Showing 234001 words to 237000 words out of 259198 words

Chapter 79 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

Nazir Mutumin kirki ne, RUƊIN ƘURUCIYA da tashen balaga ya kai ni ga yi masa tarko, kuma ya kasa tsallake tarkon nawa, muka afka ga wannan ramin da muke nadama a yanzu haka, dan Allah Mummy ku bari in Auri Nazir"

Mummy ta kalli Lilly tace "ba ki da hankali, ke kina tunanin idan ya Aureki zaki daraja a idonsa, duk abunda ze wa ɗokin kin riga kin miƙa masa a waje, har kin yiyyi ciki kin zubar dan haka babu abinda zaki burge shi da shi, kuma baze taɓa yadda da ke ba, ke a wannan rayuwar ka kaiwa ɗa namiji mutuncinka gidansa ma, cin ubanka yake balle ke da kuka gama watsewa a waje, kullum a cikin zarginki ze kasance kuma kaf danginsa ba wanda be san meyafaru ba yanzu, ba zasu dinga ganin laifinsa ba, se naki laifin, dan haka ki maida hankalinki tun wuri, tun da Allah ya sa shi wannan be san ta'asar da kika aikata ba, kuma ya ɗan kwan biyu, ze kula da ke kuma ba lallai ya damu ba, tun wuri ki manta da wannan yaron"

Lilly ta share hawayenta tace "to Mummy, nagode"

Mummy tace "kije ki nemi guri ki huta"

Lilly tace "to Mummy, da tun da farko Daddy ya Auramin Nazeer, wataƙila da wannan abun be faru ba, amma dan Allah ku yafemin"

Mummy tace "daga ni har mahaifinki, munyi kuskure, Allah ya yafe mana baki ɗaya".




Ƙarfe takwas da rabi na safe, Nana tana cikin Asibitin da aka kwantar da Sadik, Nana kasa haƙuri tai, Mother ta sa direba ya kawota kafin su zo, Nana a rikice ta shiga ɗakin da akace Sadik yana ciki, ta ƙarasa gaban gadonsa, ta zuba masa ido, rana ɗaya amma har ya rame, ga ruwa yana shiga jikinsa a hankali.
Ta ja kujera ta zauna ta zuba masa ido, a hankali ta kwantawa da kanta a ƙirjinsa, ta fara kuka.
Ji tai ya sa hannu ya riƙo nata hannun, be mata Magana ba se hawaye dake bin gefen idonsa, ta ɗan ɗago ta kalle shi tace "Sannu"
Be amsa ba se ƙara matse hannunta da yai a nasa.

Dr. Ne yai sallama shi da Khairat da Jidda, Dr. Ya ƙarasa gaban gadon yace "meye haka zaka saka yarinya a gaba kana kuka, kamar wani ƙaramin yaro salon ka sake ɗaga mata hankali?".

Jidda tace "Baby ka ƙyalesu dan Allah, kana gani tun jiya be wani yi ƙwaƙwƙwaran mosti ba, alama ce ta ya fara samun sauƙi".

Dr. Yace "duk da haka ai se ita ma ya ɗaga mata hankali".

Nana kasa ɗaga Sadik tai, shima kuma ya kasa sakin hannunta, "Allah ya baka lafiya, in dai nice kayi Aurenka in dai hakan zesa hankalinka ya kwanta"

Usman yace "ke tashi in maida ke gida, ba ze Auren ba".

Nana ta girgiza Kai tace "dan Allah Yaya Usman ku bar shi yayi, kar ya rasa ransa".

Usman ya ƙaraso ya ɓanɓare Nana daga jikin Sadik yace "wuce muje, baze sa miki hawan jinin ba kema, kun zo kunawa mutane kuka, haryanzu ba ku san kun girma ba, kun haifi ɗa amma kunawa mutane koke koke".

Nana tana kuka haka Dr. Ya sata a gaba ya maida ita gida.






"Farhan, ranar Asabar insha Allah, nake sa ran in ji feedback ɗin yayyan babana, zasu kawo kuɗin Auren mu, amma dan Allah zan miki wata tambaya, ki gayamin tsakanin ki da Allah"

Farhan tace "to doctor, Allah yasa na sani"

Abbas ya gyara zamansa yace "do you still love him?"

"Who?"

"Sadik".
Gaban Farhan ne yai wata mummunar faɗuwa, ta ja wata ajiyar zuciya tace "meyasa ka tambaye ni?"

