Showing 195001 words to 198000 words out of 259198 words
Chapter 66 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
kula da ni da min sauran ayyukan gida?"
"Kayi da kanka mana"
Sadik yace "Shikenan, tun da hakane, ki koma in ya so se a kawomin Khairat ta dinga kula da ni"
"Abunda yafi Khairat za'a kawo maka, ɗagani"
"To meye kuma na fushi, bayan ke kika ce zaki tafi"
"To na fasa" ta faɗa tana murguɗa baki.
Yace "Aikuwa se kin tafi, dama duk kin isheni, rigimammiya Kawai"
"Ba zan tafi ɗin ba" tai maganar tana share hawayen fuskarta.
Yai murmushi Sannan Yace "Stop crying, zamu je hutu insha Allah, ni kaina ina son zuwa Nigeria, ji nake akwai wani mahimmin abu da Yakamata in yi, amma na manta menene, amma zamuje tun da haka kike so"
Nana tai murmushi, tare da kwantar da kanta a na, Sadik da ke kafaɗarta.
Shiru ya ɗan gudana a tsakanin su, sannan Sadik yace "ke ya naji Kamar jikin ki na ɗaukar zafi ne?"
Nana tace "Wallahi nima ban sani ba, haka nan se in dinga jin sanyi sosai, se kuma zazzaɓi, se kuma anjima ya sauka"
"Kuma ba ki gayamin ba, se ya kwantar da ke tukuna?"
Nana tace "ai ba wani sosai yake kamani ba, shiyasa"
Yace "duk da haka yakamata muje Asibiti a duba ki"
Tace "to Besty, yadda kace, amma wallahi ba za'aimin allura ba"
"Koma dai meya ya kama yi miki za'ai, insha Allah kuma Allura ce".
"To ɗagani, tun da Mugun fata kake min"
Sadik ya ƙi ɗaga ta se murmushi da yake faman yi.
"Na shiga uku Mummy, cikina ciwo yake zan mutu, dan Allah ki taimaka min!"
Mummy tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, na rasa wannan ciwon ciki da kike fama haka Lilly, bari in wa Peter magana, ya zo ya kaimu Asibiti.
Sosai Lilly take kuka, tare da riƙe cikin ta tana wani irin murƙususu, idanunta duk suka yo warwaje!
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi a can.
Sosai Farhan ta zage, ta zazzage abunda ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya tsawon tasowarta, wanda ita kanta Umman ba ta san hakan cutarwa ne ga Farhan ɗin ba, ciki har da yadda ta ke nuna banbanci tsakanin ta da ƙannenta.
Fuskar Farhan duk hawaye tace "Umma na azabtu da wannan al'ada da bata da tushe a addini, Rayuwata ta shiga cikin garari, da kina jana a jiki ƙila da kin nusar dani illar soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, amma baki haka ba se da bakin alƙalami ya riga ya bushe, kuma still kina sake ɗoramin laifi, ina roƙonki idan wani laifin nai miki, da ya sa kike min haka, Allah ya baki haƙuri, ki yafemin"
Tana gama maganar ta tashi Fuuuuu za tai waje. Baban Huzaifa yace "dawo ki zauna ba mu gama maganar ba ai"
Farhan ta dawo ta zauna tana sheshsheƙar kuka
Baban Huzaifa ya ja ajiyar zuciya yace "gaskiya ɗan uwa kunyi kuskure, yanzu dama irin wannan rayuwar Yarinyar nan take haka? Na san muna karantawa yaranmu na fari, kamar yadda muma a kai a kanmu a zamanin mu, amma wannan zamanin idan kai haka akan yara dole su lalace"
Cikin damuwa Abba yace "wallahi ɗan uwa, ba yadda ban ba akan ta dinga sassautawa yarinyar nan, amma ta ƙi gane hakan, bayan haka muna da matuƙar tsanani akan tarbiyyar yaranmu, mussaman ita da ita kaɗaice mace a cikin yaran, Allah ya nuna mana dabarar ka ba ita ke shirya maka ɗa ba, amma Alhamdilillah daidai gwargwado mun lura da tarbiyyar Farhan, se dai kam ta rasa soyayyar uwa da ja a jiki"
Umma ta share hawaye tace "duk da haka wannan ba hujja ba ce, yaran da iyayen su suka mutu suka bar su fa?"
