Showing 213001 words to 216000 words out of 259198 words
Chapter 72 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
in da take kaji, akwai wani abu me mahimmanci da zan karɓa a gurinta"
Amir yace "gaskiya na gaya maka, ba ta kwana a gida ba"
"To a ina ta kwana?"
"Ban sani ba, bari in sauri in tafi zan makara"
Sadik ya sauke wata irin ajiyar zuciya, yana mamakin amsar da Amir ɗin ya ba shi, a yanayin da shi kansa ba ze iya tantancewa ba, ya bar ƙofar gidan ya nufi in da motarsa take, ya hau ya kunna ya fizgeta a guje, ya nufi titii, hakan yai daidai da kunnowar motar Abbas, saura ƙirisa suyi taho mu gama, saboda irin yadda Sadik yake tuƙin a haukace.
Abbas ya waiga yace "ji wani mara hankali kuma, ga abunda yai amma ko a jikinsa" ya ƙarasa maganar tare da jan tsaki ya cigaba da tafiya.
Yai parking a ƙofar Gidan su Farhan, ya kirata a waya, dan ta fito ya kaita Makaranta, sedai abun haushin tana ɗagawa muryarta kawai zaka gane mankas take, dan se surutai take, kuma galibi a surutun na ta Sadik take ambata.
Jiki a sanyaye Abbas ya kashe wayar, tare da mamakin wannan wane irin so takewa Sadik, Babu damar zuwa makaranta, kasancewar a buge take, haka nan jiki babu ƙwari ya ja motarsa ya bar ƙofar gidan.
Sadik kam abokansa me suka faɗo masa na makaranta, wanda su kansu ya manta da su gaba ɗaya, Allah ne kawai ya tsare Sadik a irin tuƙin da yake na ganganci, kowa ya gani se yai Magana.
Be tsaya ko ina ba se ƙofar makarantar su, wadda itace tushe, ko ince kanwa uwar gamin kowacce ƙaddara da ta afakawa galibin jaruman.
Sedai tun daga farkon layin makarantar, Sadik be ga ana shiga ana fita da motoci ba na masu kai 'yan Makaranta ba kamar yadda yake a da ba.
Abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, haka ya ƙarasa ƙofar gate ɗin, amma yana zuwa ya ga uban kwaɗo a tangamemen gate ɗin harabar makarantar.
"Maraba maraba, Prince yau kai ne sa kanka bayan dogon zamani ba ka waiwayo mu ba"
Sadik ya waiga yaga ɗaya daga security ɗin makarantar ne, wanda suke yawan faɗa da Sadik akan fita daga makaranta ba akan ƙa'ida ba.
Sadik kamar ze rushe da kuka yace "Ɗan Ala, ya naga kwaɗo a ƙofar makarantar?"
Ɗan ala yace "kai yanzu baka san abunda ya faru ba, ko a jarida ba ka gani ba, ko dayke ance ba ka ƙasar, abokan naka ba su gaya maka ba?"
Sadik yace "meyafaru ban sani ba"
Nan ɗan Ala ya kwashe komai ya gayawa Sadik.
Jikin Sadik ya hau wata irin tsuma, bayan tuna irin miyagun maganganu da sir Nazir ya dinga gaya masa shi da Farhan, a kiɗime yace "ɗan Ala Farhan fa, Farhan ɗina fa meyafaru da ita?"
Ɗan Ala yace "Allah sarki Baiwar Allah, tun daka bar makarantar nan duk ta ƙara zama wata iri, kamar wadda ƙwaƙwalwaeta ta samu matsala haka ta koma, a kai tayi da ita ɗalibai suka takura mata, duk ta damu kanta, tun wani zuwa da tai da kayan gida a jikinta na ganta a gurin parking ɗin motoci, da ita da Aminun ajinku da Mubarak Babba ban kuma ganinta ba, ta dena zuwa makaranta baki ɗaya"
"Kace Mubarak Babba?"
"Eh shi"
Sadik be ƙara cewa uffan ba, ya doshi motarsa zuciyarsa na wani irin tsalle kamar ta fasa ƙirjinsa.
Ɗan ala yace "Prince da gaske wai kayi Aure?"
Ai Sadik ya kurumce, be ma ji me ɗan Ala yace ba, saboda ba ya gane komai gaba ɗaya.
