta"
"Ba in da zaki, wuce ɗaki ki zauna, ke da ba ki ɗau abun kunya wani abu ba, ke da boko har gaban abada, wuce ɗaki, yadda kika samu a wannan halin na damuwa ke ma ba zaki ga da kyau ba, tun da kangarewa ki ka zaɓa ga ki ga duniyar nan"
Da ƙyar Farhan ta cira ƙafa ta koma ɗaki, zuciyarta kamar tai bindiga, ita ka a rayuwar ta wane irin laifi taiwa Umma da ta tsane ta haka? Take jifanta da mummunar kalmar kangarewa.
Nan zuciyarta ta shiga kai komo, da tsananin buƙatar nemawa kanta mafita.
Nana kam bayan sun dawo ma faɗa suka cigaba ita da Sadik, ya dinga mata masifa akan cewar dan me za ta gaisa da maza.
Tace "Ashe kai ma ka fara kishin nawa?"
"Ubanwaye ze yi kishin na ki?"
Tace "to in ba kishin ka ke ba, ina ruwanka da ni?"
"Ni kike wa haka?" Yai maganar yana nuna kansa.
Ta tura baki tace "to yadda ka ji ɗin nan, haka na ke ji idan na ga kana taɓa mata"
Ƙwafa yai ya raɓata ze wuce, se kuma ta bishi da Sauri tana faɗin "Abokina dan Allah kayi haƙuri, wallahi nima ban ji daɗi abinda nai ba, se Astagfirullah nake, wallahi nayi ne dan ka ji abunda nake ji, amma ka yai haƙuri ba zan sake ba"
"Kije ki cigaba, tunda abunda kike yi kenan a makaranta"
Ta ƙwalalo ido tace "wallahi bana taɓa maza, ka ji na rantse maka, dan Allah kayi haƙuri" tai maganar a marairaice.
Yace "Naji, jeki ki bani guri" ta ɗan zumɓura baki ta fita.
Amma a ƙasan zuciyar sa sosai, yaji pain na gaisawar da Nana tai da abokinsa, amma ya danne dan ya san shima ba shi da gaskiya.
Farhan ta na son Zuwa Makaranta sosai, dan zaman Gidan ba abunda yake sa mata se tsananin damuwa, da tsangwama da ga mahaifiyarta.
Abba ta je ta kuma samu, akan Umma ta hanata zuwa Makaranta, yace bakomai ta shirya ta koma makaranta, Umma taji hasuhin hakan, amma ba yadda ta iya da su.
Se dai yau ma da kanta taje neman maganin da Mubarak ya bata, Tasleem ta ce mata ita ma babu maganin agunta, kuma Mubarak yau be shigo makarantar ba, amma idan za ta iya, yau za'ai birthday ɗin Meena, a wani Hotel ta san babba ze je, taje se ta karɓa.
Farhan kam, ba taji za ta iya zuwa Hotel ba, dan ba ta taɓa zuwa ba, sedai da aka tashi daga Makaranta, tana dosar gidansu, ta fara jin fargaba, saboda ta san ta dawo kurkuku, yanzu za ta cigaba da jin baƙaƙen maganganun Umma, damuwa kuma za ta sake baibaye ta!
Gashi abun takaici, Ranar da ta fara fita, aka fara zunɗemta ana nuna ta da baki, akan abunda ya faru da ita.
Nan fa ta shiga tunanin meyakamata tayi ne, shan maganin nan kawai shine mafita ga damuwar ta.
Ta faki idon Umma tana banɗaki, ta ɗau hijjabin ta ta fice daga gidan.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
But Farhan ta fice daga gidan, se sauri take ta bar layinsu.
"Hajiya Farhan ina za ki ne kike sauri?"
Muryar da tafi tsana a rayuwarta taji ta daki dodon kunnenta, ta waiga ta kalli in da Sunusi ke tsaye yana ƙare mata kallo.