Malam Zakari yace "wannan daban, wannan mutuwa su kai, amma ke kina raye tana kallonki kina kallonta, amma ba zata iya zuwa ta sameki ta gaya miki damuwar ta taji daɗi ba, gaskiya akwai matsala, kuma yanzu fisabilillahi kun san ba ta son wannan yaron amma kuka dage se kun aura mata shi?"
Abba yace "wallahi ni ban san ba ta son shi ba, kuma ni ban niyyar yi mata aure yanzu ba ma, mahaifiyarta ce ta damu, ga surutu da aka fara wai ana gani ana kawota gida a Mota, amma ban taɓa sanin ba ta ƙaunar Yaron ba, kuma ni ban san tana son wani ba"
Malam Zakari yace "Farhana kin ɓata rawar ki da tsalle, kin tashi yarinya me ilimi da addini, amma kalli yadda ki ka maida kan ki 'yar shaye shaye me zaman kanta, kinwa kan ki adalci kenan?"
Farhan ta girgiza kai tace "Baba ƙaddara ce"
Yace "ba ƙaddara ba ce Farhan, ganganci ne ke ki ka kai kanki, kar ki sake ɗorawa ƙaddara"
"Baba, ni kaina ban san shaye shaye na fara ba, na fara ne da rashin iya bacci, ga damuwa na cin raina ji nake kamar kaina ze tarwatse, na fara neman maganin rage damuwa da saka bacci, har yunƙurin kashe kaina nai, Huzaifa ya hana ni, a hankali ya zamana idan ban sha abun maye ba, bana bacci, saitin zuciyata yai ta min zafi, nai haka ne duk dan in manta damuwa ta"
"To yanzu ina shi Yaron da kike so ɗin?" Malam Zakari ya tambayi Farhan yana tsareta da ido.
Tai murmushi me ciwo tace "ba Soyayya ba ce, RUƊIN ƘURUCIYA ne, hadda Soyayyar sa a cikin abunda ya jefani a damuwa, mutane sun sha gayamin Soyayyar mu RUƊIN ƘURUCIYA ce, amma na kasa yadda, ya jani a jiki, yana son farinciki na yana gudun damuwata, yana bani kulawa, na saki jiki da shi na sakankance, se ji nai yayi Aure ya tafi karatu ƙasar waje, ga shi ni kuma za'a Auran wanda ban taɓa ƙaunarsa ba a raina ba"
Abba yace "a ina shi Yaron yake ɗan waye?"
Farhan tace "Abba dan Allah a bar maganar nan, wallahi ba na son tunowa da shi, ni dai ku cigaba da yi min Addu'a Allah ya shirya ni ya sa in dena abunda nake"
Abba ze kuma magana Malam Zakari ya girgiza masa kai alamar yai Shiru ya kalli Farhan yace "munji duk bayanan ki, an miki ba daidai ba ta wani fannin amma ta wani fannin ke ma me laifi ce, yanzu kiyi ƙoƙari ki tuba ga Allah, ki dena wannan yawace yawacen da kike, bin maza baze haifar miki da ɗa me ido ba"
Yaita yiwa Farhan Nasiha, ta sunkuyar da kai tana sauraren sa, yai ya ƙare Sannan ta miƙe, ta fita waje, kayan Abinci yara suka dinga shigowa da su, suka tsaya suka bi kayan da ido, Farhan ta dawo cikin gidan, Abba yace "wannan na menene?"
Farhan tace "kayan Abinci ne Abba na kawo muku"
Umma tace "ba zamu ci kayan haram ba, ki kwashe kayanki"
Farhan tace "Umma ta ya kika san kayan haram ne? Kyautar su aka bani nima, amma bana haram bane dama kayan al'umma ne nima aka bani, Allah ya nunan lokacin da Umma zaki bani kariya ko inga soyayya ta a cikin idanun ki, ko naji abunda 'ya'ya suke ji" tana gama faɗin haka tai waje,se ƙarar kunna mota suka ji, ko a ina ta samo mota har ta iya tuƙawa da wannan ƙananun shekarun naat oho mata.
Malam Zakari yai taiwa Umma Nasiha akan tai haƙuri da halin da Farhan ta shiga, ta janyota a jiki, ko Allah ze sa a samu ta dawo hanya.