"Saboda sonki nake tsakani da Allah, ba na son in cutar da ke, ko in miki dole idan haryanzu kina son Sadik ni me fahimtar ki ne, farincikin ki nake so Farhan".

Zuciyar Farhan ce ta tsananta bugawa, amma tai jarumta tace "yanzu doctor idan ka ga zan komawa Sadik seka barni? Guda nawa yake ta yaya ze iya riƙe mata biyu?"

"Farhan, yana daga cikin matsalolin mu a yanzu, haramtawa kanmu abunda Addini ya halarta mana, Dan haka ki dena duba wannan".

Farhan tace "Doctor, ba na buƙatar Sadik a rayuwata, lokaci yayi da zan fuskanci rayuwata, dan ka dena kawo zancensa, Soyayar mu Ruɗin ƙuriciya ce kawai, dan haka a manta da wannan maganar".

Abbas ya kalleta yana wani iri murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa.

Farhan tace "dariyar me kake yi kuma?"

Yace "bakomai".




Nana tun da doctor ya dawo da ita gida, ta kasa nutsuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa in da zata saka ranta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, ko Abinci ta kasa ci haka ta wuni gaba ɗaya babu daɗi.

Se bayan ƙarfe goma na dare, sanann ta ji tsayuwar motar Abba, alamar sun dawo daga Asibiti.

Ta ɗan jira zuwa ƙarfe goma da rabi, sha ɗaya saura sannan ta shiga cikin gida.

Abba yace "Daughter ba ki bacci ba?"

Nana tace "eh, Abba ya jikin baban Sahal ɗin?"

Mother tace "ni idan kika ce baban Sahal ɗin nan, dariya kike bani da kunya".

Sukayi dariya banda Nana da fuskarta ke bayyanar da damuwa.

Abba yace "jikinsa yayi sauƙi sosai, dan ina ga gobe in Allah ya kaimu za'a sallame shi, ya tashi har yace a gaishe ku".

"Abba yayi Magana kenan?"

"Sosai makuwa, munyi hira da shi sosai".

Jiki a sanyaye Nana ta durƙusa akan gwiwowinta tace "Abba, Mother a madadin Sadik, dan Allah dan Annabi ina roƙa masa alfarma ba danmu ba, dan Allah ku ba shi dama yai Auren nan, in dai hakan ze sa ya samu farinciki".

Saroro suka bi Nana da kallo, Mother tace "ke anya kina da hankali kuwa? A biye muku kuyi ta shirme, ta yaya Sadik ze iya riƙe mata har biyu?"

Nana tace "tun da ya iya riƙeni mu biyun ma ze iya insha Allah, bana son Sahal ya zama Maraya, duk da rayuwa a hannun Allah take, Hakimi yai min Nasiha, na rungumi ƙaddara ta, zan cigaba da zama in kula da yarona, amma shi dai a ƙyaleshi ya Auri wadda yake so, tun da yace ita yake so, ita ya fara so dama".

Abba yace "Nana, tashi kije ki kwanta dare yayi".

"Abba, in kana son ka shiga cikin ceton Annabin rahama, dan Allah ku bari yayi, ka nema masa Auren nan, Mother dan Allah ki sa baki, ku bar shi yayi, in dai hakan ze sama masa kwanciyar hankali".

Abba yace "Naji, jeki za muyi shawara".

"Abba dan Allah ka yanke wannan shawarar yanzu, bana son Sahal ya rasa mahaifinsa akan abunda za'a iya magance shi, kaga yayi ƙarami ace yana da hawan jini, hawan jini se mutum ya fara tsufa, ko gane muta8fa ba yayi sosai, in dai ze iya faɗuwa jininsa ya hau saboda soyayya, to abun a duba lamarin ne, ni dan ta tawa me sauƙi ce, na yadda da ƙaddara, ƙaddarar Haihuwar Sahal ce ya sa na aure shi, amma dan Allah ku bari ya auri wadda yake so".

Wani irin tausayin Nana ne ya kama Mother, jiki a sanyaye Mother tace "Nana, shikenan kije ki samu ki kwanta".

Nana tace "to yaushe za'aje a tambayo masa Auren, bana son ya mutu" Nana tai maganar tana kuka sosai, kamar zata shiɗe.

Abba yace "Ai na riga na amince, kije Allah yai miki albarka, kin cika 'yar halak Nana, bari ya samu sauƙi zamu ga abunda zamuyi a kai".

Nana tace 'to kun yadda zaku yi masa Auren?"

Abba yace "za'ai masa, tashi kije ki dena kukan haka".

