Showing 168001 words to 171000 words out of 259198 words
Chapter 57 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
a kowane lokaci ze iya dawowa gareta, ko ta yi niyyar cire shi daga zuriyar ta, ko ta ji haushinsa se ta ji ta ka sa, se taji yakamata tai masa uzuri kan ta yanke masa hukunci, kullum Addu'ar ta Allah ya dawo da Sadik cikin Rayuwar ta.
Iyayen Sunusi sun aiko wai Ranar juma'a zasu kawo kayan lefe, duk unguwa ta ɗauka Sunusi ze auri Farhan.
Wasu suna ganin an ƙwareta, wasu kuma suna ganin ze temaka mata ne, tunda ba wanda a unguwar ba shi da labarin an kamata ita da Abbas a gidan Hajiyar sa, Kamar yadda akai ta yaya tawa a unguwar.
"Ke! Ke! Wai ba zaki tashi bane?"
A hankali Nana ta motsa tai miƙa, tare da buɗe idonta tana ɗan tura baki.
"Dalla ta shi" Sadik yai maganar yana kallon ta.
Ta tashi zaune sannan tace "dan Allah ka dena ce min ke, ni bana so"
"Zaki tashi ki barmin ɗaki, ko sena ɓaɓɓala ki na bawa karnuka".
Ta tura baki tace "wallahi na fi ƙarfin karnuka su cinye ni. Yawwa nace me zanci da safen nan ne, wallahi jiya da yunwa na kwana"
"Se ki ci kan ki ai, ba uwar da ki ka iya dafawa, sedai nike nan cikin yawon nemo miki abunda zaki ci, har ki na gayan magana"
Nana tace "To akan me zan kuma garajen shiga wannan Kitchen ɗin in ci wani abu, bayan ranar ka ce min nonon karya na sha, har yanzu istigfari nake Allah ya yafe min. kuma ni ban iya amfani da wannan kayan da suke a Kitchen ɗin ba"
Sadik yace "tashi muje Kitchen ɗin"
Nana ta miƙe ta bi shi, suka shiga nan ya dinga nuna mata komai da amfanin sa, ya nuna mata in da kayan Abinci suke.
Nana tace "ikon Allah shinkafa a kwali, ni na saba ganinta a buhu, ban taɓa zaton zan ganta a kwali ba, har su wake duk a kwali Lallai cigaba"
Sadik dai be kulata ba ya nuna mata yadda za tai amfani da gas cooker.
Nana tace ita Allah karta tsoron wannan abun take ji, kar yai bindiga da ita, sedai a san yadda za'ai a samo mata murhu, ko risho.
Sadik Kamar ya ɗora hannu a ka yai ihu, idan yai gabas se tai yamma, duk da ta ɗan waye amma haryanzu da ƙauyanci a kanta, wanda Sadik ya fi dangant hakan da hauka.
Ƙarshe Sadik ne ya kunna gas ɗin, Suka dafa tea, suka fere dankali su ka soya, kai kaca kaca da Kitchen ɗin, suna yi suna faɗa, Nana rashin kunya shi kuma masifa.
Suka gama, suka dawo falo su karya, Sadik ya ɗakko ketchop ze ci dankali da shi, Nana tace ita ma ya samata ta ci da shi, yace mata jinin alade ne, in zata iya ci kuma shikenan.
Lilly ta ɗan ƙurawa Farhan ido, kullum jiya i yau, kullum rama take da tunani.
Lilly ta kalli Haseena tace "Hassyy, dan Allah ki bani lambar Khairat ɗin nan mana, sister ɗin Sadik"
"Me zaki da ita?"
"Se kin tambayeni, abu ne me mahimmancin gaske"
Haseena tace "gaskiya ba zan bayar ba, se kin gayamin me zaki da ita"
"Ke riƙe ki cinye in Abinci ce" Lilly ta faɗa a fusace.
Haseena tace "sorry masoyiya, ai bama haka bari in baki lambar"
Ta bawa Lilly lambar Khairat.
Dama Lilly so take ta kira Khairat, a gaban Farhan in da hali ta taimaka ta basu lambar Sadik ta ƙasar waje, sedai Farhan ba ta gurin zamanta.
Library ta tafi, dan mafi akasari yanzu nan ne gurin zaman Farhan.
Aikuwa tai sa'a ta tarar da Farhan a Library, sedai idanunta sunyi wani irin ja, kamar wuta ta ƙurawa guri ɗaya ido.
Lilly tace "Farhan, ga lambar ƙanwar Sadik Khairat, na karɓo se mu kirata"
"No need" Farhan ta faɗa a hankali.