Cikin wani irin zafin Nama, ya ja mota ya bar layin, ya dinga mamakin yadda akai ƙanin Farhan yace be san in da take ba, gaba ɗaya yaji abubuwa sun dabaibaye shi ya ma rasa wani tunani yakamata yayi, meye haɗin Farhan da Mubarak Babba.
Dukan sitiyari yai, yaja wani wawan burkin da yai wannan tunanin, nan da nan zuciyarsa ta ƙara shiga taradaddi, meye haɗin Mubarak da Farhan? Babban abunda ya sake jefa shi a ruɗani be wuce yadda har abokansa ya manta da su ba.
Ya kuma fizgar motar ya cigaba da tafiya, lokacin kusan goma da rabi na safe, unguwar su Amin ya wuce, dan ɗan Ala yace masa da Amin da Mubarak da Farhan ya gani ranar ƙarshe da ta zo makaranta.
Idan yaje guri ya tarar da cunkoso a hanya, ji yake kamar yaiwa motar fuka fukai ya je in da za shi, saboda Azabar ruɗani da hanzarin son ya ga Farhan.
A ƙofar Gidan su Amin yai parking, gashi ko waya be ɗakko ba, idan ma ya ɗakko wayar ina yaga lambobin 'yan ajin na su yanzu.
Wani irin mahaukacin horn ya dinga yi, wanda se da layin gaba ɗaya ya ɗauka, a gigice megadin gidan ya fito yana wane mara tunanin wannan?
Sadik ya sauke Glass yana kallonsa, megadin yace "Ahh Yau kaine da kanka, Yaushe rabon duniya da ayyaraye, munyi cigiyarka har mun gaji"
Sadik ransa a haɗe yace "yi min magana da Ameen"
"Aminu yana makaranta ai"
"Wace makarantar?"
"Yana Makarantar nan, ta Nijar amma nasan yau zuwa gobe in Allah ya kai rai, ze shigo ko dai a satin nan"
Dukan sitiyari Sadik yai, yana wani irin huci, a hankali ya furta "Why Farhan, meya haɗaki da Mubarak, tabbas idan na kama Mubarak da aikata wani abu akan ki da hannun na zan kashe shi"
Ya kuma jan motar nan ya bar unguwar su Amin, kusan duk abokan nasa na ajinsu ya zaga, amma ba wanda ya samu balle ya samu wani information, ya koma unguwar su Farhan, ya aika yaro a kirata amma aka kuma ce masa ba ta nan.
Har ƙarfe biyar na yamma Sadik yana gararamba a gari akan yadda ze samu Farhan, amma abu ya ci tura.
Haka ya koma gida, Mother na ganinsa ta fara faɗa "daga ina kake haka? Jiya Usman yace min ya zo ya tarar da kai wani iri, na duba naga kana bacci, yau wayewar gari kan in tashi wai har ka fice daga gidan nan, kalli se yanzu biyar da rabi ka dawo, daga ina kake haka?"
Sadik yace "ba ko ina?"
"Kamar ya ba ko ina?"
"Mother bani da lafiya ne, naje Asibiti ne aka samun ruwa"
"Kuma shine ka kasa kiran kowa a waya ka sanar masa? Ya jikin naka?"
Yace "naji sauƙi Alhamdilillah"
"Sun baka magani ne?"
Sadik ya gaji da tambayoyin Mother ya jinjina mata kai kawai ya shige ɗakinsa.
Tea ta sa aka dafa masa, ta kai masa ɗaki ta takurashi akan ya sha.
Sam Sadik ya manta da wata yunwa, dan ba ya jinta sam.
Mother ta kalleshi tace "Sadik, ko dai duk akan Yarinyar nan ne kabi ka da mu ka ɗaga hankalinka?"
Da sauri Sadik yace "Mother wace Yarinyar?"
"A'a wace Yarinyar ban da matarka? Ko dan sun tafi ƙauye ne kake wannan abun harda rashin lafiya?"
Sadik ya girgiza kai yace"A'a"
Mother tace "ka dai shiga hankalinka ka dena wannan zaƙewar, su mata ba a musu haka, idan ta fuskanci irin wannan son kake mata, wahalar da kai za tai, idan kuma saboda ɗanka ne ai za su dawo, ka sha tea ɗin nan ga doya nan ka ci kan ai sallar magariba, da anyi isha'i se ka kwanta"
Da ƙyar Sadik ya cakali Abincin yaci ya bar shi, dan a ganinsa Mother ba zata gane halin da yake ciki ba.
Sunusi ne keta binciken kayansa, yayin da Haladu ke gefe yana rubutu a jikin allo.