Ƙwafa tai kawai tai gaba, dan ko ganinsa ba ta son yi, balle tuna wani abu ya taɓa haɗa ta da shi.
Ta tari abun hawa, ta gaya masa in da ze kai ta.
Suna tafe ta zubawa sabuwar dubu ɗayan da ke hannunta ido, Sadik ne ya bata ita, a ƙalla akwai kuɗi sun kai 20k a hannunta, wanda Sadik ya kan bata, kuma ya fututtuke yace se ta karɓa.
A hankali ta ji hawaye masu ɗumi na bin idonta, har yanzu zuciyarta na begen Sadik, sedai ta dage da Addu'a Allah ya sa ta manta da shi a rayuwarta.
Har gaban Hotel ɗin me abun hawan ya kai Farhan, ta sakko ta ba shi kuɗin sa, nan ta shiga rarraba ido, dan sam ba ta san in da za ta dosa ba.
Tana nan tsaye jikin wata mota, tana waige waige "What are you looking for?" Taji wata murya ta daki dodon kunnenta, a hankali ta ɗaga idanunta ta ga me maganar.
Matashi ne a ƙalla ze shekaru talatin da takwas, ya kuma cewa "wa kike nema ne?"
Janye idonta tai da ga kansa, ta cigaba da jujjuya ƙwayar idonta, ko za ta hango su Tasleem.
Yace "Ikon Allah, shikenan tun da ba za'a kulani ba, nace zan iya ɗaukar mota ta?"
Yai maganar da sigar ladabi, ɗan kallon motar Farhan tai, Sannan ta ɗan yi jimmm, a hankali kuma ta janye jikinta daga jikin Motar, ta koma gefe.
Matashin yai murmushi yace "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, dan Allah ki min magana mana" yai maganar yana kallon Farhan da ga sama zuwa ƙasa.
Ba tare da ta san in da zata nufa ba, tai gaba abunta ta bar shi a gurin, babban burinta be wuce ta ga su Babba, ta karɓi maganin nan ta koma gida ba, in ya so se taiwa Umma ƙaryar siyan magani ta fita.
Wata zuƙeƙiyar mota ce ta shigo cikin hotel ɗin, Farhan ta ɗan tsaya motar ta wuce, amma taga Motar ta tsaya a Gabanta, sauke glass ɗin motar akai, ta hango Tasleem a ciki.
"Laa Farhan, da ma zaki zo? Ya na ganki a nan?"
Farhan tace "ban san in da ake taron bane, ban ga Mubarak ɗin ba"
Tasleem tace "bari in sakko mu shiga tare.
Farhan ta kalli mutumin da suke tare da Tasleem, har ga Allah Farhan ta ɗauka baban Tasleem ne, ta durƙusa tana gaishe shi.
Amsa mata yai yana murmushi, yana binta da kallo kamar maye, ya gyara parking ya kalli Tasleem yace "Wannan sweet sixteen ɗin fa? Ya za'ayi?"
Tasleem tace "Ai fa, ido a mata, to wannan dai ba ta san wannan harkar ba, kuma ta na da taurin kai, a hankali nake son na hilato ta"
Yace "Subhanallah, Tasleem dan Allah ina son a riƙe mata wuta, ko nawa kike buƙata zan ba ki, wallahi tayi min ɗari bi sa ɗari gata 'yar Yarinya amma ƙirarta ta min wallahi"
Tasleem tace "kaga, sallameni zan tafi kuma ka dawo ka ɗauke ni"
Yace "ko nawa kike so zan baki, amma ina buƙatar Yarinyar nan, ke daga Naira ɗaya zuwa millions, zan bayar in sameta, in ajiyeta mussaman in dinga hutawa"
Tasleem tace "ba ka da case, but for now, sallameni"
"Karki ji komai, zaki ga alert irin wanda ba'a taɓa miki ba"
Tace "kaji ka, kasan nawane a account ɗina kake cewa ba a taɓai min irin alert ɗin ba? Kawai dai ina jira" daga haka ta fito daga motar.
