Showing 198001 words to 201000 words out of 259198 words

Chapter 67 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

kar wanda ya ƙara burgeki in bani ba, kin ji ko?"

Tace "to naji"

"Good girl" yai maganar yana murmushi.









Tsaye yake a bakin gate ɗin gidan, yana ƙarewa layin kallo, yana tuna Yaushe rabonsa da layin, komai yana nan yadda yake, a guje yaga an fafaro wata farar mota vibe, wata uwar ƙura ta tashi a layin, mamaki ne ya kama shi, yabi motar da kallo yana tunanin waye wannan yake gudu irin haka, a wannan ɗan ƙaramin layin?.

Mamkine ya kama shi ganin wadda ta fito daga motar, se dai yana tantama anya wadda yake tunanin ce?.

Sunusi ne ya sha gaban Farhan, ta fito daga cikin mota, sanye da riga da skirt mayafinta a hannu, da jakarta.

"Yanzu Farhan wai ba kya jin kunyar yawon da kike a gari haka?  Haba Farhan kiyi haƙuri ki zo mu sasanta in rufa miki Asiri, muyi Aurenmu ni haryanzu ina sonki wallafa"

"Lallai, ya tabatta ka haukace Sosai da sosai, kalleni ka sake kallona, ko a lokacin da aka amsa za'a baka Aurena kai ka san ni ba sa'ar Aurnka ba ce, yau Da ace kai mutumin kirki ne zan iya haƙuri in Aureka, amma mutumin banza irinka, mutum na farko da ya fara haɗani da iyayena, da in Aureka gara in ƙare rayuwata a titi ba Aure"

"Ke har ni zaki gayawa Magana, kina karuwa wulaƙantacciya, dama niyyar caka min ke a kai, Allah ya rufan Asiri"

"To tun da Allah ya rufa maka Asiri ba a caka makan ba, wani munafuncin ne ya sa ka zo kake cewa in Aureka?" Ta daki jikin motar da ƙarfi sannan ta nuna Sunusi tace "wallahi idan ba ka fita daga sabgata ba, sena sa an casa min kai wallahi, sakarai ƙazami kawai" galala Sunusi ya bi Farhan da kallo tare da mamakin maganganun ta.

Cikin Azama Abbas ya shiga cikin gidan Hajiya, yana ƙwala mata kira.

Hajiya tace "Subhanallahi, wane irin kira ne haka Abbas? Daga dawowar ka ka zo mu gaisa, seka dinga min wannan kiran?"

Ajiyar zuciya Abbas yai yace "yi haƙuri Hajiya, wallahi wani abu ne ya ɗan rikita ni, barka da gida"

"Yawwa barka, shigo"

Abbas ya shiga falon Hajiya, ya tarar da manya manyan kuloli da ta shirya masa Abinci, kwanansa biyu da dawowa, yau ya shigo gurin Hajiya.

Suka zauna su ka gaisa, tana masa ya hanya ya karatu?.

Ya nisa yace "Hajiya, wata na gani kamar Farhan, amma ina tantama, a mota na ganta da shigar da ban taɓa ganinta ba ba hijjabi a jikinta"

Hajiya tace "kai dai bari Abbas, zancen ne ba daɗi"

"Hajiya, ba daɗi kamar yaya? Meke faruwa ne?"

Hajiya tace"zancen babu daɗi Abbas, abunda a kaita gufunyne dai, yanzu Farhan ta canza daga yadda ka santa, ba a samu ɗaura Aurenta da wannan yaron ba, kamar dai yadda kai ta gargaɗi da gudun karta shiga wani hali, amma dai Allah be ba abun da ake gudun ya faru"

Abbas yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Hajiya meyasa baki gayamin ba, amma tukuna wai ma meya faru da ita ne?"

"Yawon banza Abbas, ga kuma shaye shaye, dan tun a ranar ɗaurin Aurenta tayi mankas, ba ta san me take ba"

Hannu bibbiyu Abbas ya saka ya dafe kansa, yana sauke numfashi.

Ya ɗago yace "Hajiya, iyayen Yarinyar nan ba su yiwa kansu adalci ba, Allah ya basu nutsatsiyya yarinya, amma sakaci ya sa sun bar rayuwarta ta gurɓace"

"To kowa da irinsa ne, aikin gama ya riga ya gama sedai a tayata da Addu'a, Allah ya shirya"

Abbas kasa cewa komai yai, ya shiga cikin damuwa sosai, gaba ɗaya hirar ma sama sama su kai da Hajiya, Abincin ma kaɗan yaci, yaiwa Hajiya Sallama yace tafiya zeyi.

