Showing 159001 words to 162000 words out of 259198 words

Chapter 54 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13435

haƙura, amma daga yau kawai mu haƙura mu yanke duk wata alaƙa da ke tsakanin mu, tun da mahaifinki ba ya so, kar inje ya sa a kassarani, ni kaɗai ne namiji a gurin mahaifiyata"

Tashi tai daga in da take zaune, ta zagaya in da yake ta hau kan teburin, ta ɗan ƙura masa ido sannan tace "ba zan iya rabuwa da kai ba"

"Saboda me?"

"Saboda dalili me ƙarfin gaske, kayi haƙuri da abunda mahaifina yai maka, ka bari ya wuce"

"Lilly ba zan iya mantawa da abunda mahaifinki yai min ba, dan ba wanda ya taɓa yi min abunda yai min a rayuwa ta"

Ta kai hannu kan sajensa da ke ta ƙyalli ta shafa, sannan ta ɗan lumshe idanunta ta buɗe akansa tace "na sani, amma na ari bakinsa na ci masa albasa, kayi haƙuri Please i miss You so Much, ba zan iya rabuwa da kai ba"

"Am missing you too, but is better to be apart, da Matsala ta afku"

"Meyasa kake kira mana matsala ne? Ba matsalar da zata faru Insha Allah"

Duk da ƙarancin shekaru irin na Lilly, se da tai abunda ta sa ya manta da matsalar da mu'amalarsu za ta iya haifarwa a gaba, sosai sheɗan yake ingiza su, suke ƙoƙarin sake biyewa son zuciyar su.

Takun da sukaji ne da surutu, alamar ana hawowa step ɗin benen da Office ɗin yake, ya sa Lilly saurin tashi daga jikinsa, ta daidaita nutsuwarta, ba tare da ta iya furta komai ba, tai masa alamar za su waya, ta fice daga Office ɗin, yayin da shi kuma ya lumshe ido, yana maida numfashi a hankali.

Su Taslim ne suke hawowa benen, dan zuwa ya koya musu wani aiki.

Taslim ta kalli Meena tace " ke tayani gani mana, wai meke going ne tsakanin yarinyar nan da mutumin nan?, ku san kullm fa se mun ganta a nan"

Meena tace "ba ance budurwar sa bace, ai ba abun mamaki bane"

"Duk da haka, me suke a Office su ka ɗai a saman nan, kullum fa semun ganta anya ustazancin nasa na gaske ne?"

Meena tai dariya tace "a'a sedai ki bari in mun shiga ki tambaye shi" su kai dariya gaba ɗaya suka shiga Office ɗin.





Nana ce zaune akan gadonta, ta lumshe ido tana karatun Alkur'ani a hankali, cikin sauti me daɗin sauraro, kasancewar ita kaɗai ce a ɗakin Linda ba ta nan.
Seda ta kai aya ta buɗe ido, taga Linda da wata ƙawarta sun zubo mata ido, kamar sunga wani abu daban.

Cikin harshen turanci tace "Lafiya, meyasa kuke kallona?"

Linda tace "wai dan Allah me kike karantawa haka?"

"Is my holy book qur'an"

Linda tace "wow, kuma kin san abunda kike karantawa, na ga ba kowane musulmi ne yake jin larabci ba"

Nana tai murmushi tace "Yanzu balaraben da yake Kirista, idan ya karanta bible ya san abunda yake karantawa?"

"A'a, amma ai akwai bible na larabci"

Nana tace "to Kasancewar Alqur'ani da larabci, hikima ce ta Ubangiji, karanta shi kuma ko baka san ma'anarsa ba yana samar da nustuwa a zuciyar me sauraronsa, wani abun nasan fassarar abunda nake karantawa.

"Hakane, yana da daɗin sauraro kam, amma zan so wata ran ki karanta bible, shima zaki ji daɗinsa"

Nana da hausa tace "kaji 'yar baƙin hali, ni zaki canzawa addini, amma da turanci tace "to shikenan babu damuwa"

Ƙawar Linda tace "amma meyasa kike saka hijjabi, da dogayen rigunan larabawa, ku Mutanen Africa kuna koyi da larabawa ne?"

"Ba da larabawa muke koyi ba, dokokin addinin mu muke kiyayewa, shi yai mana umarni da sanya hijjabi da suturta jikinmu"

"Amma da gaske Africa babu Abinci, duk matalauta ne?" Cewar ƙawar Linda.

