Showing 237001 words to 240000 words out of 259198 words

Chapter 80 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13353

zan ba ni ku ƙyaleni, dan Allah Inna ki tashi Alhaji, ki ce masa ya tashi kar ya tafi ya barni mana".

Inna da take zubda hawaye, ta janyo Nana jikinta tana duddukan bayanta a hankali alamar rarrashi.

Tabbas duk wanda ze ji rasuwar Hakimi barin Nana ne, tun da Allah yasa su Inna suka rasa iyayen Nana suka ɗau son duniya suka ɗora mata.
Banda Inna a tsaye take akan tarbiyyar Nana, ds a sangarce za ta tashi, dan ta Hakimi shi be ya takurawa Nana, duk abunda take so shi yake mata, kasancewar yaransu duk sun rasu se Abba, ita kaɗaice jikarsu da ke gabansu, Nana ko dangin mahaifiyarta ba ta wani sansu ba, saboda ba zuwa take ba, iyakaci sedai su su zo, sam Hakimi baya son tai nesa da shi.
Ko zaman fada da ƙyar Inna ta hana shi yi da Nana, lokacin ta fara girma, akwai matsananciyar shaƙuwa ds soyayya a tsakanin Nana da Hakimi, shaƙuwa ta gaske kuwa.

Wani dogarin Hakimi ne yai sallama a ƙofar turakar yace "A fito da shi, mutane sun idar da alwala za'a shigo da makara a ɗauke shi". (Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya Ubangijin talikai kasa ranar da zamu dawo gareka ta zama ranar farinciki a gare mu, Allah kar ka sa mu mutu ɓatattu kasa mu mutu a tafarkin ka da na manzonka".

Abba jikinsa na rawa ya miƙe, hawaye na zuba a idonsa, Faruk ma kukan yake sosai suka miƙe, dan a ɗau gawar Hakimi, amma Nana ta gigice, ta miƙe jikinta na wata irin rawa, ta riƙe gawar Hakimi tana girgiza kai tace "Inna idan kika bari suka tafi da shi, ba zan sake ganinsa ba fa, Inna kakana a duniya waze mayen gurbinsa, dan Allah kar ku tafi da shi".

Gaba ɗaya ta gigice bata hayyacinta sam, surutai kawai takeyi, duk da jikin Sadik babu ƙwari haka ya miƙe, ya janye Nana daga jikin gawar Hakimi, ta shiga ture Sadik, amma ya riƙeta sosai a jikinsa se miƙa hannu take tana kuka, yai waje da ita.

Gidan ya cika da mutane sosai da sosai, Sadik ya wuce da ita wani ɗaki, ya zauna da ita a ƙirjinsa tana ta fizge fizge se ta ƙwace.

Sadik ya rungumeta tsam a jikinsa, ya shiga faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" a kunnenta.

A hankali ta lumshe ido tana wani irin sauke nannauyan numfashi, a hankali ya kwantar da ita, sedai babu tabbacin tana hayyacinta.

Ko da Sadik ya fito har an fita da Hakimi, Sadik ya leƙa yace "Mother, maman Sahal tana can ɗakin ko zaki zauna da ita?".

Mother tace "to shikenan". Ta tashi ta tafi ɗakin da Nana ke kwance, wadda a kwance kawai take ba tare da sanin a wani yanayi take ba, suma ko ido biyu.

A kaiwa Hakimi salla, aka kai shi makwancinsa.

Hakimi kam yai jama'a sosai da sosai da sosai, bayan an masa jana'iza ma haka mutane suka cigaba da zuwa gaisuwa.

Bayan an dawo daga kai shi, su Abba suka zauna a waje suna cigaba da karɓar gaisuwa, su Inna kuma na cikin gida, Inna ko iya amsa gaisuwar ba tayi, se jinjina kai kawai, lokaci lokaci ta share hawaye.

Mother se goya Sahal tai, se uban kuka yake yi, saboda yana jin yunwa, Mummyn Khairat ke taiwa Nana fifita.

Sadik yai sallama ya shiga ɗakin yace "Mummy ba ta tashi ba ko?".

Mummy tace "kaga dai na kasa ganewa, a sume take ko idonta biyu?".

Sadik ya ƙarasa in da Nana ke kwance, ya ɗagota a hankali ya kira sunanta Husna.

Ta buɗe idanunta da sukai ƙanana ta kalleshi, sedai ba tace komai ba.

"Kina gani na?" Ya tambaye ta, ba amsa se binsa da take da ido.

