Showing 243001 words to 246000 words out of 259198 words

Chapter 82 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13307

Magana ya koma makaranta shima"

Mother tace "ni ƙyaleni da batun mijin nan naki, daɗi Aure ya zauna yai tayi, kar Allah ya sa ya koma makarantar, ni na zuba masa ido yaje yai abunda yaga dama"

"Dan Allah Mother karki ce haka, Yakamata ya cigaba da makarantar ss"

Mother tace "kunfi kusa, kema zaki iya gaya masa ai, Khairat kawo mata abinci ta ci"

Gaba ɗaya Khairat haushin Nana take ji, yanzu haka ji tai kamar ta cewa Mother ba zata zubo mata Abincin ba.

"Mother, Sahal yau yai kukan kuwa?"

Mother tace "ɗan ƙaniya, yayi amma ba sosai ba, Dr. ne ya tafi da shi, be daɗe da dawo da shi yai bacci ba"

Nana tace "to shikenan, tun da bacci yake, nima naje in ɗan kwanta".



"Ɗan uwa, wai tunda aka kawo kuɗin yarinyar nan na zata zaka zo, a tattauana yadda al'amarin ze gudana amma na jika shiru"

Abba yace "dan me ba zaka jini shiru ba, ni ka nemeni ne? Ko da kuka tashi yanke hukuncin ku ni nemana kukayi, kawai inji labarin wai kuɗin wannan yaron ka karɓar mata"

Malam Zakari yace "A'a, shi Abbas ɗin be zo ya sameka bane?"

"Ni ba wanda ya zo ya sameni"

Malam Zakari yace "to ai Abbas ɗin har gidan nan ya zo, yace min ya janyewa shi wancan yaro, kuma yai min bayani na gamsu"

Abba yace "kamsr yaya, kaga yaron kuwa? Yaro ne fa ƙarami sosai"

"To Addini ya hana ne? Na ga yaron har gidan da nake yaje, na ganshi, Abbas ya tabattar min da tana son yaron nan, kuma shima yaron yana sonta.
Ɗan uwa a karon farko kasan laifinka ne da na matarka ya ingiza yarinyar nan shiga wannan halin, a dalilin Yaron nan ta faɗa mawuyacin hali kuma ya dawo yace yana sonta a haka, addini be haramta auren nan ba, meyasa kake son kai ka haramta, mahaifinsa sanannane ne mutumin kirki, kuma duk da mutum ne me kuɗi, cikin girmamawa da mutunci suka kawo kuɗin nan, ita kanta Farhan ban tsaya bi takanta ba na karɓi kuɗin, shi wannan likita yace idan aka tsaya biye ta tata za tsce ba ta so ne, amma kuma ƙasan ta shi take so.
Zamanin iyayenmu har a shekara sha bakwai anwa ɗa Aure kuma ya zauna, addinin mu be haramta ba, dan haka ai musu addu'a kawai, kayi haƙuri ta ta ƙaddarar kenan".

Abba yai ajiyar zuciya yace "shikenan ɗan uwa, Allah ya basu zaman lafiya"

Malam Zakari ya amsa da Ameen.





Sadik yaji daɗin dawowar Faruk sosai da sosai, a wannan karon ma Khairat se ƙoƙarin yiwa Faruk ɗin bajinta take, amma shi sam be ɗau hakan a matsayin wani abu na musamman ba.
Dama da yazo jana'izar Hakimi, kwanan sa uku a ƙauye, ya koma in da yake karatu kasancewar exams zasu fara, dan haka Wannan karon da ya dawo, ɗakin Sadik Na cikin gida ya koma, kasancewar su Nana suna BQ.

Sadik yana tare da Faruk suna hira, Faruk yace "Man, gaskiya kayi ganganci Sadik, ka duba yadda ake ji da kai a gidan nan, amma kowa ya watsar da kai saboda abunda ka ɗakko, guda nawa kake da har zaka ɗorwa kanka wani ƙarin Aure, Auren ma na yarinya mara ɗa'a, dan Allah me Maman Sahal ta rage ka da shi?"

Sadik ya nisa sannan yace "Bro, kowa yaƙi fahimta ta amma ina sa ran, kai ka fahimceni" ya ɗakko wayarsa ya nunawa Faruk hoton Farhan yace "ka gane wannan yarinyar?"