Nana tace "to Abba nagode sosai, Allah ya saka muku da Alkhairi ya sa ku gama da duniya da lafiya, Allah ya baku abunda kuke nema".

Abba yace "Ameen, Allah yai miki albarka". Nana ta tashi da goyon Sahal a bayansa, ta bar falon.

Mother tace "Allah sarki, so bala'i ne, banda haka me zesa yarinyar nan ta damu aiwa Sadik abunda yake so? Waye yake son ai masa kishiya, ji nake kamar in mata kuka, ga kishi a tare da ita kuma ga mafita take nema masa, Sadik bewa kansa adalci ba"

Abba yai shiru, dan shi kansa tausayin Nana ne ya cika zuciyar sa.

Duk da wannan jihadin da Nana tai, kwana tai tana kuka, saboda tausayin kanta da kuma tsananin kishin Sadik da ya addabi zuciyarta.

Farhan kwana biyu taji wani iri, saboda sam ta dena ganin gilmawar Sadik, gashi haka kurum idan ta tuna wai kuɗin Aurenta Abbas ze kawo, se gabanta ya tsananta bugawa.



Seda Sadik ya kwa huɗu a Asibiti sannan aka sallamo shi, bayan hawan jini har da ulcer da typhoid suka kama shi, likita ya kakkafa wa Sadik dokoki, sannan aka sallami Sadik.

Mutane suka dinga zuwa duba Sadik, tsawon kwanakin nan sau biyu aka bari Nna taje ta ga Sadik, saboda koke koke take idan ta ganshi, yau tun da ya dawo ta shigo tai masa sannu ta koma gefe, Sadik se binta yake da ido, yana son yai mata magana, amma baya son yin Magana saboda hakin da yake yi.

Nana ta tausayawa Sadik yadda ya kamu da wannan ciwon, da ƙanan shekaru haka, sedai ƙasan zuciyarta ta kan ji haushin sa idan ta tuna, Aure zeyi tai sharing ɗin sa da Wata, wani irin kishi ya dinga taso mata.

Da dare yai BQ tai tafiyarta ta bar shi a nan ɗakinsa na cikin gida, yana son ta zauna a kusa da shi, amma sam taƙi kula shi, ko Sahal ta hana shi, duk da yadda yaron yake ta koke koken yana son yaje gurin Sadik, amma ta hana shi ta wayance da ai Sadik ba shi da lafiya.

Abun mamaki har su Abba sun kwanta, se ga waya daga ƙauye, hankalin Abba ya tashi sosai da sosai, ya ɗaga wayar jikinsa na rawa Mother kuma tai masa ƙuri da ido, tana jiran jin dalilin kiran.

Muryar Hakimi yaji yai masa sallama, Abba yai ajiyar zuciya yace "Alhaji da kan ka?".

Hakimi yace "eh da kai na bawan Allah, nace ya batun maganar da mu ka ne? An tambayowa Yaron nan Auren?"

Abba yace "Alhaji ai Sadik ɗin ma ba lafiya, yau muka dawo daga Asibiti".

Hakimi yace "Subhanallah, kuma ba ku faɗa ba? Ya jikin nasa?".

"Jiki yayi sauƙi, an sallamo shi ma".

"To Allah ya bashi lafiya, dan Allah Abdullahi ba na son in mutu ban cikawa Yaron nan alƙawarin sa ba, yai min halacci yana riƙe da abar ƙaunata, ba cin mutunci ba wulaƙanci, nima dan Allah ina roƙon ku bari ya auri wadda yake so, kar in zama tsohon banza, kar ku duba ƙanƙantarsa, Addini be hana masa ba, kuma kai Allah yai maka arzikin da zaka tallafa masa ya riƙe su".

Abba yace "to shikenan Alhaji, za'ai yadda kace insha Allah".

Alhaji yace "to madalla, ai masa sannu a gaidamin Nana da abokina, ace ina son su sosai, A cewa Sadik ga amanar abar ƙaunata nan, a kulamin da marainiyar Allah"

"To ranka ya daɗe insha Allah zan gaya musu".

Su kai sallama Abba yai shiru yana sake jinjina lamarin.



Sadik ya warke ras, sedai jikinsa babu wani ƙwarin kirki, hankalinsa yana kan Nana sosai, da yadda ze yaje ya ga Farhan.

Yau a bedroom ɗinsu ya tarar da Nana, ya zauna a kusa da ita, kallo ɗaya tai masa ta cigaba da danna wayarta.

