Showing 120001 words to 123000 words out of 259198 words

Chapter 41 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

ƙarami shine nace dan Allah Abba ai min rai, tunda an riga an bani ta dena kula wancan ɗin, ina jin ba daɗi a raina"

Jimm Abba yai, dan gaba ɗaya jikinsa yai sanyi da jin wannan maganar ta Sunusi, Farhan ba ta taɓa nuna masa ba ta son Sunusi ba, ko akwai wanda take so ba, amma babban abunda yafi ɗaga masa hankali be wuce zancen wani na kawota a mota ba.

Abba yai ajiyar zuciya yace "shikenan, bakomai ka kwantar da hankalin ka, zanje in shawara da mahaifiyar ta, zan ga abunda ya dace ayi haƙuri dan Allah"

"Bakomai Abba, sannan dan Allah kar ai mata faɗa, bana son ranta ya ɓaci a dai nemi wata mafita daban"

Abba ya murmusa yace "shikenan, kar ka damu" ya jiya jiki a sanyaye ya nufi gida.

Huzaifa kuwa da ya fito ze tafi, ya hangi Abba da Sunusi a wajen ƙarshen layi, Sunusi ya gurfana yana Magana, hakanan jikinsa ya bashi, wani abun Sunusin ke kitsawa.

Sunusi kuwa yana ganin Abba ya wuce yai ƙwafa yace "Ai naga alamar kan aikin nan da nake ya kammala se ina yi ina zagowa ta bayan gida, in ba haka ba Yarinyar nan za ta bani Matsala.

Abba haka ya shiga gidan jikinsa a matuƙar sanyaye, dan be taɓa tunanin faruwar hakan daga Farhan ɗin ba, ya yarda da 'yarsa matuƙa da gaske.

Umma daga yanaisa ta gane Akwai matsala, amma duk yadda tai ta tambayar sa Lafiya, ƙin gayamata yayi, dan be san ta in da ze fara mata bayanin ba, gashi ta fishi girmama abu irin wannan mussaman akan Farhan.

Sir Nazir yana nan hankali ya kasa kwanciya, saboda fargabar abunda ze taso, gashi ta dena ɗaga wayarsa gaba ɗaya.

A makaranta su Haseena suke zancen sunje sun duba Lilly, ta rame Sosai saboda rashin lafiyar da tai.
Sir Nazir ya sa aka kira masa Yasmeen, ya tambayeta ya jikin Lilly, tace "jikinta da sauƙi, amma har ƙarin jini a kai mata, amma da jikin nata da sauƙi"

Yace "ok to shikenan, jeki"

Bayan tafiyar Yasmeen ya kuma ɗaukar waya ya kira Lilly, Amma ta ƙi ɗagawa.

Yasan ba abunda ya faru, dan da tabbas in wani abu ya faru zuwa yanzu da an danƙo shi.

Kasancewar an kammala jarrabawa, ya sa Farhan na gida, saboda hutu za'ai, ga damuwa tayi mata yawa, ga ba abokin hira balle ta ɗan faɗi matsalar ta taji daɗi.



Jiki a sanyaye Farhan ta fito daga ɗakinta, zata ɗebi abun karin kumallo ta tarar da Hajiyar nan maƙociyar su ta shigo yiwa Umma sallama zata tafi umara.

Farhan na ganin mutuncin Hajiya Sosai, har ƙasa ta durƙusa ta gaisheta Kamar yadda ta saba.

Cikin sakin fuska Hajiya ta amsa tace "ke Farhan ko gaisheni ba kya ɗan shigowa kiyi, ni dama Ummanki ta barmin ke, 'yan jikokin nawa duk sunyi Aure ba me zuwa in da nake"

Murmushi Farhan tai, tana ƙoƙarin miƙewa.

Hajiya tace "Ni kam ko baki da lafiya ne naga duk kin rame"

Farhan take taji kamar ta fashe da kuka, dan marabarta da mara lafiya kaɗan ne, amma tace "A'a Hajiya lafiyata ƙalau" Farhan ta ƙarasa maganar muryarta na rawa.

Hajiya tace "tashi kije, naga ke ba son Magana kike ba, ni wallahi Umman Farhan da ina sauran ɗa da be Aure ba da nace muna kamun Farhan, ni ko a masu Auren ma in yi wani amarya da ita, ina son Farhan wallahi"

Umma tace "Allah sarki, ai an mata miji, ɗan lokaci kawai ake jira a fara Maganar Aure"

Hajiya tace "Allah sarki, ashe an rigamu to Allah ya tabattar da Alkhairi, na so ace cikin iyalina ta shigo, Farhan akwai nutsuwa"

Suka cigaba da hirarsu da Umma, yayin da Farhan ta koma ɗaki ta zubawa kayan karin kumallo ido, ta kasa ci se zafi da ƙirjinta ke mata.