Faruk ya ɗanyi shiru sannan yace "nasan fuskar nan amma na manta in da na santa"

Sadik yace "2yrs back, ita ce yarinyar da na ɗorawa raina cewar Lallai sena Aureta, na dinga cewa Aure nake so kana cemin RUƊIN ƘURUCIYA ne, itace yarinya ta farko da na fara so a rayuwata, ka san meya ja hankali na ta burgeni na fara sonta? Tsananin kamun kai da tarbiyyar ta, da karatun addini.
Tun yarinyar nan tana guduna, se da ta fara yadda da ni, soyayya me ƙarfin gaske ta shiga tsakaninmu, zanniya cewa ƙaddarar haihuwar Sahal ce ta gifta Hakimi ya Auramin Nana, a lokacin da gaba ɗaya aka shafe tunanin Farhan a zuciyata na manta da ita, cikin ikon Allah Maman Sahal ta zo da gagarumin sauyi a rayuwata, kuma ta zame min wani kyakkyawan bago da na jingina a jiki.
Duk abunda Farhan tai na lalacewa, nine sila Faruk, Yarinya ce me tarbiyya duk a sanadina komai ya sameta, yanzu idan na gujeta na ƙi Aurenta naiwa kaina adalci? Nima fa yanzu na zama uba, na fara tara iyali, ba zan so aiwa ɗana abunda naiwa Farhan ba, duk da shi Allah ba'a masa wayo.
Amma su Mother sunƙi su saurareni balle su ji uzurina, a tunaninsu son zuciya ne kawai yasa nake son ƙara Auren nan, amma hatta jumping class da nai, duk cikin planing ɗina ne na in auri Farhan, ina matuƙar sonta she's my first Love, gashi Husna kanta yanzu haushina take ji, ta dena shiga sabgata wanda hakan shima ba ƙaramin damuna yake ba, duk da nasan kishi ke damunta, amma ba zan hanata kishi a kaina ba, saboda koma mene laifina ne na shammaceta ban taɓa nuna mata nai soyayya da wata ba, wanda nima ba laifina bane, yadda nake ɗin nan fa nake Magana ina kan maganin hawan jini ne fa haryanzu, na rasa in da zan saka kaina"
Faruk yai ajiyar zuciya yace "ni na fuskance ka Sadik, zan cigaba da tayaka da addu'a Allah ya kawo komai cikin sauƙi"

Sadik ya amsa da Ameen.


Unguwar su Farhan ta ɗauka, an kai mata kuɗin Aure, dubu ɗari amma an rasa waye mijin, an bi diddigi an tarar ba Abbas bane, lallai tayi goshi saɓanin lokacin da Sunusi ya kai mata dubu Ashirin da biyar, sam Abbas ya ɗauke ƙafarsa, dan baya son ya cigaba da zuwa, su samu Matsala da Sadik, dan haka daga gefe ya cigaba da yi mata fatan alkhairi, tare da rarrashinta ta waya, wanda shima daurewa kawai yake yi, amma har ga Allah yana ƙaunar Farhan dagaske ba wasa ba.
Sadik kuwa in dai yazo wataran taƙi fitowa, ko ta fito suyi faɗa ya tafi, wanda hakan shima ya sa ya dena zuwa, hakan yasa 'yan unguwar ba su san waye ya kaiwa Farhan kuɗin ba, dan an dena ganin kowa yana zuwa in da take.
Da Sunusi ya samu labari kuwa ji yake kamar yai hauka, dan be taɓa tunanin wani ze fito haka ya iya yunƙurin Auren Farhan ba, yai iya yinsa amma be gano waye ba, dan sam be kawo Sadik ba, saboda a ganinsa yarone waze bashi Auren 'ya?.




Sosai aka gyara gidan da Sadik ze zauna, wanda ba shi da wani nisa sosai daga gidan su Sadik, gidan yayi kyau sosai da sosai, Sadik shikaɗai yake fafutukar shirin Aurensa, se Anty Jidda da ya kan tambaya wasu abubuwan se ɗan uwa Faruk, duk da har ga Allah daga Faruk har Anty Jidda Nana suke yi suma, amma Sadik abun a tausaya masa ne shima.

A gidan dr. Ya haɗa lefensa cif, Abba yai Maganar ze saiwa Nana furnitures, Sadik yace Abba ya bari shi ya sai mata, tunda kayan lefenta suna nan ba abunda ta taɓa, base yai mata kayan faɗar kishiya ba se yai mata furnitures, amma Abba yace basa buƙatar kayansa.