Farhan tai mamakin shigar da ke jikin Tasleem, wando ne jeans ya matse ta sosai kamar tai juyi ya tsage, ga wata matatsiyar riga a jikinta, attachment ɗin ta har ɗuwawu, kuma kanta ba ko ɗan kwali se uban glass baƙi ƙirin a Fuskarta.
Tace "Farhan muje ko" ba musu Farhan ta bi Tasleem, Kamar raƙumi da akala, se kallon Tasleem take sake yi.
Wani ƙaramin hall ne a wani ɓangare na Hotel ɗin, kallo ɗaya za kaiwa wanda suke gurin, kasan ba Mutanen kirki bane, gaba ɗaya Farhan ta sha jinin jikinta, take ta tuna lokacin da a kai na ta birthday ɗin, abunda ya gudana a gurin tsakanin ta da Sadik.
Take ta ji hawaye ya ƙwace mata, Babba ne ya hango su ya ƙaraso in da suke ya kalli Tasleem yace "ya kuma take kuka?"
Tasleem tace "Nima ban sani ba"
Yace "Common beb, whats wrong?" Yai Maganar yana ƙoƙarin janyota jikinsa.
Haɗe rai tai ta matsa tace "don't try it, ka bani zan tafi"
Yai murmushi yace "shikenan, zan baki, bari Nas ya ƙaraso suna hannunsa"
Suka bawa Farhan guri ta zauna, sam ta dena fargabar za'ai mata faɗa a gida, babban burinta be wuce ta ga maganin nan ya zo hannunta ba, dan tai imanin idan ba shi ta sha ba, shikenan sun ƙulla da damuwa kenan.
Tana nan zaune Tasleem ta kawo mata ruwa tace "Farhan ga ruwa, kan su kawo miki"
"Ni ba na sha, so nake a bani in tafi, kar a neme ni a gida"
Tasleem tace "ba komai, karki damu, yanzu za su kawo dan Allah ki sha ruwa mana"
Ba tai tunanin komai ba, ta karɓi ruwan nan ta sha sosai, ta ajiye sauran.
Ko mintuna goma ba'ai ba, Farhan ta ɓingire a gurin ta na bacci.
Sadik ji yake kamar an kunna wuta a cikin zuciyarsa, ya miƙe ya kai ya kawo a ɗakinsa, ya kaiwa iska naushi yana wani irin huci, ba tare da ya san meya haddasa masa hakan ba.
Ya zauna a gefen gado, ya dafe kansa yana jujjuya kai, yana son gano matsalar sa amma ya kasa.
Kawai ya fashe da kuka, hawaye wani na bin wani.
Nana ce tai sallama ɗakin na sa ta na faɗin "Aboki, dan Allah ka koyamin wannan Assignment ɗin, koyamin za kai, ba yi min za kai ba, sabo.......
Se kuma tai turus, ganin Sadik na kuka, a kiɗime ta ƙarasa in da yake, ta jefar da littafin hannunta ta zaune, tana janye hannunsa daga dafe kan da yai "Sadik meye ya faru? Me a kai maka?" Ta jero masa tambayoyin.
Maimakon ya amsa mata se ma cigaba da kukan da yai.
Itama ta fashe da kuka tana faɗin "Dan Allah Sadik menene? Ka gayamin"
"I don't know, something is killing me inside, and i dont know what is it, ina cikin damuwa amma ban san menene ke damuna ba, zuciya ta kamar za tai bindiga"
Matsawa tai kusa da shi tana share masa hawayen, tace "dan Allah to ka dena kuka, Allah ze yaye maka damuwar ka, ka dena kaji"
Tai maganar tana zubar da hawaye, maimakon ya dena se ya kwanta a jikinta, yana jin kamar zuciyarsa za ta kama da wuta.