"Yaya wai kije inji Abba" maganar ƙninta ce Amira ta dawo da ita hankalinta, haka nan taji gabanta ya faɗi, saboda wasu lokutan kiran Abban ba ya wuce zancen Sunusi.

Kamar kasar da ta haɗiyi ƙwai, haka Farhan ta tashi ta tafi ɗakin Abba.

Umma ma na zaune a ɗakin Farhan ta shiga ta zauna tace "Abba gani"

Ya kalli Farhan yace "Farhan magana nake so muyi da ke, kuma ina son ki gayamin tsakani Allah"

Gaban Farhan ya faɗi, tace "to Abba"

"Farhan kwanaki an cemin ana kawoki a mota, amma kince min 'yar Makarantar ku ce, na ce miki bana son biyewa yaran masu kuɗi, Amma an kuma tarata ance min wani ne yake kawoki a motarsa.

Gaban Farhan ya faɗi, wane munafukin ne wannan? Rabon da Sadik ya zo an do shi wata na biyu kenan bama yanan, amma an samu wanda ya samu Abba ya gaya masa.

"Farhan waye yake kawo ki a mota?"

"Abba Sadik ne" ta faɗa kai tsaye.

"Waye Sadik" Abba ya tambaye ta.

"Wanda suka zo suka kawomin invitation ɗin bikin yayan su, shi da ƙanwarsa, motar gidan su ce, idan anzo ɗaukar su ne muke tahowa tare, kuma na dena biyosu tunda kace min baka so, nika ɗai nake tahowa gida"

Abba yace "to, ba a shedar ɗan yau, ba zan gazgata abunda kika faɗa ba, kuma ba zan ƙaryata ba, sedai ina sake jaddada miki Farhan kiji tsoron Allah, ki tsare mutuncinki, ki kula da kanki Farhan 'ya mace ce ke, kije shikenan"

Farhan ta tashi jiki a sanyaye, ta bar ɗakin.

"Nifa na fara tsorata da wannan lamuran, abu tun ana waiwai to maganin kar ayi kar a fara, kawai kacewa yaron nan ya fito, ni in babu hali ma kawai a haƙura da karatun nan, ka aurar da ita"

Abba yace "Nima ina wannan tunanin, zanwa Malamin nasu Magana kawai su turo a kawo kuɗin, muga abunda yakamata ayi"

Farhan kuwa tana tsaye a ƙofar ɗakin, a kunnenta taji Abba yana faɗin ze karɓi kuɗin Auren ta a hannun Sunusi.

Jikinta na rawa ta ƙarasa ɗakinta, ta na zuwa ta durƙushe, ta nannaɗe a cikin hijjabi tana faman kuka.

Kamar yadda Abba ya yanke shawara shi da Maman Farhan, washegari yaje ya samu malamin su Sunusi.

Ya tarar da shi da Almajirai, Yana ganin Abba ya taso yana murmushi, suka koma gefe suka gaisa, Malam yace "Malam Mahmud, ina fatan dai lafiya?"

Abba yace "lafiya ƙalau, dama ba wani abu bane, magana ce akan Farhan da Sunusi".

"Eh to ya ake ciki?"

Abba yace "ka san yanayin zamanin nan da muke ciki, da kuma halin ɗan yau, shine nace idan ba damuwa Sunusi ya fito kawai ya kawo kuɗin Aure"

Malam yace "Alhamdilillah, amma gaskiya naji daɗin wannan magana ta ka sosai da sosai, ubangiji Allah ya ƙara girma, zanyi Magana da shi Sunusin, muje can garin nasu a tattauna da magabantasa se ya fito, Nagode ƙwarai da karamcin ka, Allah ya nuna mana lokacin Auren"

Abba ya amsa da Ameen, daga nan su kai sallama.


Fafur Abba ya fututtuke ya hana Mother Zuwa in da Sadik yake, tun tana damuwa tana kuka harta dangana ta saba, dan Sadik ya kusa watanni biyu a garin nan, ba tare da ta sake sa Sadik ɗin a idonta ba.

Takanas su Nas sukaje har gida, dan kaiwa Sadik ziyara amma aka sanar da su baya gari, Faruk ne ya gaya musu, Amma be gaya musu in da Sadik ɗin yake ba.