Ita Umma har ga Allah lokacin da ta haifi Farhan, tana ƙaunar 'yar ta sosai da sosai, sedai a garinsu ta haifeta, kuma seda Farhan tai wata uku Sannan ta dawo, tun a can garin dama sun saba, ɗan fari ba a jansa a jiki sam.
Kuma ga ƙarancin shekaru lokacin, da tai wani yunƙuri na bawa Farhan kulawa se ayo caaa a kanta ana cewa ba ta da Kunya, ko Shayar da Farhan ba ta iya sakin jiki tayi, a garin gudun kar tai wani abu da zesa ace tai rashin kunya, ta fara watsi da lamarin Farhan, se ta ke ganin ai Kamar ba'a san ɗan fari ne, dan haka har suka dawo gida sam ba ta wani kula da Farhan.
Watan Farhan biyar ta samu wani cikin, dan haka tai ta fama da laulayi, daga can garinsu aka zo aka tafi da Farhan, aka yayeta tana da wata takwas, wataran Abba yaje duba Farhan a garin, ya tarar ba ta da lafiya kuma anƙi kai ta Asibiti se jiƙe jiƙe ake mata a gida, aiko yace da ita ze tafi, an kai ruwa rana sosai da Abba, tare da ƙananun maganganu akan rashin ta ido da ya nuna, dan seda Auren ya so ya samu matsala.
Umma taji haushin Abunda Abba yai Sosai, a cewarta ya zubar mata da mutunci a rigarsu.
Hakan ya sa ba ta wani bi ta kan Farhan, tana fama da laulayinta kusan Abba ne yakewa Farhan Komai, a haka har Umma ta haihu, ta haifi Amir aka sa masa sunan mahaifinta, nan ta ɗau ƙaunar duniya ta ɗora akan Amir, amma ba ta damu da Farhan ba, a haka Farhan ta tashi.
Wani uban gumi ne yake ketowa Sadik, tun bayan da sakamakon gwajin da akai wa Nana ya tabattar da tana da juna biyu har na watanni uku da sati biyu, idan lissafin sa daidai ne, to a karon farko da ya kasance da ita ta samu cikin turƙashi!.
Ya san akwai daru na gaske, idan har Nana ta san tana ɗauke da juna biyu, shi kansa wata irin kunya ce ta kama shi, da wani ido ze kalli iyayensa musamman Mother, da ta ke ta kumfar bakin ita ɗanta be isa Aure ba, ga kashedin ta a gareshi na babu ruwansa da Nana.
Da wani idon ze kalli Inna, da ya gama ce musu baya son jikarsu, katsam se su koma a ganta da ciki, ya fito da niyyar tafiya pharmacy ya karɓo magunan da likita ya tura musu, yaje ya karɓa, ya hangi Nana tana ta ciye ciyenta hankalinta a kwance tana kalle kalle, gaba ɗaya ƙuruciyarta ta sake fitowa Yarinya ce sharaf, chocolate ɗin da take sha, duk ta ɓata gefen bakinta da ita, kuma hankali kwance take sha, tan kaɗa ƙafafuwan ta.
Sadik ya kalli kamsa a madubi, shi kamsa kunyar kansa ce ta kama shi, as he is, he impregnent this little girl Subhanallah, abun kunya ya afku.
Yaje ya karɓo mata maganin, ya zo in da take zaune ya kalleta yace "taso mu tafi gida"
Ta ɗan ɓata fuska tace "ɗan yi haƙuri in ƙara hutawa, ƙamshin Asibitin ne yai min daɗi"
"Meye abun so a nan, ban da warin magani ba abunda Asibitin yake fa"
Nana tace "Wallahi ni dai ya min daɗi"
"Kimga ta so mu tafi, ko in barki a nan ina son zan shiga school ne, muna da training yau"
Nana ta tashi ta bi bayan Sadik, suna tafe a hanya tana ta sashi kashe kuɗi, tace zata ci wannan tace za ta ci wancan, shikam abun duniya ya ishe shi.
Tunani yake ta yaya ciki ze rayu a jikin Nana, da wani idon za su kalli iyayensu idan sun koma gida?"
Suna zuwa gida, Nana tun a falo ta cire kayan jikinta, ta bi lafiyar kujera ta kwanta, dan abu kaɗan yanzu se ta ji ta gaji, Sadik ya ɗan ƙurawa cikin ta ido, tabbas cikin ta ya ɗan ɗaga.
"Wai ya na ga kana ta kallona ne, Lafiya kuwa?"
