Showing 201001 words to 204000 words out of 259198 words
Chapter 68 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
ai min maganinka banza kawai"
Sunusi ya gama banbamin masifarsa yai gaba.
Abbas ya girgiza kai yace "dan Allah Farhan, duk sanda ya zo yana wannan abun ki dena kula shi, kuma kiyi ta addu'a, kar bakin nan da yake miki tai taisiri a kanki"
Cikin rawar murya Farhan tace "tasiri kuma na nawa? Bayan yadda ya dinga aibata ni da bakinsa tun a baya yana ɓatamin suna, na bar shi da Allah kawai, ka gaida gida se da safe" daga haka ta juya gida tana zubar da hawaye.
Ba zato ba tsammani taji Umma ta shigo ɗakinta, ta zauna a gefen katifar Farhan tace "har ya tafi ne?"
Idon Farhan duka hawaye ta kalli Farhan tace "lafiya kuwa?"
Farhan tace "lafiya ƙalau"
"Amma kike kuka?" "Umma bakomai fa"
"Shikenan, nace to ya batun Abbas ɗin, shi kina son nasa?"
"Umma nifa ba zan yi Aure ba"
"Saboda me?"
"Na ɗau darasi a Soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, sannan ga abunda ya faru da rayuwata Yanzu, gara in rayuwata kawai nika ɗai"
"Yanzu kin zaɓi ki cigaba da yawo, Shekarunki ba sj kai sun kawo ba, amma kalli yadda kika maida kanki, Auren shine rufin Asirinki ai"
Tsurawa Umma ido Farhan tai, a hankali ta matsa kusa da Umma, ta kwanta a jikin Umman, ta maƙalƙaleta kamar wani ze ƙwaceta sanann cikin hawaye tace "wannan nake buƙata Umma, idan da wannan ba na buƙatar wani namiji ya kuma shigowa rayuwata, kulawarki da addu'arki, dan Allah Umma ki dinga sona kamar yadda ake son kowane ɗa, ki dena tsanata dan Allah ina sonki sosai Ummana amma kin ƙi bani damar more Soyayyar uwata" tausayin Farhan ya mamaye zuciyar Umman, a hankali ta rungume Farhan ɗin, tai shiru tana jin yadda Farhan ɗin ke kuka cike da ajiyar zuciya.
Ya zubawa Nana ido da cikinta da ya fito sosai, ta ƙara ƙiba ga wani shape da tai, wani ɗan gajeren wando ne a jikinta da half vest, hakan ya sake bawa cikin nata damar fitowa ras.
Se shirya musu kaya take a cikin akwati, cike da farinciki, se ta ɗago riga tace "Friend kalli, ni ina ga base mun tafi da wannan ba, ta dena shiga ta, kalli wannan wandon ma, duk son da nake masa, amma sedai kawai in ajiye ba ze shigeni ba"
Ta kalli Sadik taga yadda yai zuruuu da ido yana kallonta.
"Tunanin me kake ne?"
"Mhmm, bakomai naga bakinki yaƙi rufuwa ne"
Nana ta ɗan yi fari da ido tace "ta yaya bakina ma ze rufu, zan koma in ga Innata da Hakimina tsoho me ran ƙarfe, idan muka koma Nigeria ni da ƙasar nan se da ziyara"
Ya kalleta yace "saboda me?"
Ta ɗan yatsuna fuska tace "to idan na haihu da ɗan zan taho?"
"Eh, da shi zamu taho"
"Kuma se in dinga zuwa da shi Makaranta? Gaskiya ni ba zan dawo ba"
Yace "ashe kuwa zaki zauna, ba tare da kin koma gida ba" ɗan haɗe rai tai ba tare da ta kuma cewa komai ba.
Murna a gurin Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna da farinciki, yau ita ce za ta koma gida Nigeria, bayan shafe shekara guda da watanni ba tare da taje ƙasar tata ta haihuwa ba, seda sukaje gidan Steve su kai masa sallama, shine ya kaisu har airport, suka hau jirgi.
Nana kam murna take tana lissafa kala kalar Abincin da za ta ci wanda tai missing, Sadik jinta kawai yake, amma tunanin artabun da za suyi da Mother kawai yake.
