Showing 258001 words to 259198 words out of 259198 words

Chapter 87 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

01 Sep 2025

13387

zani, gara in haƙura da Auren tun da Mother ba ta so"

Nana tace "Haba Princess, in kika tafi bamu da Princess ɗin da zata maye mana gurbinki, dan Allah a madadin Mother ina baki haƙuri, dan Allah karki tafi, Farhan nice ƙaddarar da ta ratsa tsakanin soyayyarku, ban san haka abubuwan suke ba, dan Allah kiyi haƙuri ki zauna"
Rungume Nana Farhan tai tana kuka tace "Besty Mother ba ta sona"

"A'a tana sonki" Nana tai maganar cike da tausayin Farhan, tana ji a jikinta idan har ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, to be kamata ta ga Farhan na zub da hawaye ba, saboda ta sha wahala.

Sadik ya ƙaraso ya rungumesu gaba ɗaya, yana faɗin 'kukan ya isa haka, ke kuma da kika goya Sahal ina zaki da shi?"

Ta share hawaye tace "da shi zan tafi"

Sadik ji yai kamar yai dariya, saboda wauta da yarinta, za tai yaji amma za ta tafi da ɗan da ba nata ba.
Yayin da yake sake mamakin Nana, saboda ita a rayuwarta ba ta son ta ga wani yana kuka, sosai kimarta ta ƙaru a idon Sadik.


Mother da kanta taje gidan Sadik, cike da borin kunya, ta nunawa Farhan komai ya wuce.


Sunusi kuwa ciwo yake tuburan, da fari abun kamar aljanu, daga baya kuma likitoci sukace ya samu brain tumor, ya dinga wani irin ciwon kai, da fizge fizge irin na mahakata, ana neman wasu uban miliyoyi ai masa aiki, wanda ba wanda yake da wannan uban kuɗi.



Wata irin kulawa Sadik yake bawa iyalan nasa, cikin taka tsantsan ba tare da ya shiga haƙƙin wani ba, da tsohon ciki Farhan ta gama sakandare, idan kai baƙo ne ka zo gidan ba zaka ce kishiyoyi bane, balle ka gane wacece ta haifi Sahal, dan tunda Nana ta yaye shi, Farhan ta karɓe shi.
Watan cikin Farhan tara, ta haifi sankaceciyar jaririya, ta haihu daf da bikin Faruk da Khairat, Nana ta dinga murna kamar ita ta haihu, dan ba ƙaramin son 'ya mace take ba.
S kace za'a haɗe bikin Khairat da sunan Farhan, idan Sahal ya ga Farhan ta rungume jaririya tana shayarwa, se yai ta tureta, wai dole se an saketa daga kan cinyarsa.

Nana tace "ban taɓa ganin garujen yaya ba, irin Sahal.

Haihuwar Farhan ma ta cika ko ina, aka haɗe suna da bikin Faruk, akai gagarumin shagali.
Farhan tace sunan mahaifiyar Nana take so a sawa jaririyar, Sadik kam be musu ba ya amince, Nana taji daɗin karar da Sadik sukai mata, hakan ya sa ta ƙara ƙaunar jaririyar da mahaifiyarta, aka sa mata suna Khadijah sunan mahaifiyar Nana, suke ce mata Neehal. Umman Farhan kuwa dai-dai gwargwado tai playing role ɗinta na uwa da Farhan ta haihu, saboda tai dana sanin irin riƙon da taiwa Farhan a baya.


Sir Nazir ya gama shekaru biyunsa, ya koma garinsu, sedai zaman garin ya gagare shi, saboda da ya fita ake nuna shi ana zunɗensa.
Ya tattara kansa ya koma Lagos neman kuɗi, a can ya haɗu da wata ya aura, sedai shima ya tarar da ragowar wani ya aura, sedai ba shi da cewa saboda Abunda ya aikata shima.



Sadik ya kammala karatun sa, be dogara da aikin gwamnati ba, ya cigaba da harkar kasuwancinsa, gidansa ya tsaya tsayin daka gidansa babu ɓaraka, kansu Nana a haɗe yake,
Sosai Nana ta ke riƙon Neehal, da soyayya da ƙauna kamar yadda Inna ta riƙeta, Sahal kuma ya zama ɗan gidan Farhan, ya cewa Farhan Mummy, ya cewa Nana Besty.