Haryai niyyar hawa motarsa ya tafi, amma ya hangi motar Da ya hangi Farhan ta zo da ita ɗazu.

Ƙofar gidan su Farhan ɗin ya nufa, yana nan tsaye yana kallon Motar, sega wani Almajiri ze wuce, yace ya shiga gidan yace ana sallama da Farhan.

Tace Ba za ta zo ba, shine amsar da yaron ya bawa Abbas, yace inji Farhan.

Guri ya nema ya zauna akan wata baranda, yana ta juya tare da mamakin yadda Farhan wai ta koma yawon banza.

Yana nan zaune sega Farhan ta fito cikin wata haɗaɗiyar purple ɗin abaya, ta sha duwatsu Fuskarta tai fresh, tare da bayyanar da tsantsar yarintar ta.

"Assalamu alaikum" shine abunda kunnuwan Farhan suka jiyo, fasa buɗe motar tai, ta waiwayo ga mamakinta se ta ga Abbas a tsaye.

Faɗaɗa murmushin ta tai tace "Saukar Yaushe ba labari?"

Murmushin ƙarfin hali yai yace "kinyi mamakin ganina ko? Tun shekaranjiya na sauka amma se yau na shigo unguwar ta ku"

"Masha Allah, ka kammala course ɗin kenan?"

"Eh na kammala Alhamdilillah, dan se da na ƙara watanni ma na huta sosai"

"To Allah ya Sanya albarka a abunda ka karanta, yasa al'umma su amfana"

Abbas yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nace in ba damuwa ko in zo in rakaki in da zaki?"

Ta girgiza kai tace "a'a Nagode"

"Meyasa ba kya son rakiyar tawa?"

"Haka kawai" ta bashi amsa.

"Ban taɓa tunanin zan dawo in ganki a wannan yanayin ba Farhan, why? Garin yaya haka ta faru?"

Farhan ji tai kamar ya soso mata in da yake mata ƙaiƙayi se hawaye.

Ya ɗan matsa gabanta yace "Farhan why? Kalli yadda kika maida rayuwar ki, kina ɗaya daga cikin wanda ake kwatancen nagartattun yara ne masu tarbiyya a unguwar nan, meyasa kika zaɓi canza akalar waccan rayuwar zuwa wannan me munin?"

Ba ta ce masa uffan ba, tana kuka ta buɗe motar, ta shiga ta tafi. Abbas ya daɗe a tsaye yana jinjina lamarin, Farhan Just needs guidance and counseling to save her, and he promised to do so for her, saboda yana matuƙar jin tausayin ta.







"Sadik dan Allah kai min magana, a tsorace nake amma na gaya maka abunda ke damuna ka ƙi kulani"

Sadik yace "to me zance miki?"

"Kalleni fa, kalli yadda na koma, na zama wata ƙatuwa, wallahi wani abu ne yake min yawo a ciki na, kuma kalli cikin ƙara girma yake dan Allah ka mai da ni Asibiti" tai maganar cikin kuka.

'malama karki ɗaga min hankali, Abincin da kike ci ne yai yawa, shiyasa cikin yake girma"

"Ni yaushe nake cin abinci balle cikina yai girma, shikenan wata Cutar ce ta kamani, dan Allah ka maida ni Asibiti"

"Ke, ciki ne ba wani abu ba" ya bata amsa kai tsaye.

Saroro tai tana kallon Sadik, se taji kamar ba ta ji daidai ba, tace "me kace?"

"You Are pregnant, abunda likitoci suka gayamin kenan wancan lokacin da muka je Asibiti, You Are four months pregnant"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Ciki ne dani? Na shiga uku na lalace"

"Ke meye haka? Wace irin magana ce haka kin shiga uku kin lalace"

"Ban sani ba, shikenan ka gama da rayuwa ta, ya zanyi da ciki Sadik? Kawai se in koma gida a ganni da ciki na shiga uku, wallahi se an zubar da shi lalacewar tai min yawa"


Wani Mugun kallo Sadik yaiwa Nana yace "mutuwa zaki a banza, ƙarafa za su sa miki a jiki, in aka zubar da cikin ki mutu a banza, wani Auren zanyi ni ba ruwana"