Aƙalla Sunusi ya shafe da mintuna talatin yana zazzage kaya yana mayarwa, amma Haladu be ce masa uffan ba.
Sunusi ya ɗago ya kalli Haladu a fusace yace "Haladu"
Haladu ya ɗago ya kalleshi yace "ya akayi?"
"Ka taɓa min kaya da bana nan"
"Ban fahimci me kake faɗa ba, Kamar ya ina taɓa maka kaya, ƙaddara ma ina taɓa maka yau na fara taɓa kayanka ko kai ka taɓa nawa, ka taɓa ganin na maka sata ne, ko ba ka nan na ɗau abu ka dawo ina gaya maka"
Sunusi yace "kar ka rainamin hankali mana, ba yau ka saba ta;a kayana ba amma tun ɗazu nake neman abu ko ka tambayi me nake nema?"
"Meyasa zan tambaye ka bayan nasan ban ɗaukar maka komai ba"
Sunusi yai shiru can yace "kai wallahi Haladu kai ne, in ba kai ba ba wanda ze ɗau abunda nake nema"
"To wai me kake nema ne?"
Sunusi yace "jakar da nake ajiye ajiyen aikin da nakewa mutune aka taɓa min, na nemi wasu laƙanai da nayi ban gani ba, kuma ni gani nake kamar an sauya min layoyin nan da wasu"
"Kuma shikenan sekace nine na ɗauka, meye haɗina da aikin da kakewa mutane da ze sa in ɗaukar maka, na taɓa yi maka hakane?"
Sunusi ya dawo gaban Haladu ya tsuguna yace "Haladu, naga take takenka ne a 'yan kwanakin nan, ka damu da lamarin Yarinyar nan, matar da zan Aura, wallahi ka sake ka shiga hurumin da ba naka ba, ko kuma na gano kai ka ɗau abinda nake nema, zaka ga abunda ze biyo biya"
Seda cikin Haladu yai wata irin ƙara saboda yasan Sunusi ze iya, amma ya dake yace "ba ka isa kai min abunda Allah be min ba, kuma Yarinyar da kake iƙrarin zaka Aura, ba sonta kake ba wallahi, kuma ba zaka taɓa mallakar ta ba tunda Allah ba ya barin zalunci sam"
Malam Labaran ne yai gyaran murya yace "wai meke faruwa ne, hatsaniyar me kuke ne?x
Sunusi yai saurin cewa "bakomai Malam, saɓanin fahimta ne kuma Komai ya wuce"
"Ku dinga ƙoƙarin kai zuciyarku nesa, ku dena irin wannan hatsaniyar yaran nan da ku suke koyi, ku dena aikata rashin ɗa'a suna jinku"
Sunusi yace "to malam, insha Allah"
Malam na barin gurin, Sunusi yaiwa Haladu wani Mugun kallo irin na zan haɗu da kai ne, sannan ya fice.
Haladu kuwa ajiyar zuciya yai yana fatan Allah ya tsare shi daga Sharrin Sunusi, dan Sunusi ba shi da imani sam.
Kwana uku kenan, Sadik yana sintiri a tsakanin gidan su Farhan da na su Amin, har gidan su Nas yaje, amma akace shima baya nan yana dutse, baya so ya tunkari in da Mubarak babba yake ba tare da ya san in da Farhan take ba.
Abun duniya ya damu Sadik, ya rasa in da ze sa ransa, gaba ɗaya Mother ta kasa gane kan Sadik gaba ɗaya, baya wuni a gida baya cin abinci, tun tana mitar har ta gaji ta ƙyaleshi, ta zata kawai kewar matarsa yake da ɗan sa, dama kuma tun da suka dawo Nigeria ba wani fita yake ba, dan haka kawai ta zaci se yanzu yake zaga abokansa.
Wanka ma se yayi dagaske yake iyayi, salla kawai yake cikin kwanciyar hankali, raba dare yake ido biyu, haryanzu ya kasa gane dalilin da yasa ya manta da Farhan a duniyarsa, babban abunda yake ɗaga masa hankali be wuce batun Ganin Farhan da Mubarak da akace anyi ba, ya rasa in da ze sa kansa ya ji daɗi ba shi da wani burin da ya wuce ya saka Farhan a idonsa.