"Meyasa zaki ce haka? Ai yakamata kiji a wani babin ya ajiyeki, dakon soyayya wahala ce Farhan"
"No need! Soyayya ta da Sadik RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai, an sha gayamin ban yadda ba, duk Makaranta ta ɗauka he got married to his cousin"
"Waye ya gaya miki wannan maganar, ta yaya Sadik ze yi Aure a wannan ƙananan shekarun?"
"Is possible, har nan Abokinsa ya zo ya gayamin, ya haɗu da yayansa yau a airport, yaje raka babansa, Yayan Sadik ne ya tabbatar da hakan, am fool da na tsaya na yadda da maganganun Sadik da ya dinga furta su, ni kuma RUƊIN ƘURUCIYA ya ɗebe ni na amince da shi, am Stupid, am more than fool, am idiot!"
Cikin ɗaga murya take Maganar, dan ma Library ɗin ba kowa, jikinta na tsuma ta fice daga Library ɗin.
Ba a tashi ba, amma Farhan ta tafi gida, idonta ya bushe babu hawaye, ƙoƙari take ta ga ko zata iya samawa Sunusi matsuguni a zuciyar ta, dan ta cire Sadik amma ina, Sadik ya mamaye ko ina, ya mu'amalance ta da kyakykyawar mu'amala a lokacin da ta rasa wanda zata raɓa.
Gidansu babu kowa, Umma ba ta nan suna ta shirye-shirye, ta tafi kasuwa, kuma a yau ne za'a saka ranar Aurenta, wanda baze fi sati biyu ba.
Wata irin wuta ce ta ke cin zuciyarta, ta rasa me za tai taji daɗi, ta buɗe jakarta ta ɗakko sauran maganin baccin nan da aka bata, uku kawai ta sha a jiki Kamar yadda me chemist ya gaya Mata.
A take ta ɓalle uku ta watsa ta kora da ruwa, ta runtse idonta ta na jiran ta ji bacci ya ɗauketa amma abu ya gagara.
Ta dinga watsi da kayan da ke ɗakinta Kamar Mahaukaciya, ta watsar da komai tana zazzare ido, amma ba taji sauƙin abunda ke ranta ba, ta toshe kunnenta ta ƙwala ƙara, gaba ɗaya ta firgice ta fita hayyacinta, tamkar Mahaukaciya.
Cikin azama ta fito daga ɗakin ta, ta shiga Kitchen ta hau sauke kwanuka ta na dube dube, ta zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa jikinta na ta karkarwa!!! (This is deprssion!)
(ME KUKE TUNANIN FARHAN ZA TAI? YA KUKE TUNANIN ZAMAN NANA DA SADIK? WACE IRIN RAYUWA FARHAN KE SHIRIN FAƊAWA? KUNA TUNANIN AUREN FARHAN DA SUNUSI ZE YUWU? WANE IRIN ZAMA ZA SUYI? 💃💃💃💃💃💃💃💃HAR KULLUM COOL TAKU CE, INA FATAN ANA ƊAUKAR DARUSSAN DA KE CIKIN LITTAFIN).
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
"Farhan!" Huzaifa ya kira sunanta da ƙarfi, ya saki kayan hannunsa ya ƙaraso in da take da gudu, ya fizge wuƙar da ke hannunta, idanunta gaba ɗaya sun juye, sunyi jawur gashin kanta a hargitse kamar Mahaukaciya.
"Farhan, meyafaru haka? Meyasa zaki yunƙurin kashe kanki?"
Hannayenta ta saka ta rufe fuskar ta, ta fashe da kuka, jikinta har rawa yake, cikin hanzari Huzaifa ya tattare kayan da ta sauke ƙasa ya kalleta yace "zo muje ɗaki ki sa ka hijjabi ki kintsa jikinki, an jima mutane zasu kawo lefenki da ga gidanmu"
Ko motsi ba tai ba se kuka da take, jijiyoyin kanta duk sun ɗaga sun kumbura, se sheshsheƙa take.
Huzaifa ba shi da zaɓi illa ya kamo hannunta, ya kaita ɗakinta ya tarar nan ma ta watsar da komai, ya shiga kwashe kayan yana mayar mata drower ɗin ta.
Ya ɗakko hijjabi ya miƙa mata ta ƙi karɓa, nan ma se shi ya samata, ya kalleta yace "Yaya, meke damunki haka? Koma meke damunki ina tauhidin ki? Wane irin hali zaki shiga ki manta da Ubangiji ki zaɓi nema ki kashe kanki? Kin san wuta ce makomar duk wanda ya kashe kansa, amma ki kai yunƙurin halaka kanki, haba Yaya meyasa?"