Nana ta sake ɓare baki tana hawaye, har da majina tace "shikenan ka gama da Rayuwata, 'yar yarinyata da ni ace ina da ciki, shikenan na dena zuwa Makaranta, Inna kasheni za tai ta koreni daga ƙauye, ina zan sa kaina? Wallahi seka sakeni, ba zan cigaba da zama ba kana cuta ta"

Sadik ya shafi sumarsa yace "Aikin gama ya gama Yarinya, ko na sakeki kin zama bazawara ba zaki taɓa komawa yadda kike ba, kuma ma abun tausayin da kike bani, 'ya'ya biyar ne a cikin na ki, Allah sarki shikenan zaki zama Mama, ga 'ya'ya na binki ba karatu ba gayu, inje a kuma Auramin wata gallaliyar Yarinyar.
Kuma wallahi ki kai wani ganganci akan cikin nan sena ɓata miki rai"

"Na shiga uku ni Asma'u, wallahi ka gama dani, Allah seya saka min wallahi, kuma nasan mutuwa zan yi, ta ina 'ya'ya biyar za su zauna a cikina, shikenan ratuwata ta zo ƙarshe"

Sadik ya rungumota jikinsa yace "Allah sarki, nima kin bani tausayi wallahi, ɗan yaron mijinki ya jefaki a wani hali sorry baby" yai maganar yana mata dariyar mugunta.
Yayin da gefe guda kuma zuciyarsa cike take da zullumin yadda ze fuskanci wannan ƙalubalen da ke gabansa, na bayyanar ciki a jikin Nana.
COOL CE
Contact me at 07063065680 to subscribe, at affordable price or visit Arewabooks to purchase.





Kafin Lilly da mamanta su ƙaraso tuni major yai umarni aka ja motar, aka barsu a nan, ƙarshe se daidaita sahu suka hau zuwa gida.

Suna tafe Lilly na kuka, a fusace Mummy tace "ki rufen baki ko in jefaki kan kwalta dan uwarki, kalli halin da kika jefamu a ciki, ƙanƙanuwarki da ke wai kin san ki bi namiji har yai miki ciki ki zubar, turr da halinki" haka Mummy tai ta mata masifa har sukaje gida.

Suna zuwa gida suka shiga falo, suka tarar da Major yana muzurai, a fusace yace "ban ce karki dawo min da Yarinyar nan gida ba? Tun wuri ki san in da zaki kaita ta barmin gida"

"Wasa ma kenan, ai kaima kasan wannan Magana faɗa kawai kake, ina ka ke so in kaita?"

"Duk in da ki ka ga ya dace, tun da a garin sokoncin ki da hauka, kika bari harta ke yawo baki sani ba, kina uwa 'yar ki na bin maza amma kika gaza ganewa"

A ƙufule Mummy tace "haramun ne kai a matsayinka na ubanta idan ka gano hakan? Ina ni da ita duk a ƙarƙashin ka muke, alhakin kula da mu a wuyan ka yake, ko kuma ni kaɗai Allah ya ɗorawa Alhakin kula tarbiyyar yaran?, su sauran da nai tarbiyyar su har su kai Aure, ka taɓa zaunar da ni kace ka gode naiwa yaranka tarbiyya ba su lalace ba, se yanzu dan wannan ta lalace zakace inje in san yadda zan da ita, 'yar ka ce kaima zaka iya ɗaukarta ka kaita duk in da ka ga dama"

"Ni kike gayawa haka?"

"Na gaya maka ɗin, akan me zaka ɗaga min hankali? Bari in tuna maka wani abu da kake ƙoƙarin mantawa, barewa ba ta gudu ɗanta yai rarrafe, a yawace yawacen aikinka kai meye ba kai ba, ko ka ɗauka ka ci bulus ne? Better get back to your sense, ka ɗau mataki a cikin hankalinka, kar ka yanke hukunci cikin fushi abunda ba kai zato ba ya biyo baya"

Sororo Major yai yana kallon Mummy, tai wucewarta ɗaki ta bar su a tsaye shi da Lilly.

Wata uwar ƙwafa yayi, sannan shima ya bara falon, Lilly ta durƙushe a gurin tana kuka, tabbas koma meyafaru ita ta janyo shi, ta ɗora laifin kacokan akanta, take taji nadamar abubuwan da ta aikata suka baibaye ta, shikenan yanzu ba ta da sauran wata kima da mutunci, ta zubar da su a dalilin banza da na wofi, yanzu Allah ne kaɗai yasan matakin da mahaifinta ze ɗauka a kanta.