Abubuwa har mamaki suke bawa Nana yadda Mother ta sauya, dan ita ta sai mata komai na kayan kitchen, duk abunda uwa za taiwa 'ya, Mother ta saiwa Nana shi, dan dama bata da 'ya mace, bata taɓa Auren 'ya ba, dan haka ta kashewa Nana kuɗi sosai, aka zuba a sashin Nana da ke sabon gidan da zasu zauna.

Gashi musamman Mother ta biya kuɗi aka ɗakko me gyaran jiki, take gyara Nana, wanda ko da aurenta ba wanda yai mata wannan haka nan zallarta aka bawa Sadik (lolz🤣).


Gidansu Farhan na ta shiri, ita kuwa sam ta rasa farinciki take ji ko haushin wannan Auren take, dan sam ba ta farinciki ji take tayi butulci na gaske na ƙin Auren Abbas, musamman idan ta tuna irin ɗawainiyar da shi da mahaifiyarsa suka dinga yi da ita.



"Amm dama nace, dan Allah ina son zuwa ƙauye, ko sati ɗaya muyi".

"Se yanzu da buƙatar kanki ta taso kika tuna dani Husna?" Banza Nana tai masa tana tura baki.

"Gaba ɗaya kin mai da ni hoto ba ruwanki dani, anya rayuwa za ta tafi a haka? Dan kawai nace zan aure shikenan kika watsar da ni"

"Dan Allah ni a bar wannan zancen, bana so"

Sadik yace "wane zancen?"

"Zancen Aurenka ni bana so".

"To na dena" ya bata amsa.

"To ka barni?" Tai maganar idonta fal hawaye.

Wata irin kewarta ce ke fuzgarshi, shi kansa ya san yayi dauriya, dan rabonsa da ita har ya manta.

"Uhmm kayi magana mana" tai maganar a shagwaɓe.

Rungumota yai cikin bazata yana kissing ɗin ta.

"Wayyo Allah na, Mother" da sauri Sadik ya cikata yace "Besty meye haka kamar wata ƙaramar yarinya?"
Yadda take tura baki tana hararsa ne, ya ga ta koma yarinyarta sosai, ya ɗan lumshe idonsa yace "kinyi kyau sosai, nai missing ɗinki zo kiji"

Noƙe kafaɗa tai tana share hawaye, yace "Shikenan, dan Allah goge hawayen, idan Mutan gidan nan sukaga kina hawaye se su rufeni da duka yadda suke jin haushin nan nawa, jeki Allah ya kaiku lafiya".

A ciki ta amsa Ameen ɗin, tai waje ita kanta tai missing ɗin Sadik, amma tsabar yarinta, taurin rai da baƙin kishi yasa Nana ba ta jin hakan da take a matsayin wani laifi.



Tun da Hakimi ya rasu Nana ba ta sake zuwa ƙauye ba yau, tai murna sosai da ganin Inna, amma tana kallon turakar Hakimi se kuka, Inna tai ta mata nasiha akan ta de na yi masa kuka Addu'a za tai masa.

A yanayin bugun cikin Nana da Inna tai, ta fuskanci sam Nana bata shiga shirgin Sadik, haryanzu Nana tana fama da tarin ƙuruciya da wauta.

Inna ta zauna ta dinga yi mata nasiha da hatsarin de na shiga sabgar Sadik da tai har take bata misali da "da uwar mijinki ai bata ƙaunarki, amma sannu a hankali da ki kai haƙuri ba gashi komai ya wuce ba, har siyayya tai miki kamar 'ya da uwa ba? To komai na rayuwa haƙuri ake me wucewa ne. Kuma tun da sabon Aure yai zakiga abunda ba kya so, amma ni daure ki ɗauke kai ki kwantar da hankalinki, komai ze wuce bance ki saki jiki a wulaƙanta ki ba, ki kama mutuncinki amma karki wulaƙanta mijinki, yana ƙaunarki sosai".
Nana dai tai shiru tana sauraren Inna, amma tana jinjina lamarin dan babu sauƙi sam.




Yau da Sadik yaje gidansu Farhan, Abba na nan dan haka dolenta ta fito, suna tsaye yana ta Magana tai banza da shi, sega wata danƙareriyar mota, Wannan mutumin da suka taɓa Faɗa da Sadik akan Farhan ne ya fito, a fusace ya tunkaro su yana zuwa ya kalli Farhan yace "mayaudariya munafuka, nai nai ki Aureni kika ƙi, amma naji labarin wai zaki Aure, bayan kin gama sawa na kashe miki kuɗi, to ki tattaro duk abunda kika san na baki, na kashe miki ki dawon da abina".