Yace "Lafiya ƙalau"
Tace "yawwa, ni ba ka gayamin me ma sukace ba fa"
Ya ɗan yi ajiyar zuciya yace "ba su ce komai ba, magunguna ne ga su nan in kin tashi shiga ɗaki seki tafi da su"
Nana tace "to, amma meye yake damun?"
"Malarai ce kawai"
"Malarai kuma? A ina sauro ya ganni ya ciza, ai nan ƙasar babu sauro, ta yaya na samu malarai?"
Nana kenan, akwai shegiyar tambaya da kaifin basira.
Sadik yace "ke bana son yawan surutu, da wannan tambayoyin naki, typhoid ne kawai, da Ulcer kuma sunce idan ba kya cin Abinci mutuwa zaki, hanjinki ya tsitsinke"
Zare ido Nana tai tace "Na shiga uku, wani irin hanjina ya tsitsinke kamar taliya, wannan ai ba maganar da ya dace a gayawa mara lafiya bane"
"Ai in dai ba zaki kula da kan ki ba, ki maida kai ki dinga cin abinci ba, abunda ze faru da ke kenan"
"To ni ba amai nake ba idan naci, ba abunda ze sameni Insha Allah, ji min mutane da kalen tsiya" tai ta mitarta, Yayin da Sadik gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake.
"Lilly ki gayamin Wanda yai miki cikin nan tun kan mahaifinki ya dawo, wallahi idan kika bari ya dawo daga ni har ke mun shiga uku, ki gayamin waye?"
Sosai Lilly take kuka tare da girgiza kai, amma ta kasa furta komai, se hawaye da ke zuba daga idanunta, ga wani uban gumi da ta haɗa, kamar me naƙuda.
Cikin zafin zuciya Mummy tace "zaki gayamin ne ko sena danne ki na shaƙeki, kan shi ya dawo ya kashe ki?"
"Mummy ban sani ba wallahi" Lilly tai Maganar da ƙyar kamar numfashinta ze ɗauke.
"Ƙarya kike munafuka, shegiya maƙaryaciya, ni zaki rainawa hankali, likita ya tabbatar min da ba wannan ne karonki na farko ba, wai Lilly har kin san ki ɗau ciki ki zubar, a wannan ƙananan shekarun naki Lilly, zaki gayamin waye ko sena yanka ki"
"Wallahi Mummy ban sani ba" tai maganar tana ja da baya.
"Kika kuma cemin ba ki sani ba, sena gwara kanki na fasa miki kai, ni zaki wa ƙarya? A ruwa kika sha dan ubanki? Ko a iska kika shaƙa, wane tsinanan ne yai miki ciki, zan farke wannan ɗinkin da ke jikinki idan baki gayamin gaskiya ba" Mummy tai maganar tana shaƙo wuyan Lilly.
Jikin Lilly na wata irin rawa, laɓɓanta se kakkarwa suke, ga gumi da yake ɗiga daga jikinta tamkar ana narka mai, ta janyo numfashinta da ke barazanar barin huhunta tace "zan faɗa miki Mummy, zan faɗa amma dan Allah kar ki kashe ni, ki cikani ba na iya shaƙar numfashi"
Tai jifa da Lilly a gurin, take Lilly ta fasa wata uwar ƙara, ta dafe cikin ta in daa a kai mata aiki, abunka da uwa, nan da nan kuma hankalin Mummy ya tashi, ta yo kan Lilly da gudu tana taɓata.
Tana duba gurin da a kai mata ɗinkin, taga yana tsatsafar da jini, alamar fama gurin tai, da fari ji tai kamar tai banza da ita ta ƙyaleta, amma taji ba zata iya ba, haka ta ɗau mayafi suka koma Asibiti.
Se da aka sake dressing ɗin gurin, likita yai ta mita yace "Hajiya, ki kwantar da hankalinki wannan abun ba akan ku aka fara ba, sakaci ne dai an riga anyi shi, aikin gama ya gama, duk wata tuhuma da za kuyi mata, ku bari ta warke ta samu Lafiya tukuna, idan ba haka ba, zaku mayar mana da aiki baya ne, idan tana famawa gurin baze warke da wuri ba" haka yaita faɗa sannan ya sallame su suka koma gida.