Abbas mussaman yaje har gida yai sallama da baban Farhan, Abba baze manta da Abbas ba, duba da irin taimakon da yai lokacin rashin lafiya Farhan.
Abba cikin fara'a ya saki fuska suka gaisa da Abbas, yake ce masa "Nikam yaushe rabon da in ganka, harna manta"

Abbas yai murmushi yace "da yake watana kusan goma bana gari, naje ƙaro karatu ne"

Abba yace "Allah sarki, Allah ya yi jagora ya dafa"

Ya amsa da Ameen Sannan ya ɗora da cewa "dama Abba na zo muyi magana ne akan lamarin Farhan"

Jiki a sanyaye Abba yace "wani abun tai maka ne?"

"A'a ko ɗaya, se dai in baka manta ba tun bayan rashin lafiyar ta, na baku shawarar sa ido akanta da kula da ita, sedai bayan dawowata banji daɗin yadda na tarar da ita ba, tun kan in tafi na lura akwai damuwa me yawa a tare da ita, tana cikin yanayi na son wani, ku kuma kuna yunƙurin aura mata wani, kuma ba zata iya yi muku musu ba.
To a yanzu ma nai interview da ita, na gano meye damuwar ta, sedai ina son ku bani haɗin kai gurin ceto rayuwar ta"

Abba yace "tayaya kenan?"

Abbas yace "Masha Allah, dan Allah Abba duk da halin da take ciki a yanzu, na san baya muku daɗi, amma dan Allah banda tsangwama, kar a tsangwameta, ayi haƙuri a ja ta a jiki, yana daga cikin abunda ta rasa harta faɗa soyayya me zurfin gaske, rashin ja a jiki, da ba ta samu a gida ba shine taje ta samu a waje, wanda ya jefa ta cikin soyaya RUƊIN ƘURUCIYA"

Abba ya nunfasa yace "hakane, dama ni ban tsangwameta ba, ina mata Addu'a ne Allah ya shirya ta, dama matsalar daga mahaifiyarta ne, kuma ita ma tayi nadama yanzu"

Abbas yace "Masha Allah, sannaan abu na gaba shine, Abba nace idan ba damuwa ina Neman wata alfarma guda ɗaya a gurinka"

Abba yace "wace alfarmar ce haka?"

"Ina son ka bani Auren Farhan"

Abba ya kalli Abbas yace "Malam Abbas ka san me kake faɗa kuwa? Ba ka ga yadda ta koma bane, ba Farhan ɗin da ka sani a baya bace ba fa"

"Eh Abba na sani, ina son in temakawa rayuwarta ne, dan Allah ka duba lamarin"

Abba yai shiru Sannan yace "komai nufi ne ne Allah, bana son sake maimaita kuskuren da nai a baya, amma ka nemi yardarta in dai daga gareka ba wata matsala kuma ta amince shikenan"

Abbas yai murmushi yace "nagode Sosai Abba"

Abba yace "bakomai, ka gaida gida"

Su kai sallama da Abba, sannan ya nufi gidan Hajiya, se a lokacin wata fargaba ta zo masa, dan be san ya abun ze kasance ba, Hajiya za tai murna da hakan ko kuma zata ce ba ta yadda ba.

Abba ya je wa da Umman Farhan abunda suka tattauna da Abbas Umma tace "Anya kana ganin wannan lamarin ze yuwu, Yarinyar nan ta riga ta ɓata rawarta da tsalle, ba na jin mahaifiyarsa ma za ta yadda"

Abba yace "to, ni dai ba ni da ta cewa, na bar komai a hannun Allah, Allah ya iya mana"

Umma tace "Ameen".

Ranar gardaution ɗin su Tasleem, ana party a makaranta, ana ta kaiwa ana komowa, yara cikin shiga kala kala, ta arziki da ta banza, se cahsewa ake, ana ciye ciye da shaye shaye, labari ya karaɗa makaranta an kama sir Nazir, amma babu wanda ya san dalilin kamun nasa.
Ba zato babu tsammani 'yan sanda sukai dirar mikiya a makarantar, aka kama Director makarantar, da principal, aka kama 'yan ajinsu Lilly, a nan 'yan Sanda su kai katarin kama su Nas da ƙwayoyi a jkinsu ranar graduation ɗin, dan haka aka tattarasu duk zuwa police station.
Aka kori kowa gida, aka garƙame makarantar.

