Showing 240001 words to 243000 words out of 259198 words

Chapter 81 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

ya Auramin ita muka tafi karatu tare, ƙanwata ce, amma dan Allah ka tayani bata haƙuri Wallahi ina sonta da gaske, ni ba ruwana da wace rayuwa tayi, komenene nasan nine sila, amma dan Allah ta yafemin, ka ga ni yanzu haka, nai magana da babana, za'a zo tambayar min Aurenta, ina da halin da zan riƙesu gaba ɗaya".

Huzaifa ya ɗanyi shiru sannan yace "to ai anyi Magana da wani, ze kawo nasa kuɗin"

Sadik yace "ina jin tsoron ta auri wanda ze wulaƙanta ta a gaba, saboda tambarin da taiwa kanta, ni ɗin dai tunda nine silar komai ban isa in mata gori ko wulaƙanci ba, saboda nine sila, yanzu idan ka ban Alqur'ani zan dafa in rantse maka Farhan duk yawon Hotel ɗin da take ba ta bin maza, saboda Soyayar kanta nine na koya mata, nasan halinta kamar yunwar cikina, shikuwa wancan ba si da wannan tabbacin, kai nifa ko mazan take bi, naji na gani ina so zan aureta in zauna da ita ina sonta, ita na fara so, dan Allah ka tayani rarrashinta, da kuma bawa Abba haƙuri akan ya amince dan Allah"

Gaba ɗaya tausayin Sadik da na Farhan ya kama shi, yai ajiyar zuciya yace "bakomai, Allah ya wuce mana gaba, bari inje in mata magana"

Sadik yace "to shikenan nagode sosai"

Sadik be wani sa ran fitowar Farhan ba, kuma sam ba ya jin fargabar Abba ya sake ganinsa, ko da kuwa ze kuma yi masa faɗa idan ya ganshi.

Yana nan tsaye yana tunani, ya ɗaga kai ya hango Farhan, cikin dogon hijjabi, a hankali ta ƙaraso in da yake tsaye ta kalleshi, ya ƙara rama se tsawo, yana cikin farar jallabiya, sedai ya ƙara kwarjini sosai, a ɗan tsiwace tace "Sannu ko"

Ɗan tsura mata ido yai sannan yace "Yawwa ya kike?"

"Lafiya ƙalau, ashe Allah yaiwa kakanku rasuwa"

Sadik yace "Wallahi kuwa, Hakimi sa'i yayi, ashe kin samu labari?"

Tace "eh na gani a social media, ina Addu'a Allah yai masa rahama, yasa aljanna ce makomarsa, ku kuma Allah ya baku haƙurin jure rashin sa"

Sadik yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nagode sosai da sosai Princess" juyawa tai za ta koma yace "A'a Farhan ya haka, ina zaki kuma?"

"Au har ka manta kashedin da Abba yai maka ne? In ka manta ni ba manta ba"

"Nasan da kashedin Abba, kuma ba dan in fatali da kashedin na sa na zo ba, Abba ne za su zo nema min Aurenki ranar Asabar insha Allah".

"Wai kai Sadik ba ka ganewa ne? Sau nawa zan gaya maka wani ya riga ka, Aure zanyi dan Allah ka ƙyalemin rayuwata ta huta"

"Ke zaki bada damar rayuwata da taki su huta"

"Aikuwa sedai kar su huta, dan ranar Asbar Abbas ze kawon kuɗin Aure, kuma sati biyu za'a saka"

"Hakan ba damuwa ta bace, kaina na sani" daga haka ya juya ya barta a tsaye tana jinjinawa ƙarfin halin Sadik.




Ganin damuwar ta Nana tayi yawa, ya sa Abba ya nema mata makaranta, a satin ya sa direba ya fara kaita, ya ɗakkota Sahal kuma yana gida, sedai babu wanda za'a cewa Nana matar Aurece ya yadda.
Abba yai mata nasiha sosai akan ta saki ranta ta maida hankalinta tai karatu, sannan ta kula sosai tunda ta san cewar ita matar Aurece.
Nana ta koma ɓangaren su na BQ, sedai tsakaninta da Sadik sedai ido, gaba ɗaya ta dena walwala ta zama kamar wata me jinya, daga salla se kwanciya, se taji yunwa zata kassarata Sannan ta nemi Abinci ta ci.