Karɓe wayar yai, ya ɗan tsura mata ido sannan yace "haryanzu fushi kike da ni ko Nana?"

"Akan me zan fushi da kai kuma?"

"Ba gashi ba, tun da na dawo bata sauya zani ba, sam bana gabanki"

Nana tace "A'a, meye nawa na cigaba da shishshigi kuma, ai na sadsƙar, ni yanzu zaman ɗana zan yi kawai".

"Nana me zan gaya miki wanda ze sa ki yarda da ni?".

"Ka ga Please, haryanzu ba ka da lafiya, kar kaje ka kuma sumewa, in dai nice kaje kai Aurenka ka dena faɗuwa kana suma saboda soyayya".

Shiru yai yana cigaba da binta da ido, se ƙoƙarin mai da hawaye take kar su zubo, kishinta ƙarara ya kasa ɓoyuwa.

"Ni me laifi ne a gareki, ba zan fasa baki haƙuri ba, amma ina sonki Nana ba zan taɓa wulaƙanta ki ba".

"Dan girman Allah ka dena gayamin kalmar nan, ƙona min zuciya kake, ka dena yaudarata da kana sona, bana son ji dan Allah" ta ƙarasa maganar hawayen da take riƙewa suna zubowa.

Jiki a sanyaye ya tashi ya bar mata ɗakin, ya fita ya ɗau mota ya bar gidan.

A ƙofar gidansu Farhan ya ja ya tsaya, yana ta waige waige, yana son ya samu wanda ze aika ya kira masa ita.

Kawai ya hango ta tana ƙoƙarin shiga gida, hannunta riƙe da leda "'yan mata daga ina"? Yai maganar cikin sanyin murya.

Se da gaban Farhan ya faɗi, yadda Sadik yai duhu ga rama, alamu suka Bayyana ba shi da lafiya.

Hararsa tai zata wuce, amma ƙasan zuciyarta ji taka tamkar cikin shagwaɓa ta tambayi meya same shi haka.

Ledar hannunta ya ƙurwa ido, tana ƙoƙarin wuce shi ya fizge ledar hannunta, ya buɗe maganin tari ne da wasu ƙwayoyi a ciki, se da kan Sadik ya sara yace "Farhan, yanzu kuma meye damuwarki da zaki sha wani abu?"

"Ka aikeni ne? Bani ledata in wuce".

"Ba zan bayar ba, Wallahi ka fita daga sabgata na gaya maka".

"Ba zan fita ba, ki kiyayeni Farhan ki bar ganin ina lallaɓa ki, Farhan meye daɗi a cikin wannan shaye shayen da kike?"

Farhan na ɗaga kai ta ga motar Abbas na shigowa, ta ɗaya ɓangaren kuma Abba ne ke tunkaro gida shima.

Kasa motsawa Farhan tai daga in da take, se tsananin bugawa da ƙirjinta yake.

"Ke Farhan, ban hanaki tsayuwa da wannan yaron ba?" Abba ya fara magana tun kan ya ƙarasa.

Kasa Magana tai, Abba ya ƙaraso ya dinga faɗa ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, kamar ze ari baki, daga Sadik har Farhan aka rasa me motsawa.
Abbas kam zama yai yaƙi fitowa daga cikin motar.

Abba ya cigaba da sababi, "ke banda shashanci me zaki da wannan yaron? Ina Hankali ya gama ratsa shi? Wuce ki bar nan kan in saɓa miki, kai kuma zan maka kashedi na ƙarshe, kar in sake ganinka a ƙofar gidana, ko ta rasa mijin Aure ba zan taɓa aura mata mutumin kawai irinka ba, dan haka ka ƙyalemin yarinya tai Aure na karɓi kuɗin Aurenta bana son shirirta da RUƊIN ƘURUCIYA".

Huzaifa yana tsaye a soron gidan su Farhan yana jin komai, ya jinjina kai a ransa  yace "wannan ne Sadik ɗin kenan? Idan kuwa hakane Abba yana shirin sake tafka kuskure dan haryanzu Farhan tana son Sadik'.

Farhan ko lura da Huzaifa ba tai ba, ta wuce cikin gida ranta a ɓace ba tare da ta san dalilin ɓacin ran ba.

Se da Abba ya gama faɗansa, Sannan Sadik ya juya, yana jin wani irin jiri ya nufi motarsa, kasa buɗewa yai ya jingina da jikin motar tare da dafe kansa.
Dafa shi yaji anyi ance "ɗan uwa ya dai?"

Sadik ya ɗago ya kalli Huzaifa yace "bakomai".