Maimakon tai Magana, sema ta nemi guri ta kwanta, saboda ji da tai kanta yana wata irin juyawa, tana ganin duhu a idonta.
Huzaifa ya ƙura mata ido,yana jin wani irin matsanancin tausayinta ya na ratsa shi.
Ya fuskanci kamar bacci ne ya ɗauketa, harya yunƙura ze tashi ya fita, yaji ta fara surutai.
"Meyasa! Meyasa zaka min haka? I still love you, but why? Why me?!"
Huzaifa ya san Farhan ba ta son Auren nan, akwai wanda take so, amma ba bu wanda ya taɓa tunanin zama da ita ya ji damuwarta.
Ya girgiza kai ya koma tsakar gida, dan kar ta farka ta kuma yunƙurin aikata wani abu.
Yau a falo Nana ta tarar da Sadik, ta ga kamar fuskaarsa a ɗan kumbure take, yana kwance akan kujera ya ɗage ƙafafunsa tare da lumshe idanunsa.
"Nace ba, yau me zamu ci?" Tai maganar tana hamma.
A ransa yace 'ji jarababbiya, ba ta da zance se na Abinci'
Banza yai mata yaƙi buɗe idonsa.
"Magana fa nake" ta maimaita cikin tsiwa.
Sadik be kulata ba se ma tari da ya fara yi, da alama mura ta kama shi sosai, se tari yake.
Nana tace "lokacin da kake shan ruwan sanyi, da nayi magana se kace bani da kunya, amma da nai maka shiru gashi nan jikinka ya na gaya maka"
Buɗe idonsa yai yana bin Nana da kallo, yadda take masa faɗa Kamar wata uwarsa.
Ya maida idanunsa ya lumshe, yana jin yadda kansa ke masa ciwo.
Ta wuce shi ta barshi a falo, can mintuna goma se gata ta dawo da tea a cup, ta ajiye masa tace "ga shayi ka sha, se ka je Asibiti a duba ka"
Be kulata ba yai banza da ita, hakan ba ƙaramin bawa Nana haushi yai ba, tace "wai ba zaka sha ba ne?"
"Ke! Dalla ki ƙyaleni, ina ruwanki da ni ne, dole ne se kin shiga sabgata?"
Seda ta razana saboda tsawar da yai mata, tace "Allah ya baka haƙuri"
Ta koma gefe ta tsura masa ido, se atishawa yake yana tari, da alama ba ƙaramin kamu murar nan tai masaba.
Ya bi ya dunƙule guri ɗaya, da alama har da sanyi yake ji.
"Ko in ɗakko maka bargo, na ga kamar ka na jin sanyi?"
Se da ya harareta ta tuna yace karta kuma shiga harkarsa.
Suna nan zaune kamar kurame, taji ana kaɗa bell ɗin ƙofar gida.
Tun da suka zo gidan nan, da wasa ba ta taɓa leƙawa ko ƙofar gida ba, ta tashi da nufin ta je ta buɗe ƙofar amma ta kasa, tana ta kokawa da ƙofar, se ji tai an tureta gefe, ta ɗaga kai ta ga Sadik ne.
Ya buɗe ƙofar, wasu yaran turawa ne sa'anin Sadik uku maza, biyu mata.
Sadik yana ganinsu ya fara murmushi,yai musu iso zuwa cikin falo, ya bar Nana a bakin ƙofa.
Ta biyo bayansu, ɗaya daga cikin matan, ta zauna a kusa da Sadik ta dafa goshin sa, cikin kulawa take masa sannu da harshen turanci.
Nana kam se bin su take da ido, ɗaya daga cikin su ya kalli Nana, ya tambayi Sadik wannan fa.
Sadik ya kalli Nana yace "she's my made"
"Wow she's beautiful" cewar ɗaya daga cikin 'yan matan.
Ɗayar tacewa Nana "ya kike?"
Wata uwar harara Nana tai watsawa Yarinyar, Sadik yace "karki damu, ba ta jin turanci ai"
Wani abu ya tokarewa Nana a zuciya, ita Sadik ya kira da 'yar aiki, lallai wannan ƙarshen cin mutumci ne a gareta, seda ta ji wata ƙwallar baƙin ciki ta taru a idonta, ta wuce ɗakinta.
Nan suka baje kayan ciye ciye, suna ci su da Sadik, Kamar gidansu haka suka dinga shagalinsu a gidan.