Sadik yai caraf yace "An cinye ƙarfi ya ƙwata, kaje ka kai duk in da zaka kai, lokacin da kake bata kunyi a rubuce cewar zata Aureka dan haka zaka kashe mata kuɗi? Ko kuma ita ta roƙe ka? Dan haka ka saurara, kaje ka kai in da kaga za'a ƙwatar maka"

A fusace yace "kai ka kiyayeni,kar ka min rashin kunya"

"Anyi maka rashin Kunyar, kaje ka kai in da duk zaka kai"
Haka Mutumin nan ya ƙaraci borin kunyarsa ya tafi, Sadik ya sanarwa da Farhan cewar saura kwana uku su kawo lefe.

Ko da aka kai kayan lefen nan duk da gidansu Huzaifa aka kai kayan, unguwar su Farhan ta ɗauka, aka dinga zuwa kallo, Akwatuna Bakwai ne na gaske masu kyan gaske, kayanta 'yan cif se tsada, har da gwal biyu a ciki, kayanta manyan kaya sosai da sosai, da babban buhun shinkafa.

Akace se yanzu a kaiwa Farhan lefe, ba kayan Sunusi ba Akwati biyu har da hodar nan irinsu Aisha tsamiya a ciki.

Nana bata dawo ba se satin biki, shima Mother ce tai waya tace Lallai ta dawo.


Mutane nata surutun Faruk ko Auren fari be ba, amma an bar Sadik se Aure aure yake.

Nana kawai yaƙe take, amma ƙasan zuciyarta daurewa kawai take, ana gobe za'a fara biki Sadik ya tarar da Nana a ɗakin Mother, fatar jikinta har wani sheƙi take, gashin kanta an gyara shi an masa ƙananan kitso, ta sha lalle ja da baƙi, tai shar Kamar ba ita ba se ƙamshi take.

"Madam ina Mother?"

Ba tare da ta kalleshi ba tace "tana gurin Abba"

"Sahal fa?"

"Yana gurin babansa"

Sadik yace "wane baban nasa?"

"To shi da yake da iyaye da yawa, yana gurin Uncle Faruk"

Sadik ya ƙara so kusa da ita ya zauna yace "You look young and beautiful, kamar in sace ki in gudu, dan Allah Nana ki dawo part ɗinmu mu kwana tare"

"Kana ganin gidan cike da mutane, Mother faɗa za tai min"

"Allah ba abunda za tace miki, Please Besty"

Kasa jurewa tai ta fara kuka, kuka sosai da hawaye saboda abun ya motsa.

"Besty kuka kuma? Na miki laifi amma kamar yadda na gaya miki Ina sonki Husna, ba zan taɓa wulaƙanta ki dan na Auri Farhan ba, dan Allah ki dena kukan nan se in zaci wani abun daban" ya rungumeta yana share mata hawaye tare da kwantar mata da hankali.

"Kina buƙatar wani abu ne?"
Nana ta girgiza masa kai.

"Dan Allah ki min alfarma ki dena wannan kukan"

"In ban kukan ba wani abu ne yake tsayamin a wuyana yaƙi tafiya"

Sadik yace "Yasalam, na san ba daɗi amma ki dena dan Allah".

"To zan dena insha Allah"

Ya ɗanyi ƙasa da murya yace "to yaya, zaki rakani BQ ɗin?"

"Mother za tai min faɗa Wallahi"

"To shikenan, kayan da Abba ya sai miki sunyi kyau sosai, bari in nuna miki"

"A'a ka bari in muka tare na gani"

"To shikenan, dan Allah Besty ki tayani basu haƙuri nasan suna fushi da ni, naga yanzu kece 'yar gaban goshi"

Nana tace "to ai Inna tace ze wuce, na gayamata ta yiwa Abba Magana ma"

"Akan suna fushi da ni ko?"

Ta jinjina masa kai.

Yace "Allah Sarki Besty na, You will remain my Besty forever inshallah, i will not fail you" yai maganar yana shafa hannunta.

Maganar Mother ya jiyo, hakan yasa Sadik cikin azama ya tashi, Mother ta shigo tana masa kallon tuhuma.

"Dan ubanka me kai mata?"

Sadik yace "Wallahi Mother ban mata komai ba".

"Ƙarya kake yi, me yai miki?"

