Showing 105001 words to 108000 words out of 259198 words
Chapter 36 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
Hajiyan ta dawo da shi daga tunanin da yake.
Yace "Amm Hajiya, dama Sadik ne yake aike na"
"Yake aiken ka ina?" Tai maganar tana tsare shi da ido.
"Yake aike na, wani guri"
"Wani guri ina? Gurin ba shi da suna ne?"
"A'a Hajiya, amma dai sa da ze fi kyau ki tambaye shi da kan ki"
Ɗan shiru tai sannan tace "shikenan, in kayi sallar azahar kaje gidan Mummy, kace ta baka saƙon ka kawo min"
Yace "to Hajiya, bari in sallar in je"
Daga haka Ya miƙe ya fice daga Falon, yana godewa Allah da ba ta titsiye shi tace lallai se ya gaya mata ba.
Mother na nan zaune a falo, Sega Sadik ya shigo yana 'yan waƙe waƙensa, be kalli in da Mother take ba, ya nufi Kitchen.
"Sadik zo nan" Mother ta kira shi.
Juyowa yai ya dawo in da Mother take, ya nemi guri ya zauna yace "gani"
"Ina kake aiken Malam Ayuba direba, da kusan kullum se ya fita?"
Sadik ya kalli Mother yace "wani abun yace miki ne?"
"A'a be ce min komai ba, na tambaye shi yace in tambayeka, tun ɗazu nake jiransa zan aike shi baya nan"
Sadik yace "eh yana ɗan min wani aiki ne"
"Wane aikin kenan?"
"Mother, wata yarinya ce nasa yake kaiwa gida"
"Ita yarinyar gidansu babu motar da za'a ɗauketa, ko se ubanka ne me arzikin banza na baitil mali?"
Sadik ya ɗan tsuke fuska yace "dan Allah Mother ki dena, da suna da motar ai na zan sa a dinga kaita gidan ba, kuma kamar taimako ne, mu baga motocin nan birjik a gidan nan ba, gamu da ma'aikata, ba fa abun damuwa bane".
"Kaga Sadik ka kiyayeni akan batun matan nan, duk makarantar ku babu wanda zaka ce min gidansu babu motar da ba za'a iya zuwa a ɗauke shi ba, bana son aikin rashin gaskiya fa"
Haushi ne ya kama Sadik, Mother ba dai faɗa ba akan abun da be taka kara ya karya ba, tai ta mita akan abunda ta riga tafi ƙarfinsa.
Miƙewa Sadik yai ya bar mata falon yana kumbure kumburen baki.
A harabar gidan Sadik ya samu Ayuba direba yace "ka gayawa Mother in da nake aiken ka ne?"
"A'a ban gayamata ba, cewa nai kawai ta tambaye ka"
Sadik yace "ok, shikenan"
Ayuba yace "Yawwa, Yarinyar dama tace min wai kar in ƙara zuwa ɗaukan ta, zata dinga tafiya da kanta"
Sadik yace "saboda me tace hakan?"
"Wallahi nima ban sani ba" ya bawa Sadik amsa.
Sadik yai shiru yace "shikenan, bakomai nagode Sosai"
Ya juya ya nufi BQ.
"Sadik ka dena sona ko? Ka dena zuwa in da nake, ka dena duba saƙona, na baka haƙuri kaƙi haƙura ko? shikenan Nagode sosai"
Message ɗin Farhan kenan, da Sadik ya ci karo da shi a wayarsa.
Take se yaji tausayinta, yaga be dace ya wanata haka ba.
Kiran wayarta yai, baiwar Allah ba tai zuciya ba ta ɗaga wayar, kasancewar tana makarantar Islamiyya.
Tana ɗagawa ta sa masa kuka.
"Wayyo Allah, am sorry my dear, na san ban kyauta ba dan Allah ki min Afuwa, wallahi ni kaina kewar ki ta dameni sosai"
Cikin kuka tace "ba wani nan, ka dena sona wallahi ko Abincin kirki ba na iya ci saboda damuwa, Why are you playing with my emotion?"
"Yi haƙuri am really sorry, kina jina?"
"Ni ba abunda zan ji, ka dena sona na gane" ta katse kiran.
Ajiyar zuciya Sadik yai, dole yaje ya ga Farhan yau, dan yana missing ɗin ta sosai da sosai.
A ƙoƙarin kaucewa fushin Abba, yasa da Mother taji Abba da Usman zasu koma ƙauye dubiya, tace zata bisu taje taga jikin Hakimi, ko ta huta da fushin Abba.