Nana ba ta sake fitowa ba, har Azahar suna gidan, se bayan azahar Sannan ta dena jiyo motsinsu, ko da ta fito falon ta tarar ba sa nan har Sadik ɗin.
Sunyi kaca kaca da Gidan, kuma sunyi tafiyar su sun bar gidan a haka, haka Nana ta zage ta na gyarawa, tare da tunanin in da Sadik ya tafi alhalin ba shi da lafiya.
Yau abun na Sadik ya zarce tunani, dan har fiye da ƙarfe goma na dare ba ta ji dawowarsa ba.
Tsoro ya gama cika zuciyar Nana, ta dawo jikin ƙofar gida ta zauna ta takure jikinta Sosai, a haka wani wahallalen bacci ya kwashe ta.
Se sha biyun dare sannan Sadik ya dawo, dan yawo suka tafi da abokansa, suka sai ticket suka tafi kallon ball, be sake tunawa da Nana ba seda ya dawo ya tarar da ita a takure a bayan ƙofa tana bacci.
Har yai gaba abunsa ze barta a gurin, se yag rashin dacewar hakan, ya dawo da baya yasa ƙafarsa yana taɓata.
A razane ta buɗe ido, ga miƙe tsaye tana waige waige, ta kalli Sadik ta kalli agogon da ke falon, ba tace masa uffan ba ta wuce ta kama hanyar ɗakinta ta na tangaɗi saboda baccin da take ji.
Jin hayaniyar da tai ne ya sa ta buɗe idonta a hankali, ta farka da wani irin matsanancin ciwon kai, se hayaniya take jiyowa sama sama.
"Ke Farhana, wai wannan wane irin bacci ne haka, ki tashi ki alwala ki sallar isha'i, tun da muka dawo Gidan nan kike bacci, ba yadda ba muyi ba ki tashi amma kin ƙi, wane irin bacci ne haka?"
Seda tai shiru na wasu lokuta, sa'annan ta gane muryar Maman Huzaifa ce.
A hankali ta gyara kwanciyarta, ta tashi zaune, sedai kanta juyawa kawai yake, ta yunƙura ta miƙe tsaye amma ta tafi luuuu za ta faɗi.
Maman Huzaifa ta riƙeta tace "ko baki da lafiya ne?"
Farhan ba tace mata komai ba, ta fara takawa, amma se ta dinga ganin Kamar ginin Gidan ze ruso a kanta, da kyar ta kai kanta banɗaki, tai alwala ta na jan ƙafa ta koma ɗaki.
Gidan Mutane se shiga suke suna fita, ana ganin kayan lefenta, sedai har ta fito tai alwala ba wanda ya kula da ita.
Ta jero sallolin da ba tai ba, ta idar ta dinga yiwa Allah godiya da be sa ta aikata abunda tai niyya ba, na kashe kanta.
Sedai jikinta sam ba ƙwari, tana kwance aka kawo mata Abincin dare, amma sam, ba ta jin za ta iya cin Abincin.
Sama sama take jin ana cewa "Masha Allah, kaya sunyi kyau, an saka sati huɗu biki, Akwatinan ta guda biyu, ƙatuwa da 'yar ƙarama se jakar bagco"
Ana haka kunnuwanta suka jiyo ana cewa, wai ana Sallama da ita inji Sunusi, Adda tace ba ta da lafiya yayi haƙuri ba zata iya fita ba.
Da haka wani baccin ya kuma awon gaba da ita.
Farhan ba ta gane a zahiri take ko a mafarki, Sadik take gani kwance a kusa da ita yana mata murmushi yace "Princess, kin rame Sosai meyasa?"
"Ba tafiya kai ka bar ni ba, bayan kace ba zaka bari a Auramin Sunusi ba, meyasa ka tafi ba ka dawo ba?"
"Ai na dawo ba gani ba"
Ta matsa ku sa da shi, ta rungume shi, tana shaƙar ƙamshin turarensa, yayin da a zahiri kuwa pillow ne take gani kamar Sadik yana mata Magana, ta ƙanƙame pillown ta na cigaba da surutai, ta na jin Tamkar Sadik ta rungume.
Ba Adda Maryam ba, hatta Umma abun ya bata mamaki, yadda Farhan ke wani irin bacci na rashin kan gado, har sha biyun rana bacci take taƙi tashi, ko sallar Asuba ba tai ba, anyi anyi ta tashi amma Abu ya gagara.
Da ƙyar ta iya tashi, ta haɗa sallar Asuba da ta Azahar, sedai gaba ɗaya jikinta a mace yake, ko Abinci ba ta ci.