"Meye yake miki ciwo?"

Nan ma ba amsa se ido kawai.

Khairat ta zubawa Sarautar Allah ido, yarinyar da suke kafsa uban faɗa da Sadik, itace Yanzu yake ririta ta a matsayin matarsa.

"Tabbas munyi babban rashi, mun rasa Hakimi, amma kowa na hakane duk zaman jiranta muke yi, dan Allah ki kwantar da hankalinki, muyiwa kakanmu Addu'a Allah ya sada shi da rahamar sa, halinsa na gari ya bishi, dan Allah Husna kiyi Magana bana son wani abu ya sameki". Yai maganar hawayensa na ɗiga a kan kuncinta.

Nana ko motsi ba ta iya yi, se bin idon Sadik da kallo, ita ma hawaye na zuba daga nata idon.

Mummy tace "Sadik meye haka? Kai da zaka kwantar mata da hankali, se ka sakata a gaba kana kuka kuma?".

Sadik be saurari Mummy ba, ya cigaba da zubda hawaye.

Mother ta shigo, hannunta riƙe da kofi da ta sa aka samo mata madarar shanu ta bawa Sahal, dan yunwa yake ji, yana ta kuka.

"Sadik meye haka kake yi ne?"

itama Mother be tanka mata ba.

"Kai wannan ai shirme ne, tana buƙatar kalma me daɗi da zata kwantar mata da hankali, kai kuma kazo ka sakata gaba kana kuka, wannan ai shirme ne"

Ganin Sadik ba shi da niyyar cika Nana, balle su dena kukan yasa Mother, ta sa aka kira mata dr.

Usman ya kallesu, Sadik ya fiye abun haushi wasu lokutan, wai nan magidanci ne har da ɗa, amma yakasa rarrashin Matarsa, ya zauna tayata kuka.

"Wai dan Allah Sadii se a yaushe zaka girma ne? Kai da zaka rarrasheta, amma kun haɗa kai kuna aikin kuka, meye haka?" Yai maganar tare da ƙaraswa ze janye Sadik.

Mummy ce tace "Usman, ƙyale su kowanne dole zeji mutuwar nan, shi da alama bayan mutuwar har da tausayinta da yake ji, ka ƙyale su kawai.

Mother tace 'yo banda abun kunya, gidan surukai azo a tarar ka ƙanƙame mata kana tayata kuka, wannan ai ragwanci ne"

Mummy tace "suwaye sirikan, ba duk abu ɗaya bane? Ku ƙyaleshi kawai".

Sadik se da yai me isarsa, Sannan ya gyarawa Nana kwamciya, ya samu abun fifita ya dinga fifita ta, sedai gata nan ne dai kawai, ba ta gane komai.




"Farhan, yaushe rabon da Sadik ya sake zuwa gurinki?" Abbas yaiwa Farhan tambayar.
A bazata taji maganar ta sa, ta kalleshi da mamaki tace "wace irin tambaya ce wannan?"
Abbas yace "kawai dai na tambaya ne".

"Banji daɗin wannan tambayar ba, kana gani ina fama ya rabu da ni ya den bina, kai kuma kana tambayata shi".

Abbas yace "baki tunanin meyasa kwana biyu ya dena zuwa ba?".

"Abba ne yace kar ya sake zuwa, Aure zanyi".

"Hmmm, hakane amma a yadda yake nace miki kina ganin kashedin Abba kawai ze hana shi ya cigaba da biniyarki?" Ɗan shiru Farhan tai, dan wancan karon ma Abban ya masa kashedi amma ya kuma dawowa.

"Kin san wani abu, ranar nazo na daɗe a tsaye ina kallonku ke da shi, har Abba ya zo ya sameku, dui da ba na jin abunda kuke cewa, amma nasan Abba kashedi yake masa, haka nan naji ya bani tausayi yaron".

Farhan tace "to me kake nufi?"

"Ba abunda nake nufi, amma ba shi da lafiya"

"Haba dai? Meyasame shi?" Reaction ɗinta kawai Abbas yabi da kallo, wata zabura tai lokacin da zata tambayeshi, wanda ita ba ta san tayi ba.

Abbas yace "nima ban sani ba, yanayin sa na kalla tun a lokacin, naga akwai banbanci da ranar da na fara ganinsa da kuma ganin ƙarshe da nai masa, duk yayi wani iri, akwai alamun rashin lafiya a tare da shi, da kuma damuwa"

Shiru tai ta tafi tunani.