Umman Farhan na ta murna Farhan ta dena yawo, gashi za'a kawo kuɗin Aurenta, se murna take yi, akan za ta samu ta aurar da ita, ta huta da wannan zullumi da tashin hankali, se Addu'a take Allah ya tabattar da lamarin nan.

Farhan kuwa na ɗakinta, tana kwance tana karatun Alkur'ani a hankali, tana tunanin yadda ta bar makaranta ta ada karatunta na Addini, gaba ɗaya taji wata Nadama na zuwar mata.

"Farhan! Farhan kina ina?" Ta jiyo muryar Abba a tsakar gida.

Da sauri ta tashi ta fita, tana tunanin kiran Me Abba yake mata haka?.

"Burinki ya cika, a karo na barkatai kin kuma maida ni mutumin banza, shine kika zagaya ki ka samu ɗan uwa kika ce masa wannan yaron kike so, kwana biyar ashe iyayensa sun kai kuɗi, ina nan na saki baki likitan nan iyayensa su kai kuɗi, ashe ni kika mayar mutumin banza, Yaron da yai silar ɓata rayuwar ki, nai miki iyaka da shi amma kika zaɓe shi a kaina, to kije gaki gashi nan, tunda kin fifita shi a kaina kije ki ƙarata, ba dai ke kwaɗayi ba zai Auri yaro ƙarami kamar wannan kije, gaki nan gashi ina ga yaron nan shine ajalinki" ƙura masa ido Farhan tai, ba tare da ta iya firta wani abu ba, saboda tsananin mamaki ta ma rasa wane irin tunani za tai, waye ya kai Sadik gurin Malam Zakari? Ya akai ba wanda ya gayamata an kai kuɗin? Kuma shi kansa Sadik ɗin ba ta sake ganinsa ba? Tambayoyi barkatai suka cika mata kai, ta ina zata fara yiwa Abba bayanin bata san maganar da yake ba se yanzu? Lokacin da take yawonta ma be mata Wannan alkaba'in ba se yanzu akan Sadik, aiko me za'ai ba ita ba Auren Sadik musamman da Abba yai mata wannan maganganun, kuma ba zata zama me cin Amana ba, idan akai haka ba'aiwa Abbas adalci ba"

Tun da Nana ta samu labarin kai kuɗin nan, ta ƙara takure kanta, ta shiga wata damuwar saboda ba abunda take hangowa se bankwana da ɗan ragowar farinciki da ya rage mata.

Abba ya tura Sadik ya duba gidan da yake so, a gidajen Abban, wanda Hakimi kan ya rasu, seda ya bada kuɗin da za'a saiwa Sadik gida a matsayin gudunmawarsa.

Sadik ya dawo daga sallar isha'i, ya shiga suyi magana da Abba, ya tarar da Usman, da Abba a zaune da alama Magana suke me mahimmanci.

Abba yace "madalla dama kai muke jira"

Sadik ya ƙarasa ya zauna yana jiran yaji jiran me ake masa?

Abba ya miƙa masa wata takarda yace "duba Wannan"

Sadik ya karɓa ya buɗe ya fara karantar, sedai tun ba aje ko ina ba, jikinsa ya hau rawa, gumi ya wanke masa goshi ya shiga tashin hankali.

Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680



AFUWAN BA EDITING.






Bakomai ne a cikin takardar ba face, bayani ne akayi shi dogo akan Farhan, na miyagun halayenta na shaye shaye, da bin maza da takeyi, da gantalin kwana a hotel.
Sadik yayi mamakin wani ƙasaitaccen munafukin ne ya zauna ya shirya wannan kitumurmurar.

Abba yace "ina fatan ka karanta abunda ke ciki?".

Sadik ya jinjina kai jiki a sanyaye, yace "Abba sharri....

"Dakata Sadik, kan in kiraka in nuna maka takardar nan, yau kwananta uku a gidan nan, na saka Usman yaje ya bincika min gaskiyar maganar ne, amma maganganun da ke fitowa, akan yarinyar suna cin karo da juna.

Wasu na sheda mutuniyar kirki ce, wasu na sheda akasin haka, amma batu mafi rinjaye, banji daɗin bayanan da aka samo min akan yarinyar ba, kai ka san a haka take amma kaje zaka jajubo ta ka sakamana ita a cikin zuriyar mu? To da sake ba zan lamunci hakan ba, kaje zan cigaba da bincike hukunci kuma zaga abunda ya dace".