Nana tace "bakomai"

"To fita ka bar min ɗaki"
Bayan fitar Sadik Mother tace "idan kika kuskura kika yadda da shi, kan ku tare a gidanku ni da kene, ba ya zo yana kashe miki murya ba"

Nana tai shiru cike da jin nauyin Mother.
  Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680








Farhan jin abubuwan take tamkar a mafarki, wai ita ke shirin Auren Sadik abun Kamar almara.

Dangin Babar Umma se cewa suke Allah ya musanya mata me arziki, akan kayan tsiyar da Sunusi ya kawo mata.


A wannan karon Umma anyi abun arziki, dan cikin tsananin kunya, ta sa aka samo mata wata da take gyarawa Farhan jiki, a wannan karon ma ɗaya gyaran Hajiya ce ta ɗauki ragamar gyara Farhan ɗin, tai shar da ita kamar ba ita ba.

Ta sha gyaran gashi da ƙunshi, sedai haryanzu Farhan gani take kamar a mafarki, wai zata auri Sadik, sedai ta kasa farinciki, musamman idan ta tuna irin ɗawainiyar da Abbas yai da ita, kuma ga mahaifiyarsa tana ta cigaba da yi mata ƙoƙari.



Sadik na zaune ya shiga social media, ya ga hotunansa nata trending, wai ɗan Auta  gidan Alhaji Abdullahi Rano, ze auri mata ta biyu yana da shekaru Ashirin a duniya, nan ya dinga ganin Comments kala kala, wasu suna cewa iyayen da suke ba shi yaran ne mahaukata, wasu suce tunda iyayensu ɓarayin ƙasa ne, dole suyi abund suka ga dama, nan ba da daɗewa ba ze sake su a aura masa wasu, haka dai kowa da kalar abunda yake faɗa, wani na alkhairi wani na sharri, Sadik ya rufe datarsa yace "Insha Allah, Allah baze bamu kunya ba".

A wannan karon ma Abbas da kansa ya kaiwa Farhan dubu hamsin, ta kasa masa godiya se kuka, kamar wadda a kaiwa mutuwa, yai ta bata haƙuri yana kwantar mata da hankali tare da yi mata Nasiha.

Babban abunda yake sake faɗarwa da Farhan gaba be wuce yadda ba zata kai mutuncinta gidan Sadik ba, ta san abu ne mawuyaci duk da son da Sadik hake mata tai mutunci a idonsa, saboda budurcin mace shine 'yan cinta a gidan miji, ga shi tana da abokiyar zama, tabbas ta san akwai damuwa a wannan lamari, gaba ɗaya jikinta ya ƙara sanyi sosai da sosai.

Sadik ba yadda be da Farhan ba akan ya kama mata guri, tai walima tace ba ta so, a layinsu a ka kafa runfuna aka kira malamai mata sukai lecture, akai mata kamu aka ci Abinci aka sha daidai gwargwado.

Duk yadda Nana ta so dakewa kasawa take yi, dauriya kawai take tana sabgoginta, amma abun yana dukanta sosai da sosai, gashi Sadik se kujiba kujibarsa yake yi, ko ganinsa ba ta samun yi sosai, sedai ta hange shi.

Faruk na zaune a falo yanawaa Sahal wasa, Khairat ta zo tana yauƙi ta ɗan kashe murya tace "Man a kawo coffee ne?"

Faruk yace "No thank you"

Nana da ke gefe tace "gaskiya Uncle ka yunƙura, zan tsaya maka bana son ganinka a haka ba Aure, karka fara tsufa fa"

Faruk yai murmushi yace "kedai bari kawai, ni da ban wani damu in Auren nan ba, amma tun da Allah ya sa aka haifi Sahal, na samu abun wasa, naji nima ina son in auren, a haifamin abun wasa ko Abbana" yai maganar yana ɗaga Sahal sama.

Nana tace "gaskiya uncle ka motsa".

"To maman Sahal, amma kin san matan ne se a hankali, samun tagarin ne se a slow".

Su Nana ba rufi se cewa tai, "Ba wani se a slow, ga mata a gida se ka tafi dawa, naga ga Khairat nan tana ƙwanƙwasa, dan Allah ka bada dama a wuce gurin".

Shi kansa Faruk se yaji kunya, balle Khairat da Nana ta farkewa laya haka ba rufi, Khairat taji kamar ƙasa ta tsage ta nutse.

Nana tace "ya naji kun wani yi shiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login