Ko da sukaje garin ƙin sakin jikinta tai, dan a fili ta dinga nuna ƙyamar garin, duk da irin tarin tsafta ta Inna.
Nana kuwa dama tunda suka gaisa, ta fita ta basu guri, dan jininsu baya haɗuwa da Mother kwata kwata, dan ba zata manta yadda Mother ta dinga mata ba a ɗan zaman da su kai a gidan su ba.
Shi Usman kam dama kamar yadda yake ɗabi'arsa, tunda aka gaisa yaiwa Hakimi ya jiki, ya koma gefe ya tsuke bakinsa, se idan Wani ne yai masa Magana se ya amsa.
Abba yace "Alhaji jikin nan naka kamar babu wani cigaba fa, ni dai dan Allah ka bari mu tafi da kai a duba ka yadda yakamata"
Hakimi yace "A'a, Asibitin nan namu baka ga yadda suke ƙoƙarin su ba, sunce hadda shekaru ma da suka ja, ka kalla fa cikin ikon Allah da ƙudurar sa naga Auren jikana namiji, ai Alhamdilillah ko yau muka tafi Allah yai mana ni'ima se fatan dacewa, ina Faruku ne wannan karon ba ka zomin da shi ba"
Abba yace "ai ka san yana ta fama da shirye shiryen tafiyar sa, yaje yin clearance ne, ina ga a satin nan, ze tafi ƙaro karatu Insha Allah"
Hakimi yace "to su haka zasu ƙare a yawon neman boko, baze Aure ba tukuna"
Mother da ba da ita suke hirar ba tai farat tace "Ranka ya daɗe, ai haryanzu yaro ne, kallon dai babba kuke masa amma yarone ƙarami, gara tunda ƙuriciyar su suyi karatun kan nauyi ya hau kansu"
"Eh hakane kam, to shi ɗaya abokin nawa fa, da yace wata shekarar zan koma ɗaurin Aurensa, kun masa Auren ne?"
Abba yai dariya yace "Allah ya temake ka, yayansa ma be yi ba se shi? Ai shirme ne kawai irin na Sadik, nan da 'yan watanni shima yana Turai ƙaro karatu"
Hakimi yace "ku dai naga kun bawa Boko mahimmanci sosai, ko da yake ai Ilimi abune me mahimmanci, amma Yakamata a dinga sara ana duban bakin gatari, ni karatun ma da ze yuwu suyi shi a gabanku kuna sa ido yafi ka kai yaro turai, baka san me yake ba"
Abba yace "eh hakane, amma jami'oin namu ne na nan, kullum cikin yajin aiki da sauran matsaloli, shiyasa gara a can ƙasashen ƙetaren, nan da nan su gama su huta"
"Hakane, amma ina fatan ze zo ya ganni kan ya tafi turan, dan babu lallai harya dawo ina raye"
Abba yace "insha Allah ze dawo kana raye, ka dena wannan maganar, Ranar Asabar insha Allah, zan zo maka da shi ya duba ka"
Hakimi yai murmushi yace Allah ya kaimu"
Mother kamar a kan ƙaya take, dan Alla Alla take suyi su tafi, aikuwa da yin Azahar suka juya zuwa gida.
Sadik yayi zarya a layin su Farhan dan ya samu ya ganta amma baya ganin wucewar ta, ya je Makaranta amma ya tarar wai kwana biyu ba taje ba, nan da nan hankalinsa ya tashi, ya kira wayarta amma ba ta shiga, ya tura mata messages amma babu reply.
Tun magariba, har kusan ƙarfe tara yana unguwar su Farhan, amma be samu ganinta ba, Jiki a sanyaye ya koma gida, ya tarar da Su Mother sun dawo daga ƙauye.
Sadik yace "wai ina kuka tafi haka, na shigo ba kowa a gidan nan, na kira wayarki ba ta shiga"
Mother tace "hmm ƙauye mukaje duba Kakanku"
"Wai haryanzu be warke bane?".
"To jikin nasa dai da sauƙi, but he is seriously sick, Abbanka yace jibi in Allah ya kaimu ze koma, kuma tare zaku tafi, kaje ka duba shi, dan wannan tsohuwar ta fara mita"
Sadik yace "nifa bana san zuwa garin nan, wannan tsohuwar ta sa mutum a gaba da masifa, tun da na masa Addu'a ba shikenan ba?"