"Abba, dan Allah idan ka tashi yanke hukuncin, ka yanke wanda zan iya ɗauka dan Allah kar ka yanke wanda ze rabani da Farhan"

Usman yace "wai anya Sadik ba ka fara shaye shaye ba kuwa? Ko ba da hausa aka rubuta takardar da ka karanta ba"

Sadik yace "Na sani, na karanta amma dan Allah ku fahimce ni, ni dai dan Allah karku rabani da Farhan"

Usman yace "Anya Abba ba asiri a kaiwa Yaron nan ba?"

Abba yace "ba wani Asiri da akai masa, shashanci ne kawai, tashi ka bawa mutane guri"

Sadik a ransa yace 'Abba ba zaku gane dalilin da ya sa na dage ba, duk da kun nuna ba kwa so' haka nan jiki a sanyaye ya bar sashin, yana tunanin waye da wannan kuturun baƙin munafunci da ya kawo Wannan takardar?.

Jiki ba daɗi ya isa nasu part ɗin, Nana tana nan zaune tana aikin nata na tunani, duk ta rame tai wani iri, Sahal na bacci ita kuma ta zubawa guri ɗaya ido, da alama tai zurfin gaske a tunanin.
A hankali Sadik ya ɗanyi gyaran murya, ta ɗago ta kalleshi, amma ta kasa dena kallonsa kuma ta gaza furta komai.
Ya kalli in da aka kawo kwanukan Abinci da alama ba taci ba, ya ƙarasa ya buɗe babban food flask ɗin, tuwon shinkafa ne da miyar taushe ta sha nama, ya zubo kaɗan ya zo gaban Nana ya zauna ya ajiye mata, yana tausayinta sosai ba ya son ya shiga hakkinta da yawa, gaba ɗaya ta dena walwala ta takure kanta fiye da kima, ba'a ta ɓa yiwa Nana rasuwa ba, dan haka dole wannan ta shigeta sosai.

"Bismillah, ci Abinci" ya faɗa cikin bada umarni.

"Na ƙoshi" ta bashi amsa.

"Kika ƙoshi da kika ci me?"

"Na sha shayi" ta bashi amsa.

"Abinci zaki ci, Nana meyasa kike son sekin illata kanki ne? Kin saka damuwa a ranki, ga yaron nam shi ba saurarar miki yake ba idan ya na jin yunwa, haba ki zama me karɓar ƙaddara mana, kiyi haƙuri ki ci-gaba da yiwa Hakimi addu'a, in kuma kema so kike ki rasa ranki kuma se inji"

"Saboda iyayenka suna raye, uwa da uba, kuma yanzu Magana ake ta zaka Auri wadda kake so, ni ban san uwar ba ban san uban ba, babban bango a rayuwata ya faɗi, ban taɓa ɗanɗanan ɗacin rashi ba se a wannan karon. Nima fa ba jin daɗin yanayin da nake ciki na nake, nayi iya ƙoƙarina amma na kasa daurewa, komai ya fita daga raina, dan Allah ka ƙyaleni idan da rabon in koma yadda nake shikenan, in kuma nima a zan mutu shikenan Ka bawa Mother Sahal, ko Su Anty Jidda"

"Meyasa zan ƙyaleki? Yadda kike cewa farincikin Sahal da naki ya na tattarr da farincikina, haka nima farimcikina da na Sahal suna tattare da naki ne, insha Allah da kanmu zamu raini Sahal muyi tarbiyyar sa, ki dena irin wannan tunanin, komai ze wuce Insha Allah, kan ki rasa Hakimi mahaifinki suka rasa, kuma suka cigaba da rayuwa, har kika girma, kowa yana jin haka idan yai rashin wani abu da yake so, dan Allah ki kwantar da hankalinki ki dena koke koken nan".

"He is very kind and generous, wannan halin nasa na tausayi da kulawa ne yasa na fara son shi, ashe shi da wadda yake so, kar ya cigaba da yaudarata da wannan halin nasa, yasa in cigaba da son sa, amma hanklinsa ya koma kan wata gaba ɗaya" a zuciyarta tai ta wannan tunanin, a zahiri kuma take kallonsa yadda yake ta rarashinta cikin kulawa da tausayawa.





"Doctor magana nake amma kai banza dani, meyasa zaka min haka? Akan me meyasa? Ka dena ɗaga wayata ka dena zuwa gidanmu, kuma kana jina ina ta magana kai banza da ni" Farhan tai Maganar cikin ɓacin rai.
Abbas ya tashi yaje ya kulle ƙofar Office ɗinsa, Sannan ya jingina da ƙofar ya kalli Farhan yace 'gayamin, me kike so ayi, ko kuma meye baki gane ba?"