"Ji shegiya da fuska kamar alade, Abincin gidan ubanki muke ci muka girma, ji 'yar banza me koɗaɗɗiyar fuska"

Linda tace "ba mu gane me kike cewa ba"

Nana tace "Addu'a nake da hausa, bacci nake ji yanzu, ma cigaba wataran"

Ta juya ta kwanta ta na cigaba da ƙunƙuni da mita.



Mother gani tai lamarin Abba dagaske yake, ya watsar da ita ya fita harkarta gaba ɗaya, sabgar gabansa kawai yake, haka ta dinga lallaɓashi, kamar ta zubar da makamanta, har ta samu ta shawo kansa da ƙyar, ya ɗan sakko ya rage fushin da yake, har suka koma cin Abinci tare da kwana guri ɗaya.

Faruk ma yana ta shirye shiryen komawa South Africa, in da zeyi master's ɗin sa, yayin da Khairat ta kamu da tsananin ƙaunarsa, tana ta nan nan da shi tana ba shi kulawa ta mussaman, sam shi be taɓa kawo wani abu ne a ranta na Soyayya ba, ga shi Haseena na ta takura mata, akan dan Allah wai ta haɗa da Faruk tana sonsa.

Kwanci tashi asarar rai, tamkar ana jan kwanakin, haka suka dinga gudu, awanni, da ranaku suna shuɗewa, zuciyar Farhan cike da burin sake tozali da masoyinta ta kasa fidda ran Sadik ɗin ta ze dawo gareta, ko ta samu ta rabu da Sunusi, dan yau kusan wata guda kenan da sa ranar Aurenta da Sunusi.
Ko a makaranta yanzu ba ta ƙoƙari, bata iya fahimtar karatu sam, in akai test ko jarrabawa ma faɗuwa take a wasu, grade ɗinta yai ƙasa sosai, kullum tana zaune shiru ba sawa ba fitarwa.

Kamar kullum, tana wannan tafiyar tata kamar wadda a kaiwa dole, fitowarta daga Makaranta kenan, ta miƙo hanya za ta fito titi ta samu abun hawa, taji ana mata horn, cikin hanzari ta waiga, zaton ta za taga Sadik.

"Sena buge ki ki lanjare ko? Kina tafiya kamar ba kya so, ko haryanzu jikin ne?"

Murmushin ƙarfin hali tai tace "ina wuni"

"Lafiya ƙalau, dama makarantar nan kike zuwa?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Yace "Masha Allah, shigo mu tafi'

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Wasa nake da ke, shigo mu tafi nace"  yai maganar yana haɗe rai sosai.

Tana matuƙar jin nauyin Abbas sosai, ta buɗe baya zata shiga ya kalleta yace "waye direbanki, gaba zaki shigo"

Jin ta take kamar zata aikata zunubi, ba wanda ta taɓa shiga gaban motar sa banda Sadik, wata zuciyar tace idan Sadik ya ganki fa? Ze iya jin ba da daɗi.

Haka ta shiga tana wasi wasi, ya ja Motar suka fara tafiya.

Abbas yace "Lalallai Baba yayi ƙoƙari, wannan makarantar kike zuwa?"

"Scholarship ne na samu"

Yace "Masha Allah, you deserves it, dama nasan kina da ƙoƙari ai"

Tai murmushi tare da sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta, kawai Sadik take tunawa, ta kalli hannun Abbas da yake tuƙi, taji ina ma zata ga hannun Sadik me ɗauke da agogo da zoben azurfa, ta ɗaga kai ta kalleshi ya waigo ya kashe mata ido ɗaya Allah sarki Sadik. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, wadda se da Abbas ya waigo ya kalleta yace "Lafiya kuwa?"

"Lafiya ƙalau" ta bashi amsa a hankali.

"Baki tambaye ni ya akai kika ganni ba, bayan nace miki zanje ƙaro karatu"

"Mantawa nayi"

Murmushi yai yace "kinji ki, wai mantawa ki kai, ba ki niyya ba dai,na gama clearance next week zan tafi insha Allah"

"Allah sarki, Allah ya bada sa'a"

"Ameen, Farhan, idan kika kammala secondary School, insha Allah zan karɓi takaddun ki, school of Nursing zaki tafi, zaki dace da aikin jinya, duk da ban san meye ambition ɗin ki ba"

Ai kamar ya taɓo mata wani abu da yake damunta ta fashe da kuka.