"You still love him Farhan".

Farhan tace "A'a ni bana son Sadik, wai se yaushe zaka yadda da hakan?"

"Kinga yadda yanayinki ya canza kuwa? Ina ta baki dama ne kar in tauyeki, idan haryanzu kina son sa, ni me iya jagora ne in samu Abba in masa bayani yadda ze fahimta".

"Doctor, dan Allah ka fahimceni, a baya na so Sadik, so ba na wasa ba, ya bani kulawa da soyayya a lokacin da na rasa hakan daga in da Yakamata, ya soni ya kula da ni, amma ƙaddara ta gifta, ba zan iya Auren Sadik ba, faɗan da Abba ma yake yi wai me zan da wannan Yaron, kuma idan na ce ina son Sadik ban maka adalci ba doctor"

"Saboda ki min adalci ke se in kasa yi muku adalci? Ai soyayyar gaskiya shine sadaukarwa dan samawa wanda kake so farinciki, abunda iyayenmu basu gane ba, ita soyayya ba yin mutum bace, sirrin Allah ce a zukatan bayinsa, ba kowa ke iya sarrafa soyayya ba, idan kika tabattar min da kina son Sadik, ni kuma zan wuce gaba in wa Abba bayani, kuma batun yarintar sa iyayenmu da kakanni shekaru nawa suke Aure?".

Cikin kuka tace "Ni bana son sa, bana son Sadik doctor, ni dan Allah ka hanzarta a kawo kuɗin nan in huta da nacinsa, dan Allah"

Abbas yace "to naji, ya isa dena kukan haka, amma kiyi addu'a Allah ya sa yana lafiya, ranar da ya bar nan da ƙyar ya iya shiga motarsa".

Shiru Farhan tai tana goge hawaye, yayin da ƙasan zuciyarta tsananin tausayin Sadik ya cikata.


Sunusi ne yake huci Kamar kumurci yace "Wallahi Haladu zan maka abunda ba zaka taɓa mantawa ba, kai ne ka sace min kayana".

Haladu yace "in sace su in uwar me da su wai, wai meke damunka ne haka?"

"Dole ka faɗi haka mana, ka ɓatamin aikina naga wannan ɗan iskan yaron ya dawo rayuwata"

Haladu yace "ita wa kenan?"

"Farhan matata mana, wannan yaron ya dawo rayuwarta na ganshi a ƙofar gidansu"

Haladu yace "Masha Allah, Alhamdilillah ai dama irin wannan Asirin ba ya daɗewa yake karyewa".

"Kenan ya tabatta kai ne ka sacemin kaya ka ɓata min aiki?"

"Na san yadda kai aikin ne balle in ɓata maka?"

Sunusi yace "ƙarya kake Haladu, Wallahi sena sake sabon aiki a kansu, ba su kɗai  ba har kai, za ka ga abunda zan maka, kowa yaci tuwo da ni miya ya sha, zaka san ka shiga aikina ka min shishshigi"

"Wallahi Sunusi idan ba ka ji tsoron Allah ba, se ka wulaƙanta, iliminka be maka amfani ba, yanzu na sake fuskantar dalilin da ya sa wasu ke ƙalubalantar ilimin soro, Alƙur'ani kawai muka sani, bamu san tauhidi da sauran litattafai na addini ba, Alqur'ani kawai muka sani, kuma wasunmu irinka muna amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba, irinka suke surkulle da shi saboda rashin tsoron Allah, Wallahi Sunusi kaji tsoron Allah kafin hakkin mutane, musamman na yarinyar nan ya kama ka".

"Dalla rufemin baki, ka zuba ido zaka gani, daga kai har ita da wannan sakaran a wannan karon zasuga abunda zan musu" daga haka ya fice yana kumbura wuya.

Har bayan la'asar Nana ba ta magana sam, kuma ba ta ci komai ba, gashi rabonta da Abinci tun jiya da rana, se bayan la'asar sanann Inna ta zo kan Nana, ta tashe ta ta tashi zaune amma ba Magana.

Inna ta rungumeta, ta shiga karanto mata adduoi, kusan mintuna Ashirin sannan Nana ta fara ajiyar zuciya, sautin sheshsheƙa kukanta ya fara fita  tace "Inna"

Inna tace "ya isa haka kukan Nana, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shi zaki ta maimaitawa"

Zata kuma magana Inna ta girgiza mata tace "yi ta maimaitawa Innalillahi wa Innalillahi raji'un".