Gefe guda kuma yana jin, wannan abun da yake damun zuciyarsa, wanda ya rasa ko menene, se Alla Alla yake su sauka ko Allah ze temake shi ya tuna wannan abu da yake damun zuciyarsa.
Abba da Dr. Tuni suna airport, suna jiran saukar su Sadik, tun daga nesa Sadik ya taka da gudu yaje ya runume Abba yana Abbana i miss You.
"I miss You too my lovely Auta"
Usman yace "ji sha sha sha, se kuma ka bar mata dakon Akwatunan"
Nana ta ƙaraso tace "gaskiya Akwatunan nan sun min nauyi, da wanne zan ji"
Ta kalli Abba ta durƙusa har ƙasa tana gaishe shi.
'Abba yace Masha Allah, Mamana kinga yadda kika koma kuwa, Alhamdilillah ya karatu?"
"Lafy ƙalau Abba, Uncle Usman ina wuni"
"Lafy ƙalau ya school"
Tace "School Alhamdilillah"
Sadik yace "Abba ina Mother?"
Abba yace "tana can tana ta shirin tarbar ku" haka suka rankaya zuwa gida baki ɗaya.
Mother na jin ƙarar mota ta fito harabar gidan cikin hanzari, Khairat ta biyo bayanta tare da Jidda matar dr.
Sadik da Mother suka rungume juna, cike kewar juna tana cewa "I miss You Autana"
Nana kuwa se bin su take da kallo gwanin sha'awa tana murmushi.
Cikin rawar jiki Nana take gaida Mother, amma Mother ta amsa a wulaƙance, Sadik ne kawa ya lura da abunda Mother yai, ya basar bece komai ba.
Jidda ta rungume Nana tana faɗin "Masha Allah, Nana kinga yadda kika ƙara girma kuwa, lallai Sadik ya iya kiwo"
Nana ba abunda take se yaƙe, dan ta san ba zasu samu jituwa da Mother ba, ta dinga fatan Allah ya sa a yau ba se gobe ba a maida ita ƙauye gurin Inna.
Ma'aikatan gidan kansu se barka da dawowa sukewa Sadik.
Suka rankaya zuwa cikin gida gaba ɗaya, Mother kamar ta maida Sadik cikinta saboda murna, Khairat ma se wani shishshsigi ta kewa Sadik, sedai ta lura Sadik ɗin yanzu ba irin na da bane, se wani basarwa yake yana kamewa.
Suka gabatar da sallar la'asar, jikin Nana duk yai mata tsami, gashi ta kasa sakewa, ƙafafunta duk sun kukkumbura se sake duƙunƙunewa take ciki doguwar rigarta me haɗe da hijjabi, saboda kar a ga cikin nan.
Aka baje kayan Abinci, fried rice ya sha kayan lambu se ƙamshi take, ga nama nan ya sha kayan ƙamshi da lemuka, duk saboda Dawowar Sadik, sedai fuskar Nana kawai Sadik ya kalla ya san ba tai na'am da wannan Abincin ba ba lallai ta ci.
Ta dinga zuba zoɓo tana sha, amma ta ƙi cin Abinci.
Sadik se kallonta yake gashi ba ya son yai wani abu da ze sa Mother, ta fuskanci wani abu a tsakanin su.
Jidda tace 'Nana ki ci Abincin mana, naga se juya spoon kike"
Sadik ya wani maze, Nana tace "ina ci fa Anty Jidda"
Jidda tace "kunya dai kike ji, ko a kai miki ɗaki ki ci?"
Abba yace "waye baƙonta a nan dan ƙaniyarta, ki zage ki ci Abinci Mamana"
Nana kawai tai murmushi tana sunkuyar da kai.
Yayin da Mother se wurga mata uwar harara, Sadik ya faki idon Mother yaiwa Nana alamar ta ci Abincin.
Amma ta tura baki tana yatsuna fuska.
Ta ɗau spoon ɗin ta fara cin abincin, se dai sam ba ta ji dadin Abincin ba, ji tai ma yana taso mata.