Sumar kansa ta shiga shafawa, tana cewa "Allah Ubangiji ya yaye maka damuwar ka, Allah Munyi tawassalli da sunayenka Allah ka yayewa yayana damuwar sa, ka iya 40 rabbana?" Ta tambaye shi tana kallonsa.
Girgiza mata kai yai alamar a'a.
Tace "Inna ce ta koyamin su, ta sa na haddace su, tace in dinga yawan yi, idan aka ɓatamin rai na karanta ina jin daɗin su sosai, bari in karanta maka kaji"
Ya jinjina mata kai, jikinsa ya ɗau zafi , idanunsa sunyi wani irin ja kamar wuta, se jan numfashi yake.
Ta ɗora hannunta, akn ƙirjin Sadik saitin zuciyarsa, se da ta ɗan tsorata ko dai zuciyar Sadik ke ciwo, wani irin harbawa ta ji zuciyar ta sa nayi, da sauri sauri.
A hankali ta fara karanto Addu'oin rabbana rabbana da suke cikin Alqur'ani.
Hannayensa ya sa ya danna hannun Nana sosai a saitin zuciyarta sa yace "Nana ciwo take min, wani abu na barazana ga rayuwata da farincikina, ina jin kamar wani abu nawa me mahimmanci da yake neman rabuwa da ni"
Yai maganar yana kuka sosai kamar ɗan ƙaramin yaro, sosai ita ma Nana take kuka tace "duk abunda yake naka ne, in dai rabonka ne se ka same shi, insha Allah ba abunda ze same ka, yi shiru in karanto maka Addu'oin"
Yai shiru tare da rungume hannayenta sosai a ƙirjin na sa, har ba ya son ta motsa hannun na ta.
Nan ta shiga karanto masa Addu'oin, ya lumshe idanunsa ya na sauraren ta.
Wani irin releif ne ya shiga ratsa Sadik, a hankali ya fara jin sassauci daga tsananin bugun da zuciyar ta sa take yi.
Jin Nana tai Shiru ne ya sa yace "Nana"
Tace "Na'am, ya kake ji yanzu?"
"Alhamdilillah, Nagode sosai naji yana min sauƙi, ki sake karanta min"
"To Alhamdilillah, amma ka san wani abu?"
Yace "A'a"
"Na san za ka ji haushi, amma gara in gaya maka, Aboki Inna ta na gayamin, a duk lokacin da mutum yai nesa da Allah, abubuwan damuwa suna zuwa su dami rayuwarsa, amma idan mutum yana tare da Allah a ko yaushe, to abubuwa na zuwar masa da sauƙi.
Ka ga ba kullum kake salla a jam'i ba, kuma alhalin ba mu da nisa da masallaci sosai, kuma idan ka salla ko tasbihi ba ka yi, shafawa kawai kake ka tashi, balle Azkar ɗin safe da yamma.
Alqur'ani ko ba ka karanta ba, ka kunna a wayarka ka saurara, insha Allah zaka dinga samun mafita a cikin Al'amura.
Sannan wannan yawon kallon ball ɗin da kake ba yau ba gobe, da yawon darw duk ka dena su, ni Allah ya sa ma ba aljanu ne suka kama ka ba*.
Duk maganganun ta da take, idanunsa a rufe suke, se da tai maganar aljanu Sannan ya buɗe idonsa ya kalleta yace "ubanwa Aljanun suka kama??"
Tace "Ni bance sun kama ka ba, cewa nai Allah yasa ba su bane"
"Nafi ƙarfin aljanu su kamani"
Nana tace "da kana Azkar ne se kai wannan cika bakin"
"Dan kin ganni akan cinyar ki kike gayan magana ko?"
Tace "haba Aboki, ni na isa in gaya maka Magana, Allah ya baka haƙuri gaskiya nake gaya maka ne, zamu dinga karanta rabbana nan tare, har Allah yasa kaima ka haddace ka dinga karantawa"
"Naji, amma dai yanzu cigaba da karanta min"
Murmushi tai tana jinjina rigima irin ta Sadik, shi da ta samu a galabaice amma harya samu kansa ze fara masifa.
