Showing 180001 words to 183000 words out of 259198 words

Chapter 61 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

ba ƙaramin guri ba balle yace bari ya zaga ko ze ganta, idan ma zagawar ze ta ina ze fara.
Nan da nan ransa ya fara ɓaci, wannan wace irin kudahumar Yarinya ce da ba aiwa abun arziki, daga zuwa da ita guri ta kama Gabanta.
  Tun Sadik yana ɗaukar abun wasa, ya ga Dagaske ba ta gurin,ba ita ba alamunta, nan hankalinsa ya ƙara tashi, gashi babu waya a hannunta a balle yai mata waya yaji ina ta shiga.
Ga duhun magariba ya fara yi, ga London ba Nigeria bace, kowa sabgar gabansa yake, balle ya bi mutane ya fara tambayar su, to wa ma ze tambaya, kuma ma me ze ce?.

Ya kuma komawa im da take zaune da farko, amma be ganta ba, nan ya fara tunanin ko report ze kai, Gurin jami'an tsaro? Yarinyar nan idan ɓata ta yi me zance wa Abba?" Ya tambayi kansa yana cigaba da rarraba ido.

Abu kamar wasa har isha'i, Sadik yana neman Nana amma be ganta ba, ya yanke shawarar bari yaje gida, daga nan ya ga me ya dace yayi.

Haka ya kama hanyar tafiya gida, ya manta da batun ɗakko kayan da suka siya a shagon siyayya gaba ɗaya hankalinsa na kan, ina ze ga Nana.

Se da yana zuwa gida, ya tarar da ita a gida tana kwance abunta tana kallon cartoon, tana ciye ciye.

"Ke, dama gida kika taho, ki barni ina ta bulayin nemanki tun ɗazu?"

"Eh, gida na taho, na biyo wasu 'yan makarantar mu da na gani, suka kawo ni gida suka tafi,  na barka, kaji daɗin rungume mata son ranka, dan ni ba zan iya kallon zunubi ba, tun da kai in baka taɓa mata ba baka jin daɗin rayuwa" tai maganar cikin tsiwa da tsantsar kishi.

Wani irin marurun baƙin ciki ne ya turnuƙe Sadik, ji yake tamkar ya rufeta da duka, saboda ba ƙaramin tashi hankalinsa yai ba, yai zaton ɓata  yi.
Bece mata uffan ba ya wuce ɗakinsa ya barta, tun da ya shiga ɗakinsa be kuma fitowa ba, har gari ya waye.

Da sassafe Nana ta shiga ɗakinsa, dan tai dutyn ta da ta saba, ta tarar Sadik yana toilet yana wanka, ta fara gyara masa gafoy, tana cikin gyarawa ya fito.

"Me kike min a ɗaki?" Ya faɗa a kausashe.

"A'a, me kuwa nake yi, gyara maka mana kar in makara"

"Get out from my room" ya faɗa cikin tsawa.

Nana tace "to me nai maka?"

"I said get out" ya maimaita.

A razane ta juya ta fita, dan ya koma Sadik ɗin sa na ainihi.

Se kuma ta tuna abunda tai masa jiya, tai shiru tace "haushi yaji kenan? To amma ai gaskiya na faɗa ba ƙarya nai ba.

Sedai kuma a wani ɓangare na zuciyarta, sam ba ta ji daɗin yadda Sadik yai watsi da ita ba, dan a 'yan kwanakin nan tafi sakewa, da suke shiri da shi.

Haka nan ta tafi Makarantar sukuku.

Farhan maye sosai take a ɗakinta, dan bata san in da kanta yake ba, ba ta gane mafarki take ko zahiri ne abunda ke faruwa.
  An girke tukwanen biki, ana ƙoƙarin aza wutar tuwon 'yan ɗaurin Aure.

Malam Zakari ya tashi ɗan aike, yace ace a gayawa malam Labaran da magabatan Sunusi cewar, muddin be nuna musu in da ze Ajiye musu 'ya ba baza'a ɗaura Auren nan ba, kuma ya tabattar Ya zo da takaddar gwajin Asibiti, na lafiyarsa, idan ba haka ba ba za su ba su 'yar su ba.

Shi ko Sunusi na can garinsu, ana ta shiri daga can zasu ta ho gaba ɗaya gurin ɗaurin Aure.