"Nana ba zaki sha kunun nan ba se ya huce, se fama kike da waya a hannu tun ɗazu"
Nana ta ɗan ɓata fuska tace "Inna, Besty yau kusan kwana Biyar be kira mu ba, kuma ni na kira wayarsa amma ba ta shiga"
Inna tace "waye kuma haka?"
Nana ce "baban Sahal mana, kullum fa se ya kirani a waya, yace in kara wayar a jikin Sahal yaji numfashinsa amma kwana biyar be neme mu ba"
Inna tace "to jiki da jink, ai dole wataran ze gaji ko?"
"Inna yau fa kwana biyar, Allah ya sa Lafiya yake hankalina ya fara tashi"
"Ban da abunki ai Lafiya ita ke ɓuya, yana nan lafiya insha Allah"
"To Inna Allah yasa, amma yana da kula sosai in lafiya baze kasa kiranmu tsawon wannan lokacin ba"
Inna tace "to ai se kiyi, tun da akan ku ze ƙare" Nana ta ja bakinta tai shiru, amma dai jikinta na bata akwai wani abu a ƙasa.
Yauma da safiyar Allah Sadik yana hanya gari ya ƙarasa wayewa, hanyar makarantar su Amir ƙanin Farhan yaje ya tsaya, da Amir yaga Sadik se da abun ya bashi mamaki ba ze iya faɗin sau nawa yaga Sadik ba, ba yau ba gobe cikin sintiri yake, gashi kamar Farhan ta san da zuwansa taƙi zaman gida sam.
Sadik ya nufo Amir, Amira ya gaisheshi ya amsa sannan yace "Ameer dan Allah ko lambar Farhan ka bani mana"
Ameer yace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba ta nan, dan Allah in wani abun tai maka kayi haƙuri, ka barta ta ji da halin da take ciki"
Sadik yace "a wani halin take dan Allah, ka gayamin"
Shiru Amir yai, se ga ƙwalla ta taru a idonsa zeyi kuka.
Sadik ya dafa kafaɗun Amir yace "dan Allah ka gayamin halin da take ciki, da kuma in da zan sameta"
'gaskiya ko ɗaya ba zan iya gaya maka ba, amma kaje gobe in Allah ya kaimu zan nemo lambar ta ka zo in baka"
Daga haka Amira ya zame kafaɗarsa yai gaba abunsa.
Sadik ya koma cikin mota ya kifa kansa a kan sitiyari, yana sauke numfashi da kyar, ga cikinsa har wani ciwo yake, saboda Azabar yunwa har wata ramar dole yayi.
Wasa wasa Har ta gaji da kiran layin Sadik amma kullum a kashe, dan harta fara kuka a ɓoye dan kar Inna ta gane tai ta mata faɗa.
Amir har mamakin nacin Sadik yake, dan a ƙofar Gidan ya tarar da Sadik da uwar sassafiya.
Ya koma gida ya ɗakkowa Sadik lambar Farhan a jikin takadda.
Wata irin ajiyar zuciya Sadik yai, ji yake tamkar yaga Farhan, dubu biyar ya bawa Amir, amma fafur yaƙi karɓa.
Se dai Sadik be fito da waya ba, dan haka ya nufi gida, kawai ya ratse hanya ya koma gidansu Amin.
Megadin su Amin na ganinsa yai murmushi yace "a wannan karon kayi sa'a, ya shigo jiya da daddare, bari in masa Magana.
Kusan mintuna biyar da shigar megadin, se gasu tare da Amin, shima ya ƙara girma yai fresh, ya fito fuskar sa cike da fara'a yana "Takawarka lafiya Prince namu, ba amana wallahi"
A Wani irin fusace Sadik ya buɗe murfin motar ya fito, fuskar sa babu walwala ya ƙure Amin da ido, cikin huci yace "Aminu ina Farhan take?"
Amin yace "wacw irin tambaya ce wannan? Ai kai zan wa wannan tambayar"
"Kayi haukane Amin? Ina tambayar ka kana nema ka raina min hankali?"
"Kai zan tambaya ko kayi hauka ne? Ni ka barwa ajiyarta ne? Ka tafi ka manta da batun Yarinyar mutane tsawon lokaci, kaje kai Aurenka kuma ka zo nan kana min hauka, kaje gidansu mana ka tambaya"
A fusace Sadik ya fizgo Amin, ya haɗa shi da jikin mota ya zuba masa ido jikinsa na rawa yace "Al'ameen kai na barwa Amanar Farhan kan in tafi, ko ka manta Sadik baya mantuwa? Amina meye haɗin Farhan da Mubarak, Ɗan Ala ya gayamin ranar ƙarshe da ta zo makaranta tare ya ganku kai da ita da shi"
Sadik ya haɗa hannayensa kamar me neman gafara 🙏 cikin rauni yace "Amin, kar ka gayamin kun ɓata min Farhan, ka buɗe baki kaimin bayani, ka tsaya kana kallona" ya ƙarasa maganar cikin tsawa idonsa yai wani irin ja.