"Subhanallah, meya saki kuka kuma?"

Cikin kuka Farhan tace "burina ba ze cika ba doctor, Babana Aure ze min"

"Aure kuma? Na zaci da wasa Hajiya take min da tace min an kawo kuɗin Auren ki"

Wani irin tausayin Farhan ya mamaye shi, yace "calm down please, yi haƙuri ki share hawayen ki, ai darajar 'ya mace in ba Gidan iyayen ta ba dama to ɗakin mijinta, in dai ze barki ki cigaba Alhamdilillah"

Duk da rashin son Magana, da tsananin zurfin ciki irin na Farhan, amma ta tsinci kanta da cewa "bana son sa, ba na ƙaunarsa, ban taɓa son sa ba"

Jiki a sanyaye ya kalli Farhan yace "kina nufin ba ke kika kaishi kika ce kina so ba?"

"Bana son shi, maganar Soyayya ba ta taɓa haɗani da shi ba, ya tura aka nema masa aurena a gurin Abba, Abba kuma ya amince, Amma bana son shi"

"Ya Salam, yanzu na ƙara gano dalilin rashin lafiya da ki kai, amma kin gayawa Abban cewar ba kya son sa?"

"Ai ba su taɓa tambayata ko ina son sa ko bana so ba, koma sun tambaya ba zan iya bijire musu ba, saboda sun min komai a rayuwa, ba zan iya bijirewa ba" tai maganar tana wata irin sheshsheƙa.

Ya ɗan zuba mata ido, yarinya ce Sosai, sedai ba kowa Allah ke bawa yaro me nustuwa da biyayya a wannan zamanin ba, ba kowace Yarinya ce zata iya hangen nesa da kuma iya Magana kamar Farhan ba.

Yai ƙasa da murya yace "ni kin bani dama in tari baban in gaya masa ba kya son Auren?"

Tai saurin girgiza kai tace "wannan sirri ne na gaya maka, dan Allah kar ka gaya musu, nasan ba wani dalili da zesa a fasa Auren nan, dangin mahaifiyata ba zasu yadda ba, dan sune suka asassasa lallai a bar karatuna ai min Aure"

Abbas ya shiga mamakin wannan wace irin rayuwa ce, akwai banbancim zamani tsakanin rayuwar da su kai a baya da wadda ake a yanzu, amma an takura Yarinyar nan da yawa, gaba ɗaya jikinsa yai sanyi wani irin tausayin ta ya mamaye shi gaba ɗaya.

Ya kuma kallonta yace "to ya batun Sadik fa?"

Ta share hawayen ta tace "na fara yadda da maganar ka, na Sadik ya barni amma zuciyata ta kasa gazgata hakan, Sadik ba ze taɓa barina ba"

"How sure are you,ba ze taɓa barinki ba?"

Shiru tai ta kasa Magana.

"Ki bawa wanda zaki Aura ɗin dama mana, he might be more than Sadik"

A hankali ta girgiza kai tace "Never, he is irreplaceable! Ba Wanda ze iya maye gurbin sa" Tana gama maganar ta fita daga cikin Motar Abbas, sedai tana fita ɗin Sunusi na jikin pole a tsaye, yana binta da ido!.



Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.






Mother ta kalli Faruk tace "ni miƙomin wayar in ga meka nuna masa haka?"

Faruk ya miƙa mata wayar, hoton Sadik ne a beach, daga shi se gajeren wando, ya tara uwar suma kaya guda a kansa, ya yiwa gefenta ado da pink color, ga matan turawa da bikini, irin watsatsun kayan nan da suke sawa, halittu a waje, duk halittu da tsiraicin su a waje.
Ya ɗaura wani ƙaramin abu a wuyansa, fuskarsa ɗauke da baƙin glass, matan nan duk suna kusa da shi su kusan huɗu a kai hoton.

Mother tai scrolling, hotuna kala kala, na Sadik da wannan mata, wasu da abokansa, wasu a club babu guda ɗaya da yayi ma a cikin ajin.

Mother tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Faruk meyasa ka nuna masa?"

Faruk yace "wallahi rikicewa nayi, kuma ko ban Gaya masa ba ze iya samun labarin hakan"

Mother tace "kaiii, Sadik sam baya gudun matsala, kullum cikin jawa kansa magana yake, Allah kaɗai yasan hukuncin da ze yanke a kansa.