Seda Adda Maryam tai ta mata masifa, sannan ta sata gab ta sha kunun tsamiya daga haka ta ƙi cin komai.
Adda Maryam zaton ta kawai miskilancin Farhan ne, da kuma rashin lafiya dan haka ta ƙyale Farhan ɗin.
Tana nan kwance akan katifar ta, ta ƙurawa fankar sama dake ɗakinta ido, tamkar za taga Sadik a jiki, tana tuna irin rayuwar da sukai, me cike da kulawa da Soyayya, ko da wasa ba ta taɓa kawo Sadik ze iya Auren wata ya barta ba.
"Assalamu alaikum" taji anyi sallama a ɗakin.
A hankali ta juya ƙwayar idonta, dan ganin me yin sallamar, Hajiyar Abbas ta gani, nan da nan ta yunƙura ta tashi zaune, kanta kuwa ya sara seda ta ɗan rintse ido.
"Hajiya ina wuni" ta faɗa a hankali.
Hajiya ta ɗan tsura mata ido tace "Lafiya ƙalau Farhan, ohh ni Maimuna, Amare na ƙyalli ke kina baƙi, fatar duk tai duhu kin rame se idanuwa haka, anya Farhan, wace irin rashin lafiya ke damunki haka?"
Farhan tace "bakomai Hajiya"
"A'a fa, ban yadda bakomai ba, kimga daga ni seke a ɗakin nan, gayamin menene?"
"Dagaske nake Hajiya bakomai"
"Hmm, ko dai Auren ne ba kya so?"
Farhan ta girgiza kai tace "A'a"
Ba ta san Abbas ya riga ya gayawa Hajiya, ba ta so Auren ba, nan Hajiyar ta sake jinjina zurfin ciki irin na Farhan.
"Farhan, shi lamarin rayuwa haƙuri ake da shi, ƙaddara duk a yadda ta zowa bawa haƙuri yake ya karɓeta, dama nace nasan iyayenki ba lallai su damu da yi miki wani abu ba, ga Aure zaki yi, kuma shi Aure mace duk in da take se da gyara, ana zaunar da ke ai miki faɗa akan yadda zaman Aure yake?" Farhan ta girgiza kai alamar a'a.
Hajiya a ranta tace 'se aukin siyan kwanuka kawai suka sani, ba a san a gayawa yaro wace irin rayuwa ze fuskanta ba'
Hajiya ta kalli Farhan tace "idan kinje kama ruwa, kina ganin farin Ruwa, ko ƙaiƙayi a al'aurar ki alamu na sanyi?"
Farhan ta ɗanyi jimm, ta ƙi Magana.
Hajiya tace "ke kalle ni nan, ni ba wadda zaki ji kunya bace, na haifa nima 'ya ki ke agurina, ki gayamin"
Nan ma Farhan ta girgizawa Hajiya kai, alamar a'a.
Tace "to shikenan, duk da haka dai na sa a haɗamin magungunan sanyi, akwai saiwar zogale da jar kanwa, zan dafa in aiko miki da shi, maganin sanyi ne sosai, in ma akwai a jikinki ze temaka miki".
Farhan dai tai shiru ba tace komai ba.
Hajiya ta numfasa tace "Abbas ya takuramin akan lallai yana son Magana da ke, bari in kirashi in haɗaki da shi"
Tai maganar tana danna wayar hannunta.
Tai ringing na seconds, sannaan ya ɗaga Tare da yin Sallama.
Hajiya ta amsa sannan tace "Ga Farhan ɗin" ta miƙawa Farhan wayar tace "in kin gama, ki bawa ko su Amir ne su kai min Wayar"
Farhan ta jinjina kai sannan ta karɓi wayar ta saka a kunnenta.
"Assalam Alaikum" yai mata sallama.
A hankali ta amsa sa da "wa'alaikum salam"
"Daughter, jikin ne dai kokuwa, naji muryarki a ƙasa ƙasa?"
"A'a, lafiyata ƙalau"
Yai ajiyar zuciya yace "jikina ya bani ba lafiya ƙalau kike ba, duk da muryarki a haka take, Amma tana ɗauke da damuwa meyafaru ne?"
Kamar ya na ganinta ta girgiza kai tace "bakomai"
Yace "Shikenan, Hajiya tace min an kawo lefenki an saka wata ɗaya ko?"
"Mmmm" shine abun da ta iya cewa.
"Farhan" ya kira sunanta.
"Na'am"
"Kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki irin taki jarrabawar kenan, Allah ya baku zaman lafiya, Allah ze baki ladan biyayyar da ki kaiwa iyaye"
Se da ya kai aya,