A station director se masifa yake, wai anci zarafinsa ana neman a ɓata masa sunan makaranta, an kama shi da ɗalibansa anci zarafinsa.

Aka shiga da shi wani Office, da sauran malamai aka zo da Lilly da malam Nazir, aka warware abunda yake faruwa a tsakanin su, ga kuma su Nas da aka kama da ƙwayoyi a wannan shekarun nasu.

Nan aka shiga kiran iyayen yara suka cika police station, yadda aka faɗi da yadda Lilly ta lalace, ya bawa iyaye da yawa tsoro da Mamaki.
Su kansu su Haseena da Yasmin akace ba'a yadda da su ba, se anje anyi musu screening tun da tare suke karance karancen, a nan allura ta dinga tono garma, dan a ɗaliban har da masu Implant a jikinsu, banda wanda aka samu da ciki, banda masu ɗabi'ar neman jinsin su (Subhanallah).

Baban Lilly yace "baze bar wannan rashin Albarka ba, se an bi masa haƙƙin 'yar sa.

Labari ya karaɗa gari, akan irin ta'asar da aka bankaɗo a wannan makarantar, wadda tai ƙauran suna akan makaranta ce ta yaran masu hannu da shuni.





Abbas ne a gaban Farhan, ya zuba mata idanunsa, ita kuwa ta ɗauke kai gefe se tura baki take.
Fitilar wayarsa ya sa ya haskata, ta sa hannu ta rufe fuskar ta ta saboda hasken fitilar.
"Farhan" ya kira sunanta. Ƙin kallonsa tai gaba ɗaya.
"Farhan, meyasa ba kya so na?"
"Ni na ce maka ba zan yi Aure ba"
"Meyasa? Kin fi so ki cigaba da rayuwa a haka?"
Farhan tace "meyasa zaka auri ragowar wasu, ba ka cancanci Auren yarinya iri na ba"
Abbas ya nisa yace "ke kika cemin ba kya zina ai, kuma ma ni ba wannan nake dubawa ba, makomar rayuwar ki nake dubawa"
"Kai in ba abunda nake kenan ba, a ina kake tunanin nake samun maƙudan kuɗaɗe? A banza maza za su dinga bani kuɗi ne ba wani dalili, ai maza ba kwa abu dan Allah se da dalili"
Abbas yai murmushi yace "kar ki mana kuɗin goro mana, ke dai kawai ki ce min har yanzu Sadik kike so"
Take ta haɗe rai ta kalleshi tace "bana buƙatar ko sake jin sunan sa a ratuwata, dan Allah kar ka kuma sako min zancensa"
"To in ba Sadik kike so har yanzu ba, meyasa ba kya so na? Na miki tsufa ko?"
Murmushi tai tace "kai nagartaccen mutum ne, me tausayi da sanin yakamata, ni kuma 'yar shaye shaye ce kuma.....

"Shhhhhh, ki dena wannan maganar dan Allah, keep it aside, ina sonki Farhan dan Allah ki bani dama na Aureki"
Noƙe kafaɗa tai irin na yara tana sake tura bakinta gaba.
"Ikon Allah, is all this for me? Ni in ki na hakan nan burgeni kike"
Take jikinta yai sanyi, haka Sadik ma yake mata, yai ta cewa tana shagwaɓa, wadda ba ta san ta na yi ba.

"To munafukin Allah ta'ala, ka zo duhu zaka cigaba da lalube min mata, wanda kai a baya be isheka ba, to wallahi babu me mallakarta tunda ban mallaketa ba" Sunusi ne tsaye akan su Farhan yana Wannan banbamin.

Wani irin ɓacin rai ne ya baibaye Farhan, ta rasa yadda za tai tai maganin wannan katsalan dan da yake mata a cikin rayuwarta, ya hanata sakat duk wani motsinta akan idonsa, kuma se ya san yadda yai ya ci mutuncin ta.

Abbas yace "dan Allah, kai kuwa me mu kai maka haka? Allah be yi ka Aureta ba, kuma seka dinga masifa wani baze Aureta ba?"

Sunusi yace "ai wallahi yadda ban Aureta ba babu me Aurenta, in kaga wani ya Aureta se dai in bana raye, sedai ta ƙare rayuwarta a karuwanci amma ba dai tai Aure ba"

"To Sunusi dan ban Aure ba se me, da dai in Auri sakarai irinka gara ban Auren ba, ka cigaba da min shishshsigi a cikin lamurana, zan sa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login