Amin yace "Am sorry Sadik"
"Sorry for what? Kai min bayani"
"Sadik, ba laifina bane, nayi iya yina gurin bata kariya, but i fails you, I don't know how to explain amma koma mene da sa hannun Babba da Taslim da kuma Nas"
Sadik ya danƙi sumar kansa yana jin yadda kalaman Amin ke sukar zuciyarsa ɗaya bayan ɗaya.
"Just cut the story Amin, nagode Sosai da sosai, ka gayawa Mubarak Babba da Nas, idona idon ɗaya daga cikin su sena kashesu, mussaman Mubarak"
Amin yace "Sadik kabi komai a hankali, kar kai kisan kai, kuma koma menene laifinka ne daka tsallake ka tafi ka barta kaje kai Auren ka, ka sa......
"Shut up kan in fara ta kanka" yai maganar yana shaƙe Amina. A guje megadin ya zo ya raba su yana mamakin meya haɗasu haka? Yasan abokaine sosai da sosai amma ya haka ta faru a tsakanin su bayan shafe dogon lokaci basu haɗu ba.
Sadik be jira komai ba ya hau mota, da fari farautar Mubarak ya so yayi, amma se yaga ɓata lokaci ne, sanin in da Farhan take shi yafi mahimmanci, dan haka ya nufi gida, jikinsa na wata irin tsuma kamar wanda ake bugawa gangi.
Yana zuwa gida beyi wata wata ba, ya ɗau wayarsa ya kunna, ya saka lambar Farhan a ciki, ya shiga kiran layin.
Sedai ko da yaji wayar ta shiga, se ƙirjinsa ya tsananta bugawa, har ya fara jin Kamar zuciyarsa na barazanar tsaga ƙirjinsa, amma haka ya dake cike da ƙwarin gwiwa yana sauraron amon shigar wayar.
Farhan kuwa tana cikin maye, dan haka ko yatsanta kasa ɗagawa tayi, tana kwance tana jin wayar na ringing ta miƙa hannunta ta ɗau wayar abu ya gagara, idanunta suka cigaba da lumshewa ta cigaba da baccinta.
Sadik ya kirata ya kai sau talatin, amma ba wanda ta ɗaga, be san lokacin da zuciya ta ɗebe shi, yai jifa da wayar ba, Ta faɗi ta tarwatse a gurin, ya koma gefe yana huci, ya kai idonsa kan hoton Farhan a jikin laptop ɗin sa, yace "Why Princess, why don't you pick my calls? Kina son in mutu ne?" Ya ƙarasa maganar yana dafe goshinsa.
A ranar Sadik ya fita ya siyo wata wayar, Mother se masifa take akan ta gaji da wannan jigilar da yake, na tare da tasan in da yake zuwa ba, ai be kula Mother ba ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofa.
Haka ya wanzu har cikin dare yana kiran layin Farhan, amma ba bu amsa.
Wata shawara ya yanke a ransa, kasamcewar ya san kan computer sosai da sosai, nan ya shiga ƙoƙarin bin diddigin layin Farhan, amma Network ya hanashi samun abinda yake so.
Yadda yaga rana haka yaga dare, ko kaɗan be rintsa ba, sam baya jin baccin ma.
Wayewar garin Allah, haka ya koma ka computer yana cigaba da ƙoƙarin locating in da Farhan take ta hanyar lambar wayarta.
Se yamma sannan Sadik ya iya gano in da Farhan take, Cikin azama ya kuma fafarar mota, ya bar gidan sannu a hankali ya shiga rukunin gidaje na Nassarawa GRA da ke garin Kano, yana yi yana duba wayarsa, a haka ya ƙaraso wani katafaren Hotel.
Saboda sauri a waje yai parking ɗin motar, ya shiga cikin Hotel ɗin, tuni zuciyar Sadik ta karaya ganin Farhan na cikin Hotel.
Sannu a hankali se gashi a ƙofar ɗaki me lamba ta goma sha ɗaya, wanda ya kasance VIP,