Allah ya temaki Farhan Tunda Mubarak Babba su kai arangama da Sadik ba ta sake ganinsa ba, dan haka ta manta da batun Mubarak Babba.


Lilly kuwa ga warke sumul kamar ba tai rashin lafiya ba, dan har zata fara zuwa Makaranta cikin hutu ai mata jarrabawar da ba ta samu tayi ba.

Ranar farko da t fara zuwa ta haɗu da Sir Nazir a makarantar, yana fama da marking ɗin takaddun

Se da gabansa ya faɗi da ya ganta, duk ta rame sosai da sosai, sedai ta ɗanyi ƙalau da ita, ko in da yake ba ta kalla ba ta shiga sabgogin ta.

A wani aji aka ware su, ita da wasu ɗalibai, wanda ba su samu damar yin jarrabawar ba.

Se shiga yake yana fita yana son samun hanyar da ze mata Magana, amma abu ya gagara.

Seda ta gama exams ɗin ta fito sannan ya samu ya biyo bayanta yana mata Magana.

"Wai dan Allah Nazir me kake so ne? Me zan maka?" (Ashsha, ya rasa wannan darajar da girmamawa ta malami da ɗalibi saboda abunda ya aikata"

"Haba Lilly, kin dena ɗaga wayata gaba ɗaya na biyoki kuma kin ƙi saurarata"

Cikin tsiwa tace "in ɗaga wayarka in ce maka me? Bayan ka cuceni ka zalunce ni Allah ne yai da sauran kwanana na gaba da yanzu wani zancen ake ba wannan bax

"Lilly ki dena ɗaga murya dan Allah kar wani yaji"

"To wanin ma yaji mana ina ruwana?"

"Lilly ni ki ke wa haka?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsansa.

Kawai kuma se taji tausayinsa ya kamata.

"Koma me nai ai kai ka janyo min, se da aka samun leda biyu na jini, dole raina ya ɓaci"

"Amma bisa amincewar ki koma mene ya faru, kuma ke kika bani damar nema mana mafita, se kuma ki dinga wulaƙanta ni dan ina binki?"

"Ni ba wulaƙanta nai ba"

"To girmamani ki kai?"

Tai shiru tare da sunkuyar da kai.

Cikin sanyin jiki yace "Tun da abun nan ya gifta a tsakanin mu nake jina cikin damuwa, amma kin kasa fahimtar hakan, nasan mun aikata Babban laifi, Amma dan Allah ki dena min haka"

"Shikenan naji"

"Shikenan kim ji kuma? Ba zaki ce Komai ba?"

"To me zance?" Ta faɗa a ɗan shagwaɓe.

"Nayi kewarki sosai Lilly"

"I miss you too"

"Ba wani ba ki missing ɗi na ba"

"Wallahi nayi missing ɗin ka, wahalar da na shiga ce yasa naji haushin ka"

Yace "to Yanzu fa?"

"Ya wuce" tai maganar tana murmushi.

"Yawwa Love, Allah ya ƙara lafiya muje restaurant mu ci Abinci tare mana"

"Daga yin salaryn in cinye maka kuɗi, karka damu"

"A'a kinga ban samu na zo duba ki ba, saboda ina tsoron ko kin faɗa a gida, muje mu ci Abincin kan azo ɗaukar ki"

"Shikenan muje" suka jera suka fita daga cikin Makarantar.



Khairat na zaune a falo, ta harɗe ƙafa tana kallon Bollywood, se ga wata 'yar makarantar Islamiyyar  su ta kawo mata ziyara.

Khairat ta dinga murmushi, ta kalli ƙawarta tace "Yasmeen, waye ya gaya miki ina nan?"

Yasmeen yace "gidanku naje, aka cemin kina Gidan su Prince, ni wai ina gayen nan, tunda ya bar school ɗin nan sau ɗaya ya zo, ko gurin budurwar ta sa ba ya zuwa?"

Khairat tace "ke yana ƙauye fa"

"Wane irin ƙauye kuma?" Yasmeen ta tambaya cike da Mamaki.

"Yana ƙauye gidan kakanninsa, sun riƙe shi a can"

Yasmeen tace "taɓ, Wannan gayen a ƙauye abun ba arziki, kin san yarinyar da yake so 'yar ajinmu ce"

"Haba dai, Farhan ne sunan nata ko wa?"

"Eh, haka sunan ta, wata 'yar talakawa sam bata waye ba"

Khairat tace "Na santa, tare muka kai mata invitation ɗin bikin dr. Ya nace yace se ita yake so, in ya tafi karatu dai kowa ya huta"

Yasmeen tace "hakane, amma meyasa ba zaki ba shi shawarar ya nemi budurwa wadda take tsarar sa ba, me ze yi da wannan?"