Adda Hafsatu ta shiga ɗakin Farhan tana mita "wai wannan wace irin Amarya ce haka? Ana ta faman shiri amma kin ƙule a ɗaka ko wanka ba ki ba, balle a sa ran ki kintsa kafin dangin mijinki su zo, ba zaki ta shi ba ina miki Magana?"

Shiru Farhan ba ta amsa ba se ma sake juyi da tayi akan katifar ta.

Zuwa tai ta daki ƙafafuwan Farhan, "ke dan ƙaniyar ki magana nake miki fa, ba zaki ta shi ba"

Cikin maye Farhan ta fara magana "Wai..wai..... Meeee zan miki ne?kiiiiiii ƙyaleni ba na son in buɗe ido na...hmmmmmm... wai ba kya ganin gini ne ze faɗo a kaina?"

Buɗe baki Adda Hafsatu tai tace "Na shiga uku ni Hafsatu, Farhan me ya sameki haka? Me kike yi haka Farhan?"

"Ni,ni,niiii dalla ki rabu da ni, ba na son kowa ya zo gurina dan Allah"

Cikin azama Adda ta fita waje, ta janyo Umman Farhan gefe tace "kin san halin da 'yar ki kuwa take ciki?"

"Kamar yaya?"

"Wallahi gani nai kamar tana maye, amma zo muje ki gani"

A tare suka shiga ɗakin Farhan, suka tarar da ita kamar Mahaukaciya, duk ta ware gyaran gashin nan, gashin na ta ya hargitse gaba ɗaya.
Ta na zaune ya jingina jikinta a bango, ta lumshe idanunta.

Umma tace "Ke! Menene haka?"

Farhan tai shiru ba ta motsa ba.

Umma ta zo, ta kai hannu ta taɓa Farhan.

Farhan ta bige hannun Umma tace "Ni,niiiii..... Kar ki sake taɓa ni......tun da kin tsane ni.. ba na son ganinki, ki tafi ki bar nii"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ke me kika sha haka? Me zan gani, maue fa take Hafsatu"

"Nima abunda na gani kenan, da ma ta na shaye shaye ne?'"

Umma cikin tashin hankali tace "Ni ina na sani? Idan ma yin take saboda tsabar wulaƙanci ta rasa lokacin da za ta sha abun maye, se lokacin aurenta, mutsne sun cika gida, dan ta kunyata ni, tana mace za tai shaye shaye, wannan wace irin yarinya ce, da ma fa nema take ta lalace, Yaron nan ya sha kawo ƙarar ya ganta cikin mota ana kawota, mahaifinta ya ƙi yadda, ji wannan abun kunya ina zan sa kaina, mace da shaye shaye?" Umma tai maganar cikin rauni.

Adda Hafsatu tace "da ma abunda ake jiye muku kenan, shiyasa muka damu a aurar da ita, ka aura da 'yar tun tana ƙarama ba ta san komai ba, shine rufin Asiri da kwanciyar hankali, amma kuka ƙi, wai ku se tai boko, ga sakamakon bokon nan ai"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu meye abun yi?"

Farhan ta kalli Ummanta, idanunta jawur, cikin maye amma ta tsurawa Umma ido Sannan ta fara Magana "Meyasa......ki ka tsane ni? Meee nai miki...... Ni bana son Auren nan, ba na son ammma kika dage, ni ki tashi ki tafi, ko in kashe kaina, zuciyata zata buga......damuwa tai min yawa ku ƙyaleniii......" Farhan ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, tare da ƙwala ihu, tana mimmiƙewa. Har se da hankalin mutane ya so ya kai gurin.

Cikin azama Umma ta miƙe jikinta na tsuma, cike da tsoro da fargaba. Ita dai a iya saninta Farhan ko ytsa ka sa mata a baki, ba lallai ta iya taunawa, amma ita ce ke wannan ƙarajin take mata tsawa.

Adda Hafsatu tace "Maryamu, wannan ba maye bane, Farhana Aljanu ne da ita wallahi, kinga muje waje maza, a samo mukulli a rufeta a ɗaki, wallahi iskokai ne, zata iya mana duka a ɗakin nan, rufe ta a ɗakin a jira zuwa lokacin da iyayenta zasu dawo daga gurin ɗaurin Aure, a ji me za su ce"

Cikin damuwa Umma tace "abun ya bani mamaki, ni na kasa gane kan wannan lamari, kuma aljanun ne se Ranar ɗaurin Aure?"