"Au kana nufin duk wannan ɓaɓatun da nake yi ba ka ma san me nake cewa ba? Ina can ina jiran ka ka kai kuɗin Aurena, kawai se inji Sadik ya kaimin kuɗin Aure how? Meyasa haka zata faru? Meyasa za kai min haka?"

"Au haba, dagaske Sadik ne ya kai kuɗin Auren, Masha Allah, Allah ya Sanya alkhairi yasa ayi damu"

Kawai Farhan ta fashe da kuka, kuka sosai har da sheshsheƙa.

Ɗan murmushin ƙarfin hali yai yace "Am sorry, ba ina nufin in saki kuka bane my dear, Farhan ni babba ne bana son in zama babban banza, ina tausaya muku da ke da Yaron ne, shiyasa na sadaukar masa da ke, a dalilinsa kika faɗa wannan mummunan halin, kuma a hakan ya dawo yace yaji ya gani, dagske yake sonki, mahaifin Huzaifa ne ya nemeni, kuma naje muka tattauna a matsayina na likita, dan shawo kan matsalar ki, muka tsaya a wannan matsaya, ina tayaki murna tare da yi miki fatan Alkhairi"

Cikin kuka tace "dama na sona kake ba? Na ɓata lokacina gurin sonka da tunanin Allah ya musanya min Sadik da kai, ashe kaima yaudarata za kai, yanzu duk azabar da naci saboda Sadik ruhina be cancanci ya huta ba zan koma gareshi, me soyayya RUƊIN ƘURUCIYA ta amfana min? Nagode da wannan sakamako da kai min, na soyayyarka da tunanin zaka tsamo ni daga tsaka me wuyar da nake ciki, Nagode da abinda kai min, kuma ka sani zanje in warware wannan maganar dan ba zan taɓa Auren Sadik ba, gara in cigaba da yawo".

Abbas yace "Subhanallah, haba Farhan ki fuskanci dalilina manax

"Ba wani dalilinka da zan fuskanta, duk mazs kun taru kun maida ni karkatacciyar bishiyarku me daɗin hawa, tamkar wata ƙwallo wannan ya jefawa wannan, in kuka haukatani kun huta ai" ta ƙarasa maganar tare da murza key ɗin ƙofar tai waje.

Abbas ya dafe kai, tare da neman guri ya zauna, ya zaci Farhan za tai murna da wannan abu da yayi, be taɓa tunanin za tai bore ba, shi kansa ba ƙaramin jihadi yai ba gurin haƙura da Aurenta, sedai ko ne haƙura da Auren nata ba, dangin mahaifinsa sunce ba shi ba Auren Farhan, saboda mugun fentin da suka ci karo da shi wajen bincike akan Farhan ɗin.

"Malam, dan Allah ka bi koma a hankali, kar a kuma haihuwa a ragaya a game da yarinyar nan, kaje ka samu Malam Zakarin ku tattauna, kaji ya akai ya karɓi kuɗin wancan yaron maimakon kuɗin gurin likitan".

Abba yace "ba in da zani, ba zasu maida ni mutumin banza ba daga shi har ita, suje suyi yadda suke so, na gaji da halin yarinyar nan da maganar da take janyo mana".

Umma tace "dan Allah kayi haƙuri, in dai wannan ɗin shi tak so, zata zauna da shi ze Aureta a haka ai shikenan, ni babban fatana shine tai Auren nan mu huta gaba ɗaya".

"To shi yanzu likitan idan ya kai nasa kuɗin ya zasu yi kenan? Bayan sun tambaya ance an basu?"

Umma tace "to kaji ance sun kai ɗin ne? Tun yaushe suke cewa zasu kai? Kayi haƙuri kaje ku tattauna"

"Kin san Allah, ba in da zani suje su ƙarata can, ai shima ubanta me ya isa da ita, dan haka ba hannuna".

Sadik yai sallma a ɗakin Nana, ya tarar tana ta shirin makaranta, ga ƙoƙarin shirya Sahal da ya hanat sakat, gaba ɗaya tausayi take ba shi,shi kansa rainon na ƙaramin ƙoƙari take yi ba.

"Makarantar zaki tafi ne?" Yai tambayar yana kallonta.

Tace "eh".