Nana tace "Inna dan Allah shikenan ba zan sake ganin Alhaji ba?"

Inna tace "mun rasa shi Nana, Allah ya buƙaci abunsa, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ki ta maimaitawa ki tashi kije, ki alwala ki salla".

Inna ce ta kamota zuwa tsakar gida, mutane na tai mata sannu suna mata gaisuwa, amma ba ta iya amsawa, sedai Inna ta amsa.

Ta rama duk sallolin da ake binta, gurin cin abinci shima haka a kai ta fama da ita da ƙyar Sadik ya sata a gaba sannan ta sha kunu kaɗan, har Sahal ya samu ya ɗan sha Nono.

Bayan azahar Mummy da Khairat suka tafi gida, karon farko a rayuwa Mother ta kwana a ƙauye, tun bayan Aurenta da Alhaji Abdullahi.

Washegari mutane suka dinga ɓarkowa, ciki harda maƙota da 'yan uwan Mother suka dinga zuwa yin gaisuwa, abunka da rasuwar an maida makokin na zamani, aka dinga shiga ana fita a gidan makokin nan, sedai wanda a kaiwa rasuwar zakaga sune cikin matsananciyar damuwa a fuskokinsu.


Abu Kamar wasa, Farhan taga Sadik ya dena zuwa, ta fara tunani kala kala a ranta, anya ba da gaske ba shi da lafiya ba kamar yadda doctor ya faɗa ba? Ko dai korar da Abba yai masa ne ya sa ya dena zuwa?.

Shiru tai ta rasa abunda za tai, a hankali ta tashi zaune, ta ɗau wayarta ta shiga yanar gizo dan rage zafi.
Sedai labarin farko da tai karo da shi ne ya girgiza ta, mutuwar kakansu Sadik.
Jikinta yai sanyi matuƙa, taji rasuwar ƙwarai da gaske, a nan taiwa Hakimi addu'a sosai.

Tana nam zaune tana tunanin yadda mutuwar kakan Sadik ta daketa sosai, Huzaifa yai sallama a ɗakin nata.

Ta amsa masa tare da faɗaɗa murmushin fuskarta.

"Hajiya Yaya ana nan ana hutawa?"

"Wallahi kuwa, daga ina haka?".

Huzaifa yace "naje wani guri ne, nace ai naga Sadik, ashe ya dawo garemu amma ba labari?"

Farhan ta haɗe rai tace "A ina ka ganshi?"

"A ƙofar gidan nan mana, sedai ban ji daɗin abunda Abba yai masa ba, yakamata a fahimci juna, yazo asha biki kawai tunda Allah ya dawo da shi"

"Huzaifa ka san me kake faɗa kuwa? Abbas ya kusa kawo kuɗin Aurena kuma kana maganar wani Sadik, dan ka bar wannan maganar, ni ba abunda zanyi da Sadik"

Huzaifa yai murmushi yace "ji kamar gaske, a tunaninki abu ne me sauƙi kice kin dena son Sadik a yarda? Ya kamata Abba yai tunani akan lamarin nan kan ya yanke hukunci, ni dai na tafi se anjima" ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, Farhan ta bi bayansa da kallo.





Kwanaki bakwai da rasuwar Hakimi, Abba yace za su tafi da Inna can Kano, su cigaba da zama amma Inna fafur tace a'a ita su barta a ɗakinta taiwa Hakimi takaba, ta duba a dangi ta samo wadda zasu dinga zama tare, amma ba zata bar gidanta ba, ba yadda Abba be da ita ba, amma taƙi yadda se haƙura yai ya ƙyaleta.
  Nana kam haka tai kwanakin nan sam ba walwala, abinci dama ba ciwuwa yake a gurinta ba, daga salla se kwanciya, duk ta rame.
Ranar kwana bakwan Abba yace tare da ita zasu koma gida, jikinta babu ƙwarin da za tai jayayya, dan haka ta bi su suka taho, tana ta kuka tana sake jin yadda mutuwar ke sake dukan ta kamar lokacin akayi ta.




Huzaifa ne zaune tare da Malam Zakari, wato mahaifinsa suna hira, Huzaifa yace "Baba ka san wani abu?"

Yace "A'a seka faɗa Huzaifa"

"Wannan yaron da Farhan take so fa ya dawo"

"Ya dawo ina?" Cewar malam Zakari.