"Ke kin san kuwa waye Sadik? So kike ya min rashin mutunci ko? Ko da wasa mutum ya kushe ta ba ki ga yadda ake kwasheta da shi ba, balle wata Shawara, ke nifa before am the one crushing on him, but now ya min yarinta kuma halinmu ba ze zo ɗaya ba, kawai na bar mata shi naga yadda yake hauka a kanta, ni ina jiran in samu wani handsome ɗin ne"

Dariya suka yi, Faruk yai Sallama falon, suka amsa gaba ɗaya.

Faruk yace "Khairat, Mother ta fitan ne?"

"Eh tun ɗazu ma, ta daɗe da fita gaskiya"

A hankali Yasmeen ta furta wow, ta kalli Faruk tace "ina wuni?"

"Lafiya ƙalau ya kike?"

Tace "Lafiya ƙalau"

Faruk yace "ke Khairat baƙuwar taki ko ruwa ba zaki bata bane?"

Cikin shagwaɓa Khairat tace "yanzu fa ta zo, zan bata ai"

"Ba wani nan, baki iya saukar baƙo ba" ya ƙarasa Maganar tare da barin falon.

"Wow, Khairat wannan ma ɗan uwan Prince ne?"

"Eh ɗan uwansa ne ba kiga suna kama ba?"

"Kai amma naga wannan fari, gaskiya yafi Prince kyau"

Khairat tace "haba da faɗ kike, dan dai wannan fari ne tas, Sadik kuma be kaishi haske ba, amma duk 'yan gidan nan ba me kyan Sadik"

Yasmeen tace "wayyo Allah, ammm da Allah kice ina gaise shi"

Dariya kawai Khairat tai, ta canza hirar.

Bayan tafiyar Yasmeen ne Khairat tai shiru tana tunani, tunda ta san ba zata samu Sadik b, Ai Faruk shi yafi dacewa ta sa a gaba, saboda shine nan da wani ɗan lokaci ze iya yin Aure.



Sunusi ne a tsaye a bakin wani ruwa, da yake ta zuba gudu ga iska na kaɗa ruwan sosai, ga duhun dare se hasken farin wata da ha gauraye gurin.

Ya ɗakko wata jar laya, ya jefata cikin ruwan, ruwan ya tafi da ita ya tsaya yana cigaba da kallon ruwan yana murmushi yace "yanzu aiki saura ƙarashe, ƙirisa ya rage in kammala aikin nan komai ya zama daidai.


Sadik yana tsaka da baccin sa, yaji tamkar an sara masa wani abu a kansa, ya taho tun daga kansa zuwa ƙahon zuciyarsa, a kiɗime ya tashi zaune yana maimaita innalillahi wa innalillahi raji'un.

Y dafe kansa yana jin yadda yake sara masa, zuciyarsa na ta bugawa da sauri da sauri.

A hankali kuma ya furta "Farhan" take zuciyarsa ta tsinke, yaji babu abinda yake son gani sama da ita, dan rabonsu da waya kusan wata guda kenan.

Kamar a mafarki haka ita ma Farhan taji an kira sunanta, ga wani irin sanyi da ya dinga ratsata, zaune ta tashi tana waige waige a ɗakin, kamar me neman wani abu.

Ita kanta bata san me take nema ba, ga wata faɗuwar gaba da ta addabe ta.

Miƙewa tai tayo Alwala, ta koma ta kwanta tana karanto duk ayar da ta zo bakinta.

Se daf da Asuba Sannan Sadik ya koma bacci, sedai mafarkin Farhan ya dinga yi, mafarkan da ya kasa gane kansu ma gaba ɗaya, daga baya kuma ya koma irin mafarkansa da ya kanyi da ita.

Mitar Inna ce ta farkar da shi daga bacci, "wai yau wane kalar rashin mutunci ne haka? Sallar ce ba zaka ba ko me, gashi can sun tayar da salla amma kana naɗe kana bacci"

A hankali ya buɗe idonsa, ya miƙe daga kan shimfiɗar sa, sedai a yanayin da yake jin jikinsa, ba ze iya salla ba se yai wanka, ga wata irin wutar son ganin Farhan da ta addabi zuciyarsa.

A hankali ya fito tsakar gida, yai karo da Inna tana salla a tsakar gida.
Ɗan gajeren tsaki yai, a ransa yace 'yau kuma meya fito da wannan tsohuwar yin salla a tsakar gida?"