Mother tace "Ni dai ba ruwana balle ace ni nake ziga ka"
Suna cikin maganar Abba ya shigo, tare da Faruk, Sadik ya kallesu yace "Abba sannu da zuwa"
"Yawwa sannu, wato kai muka shirya mukaje dubiya babu kai, wai ina ma ka shiga ne?"
Sadik ya ɗan sosa kai yace "bacci nake, ban san ma zaku ba"
"Jibi in Allah ya kaimu zan koma, in gani in ba dama zan taho da shi nan cikin gari a duba shi, in ta kama a fita da shi ne a duba yadda za'ai, tare da kai zamu tafi kaima ka duba shi, dan haka ka shirya"
Abba na gama Maganar yai gaba, dan be jira me Sadik ɗin ze ce ba.
Shi ba zuwa ƙauyen ne ma yafi damunsa ba, illa halin Inna na shegen sa ido da masifa.
Yauma haka ya kwana cike da tunanin Farhan, lallai da alama ita ma fushin take da shi, dan duk ta tosje duk wata hanya da zasu haɗu.
Farhan kam ta ajiye wayar da ya bata, ta kashe ta ta ɓoye, ta cewa direban Sadik ya dena zuwa ɗaukan ta, gashi tana tsoron Babba ya cigaba da bibiyar ta.
Dama an kusa fara exams, ba wani lesson ake musu ba, dan haka ta dena zuwa makarantar Gaba ɗaya, tace se an fara exams ta koma.
Ga damuwa ta sa ko Abinci ba ta iya sakin jiki taci, kullum ta na ɗaki, Umma kuma ba ta damu da taji meke damunta ba.
Yau gaba ɗaya zaman Gidan ya isheta, dan haka ta yanke shawarar zuwa Makarantar dare yau, ko ta ɗan samu releif.
Tana fitowa daga gida, ta kusa barin layinsu, sega Sunusi, duk da babu wuta amma yana ganinta ya ganeta.
"Hajiya Farhanatu, ance min baki da lafiya ya jikin?"
"Na ji sauƙi" ta bashi amsa tana ƙoƙarin raɓa shi ta wuce.
Sake tare ta yayi yace "haba to ki ɗan tsaya mu gaisa mana, kwana biyu fa bamu haɗu ba, haba tauraruwar zuciyata"
Cikin rawar murya kamar tai kuka tace "dan Allah ka ƙyaleni Makaranta fa zan tafi"
Ze kuma yi mata magana, ta raɓa shi tai tafiyarta.
A duk lokacin da ta ga Sunusi ji take ta ƙara shiga matsananciyar damuwa, saboda shike barazanar rabata da farincikinta.
Jefa ƙafarta kawai take yi, taji tai karo da mutum a gabanta, ta ɗago ido ta kalleshi, duk da lungun ba wuta amma hakan be hanata gane shi ba.
Kewaye shi tai zata wuce ya kuma shan gaban ta.
"Ni zakiwa wulaƙanci, kina ganina zaki tafi, waye wancan ya tsaida ke yana miki Magana?" Yai maganar a matuƙar kausashe.
Haushi ne Yakamata, duk da a ƙasan zuciyarta taji daɗin ganinsa, cikin ƙwarin gwiwa da tsiwa tace "ban sani ba"
"Ni kike cewa baki sani ba?"
Shiru tai masa zata raɓa shi ta wuce, amma ya riƙeta gam yace "muje mota"
"Ba zani ba, ka cika ni"
"Ai ba abune ne wahala ba in ɗagaki in kai ki motar ba, sedai kome za'ace a ce ba ruwana"
Ta san halin Sadik sarai, ze aikata abunda ya faɗa, dan haka ta haƙura ta bishi tana kuka, zuwa in da ya saba parking.
Sun kwashi mintuna a motar, kuka kawai take kamar ranta ze fita, a hankali yace "kukan ya isa haka, ke kullum cikin kuka ko gajiya ba kya yi?"
Shiru tai masa, tai me isarta sannan tai shiru.
"Yanzu gayamin, ma tukuna kukan me kike?"
Ko kallonsa ba tai ba, ta ɗauke kanta.
Sadik yace "Hmm, dole inyi fushi a duk lokacin da naci karo da abunda yake barazana ga soyayya ta, banji daɗin ɓoyemin batun Babba na bibiyar ki da ki kai ba, baki san hatsarin yaron nan ba"
"To shine zaka dena ɗaga wayata, ka dena kulani, shikenan tunda ka dena sona"
Sadik yai murmushi yace "Taɓ, bana tunanin akwai wannan ranar, da zan dena sonki Farhan, yanzun dai ga Abinci na taho miki da shi naji kince ko Abinci ba kya iya ci"
"Ni ba zanci ba" tai maganar tare da murguɗa baki.