Tana cikin karanta masa karo na biyu, bacci yai awon gaba da shi.
A hankali ta zame kan Sadik daga cinyarta, ta sa masa pillow, ta tashi ta ja masa ƙofar ɗakin nasa, ta koma na ta, tana masa Addu'a Allah ya ba shi mafita akan abunda yake damunsa.
A hankali ta motsa, ta buɗe idanunta da suke mata wani irin yaji, ga kanta da take jin tamkar ba na ta ba, tun tana gani dishi dishi, har Idonta ya fara washewa, se dai ba ta gani clearly.
Kwance take a wani ɗaki, da ba ta san ina ne ba, ta tashi zaune akan gadon da take kwance, ta ƙarewa ɗakin kallo.
Hijjabin ta ta gani a gefe a yashe, ga kamta babu ɗan kwali, ta janyo hijjabin ta ta saka, ta yunƙura ta miƙe tsaye, sedai tsaiwar ta gagare ta saboda yadda take tangaɗi.
Ƙofar fita daga ɗakin ta nufa, ta buɗe ta fito, duk wata gaɓa ta jikinta ciwo take mata, tana tafe tana nema tai karo da bango, a haka ta fito harabar Hotel ɗin.
Safiya ce wajen ƙarfe Goma na tara, haka ta dinga tangaɗi, ta na ƙoƙarin fita daga cikin Hotel ɗin.
Wata mota ce ta dinga mata horn, amma ta rasa daga ina motar take mata horn ɗin.
"Ohh Allah yayi yau ma mun kuma haɗuwa"
Duk da maye take, amma ta gane shi, mutumin jiya ne, da yaita mata magana ta ƙi kula shi"
Yace "ina zaki ne?"
Ta ɗan yatsina fuska tace "gida zani" ta ƙarasa maganar tana dafe kanta.
"Ina ne gidan?" Ba musu ta kwatanta masa.
Yace "to muje in sauke ki, be kamata ki fita kina maye ba"
Ba musu ta bi shi Mota, ta shiga gaban mota, tun da ta shiga ta kifa kanta, yaita mata magana amma ba ta kulashi ba.
Tiryan tiryan da ya bi kwatancen nata, se ga su a ƙofar Gidan su Farhan, layinsu shiru babu kowa.
Ta fara ƙoƙarin buɗe motar ta sauka yace "gashi mun zo amma ba ki gayan ko sunan ki ba"
"Dan Allah ka ƙyaleni" tai maganar tare da buɗe motar ta fita, ta nufi gidan su.
Yace "Ikon Allah, wannan 'ya akwai mulki"
Da ta shiga gidan shiru, babu kowa ko sallama ba tai ba, ta wuce ɗakinta, ta zube akan katifarta ta cigaba da bacci.
Kusan mintuna ashirin, Farhan taji muryar ƙaninta Ameer yace "Laaa Umma kinga Yayan a ɗakinta tana bacci"
Umma a gigice tace "dagaske?" Tai maganar tana ƙoƙarin leƙa ɗakin Farhan, aikuwa ita ɗin ce.
Tace "kira babanku kace masa ga ta ta dawo"
Tun da suka farga ba ta gida, ake nemanta tun jiya, har gurin 'yan sanda aka shigar da report, ana ta cigiya ana nemanta, lokacin da ta dawo ma, Abba ya tafi gurin 'yan sanda, Umma kuma ta na bin gidajen 'yan uwa ko za'a sameta.
Ba a jima ba sega Abba yace "Ina Farhan ɗin take?"
Ya leƙa ɗakinta ya ganta a sharɓe tana bacci, take jikinsa yai sanyi yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah na san wannan jarabtace ka jarrabe ni, Allah ka shirya