"Kin ga ni ban hanya in wuce, ba ki ji suna cewa ba sa son Auren ba, shiyasa sam ba ya walwala tun da aka fara shirin bikin nan, ashe ba ita kaɗai ba ce, ni ban hanya kan ta haɗa min jikina a safiyar nan, dama ni ba ƙwari na cika ba"

Haka suka fito suka kulle Farhan a ɗakin, ita kuwa Farhan sam ba ta san a zahiri tai wa Ummanta tsawa ba, zaton ta a mafarki komai ke faruwa!

Mutaina ta shigowa suna tambayar ina Amarya, se ace musu ai bata da lafiya, da yake a can Babban masallacin juma'a da ke unguwar su Farhan za a ɗaura aure, duk danginsu maza, sun tafi can.



Sadik kam yau, ba da iya takaicin Abun da Nana tai masa ya tashi ba, har da wata irin damuwa, da tsananin fargaba da ya ta shi da ita, wadda be san dalilin hakan ba.
Wata irin faɗuwar gaba yake ta fama da ita, haɗi da Zullumi, yai iya ƙoƙarin sa dan ya gano, meke sa shi wannan fargabar da zullumin amma ya ka sa tuna Komai.

Yana jin Nana ta fita ta tafi makaranta, amma ya na ɗakinsa be fito ba, dan ko makaranta ma ƙin zuwa yai, yai kwanciyar sa a ɗaki, yana jin yadda zuciyar sa ke ta bugawa da ƙarfin gaske.
Tunani yai kowane abune yake faruwa a gida, ya miƙa hannu ya ɗakko wayarsa, ya kira layin Mother.

Se da ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga tace "Sadik lafiya kake kirana a wannan safiyar haka?"

Yace "kune a nan safiya, amma mu a nan ai rana ta yi, barka da safiya"

"Yawwa, kana lafiya?"

"Eh, lafiya ƙalau Alhamdilillah"

Mother tace "be lectures ne, ka kirani yanzu?"

"Banje makaranta ba yau"

"Saboda me?" Ta tambaya cike da kulawa.

Yace "bana jin daɗin jikina ne gaba ɗaya"

Mother tace "Yasalam, ina fatan dai ka je Asibiti, dan na san halinka, ba ka son magani"

Yai ajiyar zuciya yace "ai ba wani abun damuwa bane zan ware Insha Allah"

Mother tace "A'a, babban ciwo da ƙarami yake faraws, kaje ka ga likita yafi"

Yace "to shikenan, insha Allah zan je ina Abba?"

'"Abbanku yana gurin aiki, ba ya gari"

"Ok, hakane na manta ne, ina Dr. Da Matarsa?"

"Duk suna nan lafiya ƙalau Alhamdilillah"

"Ba bu dai wata matsala ko?"
Mother tace "kai Sadik, ba wata matsala fa"

Yace "to shikenan, amma naji kimce Abba ya koma aiki, ya jikin Hakimin, za'a kai shi jamus ɗin kuwa?"

Mother tace "eh to, ka san halinsa, ya ɗan samu sauƙi gaskiya, yace ba in da za shi, yaje a sake wahala da shi, a barshi ya mutu a ƙasarsa a binne shi cikin salama, ba se an kai shi ya mutu a can, a wahalar da gawarsa ba"

Sadik yace "Allah sarki, cuta ai ba mutuwa bace, Allah ya ƙara sauƙi"

Ta amsa masa da Ameen, da ga nan suka ɗan taɓa hira, sannan su kai sallama.

Still dai ya ji be samu nutsuwa ba, se da ya kira Abba a waya, nan ma ya dinga tambayar Abba Komai lafiya? Abba ya tabattar masa da komai lafiya, sedai su cigaba da yiwa Hakimi Addu'ar samun lafiya a gurin Allah.

Haka Sadik ya dinga bi yana kiran waya, yana jin lafiyar 'yan uwansa, da kowa da kowa, amma be ji ance masa ga wata matsala, haka ya haƙura ya ajiye Wayar, ya cigaba da zancen zuci shikaɗai.