Lilly ta rasa in da za ta saka ranta, dan gaba ɗaya Mummy tai watsi da ita ba ta shiga harkarta, gashi ta kashe wayarta, duk wanda yaji labarina ba ta da lafiya ya zo dubiya, se ace ai appendicities ne yake damunta a kai mata aiki.
Faruk ne ke kwance yana video Call da Sadik, "Autan Mother, wai dan Allah me kake ci ne haka, ka wani zama ƙato Kamar ba kai ba"
Sadik yace "hutu da kwanciyar hankali mana"
"Lallai kam, kai karatu yana sa mutane su rame, amma kai ka zama ƙato, ni ba ka ga yadda duk na rame ba?"
Sadik yai murmushi yace "ni da kai ɗaya ne? Ko ka manta ina da Aure ai akwai banbanci"
Faruk ya kwashe da dariya yace "kaga ɗan banza, ni zaka gayawa Magana, wai kana da Aure, kamar ba kuka ka dinga yi kana cewa kai ba ka so ba"
Sadik yai dariya yace "to yanzu ina so, ya ranka?"
Faruk yace "rai na fes, ina Nanan?"
"Wai ina ruwanka da mata ta ne?"
"Allah ya shirye ka Sadik, na san wataƙila Mother ta kusa ɗaukan jika ko?"
Gaban Sadik ya faɗi, amma ya maze yace "Ni yaro ne gaskiya, akace Mother za ta ɗau jika daga gurinmu ai kashin mu ya bushe"
"Ba wani kashinku ya bushe, Kamar ba nan ka ke zuwa ka sameni kake gayamin wai kai Aure kake so ba, kai akwai wadda ka ke so something like that"
Sadik yai shiru ya fara tunani, wace ce yake so to? Kamar wani abu ya taɓa faruwa, amma ya kasa tunawa.
"Friend, wai me kake a ɗaki ne, ka zo ka taya ni kwalemar falon nan"
Sadik ya kalli Nana yace, zo ku gaisa da Faruk.
Murmushi Nana tai ta ƙaraso ta kwanta a jikin Sadik tace "Yaya Faruk ya kake?"
Faruk yace "Lafiya ƙalau Nana, ya karatu?"
"Alhamdilillah, Yaushe zaka zo ka ganmu"?
Faruk yace "Nana ina Makaranta nima, tunda na tafi bana samun lokaci isashe, amma na so zuwa nima in ganku"
Nana tace "Allah ya temaka, ai mun kusa zuwa Nigeria hutu, ko Friend?" Tai maganar tana kallon Sadik.
Sadik yace "yaushe mu kai haka dake?"
"Kai ne fa kace zamu je Nigeria in kunyi hutu"
"To mun fasa"
Hararar Sadik tai tare da tura baki, Faruk ba ƙaramin farin ciki yai ba, ganin Sadik da Nana suna cikin kwanciyar hankali, da alama babu wata damuwa a tare da su.
Faruk yace "mhmm, nikam se anjiman ku, naga abun naku bana ƙare bane"
Sadik yace "Allah sarki Gwauro, ka huta lafiya muma bari muje muyi feeding ɗin juna"
"Kaci ubanka ne, nine gwauro ko? Zan kama ka ne"
Sadik ya ajiye system ɗin tare da ɗan lumshe ido.
Nana ta kalli Fuskar Sadik, zuwa ƙirjinsa, wani kwantaccen gashi ya fito a ƙirjinsa, gashi gemu ya fara fitowa a haɓarsa.
Murmushi tai, ta kai hannu gemunsa ta shafa Sannan tace "su friend an girma, mun fara gemu irin na Yaya Faruk"
Buɗe idonsa yai ya kalleta yace "Au ke haryanzu a gurinki ban girma ba?"
"To ai se mutum yai gemu, Sannan ya zama babba, Allah yasa kai ma naka yai yawa kamar irin na Yaya Faruk"
"Hmmm, kina son gemu ne?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To daga yau ba zaki sake gaisawa da Faruk ba, tun da gemunsa burge ki yake"
Ta ɗan ɓata fuska sannan tace "daga na ce Allah ya sa gemunka ya zama irin nasa shine kuma abun Magana?"
"Eh ɗin, ɗagani ma"
Ƙara narke masa tai a jiki tana kukan shagwaɓa tace "ni fa bance yana burgeni ba, kawai cewa nai Allah yasa gemunka yai irin nasa"
"To naji, amma daga yau