Ta tashi da sauri tabi Abba ɗakinsa, ta tarar da shi a zaune a gefen gado ya dafe kansa, yai shiruuu yana tunani.

"Abba dan Allah kar wannan abun ya ɗaga maka hankali, abi komai a sannu"

Abba ya kalleta yace "karya ɗagamin hankali kika ce? Meyasa ke kullum ƙoƙarin ki ki kare yaran nan in sunyi laifi, ba tunanin yadda za'a maganace matsalar da suka ɗakko ba?. Ba zan ɗauki wannan sakarcin ba sam.
Se yanzu na sake gane hikimar Hakimi, da yace kar a turashi ƙasar waje karatu, kin sa ina ganin kamar takurawa yaran nan ake, amma Sadik kam fitinar sa ta shallake tunani na, duk 'yan uwansa da sukaje su kai karatu ba wanda yai haka se shi, gaba ɗaya ya fita zakka a cikin yaran nan, babu wanda yai fitinar sa, dole ya dawo gida, yazo yai karatun a nan, nan da shekara goma ƙila ya gama degree, iya azabar strike da strees na karatun Nigeria ma ya ishe shi"

Mother tace "dan Allah Abba, kar kace ya dawo yayi karatu a nan, dan Allah kayi haƙuri"

Abba ya miƙe yace "se kuma kiyi" daga nan ya fice ya bar mata ɗakin.

Wayarta ta ɗakko, ta kira wayar Sadik, ta kirashi ya kai sau huɗu sannan ya ɗaga, yana ɗagawa yace "what's up Mum, am sorry bana kusa da wayar ne"

"What's up ɗin ubanka? Sadik meka aikata haka?"

A ɗan shagwaɓe yace "me nayi?"

"Kamar ya me kayi, dama abunda aka turaka ƙasar waje yi kenan? Hotuna da 'yan mata tsirara"

Yace 'Mother, ba fa wani abun nai ba, naje beach ni da friend's ɗina ne, suka ganni sukace suna son muyi hoto tare, so ni kuma naga ba wani abun bane dan dai hoto kawai shine mukayi"

"Zakaga ba wani abun bane, aikuwa gashi nan ya fusata ya fara iƙirarin seka dawo Nigeria"

"In dawo Nigeria kuma? Ya akai yaga hoton ne?"

"Muna zaune muna cin abinci, Faruk ya gano hotunan a social media, ni dai ba ruwana"

Sadik ya marairaice yace "haba Mother, ba fa wani abun bane, dan Allah ki ganar da shi, ya za'ai ace in dawo Nigeria, ai se ai min dariya ma, dan Allah ki bashi haƙuri"

Mother tace "Ni kai na ba zan so ka dawo Nigeria ba, amma dai zan an yadda zan da shi, amma ka kiyaye na gaya maka, idan ka kuma ɗebo wata rigimar zan sa muku ido"

"Ok, Mum thank you very much I miss you so much"

"I miss you too, ya school ɗin?"

"Alhamdilillah, mun kusa fara exams ma"

"To masha Allah, Allah ya bada sa'a"

"Ameen, ashe Broz shima ya kusa tafiya ya barku ku kaɗai?"

"Eh a wannan watan ze tafi matsers Insha Allah, Allah ya bada sa'a"

Ya amsa da Ameen sannan ya kashe wayar.



Ana ta hayaniya gidan su Farhan, Abba ya dawo ya tarar da su cireki cirko, yace "lafiya meke faruwa ne?"

Umma tace "yarinyar nan ce, muke tunanin ko iska ta tayar"

Cikin rashin fahimta Abba yace "Iska kamar yaya?"

Adda Maryam tace "yo tun da ta shigo, ta wuce ɗaka ta faɗa kan katifa ba ta kula kowa ba, shiyasa nace wannan hadda lamarin iskokai"

Sunusi ne yai sallama a gidan ya risina ya gaida su Umma.

Abba ya kalli Sunusi yace "ya akayi ne?"

Umma tace "na aika a kirashi ne, ko karatu za'ai mata"

Abba yace A'a ba ta kai ga haka ba, bari inga Farhan ɗin.

Abba ya shiga ɗakinta, ya tarar da ita a kwance ta lumshe idanunta, kanta ko ɗankwali babu, gashin ta duk ya cukurkuɗe, da alama ko tazar Kirki baya gani, gata masha Allah tana da gashi Sosai.

Abba ya ɗakko bedsheet ɗin dake kan katifarta a ninke, ya lulluɓa mata, sannan ya sa mata hula a kanta.