Ko a jikinsa, ya wuce ya ɗau bokiti ya cika da ruwa, ya wuce banɗaki dan yanzu ya saba da wanka da ruwan sanyi.

Yai wanka yai Alwala, Sannan ya fito ya wuce ɗakinsa.

Tun da ya fito Inna ta bishi da kallo, duk da gari da sauran duhu, amma kallonsa take, ko a jikinsaya wuce ɗakinsa.

Nana tace "ji wata masifa wanka da uwar Asubar nan, se kace kif...

Ɗala mata duka Inn ai a baya yace "ban hanaki shiga sabgarsa ba? Se yazo yana zaginki ki buɗe maƙogwaro kina ihu ko?"

Nana ta ja bakinta ta tsuke.

Har zuwa safiya, jikin Sadik a matuƙar sanyaye yake, a hankali yake gudanar da komai.

A tsakar gida ya tarar da Nana, ta zubawa maguna Abinci, ita kuma tana zaune tana saƙa da ulu da kwarashi.

Gaban Nana ya ƙaraso ya tsuguna, ya zuba mata ido.

A tsorace ta kalle shi tace "meye haka?"

Ya ajiye mata wayoyinsa, yace "ina son caji a waya ta ne, zanyi amfani da su"

"To na maka kama da wutar lantarki?"

"Gurin masu caji zaki kai min"

"Ajiye ba dan halinka ba, dan wani lokacin ina ɗan jin tausayin ka, da dan halinka ne wallahi ba zan kai ba"

Kamar zeyi magana amma ya fasa, ya miƙe tsam, ya koma ɗaki.

A jakar Islamiyyar ta ta saka wayoyin, ba ta gayawa Inna ba, da aka tashi daga Makarantar ta tafi kai masa cajin.

Sedai gurin da nisan gaske, haka taje ta kai masa, wanda yai dalilin daɗewarta ba ta dawo da wuri ba.

Inna ta dinga safa da marwa, tana tunanin in da Nana ta tsaya, amma Sadik na kallonta be ce uffan ba.

An fara kiran sallar magariba sannan ta dawo gida.

Tana shigowa kallon da inna tai mata ya sa ta sha jinin jikinta.

"Zo ki gayamin in da kika je"

Nana tace "wallahi Inna ba in da naje, caji na kai masa"

Inna tace "shi wa?"

Nana ta nuna Sadik tace "wannan"

"Ƙarya kike ki gayamin gidan uban da kika tafi, ko wani ne ya tsare ki a hanya?"

"Wallahi Inna ba wanda ya tsareni, wallahi caji ya bani na kai masa"

Sadik yana zaune yana ji, ko kallonsu be ba, Inna ta kwakwkwaɗe Nana, ta ƙare mata zagi tsaf.

Ba dukan Inna ne ya ɓata mata rai ba, illa yadda Sadik yaƙi ƙwatarta ko ya gazgata shine ya aike ta.

Saboda tsabar baƙin ciki, ko Abincin dare ba ta ci ba ta kwanta bacci tana kuka.

Da Asuba su kai clashing da Sadik, ta fito daga banɗaki, aikuwa tana ganin sa tace "wallahi ba ka da imani, kuma wallahi na barka da Allay, kai ka aikeni amma kana kallo, a ka dakeni a kai min faɗa, mugu kawai"

Be ma nuna ya san yaji me tace ba, yai banza da ita, yai Alwala yaje salla.

Se da gari yai haske, ya fito tsakar gida, ya ga Inna ta shiga sashin turakar Hakimi, Nana kuma ta fito daga banɗaki ta shiga ɗakin Inna.

Ba tantamar komai, yabi bayanta, zuwa ɗakin Innan.

Har Nana ta cire hijjabi, daga ita se ɗaurin ƙirji za ta fara cin Abinci, ta ɗaga kai taga Sadik a kanta a tsaye.




Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.





Jikinta ne ya hau rawa, ta zazzaro ido ta furta "Na shiga uku, watan cin ubana a gida ya tsaya, wallahi baban mu ze iya kashe ni ya huta, Innalillahi wa innalillahi raji'un, ka cutar dani Sir"

Shima cikin damuwa yace "Please calm down, ni kaina ban san haka zata faru ba, kuma da baki zo gidana ba da duk wannan abun be faru ba"

"Au haka ma zakace ko?"

"Bahaka bane, me faruwa ta riga ta faru, yanzu abunda nake so da ke shine, ki kwantar da hankalin ki kinji, zan san abunyi a kai"

"Zaka san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login