Yai murmushi yace "lallai nayi sake wannan bafullatanar ta raina ni, har nake Magana kina mayarmin, shikenan let me feed you"
Ya takura mata harta haƙura ya dinga bata Abincin a baki da kansa.
Aikuwa ta sake taci sosai, suka fara hira, yake gayamata washegari zeje ƙauye duba kakansa.
"Amma ba zaka daɗe ba ko?"
"Taɓ, ya za'ai naje wannan ƙauyen na zauna, a goben insha Allah zan dawo"
"To shikenan, Allah ya bashi lafiya, amma dan Allah meya haɗaka da wannan Mubarak ɗin da yake nema ya shafe ni?"
Sadik ya ɗanyi Jimm sannan yace "abun babba ne, amma karki damu idan na dawo zan baki labari"
Tace "shikenan" ta kashingiɗa a jikin seat ɗin motar kamar yadda yayi.
Ta ƙura masa ido, tana jin wata irin soyayyarsa na ratsa jikinta, ba ta san wani hali za ta shiga ba idan ta Auri wani ba Sadik ba.
A hankali ya juyo da fuskar sa ya kalleta yace "Ya dai?"
"Gabana ne yake faɗuwa ban san dalili ba" tai maganar wasu hawayen na bin fuskarta.
"Please calm down, muna tare Princess, mucigaba da Addu'a duk yadda za'ai, idan naje ƙauye ina ga zan gayawa Kakana buƙatata ina ga su su fahimce ni"
A hankali ta furta "Allah yasa"
Fuskar sa ya matso daidai ta ta yace "wane irin so kike min Farhan?"
"I don't know" ta faɗa tana lumshe ido, lokacin da taji bakinsa a nata.
They really enjoys the moment, jinsu a wata duniyar ta daban, me cike da rikitattun al'amura.
(Yau Sadik watsewa yake ji🙄, ga bani da lafiya, dan haka zan fice in bar ɗakko rahoton ban son harkar watsewa 😂😂)
Sosai Sadik ɗin yake ƙoƙarin zarce tunani, duk da yadda jikinsa ke rawa idanunsa suka rufe.
Rirriƙe hannunsa Farhan tai tana kuka, tare da girgiza masa kai.
A hankali ya bar abunda yake, ya cikata ya jingina yana sauke numfashi.
Yau har ƙofar gida ya rakata, ya kalleta yace "sena dawo, kimin fatan nasara, Allah ya cika mana burinmu, sannan shi wannan me gangancin zuwa in da kike, ya kiyayi abunda yake nawa, in ba haka ba ze mamakin abunda zan masa, ko ya rabuda ke ta daɗin rai, ko kuma in masa amfani da yaren da ze fi ganewa"
Farhan bata iya cewa komai ba, se bin Sadik da kallo.
Ya juya ya fara tafiya dan barin layin.
"I love You, Please don't stay long, without hearing from you"
Ya waiwayo yai murmushi yace "I love You too"
Sunusi kuwa yana bakin layi, yaga wucewar Sadik da Farhan.
Ya jinjina kai yace "dama wani ne yake hure miki kunne yasa kike wulaƙanta ni? Zaku gane baku da wayo daga ke har shi, zan hau buzu akan ku, sena rufe zuciyarki ruf, shi kuma in kife tasa zuciyar, ze gane ba'a takara da ƙolo"
Kai tsaye ya nufi in da Sadik ke tafiya a cikin duhu!.
Sunusi yace "Aminu, jirani mana"
Sadik ya waiwayo yace "ba Aminu bane"
Sunusi yace "dan Allah Aminu meye haka? Daga ina kake haka?"
Sadik yace 'ba Aminu bane, Sadik ne"
Sunusi ya jinjina kai ya maimaita "Sadik"
INA ME BAKU HAƘURI NA JINA SHIRU DA KUKAYI, NAYI RASHIN LAFIYA NE, NAGODE SOSAI DA ADDU'AR DA KUKAMIN, I MANAGE TO TYPE FOR TWO PAGES FOR YOU, BUT I STILL NEED YOUR PRAYERS PLEASE 🙏🙏🙏)
Ayshercool
07063065680
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Jin Sunusi ya maimaita sunan Sadik yasa Sadik ɗin binsa da kallo, duk da cikin duhu ne, Sadik be damu ba ya cigaba da tafiyar sa.