Allah sarki Jidda, seda ta shekara bakwai da Aure, sannan Allah ya bata haihuwar tagwaye, Allah me kyauta da ƙari, ba wanda be musu murna ba, mahaƙurci mawadaci.

Tasleem ta haɗu da Cancer bakin mahaifa saboda azabar zubar da ciki, Meenal kuwa hauka tuburan saboda shaye shaye, Mubarak Babba da Nas ma haka aka yanke musu shekaru masu yawa a prison, saboda laifukan da aka kama su da su.




25years later.

Sanye yake cikin gajeren wando da 'yar shirt, tafiya yake cikin ƙasaita yana taje sumarsa da comb, ya shigo cikin falon da 'yan matan suka cika da surutu.
Suna ganinsa suka nutsu sukai tsit, ya ja tsaki yace "sekace gyare, muryaoyin caicaicai, ko gajiya ba kwa yi, ku ɓace min daga falon nan".

"Ba zasu tafi ba, uban masifa ba yadda yara za su sake seka zo kana muzurai" cewar wata 'yar gayun mace, da ke zaune akan dining, se da na ƙura ido naga ashe Nana ce.

Farhan tai murmushi tana fitowa daga kitchen tace "like father like son, baya son hayaniya ne, ta ho nan sweetheart, zo muje falona kaci Abinci mu bar musu nan".

Nana tace "eh naji, a ƙyalemin yara su huta, kuje can ke da ɗan naki".


Gidan Sadik kenan bayan shekaru Ashirin da biyar, Farhan na da yara uku, mata biyu, ɗaya namiji, Nana na da huɗu, biyu mata biyu maza.
In ka gansu a cikin yaran kamar yayye da ƙanne, Abba ya tara jikoki, dan Faruk kawai yaransa shida Khairat ta haifa, Dr. Kuma na da Biyar. Jikoki duk syka baibaiye Mother, tuni ta mnata da ƙiyayya ta kama sirikanta da jikokin ta, saboda ta ɗau darrusa a rayuwar Sadik da yaransa.

Farhan tai karatunta na Nursing, Nana kuma 'yar Jarida, kansu a haɗe dan hatta harkar business tare suke yi, suka riƙe mijinsu cike tsantsar soyayya da kulawa, Inna kuwa ta rasu shekaru uku bayan rasuwar Hakimi.




TAMMAT BI HAMDILLAH, ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN, DUKKAN YABO DA JININA DA KIRARI SUN TABATTA GA UBANGIJIN TALIKAI, NA FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA NA KAMMALA LAFIYA.

GODIYA TA MUSAMMAN GA MASOYA DA KU KAI HAƘURI, TARE DA JIMIRIN BIBIYAR WANNAN LITTAFI HAR NA KAMMALA.

BA ZAN SAUKE ALƘALIMINA BA HAR SE NA MIƘA JINJINA GAREKU

AUTAR MANYA, SARAUNIYAR MASOYAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA 😂, IDAN NAGA KIRANTA TO JIRAN POSTING TAKE.
ZEE KUMURYA
MUM AMNASH
INA MATUƘAR GODIYA A GAREKU, ALLAH YA BAR ZUMUNCI.

COMMENTS SECTION KUMA BA ZAN MANTA DA KU BA, YADDA KUKA DINGA NISHAƊANTAR DANI DA SHARHINKU, ALLAH YA BAR ZUMUNCI DA ƘAUNA.

DAN ALLAH INA JIRAN JIN RA'AYOYINKU AKAN LITTAFIN, KO TA GROUP KO TA PRIVATE.
GYARA KO SHARHI, KO SHAWARA, INA JIRAN RA'AYOYIN KU.


NACE BA, DUK DA ALHAMDILILLAH A WANNAN KARON BANGA ANA GANTALAMIN BOOK ƊIN BA, AMMA DUK WADDA AKA TURAWA BA TA BIYA BA, DAN ALLAH TA BANI ƊARI UKU NA, ƊARI UKU BA ZATA SAKI TALAUCI BA, KEMA DA KIKA TURA BA DA IZINI NA BA, ALLAH YANA KALLONMU GABA ƊAYA TABBAS, DAN ƊARI UKUN KI BAKI BIYANI ZAFIN DA IDONA YAKE BA, DA KUMA DARUSSAN DA KE BOOK ƊIN BA, DA ZAKI TURAWA WATA🙄🙄🙄 BANYI ALLAH YA ISA BA AMMA A BIYANI 300 NA, KO IN YI😬😬😬

AYSHERCOOL
07063065680

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login