Adda Maryam ta buɗe baki tana kallon ikon Allah, yadda yake taɓa 'yar sa ta fari ba kunya.

A hankali ya kira sunan Farhan.

Da ƙyar ta buɗe idanunta da su kai mata nauyin gaske, ta kalli cikin idon Abba.

Seda ya tsorata ganin yadda idanunta su kai jawur, tamkar an zuba mata barkono a idon.

Yace "meya sameki haka?"

Ji tai kamar tace masa Auren nan ne ba ta so.

Amma ta lumshe Idonta.

Ya kuma cewa "ki gayamin meke damunki?"

A hankali ta nuna masa kanta da ƙirjinta.

Abba yace "ciwo suke miki?"

Ta jinjina masa kai, "Sannu Allah ya baki lafiya, bari muzo mu tafi Asibiti"

Tai saurin girgizawa Abban kai.

Abba ya kalli Umma yace 'ko tana da sauran magungunan ta, a bata ta sha?"

Ita Umma ko kalar magungunan Farhan ɗin ma ba ta sani ba, balle ta san ko akwai ko babu.

Tace "ni ban san in da ta Ajiye magungunan ba"

Abba yace "shikenan, bari inwa Ko Isa me chemist ne magana ya zo ya duba, yaga maganin da za'a bata, in kuma Asibiti zamu tafi shikenan"

Abba ya fito tsakar gida, ya tarar da Sunusi a tsaye, ya kalleshi yace "karka damu, ba wasu iskokai da suke damunta, Kamar wannan ciwon da tai ne, tace kanta da ƙirjinta ke ciwo, bari inje gun yaron nan me chemist ya zo ya ga abunda ya dace ayi"

Sunusi yace "Abba ai duk ba se anyi wannan ba, bari inje in mata rubutu yanzu zata warware, ba se an kira wani ya dubata ba"

Abba yace "ban ƙi ta taka ba, amma a dubatan ma yana da kyau, saboda a san daga ina matsalar take, karka damu"

Abba yaja Sunusi suka fita.

Farhan kuwa ita kaɗai ta san abunda take ji a ranta, kwata kwata ko surutun mutane ba ta son ji, ji take ina ma zata samu wani guri in da zata kasance ita kaɗai ba tare da wani ya takurawa Rayuwar ta ba.

Ba a jima ba se ga Abba da me chemist, tana nan kwance ya auna BP ɗinta ya ga ya hau, ga zazzaɓi da ya rufeta.

Ya kalli Abba yace "gaskiya jininta ne ya hau, kuma naji ga jikinta da zafi sosai, bari in bata taimakon da zan iya, da yamma abunda hali yai in ta warware shikenan, in bata warware ba se a tafi Asibiti".

Abba yace "ba damuwa, amma ina mamakin abunda yake sa Yarinyar nan hawan jini haka, 'yar mitsitsiyar yarinya kamarta"

Ya saka mata ruwa da allurai, nan da nan wani wahallalen bacci yai awon gab da Farhan, wanda rabon da tai baccin awa biyar cikakke har ta manta.

Sunusi Kuwa cika yai tayi yana batsewa, yana hura hanci.

Haladu yace "wai yau kuma kai da wa kake ta wannan buɗe ƙofar hanci haka?"

"Wannan mutanen mana, kawai idan yarinya ba ta da lafiya se kira wani, kwazgwamemen ƙato ya rufu a kanta,nace in mata rubutu ya isa amma babanta yaƙi"

"Kaga Sunusi, har yanzu fa baka Aureta ba, suna da cikakken iko akan 'yar su, kai ka fiye Matsala wallahi"

"Wace irin matsala? Ya ni da matata ba zan kishi a kanta ba, ni bama wannan ba, ina ga nayi nasara akan wannan yaron da take kulawa Sadik, naga bam sake ganinsa ba, yanzu ɗan gidan waccan matar ne naga yana rawar kai da shishshsige mata, wallahi idan be wasa ba idan nai masa wani zazzafan aikin, se ya kusa haukacewa"

Haladu yace "Subhanallah, Sunusi wannan kuma ai kazo da son zuciya, ya zaka haukata mutum akan abunda be kai ya kawo ba"

"Agurinka ne be kai ya kawo ba, ni agurina lamari ne me girman gaske, kana ganinsa da kyau da Mota, ni ina yawo a ƙasa haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login