Tun kan mutane su gama taruwa a wajen ɗaurin Aure, Malam Zakari ya hallara, yana jiran zuwan Magabatan Sunusi, dan ya fuskanci alamu sun nuna kamar ba su da dattako ko kaɗan.
Da suka iso gari ma, ba su wuce ko ina ba, se gurin ɗaurin Aure matan ne suka tafi gidan malam Labaran, aka sauke su a can, mazan kuma suka hallara a masallaci.
Sanin sanyin hali irin na Abban Farhan, ya sa Malam Zakari tsayawa bil haƙƙi, dan ganin ba a ƙwari Farhan ba.
Bayan an gama gaisawa, ana jira mutane su ƙarasa zuwa, lokaci ya cika afara ɗaurin Aure, a gaban Liman Malam Zakari ya kalli Sunusi da ahalinsa yace "Bayin Allah, ina alƙawarin da mu kai da ku?"

Wani kawun Sunusi yace "Wane alƙawarin kuma?"

"Eh, ai shi malamin da yaron sun sani, na farko ba ku gaya mana in da za'a ajiye mana Yarinya ba, sannan abu na gaba kamar yadda na gaya muku, mu a nan ba a ɗaura Aure, se an kawo sakamakon gwaji Sannan ake ɗaura Aure".

Ƙanin baban Sunusi yace "Ikon Allah, to ai batun in ds Yarinya zata zauna, anyi wannan maganar in da za ta zauna, ai can garin su yaron ne wato Sunusi, sannan ni ban san wani batun gwajin Asibiti ba, tun da mu a ƙauye ba a yi, amma kai Sunusi ya abun yake ne?"

Malam Zakari yace "eh ai shi ya san yadda mu kai da shi, be muku bayani ba dama?"

Sunusi yace "Nifa gaskiya ba ni da halin da zan wani kama mata gida a garin nan, dama a garin mu za ta zauna, nikuma ina nan ina ɗan buge buge na ina aikata mata, amma ai an san bani da ƙarfi, tunda ba kaina zan siyar in kama nata gida ba"

A nan 'yan uwan Farhan suka fara jinjina Wannan lamari, sam Sunusi ba shi da ɗa'a, se wani Magana yake cikin gadara ba wani girmamawa.
Shi kansa Abban Farhan, be taɓa zaton haka Sunusi yake ba.

Liman ya kalli Sunusi da magabantasa yace "bayin Allah, ai ko a karkara ilimi ya wadata, ana gwaji kan Aure, dan haka mu a nan ba ma ɗaura Aure se an kawo mana sakamakon gwaji, idan ba bu kuma zakuje se an kawo sannan zan ɗaura Aure"

Malam Zakari yace "kuma, ba zamu bada 'yar mu a kai mana karkara ba, muna nan akan bakanmu, aka ma wa yarinya gida a birni, saboda karatun ta"

Liman yace "Malam Zakari, ai batun zama a ƙauye ko a birni, ba shi a cikin sharaɗin Aure".

Malam Zakari yace "duk da haka Allah gafarta malam, mu bamu gamsu da in da za'a kai mana Yarinya a ajiye ba, kuma shi angon ya san akan wannan sharaɗin muke"

Mutane sun gama taruwa, dan har sun fara ƙosawa, a ɗaura aure abu ya gagara, ga rana ta ɗaga Sosai.

Liman yace "to ku, kunji abunda iyayen wannan amarya suka ce me zaku ce, Sannan ya batun gwajin? A ɗaga ɗaurin Auren kuje ku yo gwajin ku dawo ne, ko zuwa in Allah ya kaimu la'asar se a ɗaura?"

Malam Labaran yace "to, ni Allah gafarta malam, wai me ye amfanin gwajin nan ne? Me za'a gani a gwajin?"

Liman yace "Yawwa, abunda ya kamata dama ku tambaya a wayar muku da kai kenan, idan ba ku sani ba.
Shi wannan gwajin yana da mahimmanci ƙwarai da gaske, duba da yanayin cututtukan ƙarshen Zamanin nan da su kai yawa, akwai nau'in cututtukan da idan ɗaya daga cikin ma'aurata yana da shi ɗaya ba shi da shi, to ɗaya ze shafawa ɗaya.
Ko kuma, akwai kuma wanda idan suna ɗauke da wani nau'in jini, ba ze yuwu suyi Aure ba, saboda za su iya samun yara marasa lafiya, masu ɗauke da ciwon sickler wato Amosanin jini.
Idan aka kawo mana gwajin muna Duba, rukunin jinin ze yuwu ma'auratan suyi Aure, ba tare da sun haifi yaro me larurar sickler ba.
Muna duba ciwon hanta, tun da shima likitoci ance ciwo ne da ake ɗauka, amma shi ba a fiye damuwa da duba shi ba kamar yadda muke duba ciwon ƙanjamau, wannan shine mafi hatsari ma, tun da shi ciwon hanta ana warkewa, ƙanjamau kuwa ba a warkewa, ka ga kuwa gwaje gwajen duk suna da mahimmanci, dan tabattar da babu wanda aka cuta a lamarin".