Yace "Ajiye Sahal ɗin, tashi kije Sabo ya kai ki, bari in ƙrasa shirya shi in kaiwa Mother, in an tashi zan zo in ɗakko ki"

Nana tace "to" ta ƙarasa shiryawa ta fita, shikuma Sadik ya ɗau Sahal zuwa gurin Mother.

Ya tarar da ita a falo, tana bawa Talatu umarnin, gyaran kitchen da take so ai mata yau.

Yace "Mother ina kwana" kallo ɗaya taiwa Sadik ta ɗauke kai, ba tare da ta amsa gaisuwar tasa ba ta karɓe Sahal daga hannunsa.

"Mother gaisheki fa nai".

Mother tace "Ai zuwa yanzu Sadik kafi ƙarfin ka gaisheni, ai na tashi daga matsayina na uwarka zuwa wani abu daban, tun da har zaka iya dagewa akan abunda ba na so, Yanzu Sadik ashe yarinyar da ka dage seka Aura ɗin makaranta ɗaya ku kai, bana wannan ba, an tabattar da yarinyar mutuniyar banza ce, har gida aka kawo wa ubanka takadda, kuma ya tura a kai masa bincike aka kuka tabattar masa da hakane, anya Sadik kanawa kanka adalci? Ita wadda kake tare da ita meye ta gaza da har hange hangenka ya hango maka waccan ɗin?" Sadik yai shiru ya kasa furta komai.

Mother tace "Ai shikenan kaje kayi, amma ni dai kama ba da yawuna ba".daga haka ta gyarawa Sahal kwanciyar sa a kafaɗarta da yake bacci yake, ta wuce sashinta da shi.

Sadik ya rasa abunda yake masa daɗi ga ƙoshi ga kwanan yunwa, ko ina babu daɗi, amma yasan wannan Auren da ze yana kan ƙa'idar shari'a sedai ze cigaba da Addu'a Allah ya kawo masa mafita.

Ƙarfe biyar na Yamma Sadik yana ƙofar gidansu Farhan, tun da aka kai kuɗin nan be sake zuwa ba se yau, ya tura Amir yace yai masa sallama da Farhan.
Da Amir ya samu Farhan a tsakar gida ya sanar mata, se cewa tai yaje yace masa ba zata zo ba.
Abba da yake aswaki yace "baki isa ba, tashi ki fita, tashi kan in saɓa miki"
Haka nan ta shiga ta ɗakko hijjabinta, ta saka ta fita ranta a matuƙar ɓace.

Ko da taje zuwa tai ta tsaya ko kallon in da yake taƙi yi.

"Barka da yamma 'yan mata"
"Meye kawoka gurina? Sadik meyasa zakamin haka, da izinin wa kaje kai kuɗin Aurena gurin ƙanin mahaifina?"

"Au sena nemi iznin ki? Ai tun farko na gaya miki"

"Akan me zakamin haka? Ni nace maka na dena sonka ya za'ai mutumin da ya sha wuya gurin ganin dawowar farinciki na, a lokacin da ka gujeni lokaci ɗaya ai masa haka? Na zama butulu irinka kenan?".

Sadik yace "Nine farincikin dama, da na tafi kuma gashi na dawo, dan haka kawai ki dena wannan goce gocen"

"Ba zan dena ba, ba zan dena ba ɗin, bana sonka Sadik bana son ganinka, kuma ba zan Aureka, idan kuma kai gangancin Aurena ka shirya karɓar abunda ba kai zato ba, ni ba butulu bace irinka, Abbas zan Aura, mayaudari kawai" har ta gama masifar kallonta kawai yake yi, tai masifarta ta.

Sadik yace "in kin gama masifar, ina son inji meye tsare-tsaren ki na bikin, kuɗi zan baki ko kayan lefe kike so?"

"Bana so, ka riƙe abunka dan ba zan taɓa Aurenka ba" tai wucewarta cikin gida ta barshi a tsaye yana binta da kallo.

Nana ta dawo a gajiye sosai, ta wuce ta ɗakko Sahal sannan ta koma BQ, dan ta san maybe yana nan yanawa Mother kuka.
Ta tarar ana ta shirye-shirye, Nana tace "Mother, baƙi za'ayi ne?"

Mother tace "A'a Faruk ne ze dawo, ya kammala master's ɗinsa, se abunda ba'a rasa ba"

Nana ta ɗanyi shiru Sannan tace "Mother, ki yiwa Baban Sahal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login