"Ya dawo, yace aurenta zeyi yana sonta, amma Abba ya koreshi yace karya sake zuwa"

Malam Zakari yace "Subhanallaahi, garin yaya ai ni be gayamin ba, idan da yadda za'ai kawai gara a bashi kar wata matsalar ta kunno kai".

Huzaifa yace "Baba, ka manta da anzo an tambayi Aurenta za'a kawo kuɗi"

"To ai Huzaifa, komai masalaha ake dubawa, shi wannan tunda su kai magana, shiru ba su turo ba, zanje in samu baban naku, a wannan karon ba zan so a kuma ganganci da rayuwar yarinyar nan ba, hakan akai a wancan karon aka jefa rayuwarta cikin matsala".




"Husna, duk me rai mamaci ne, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki dena wannan kukan mu cigaba da yi masa Addu'a, Allah ya sa ya dace, ki ɗau Abincinki kici kinji"

"Ka ƙyaleni, ni bana son komai bana jin daɗin komai, ka rabu da ni da wani Abinci"

"Dan Allah Nana, kici ko ba yawa Please"

"Ni ba zan ci ba, ka rabu da ni".

"Sadik, Sadik" ya jiyo muryar Abba yana kiransa a falo.

Cikin sauri Sadik ya tashi, ya fito yace "Abba gani".

Abba yace "Yawwa, ina son cika wasiyyar Hakimi da ya bari, ka gayawa iyayen yarinyar nan ranar Asabar in Allah ya kaimu, zamu kai maka kuɗin Aure, amma a cikin kuɗin ka za'a ɗauka a kai"

Sadik yace "Abba, amma me ze hana a bar kai kuɗin Hakimi yai Arba'in, kuma ga Nana haryanzu tana cikin alhini"

Abba yace "kaga, bana son wani kame kame kaji ko? Ai ka san da haka kaje gurinsa ka dage akan se an nema maka aure, abunda yafi kyautuwa a cika masa wasiyyar sa, dan haka kaje ka sanar da su" Abba be saurari abunda Sadik zece ba yai waje.

Jiki a sanyaye Sadik ya koma in da ya bar Nana, yadda ta kalleshi ne kawai ya tabbatar masa taji duk yadda su kai da Abba, gaba ɗaya ya rasa murna ze ko takaici, yana matuƙar jin tausayin Nana, ba ta shirya jin komai daga Sadik ba, dan haka ta kwanta ta juya masa baya.




Mother ta cewa Sadik ya ƙyale Nana a nan ɓangaren cikin gida, saboda yanayin da take ciki.
kullum Sadik se ya zo gurin Nana, sedai haka nan take ba walwala, cin abincin ma ba yi take ba, ba dan Sadik ya tsaya ba, da Sahal se ya yaye kansa, saboda sam ba ta damuwa da shi balle ta shayar da shi, ga shi da kukan banza.
  Nana ta rasa meyakamata tayi, ga alhinin rashin Hakimi, ga kuma tsabar kishi da ke damunta, ta rasa in da zata saka kanta ta ji daɗi.




Yau a cikin tsananin sa'a, Sadik ya je gidansu Farhan dan yana zuwa ya tarar da Huzaifa na shirin shiga gidansu Farhan.

Huzaifa ya tsaya cikin sakin fuska suka gaisa da Sadik.

Huzaifa yace "Farhan ɗin zan kira maka ne?"

Sadik yai murmushi yace "eh, Allah ya sa tana nan, dan naga gudu na take"

Huzaifa yace "ka barta kawai, ka san taji zafin abunda ya faru a tsakanin ku, haryanzu akwai wannan pain ɗin a tare da ita, gaskiya ta soka so na gaske, ta sha wahala ta azabtu a sanadin barinta da kai, ta afka mummunar hanyar shaye shaye, ga binta da sharri daban daban da wanda da za'a aura mata yai, duk wanda ya zo gurinta ko akai niyyar Aurenta, se ya bi ya hana, yaita ɓata a gurin mutane, haka ya sa ta shiga shaye shaye, da yawon kwana a hotel, ta dinga rashin lafiya ga gida babu daɗi, ta sha wahala dole ta gujeka ɗan uwa".

Sadik kamar ya fashe da kuka yace "Wallahi ba laifi na bane, Wallahi ka ji na rantse maka, yadda ka san anyi formatting memory na, haka na manta da komai, ba Farhan ba hatta makarantar da nai da abokaina da duk wata rayuwata makamanciyar wannan haka na manta da ita, ban yi dan in zalunci Farhan ba, Aure kuma da nai, na gaya mata kakana ne


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login