Sunusi yace "ni lafiyata ƙalau, babu wani gwajin da zan yi, kawai an shigo da yahudanci cikin lamarin Aure, duk dan salon barin abunda addini ya ɗora mu a kai, ai idan ma cuta ce sedai a samu a jikinta ba ni ba, dama ai jihadi zan in Aureta, babu wanda be san yawo take ba.
Maza ne ka ɗaukarta suna yawo da ita a mota, saboda shegen son abun duniya. Ranar a gabana suka shiga gida ita da wani, sunfi mintuna arba'in sannan suka fito, kuma a gaban mutane suka fito, dan se da na kira shedu suka gani, ita ba a samu ciwon a jikinta ba se ni za a samu a jikina, na ga ai temaka mata zanyi, da an san ba za a bani yarinyar nan ba se an gama wulaƙanta ni, meyasa aka ce za a bani, ko da ma can ƙaƙaba min za ai an san ba ta da lafiya, ta gama yawon banzanta, shine za a zo ana min burga, kamar tainaka min za ai"
Da ƙarfi Sunusi yake magana ba a hankali ba a hankali ba, hakan ya janyo hankalin mutane da suke gurin,  kai tsit ana sauraren sa, Abba yai shiru ya rasa abunda yake masa daɗi.

Malam Zakari yace "sadaƙallahul azeem, dama in da muke jira a zo kenan, mu ga gwajin 'yar mu a hannun mu, ba ta da ciwon Komai, lafiyarta ƙalau, kai kuma kaje sharrin da kaiwa 'yar mu mun barka da Allah, duk unguwar nan ba wanda be san tarbiyyar da yaranmu ke da ita ba, wanda har ake son haɗa zuriya da mu"

Malam Labaran yace "A'a Malam Zakari, ai ba a shedar ɗan yau, ta idonka daban, ta bayan idonka daban, amma duk da haka, nasan Sunusi be kyauta ba, haka yake da zafin zuciya idan ransa ya ɓaci, amma mutumin kirki ne, ina nan ina masa rubutun samun sanyin zuciya.
Ayi haƙuri dan Allah, yanzu dai zamu je ayo gwajin a kawo, se a ɗaura Auren"

Sunusi yace "gaskiya ni Malam, ba in da za ni, ba wani gwaji da zan, in sunga za su bani a haka su bani"

"Wai Sunus ba ka da hankali ne? Ya ana ƙoƙarin saita lamura, kai kuma ka na sake ɓata lamarin"

Malam Zakari yace "ba zamu bawa mara mutunci, wanda be san darajar kansa 'ya ba, Allah ya ha ɗa kowa da rabonsa"

Abba yace "A'a, ɗan uwa babu yadda za'ai a gyara lamarin nan? Ka ga fa mun tara jama'a"

"Dan dai jama'a, bakoma sa watse Allah ya haɗa kowa da rabonsa, dama yarinyar ba wani girma ne da ita ba, a kunnen ka ya gama ci mana mutunci, da aibata mana 'ya yaiwa kansa, tun da be san abun arziki ba"

Sunusi ya sake tinzira, ya dinga bala'i yana cigaba da aibata Farhan, a gaban al'ummar da suka zo dan halartar ɗaurin Auren.



Umma ta na cikin matuƙar zullumin halin da Farhan ke ciki, gashi tun sha ɗaya aka  ce za'a ɗaura Aure, amma har ɗaya saura shiru ba su dawo ba, ga mutane sun cika gida, babu Amarya babu dalilin ta ta na can ta na fama, ba ta san in da knata yake ba, gashi angwaye shiru suma babu su ba bu dalilin su.

Huzaifa ne yai sallama ya shigo, cikin faran shadda, Babbar rigarsa riƙe a hannunsa.

Umma na ganinsa tace "Huzaifa yaya, ina su baban naku an ɗaur ne?"

Hauzaifa yai dariya yace "aka ɗaura me? Ai an fasa Aure"

Tace "kamar yaya, kai bana son shashanci fa"

Yace "wallahi dagaske

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login