"Naga ka dafe kanka"

Sadik yace "No bani da lafiya ne, kaina yana min ciwo, amma magunguna na suna mota zan sha insha Allah, nagode sosai".

Yace "idan ba zaka iya tuƙin ba, ka jira ka samu sauƙi"

Sadik yace "No, zan iya nagode sosai".

Haka Huzaifa ya koma cikin gidan su Farhan, sedai abun mamaki ya tarar Abba ya cigaba da sababi a tsakar gida, da ya leƙa ɗakin Farhan kuwa, hangota yai ta dunƙule guri ɗaya tana kuka.

Huzaifa a ransa yace "Akwai damuwa, na rasa dalilin da yasa iyayenmu ke yanke hukunci da zuciyar su, maimakon ƙwaƙwalwa.

Duk abun nan da ya faru, akan idon Abbas ya faru, a hankali ya ja motarsa yai baya, kan Sadik ya rarako tasa motar ya zo ya buga masa, dan ya lura yaron RUƊIN ƘURUCIYA na damunsa.




Abba me ya tsare Sadik a bakin ƙofar shiga falo yace "daga ina kake?".

Sadik yace "Naje shan iska ne?"

Abba ya girgiza kai yace "Kafin ka mace mana saboda soyayya, ka gayawa yarinyar zamu zo nema maka izinin Aurenta.

Murmushi ne ya bayyana a fuskar Sadik, sedai lokaci ɗaya murmushin ya ɗauke, bayan tuna furucin Abban Farhan, da kuma Nana da ke bayan Abba, tana son su gama Magana ta wuce, da alama Abba be san tana tsaye a gurin ba, aikuwa maganar Abba ta soki zuciyar ta, take idanunta su kai ja, ta juya cikin hanzari ba tare da Abban ya ganta ba.

"Magana nake maka, amma ka tsaya kana kallona".

Sadik yace "to Abba, nagode sosai Allah ya ƙara girma".

Abba bece komai ba yai gaba abunsa.

Sedai Sadik ya rasa ƙwarin gwiwar da ze tunkari Nana, Wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa.


Nana yadda ta ga rana haka ta ga dare, saboda yadda zuciyar ta ke mata wani irin zafi, ta rasa in ds zata saka ranta taji daɗi, haka ta kwana sirr ba bacci, se nafilfili da adduoin da dinga yi, Akan Allah ya yaye mata son Sadik, da wannan kishin nasa da ke damunta.
Washegari da Sassafe Mother ta ƙwanƙwasawa Nana ƙofar ɗaki, da yake a cikin gida ta kwana yau, tace wa Nana ta shirya zasu tafi ƙauye.

Abun ya bawa Nana mamaki ƙwarai, ta tambayi Mother dalili amma Mother tace mata, Hakimi ne yake son ganinsu.

Abun mamaki daga Mother se Nana, se Jidda, har da Mummyn Khairat suka tafi a mota ɗaya, Su Abba wai tun Asuba suka tafi.

Nana tai jigumm ba tare da sanin meke damunta ba, Sahal ma kasa riƙe shi tai, se Mummyn Khairat ce ta karɓe shi, haka suka tafi ba wanda yakewa wani magana.

Sam Nana ta dena ji ta dena gani na wucin gadi, ta dena gane komai se tsintar kanta tai a cikin turakar Hakimi bisa jagorancin Mother, tana zuwa ta tarar da gawa, ga Inna da Abba, ga Sadik har da Faruk, sun kewaye gawar idanunsu sunyi jawurr.

Jiki na rawa ta ƙarasa, ba tare da wani ya dakatar da ita ba, ta ɗaga bargon da aka lulluɓe Hakimi, tai tozali da kyakywar fuskar Hakimi, cike da haiba da kamala kamar tace 'tashi Kyakywan kakana, kamar yadda ta kanyi, in ta so tsokanar sa❗❗❗
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680




AFUWAN BA EDITING.










Jikin Nana ne ya ɗau rawa kamar zata fita daga hayyacinta, ta nemi guri ta zauna daɓas, idanunta sukai jawur.

Can cikin ƙaraji Nana tace "Inna, dan girman Allah ki tasheni daga baccin nan da nakeyi, ki cemin mafarki nake ba Alhaji ne ya mutu ba, dan Allah ki tasheni dan girman Allah".

Usman yace "Nana se haƙuri,ki sassauta muryarki, dama duk me rai mamaci ne, kiyi haƙuri ki yi masa Addu'a".

"Ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login