Har ya ƙule da lungun Sunusi yana tsaye yana kallonsa, seda ya ga Sadik ya bar layin sannan yai ajiyar zuciya ya jinjina kai yace "daga yau idan aka kuma cewa ka kalli in da take ba zaka ƙara ba, dani kake zancen sena muku farraƙu"
Sadik kam a matuƙar kasalance ya nufi in da motarsa take ya ɗauka ya tafi gida, da ƙyar ya kai kansa gida, saboda yadda yake jinsa a gajimare.
Farhan kuwa tana shiga gida ta tarar da Ummanta a tsaye a tsakar gida, seda gabanta ya faɗi.
"Daga ina kike?" Umma ta tambayeta tana kallonta.
"Umma daga Makaranta nake"
"Ƙarfe nawa yanzu? Ƙarfe goma da rabi fa, ku da ake tashi tun goma, duk ƙannen ki sun dawo amma banda ke, har Amir na kuma aikawa Makaranta ya dubamin amma yace ba kya nan"
Gaba ɗaya Farhan ta rikice, dan harga Allah bata san lokaci ya ƙure haka ba, uwa uba ma ko makarantar ba taje ba.
"Ina tambayarki amma kin min shiru" Umma tai maganar a kausashe.
"Umma nifa ba in da naje, mun biya duba babar su Naja ne, an mata aiki yaron ba rai, amma ba in da na tsaya.
Umma tabi Farhan ba dan ta yadda da abunda ta faɗa ba, sema mamakin yadda yanayin maganar Farhan ɗin ke nuna ƙarya kawai take zabgawa.
Umma ba ta kuma ce mata komai ba, ta wuce ɗaki ta barta.
Farhan ta nufi ɗakinta jikinta na rawa.
Sadik kam da ya koma gida se da yai wanka, sannan yai shirin kwanciya, sedai abunda ya gudana tsakanin sa da Farhan ya sa shi a wani mawuyacin hali, me wuyar fassara.
Tashi yai daga kwanciyar da yai, ya fara zagaya ɗakinsa yana tunanin nemawa kansa mafita, tabbas yana ƙaunar Farhan, kuma a yadda yake jin kansa baze iya zama tsawon shekaru bakwai yana wata boko ba tare da yayi Aure ba.
Wata irin iska ya dinga fesarwa daga bakinsa, ya shiga safa da marwa a bedroom ɗin sa.
Ya nemi guri ya kwanta, ya janyo filo ya ƙanƙame ya runtse idanunsa, sedai surar Farhan ce ke dawo masa, yana kuma jin sa a wani yanayi.
Wasa wasa bacci ya gagari Sadik kamar yadda dariya ta gagari kare, ba abunda yake se yarfe gumi.
Wani tunani yai, a irin hirarrakin da suke da su Nas, yadda suke shawo kan irin wannan matsalar in sun tsinci kansu a ciki, sedai galibi duk ruɓaɓɓen tunani da su, dan duk ta hanyar saɓon Allah suke samun mafita.
Tsaki yai ya miƙe ya nufi cikin gida, duk kowa ya kwanta bacci, ya lallaɓa ya shiga Kitchen, tea flask ya duba ya samu tea, ya zuba cofee sosai a ciki, ya zauna a Kitchen ɗin yana sha kaɗan kaɗan.
A hankali ya kammala sha, ya koma ɗakinsa sedai babu wani canji sosai.
Ɓangaren Farhan ma seda ta tsarkake kanta, dan yau sun zarce ƙa'ida, duk da fargabar tuhumar da ta fuskanta yau, be hanata jin ta aikata ba daidai ba na biyewa Sadik da tayi yau.
Abunda ba ta taɓa zaton zata aikata ba, se gashi cikin lokaci ƙanƙani Sadik yasa duk wannan kunyar ta ta ta ajiyeta a gefe.
A hankali ta furta "Yasalam, Astagfirullah, ya Ubangiji Allah kar kasa in rasa mutuncina saboda Soyayya, Allah ka yafe mana, Allah ka tabattar min da Alkhairi tsakani na da Sadik, Allah ka tsaremu aikata Zina ka nunamin Ranar da za muyi Aure" haka ta cigaba da Addu'a ƙasa ƙasa.
Umma kam kasa zaune tai ta kasa tsaye, seda Abba ya dawo gida, ta bashi Abinci yaci ya nutsu sannan ta kalleshi tace "magana nake so muyi"
Yace "ina jinki"
"Game da wannan yarinyar ne"
Abba yace "me kuma tayi?"
"Nifa na kasa gane kan wasu abubuwa da ke aikatawa kwanan