Nana ta miƙe tace "bari inje ɗaki"
Duk da rashin magana na Usman amma seds ya magantu yace "kamar a takure take ne, anya Sadik ba wani abun kake mata a can ba naga kamar duk a takure take"
Sadik ya ɗan ɗage kafaɗa cike da basarwa, ya cigaba da cin Abincin sa ƙasan zuciyarsa kuwa so yake ya bita, yasan tana jin yunwa Sosai, kuma tunda ta ƙi cin Abincin be mata ba, da suna can ma haka take yi, in Abinci be mata ba ba zata ci ba.
Nana kuwa se da ta amayar da Abincin da ta taci tas, sannan ta samu katifa tai kwanciyarta.
Aka gama cin Abinci aka zauna hira, Mother tana gayawa Sadik yadda tai missing ɗin sa, har kusan sallar magariba ana zaune ana hira, yayin da hankalinsa yana kan Nana.
Se da aka tashi, za'ai salla sannan Abba yace "wai ina uwata ne?"
Jidda tace "tun ɗazu ta tafi ɗaki, wataƙila gajiya ce tai mata yawa"
Sadik se wani basarwa yake irin be damu ba ɗin nan, amma a ransa kamar yai layar zana ya tafi gurin matarsa.
Bayan sallar magariba, Jidda da mijinta suka shirya tafiya gida, Jidda ta leƙa ɗakin da Nana take, ta hango ta sanye da Hijjabi, alamar Salla ta idar.
Tace "Amarya, mu mun tafi Allah huta gajiya"
Nana tace "Anty Jidda tun Yanzu zaku tafi?"
"Eh mana, naga kin zo kin ƙule a ɗaki ke kaɗai"
Nana ta ɗan ɓata fuska tace "wallahi duk na gaji ne Anty Jidda"
"Eyya sannu, gara da kika huta ai, seda safe"
Nana tace "to Allah ya tashe mu lafy, ku gaida gida"
Sadik ya faki idon Mother ta shiga sashin Abba, ya nufi ɗakin da Nana suka saba zama, in sun zo gidan.
Ya tarar da ita kwance akan sallaya, ya ƙarasa ds sauri yace "lafiyar ki kuwa?"
Ta kwaɓe fuska tace "yunwa nake ji, kuma wallahi se juyawa cikin yake ya hanani sakat"
Yai ajiyar zuciya yace "to ai ina kallonki baki ci Abincin ba"
"Ni ba irin wannan nake so ba, da naci ma se da nai amai"
Yace "subhanallah, Allah ya sa ba aman nan ze dawo miki ba, amma me kike so to"
"Tuwo, ko awara, ko wainar fualawa"
"A gidan ubanwa zan samo wannan abunda kika lissafa?" Yai maganar yana hararata.
"To ba yunwa nake ji ba, kuma naga ai ba yin kaina bane, ni in baza'a samu ba na haƙura in zauna da yunwa"
Seda Sadik ya ja gajeren tsaki, dan be san ya ze wa Nana ba.
Miƙewa yai ya bar ɗakin, ya wuce Kitchen ya tarar da Talatu me aiki tana wanke wanke.
Ya kalleta yace "dan Allah baba Talatu, wainar fualawa nake son ki ɗan soyamin ko kaɗan ce"
Ta kalli Sadik da mamaki, ta san sam wannan ba cimar Sadik bace, ba ya cin wainar fulawa, amma me ze sa yace ta soya masa wainar fulawa, amma a zahiri tace "yadda kace haka za'ai ɗan auta" ya ɗanyi murmushin gefen baki ya fice.
Ya shiga ɗakinsa na nan falo an gyara shi tsaf, Abba ya fito falo shi da Mother yace "Auta wai lafiya naga gaba ɗaya uwata ta koma ɗaki ta takure?"
Sadik ya ɗan ɗage kafaɗa yace "i dont know what's wrong with her"
Abba yace "kirawota inji daga bakinta"
Sadik ya nufi ɗakin Nana, ya tarar tana zaune tana game a wayarta, yace "ki fito falo inji Abba, amma dan Allah karki abunda zamu raba hali, bana son mother ta fuskanci wani abu, balle a zo ga maganar cikin nan"
Maimakon tai magana sema sa hannu sa tai a baki tana bin Sadik da kallo.
"Husna magana fa nake miki"
"Ni wallahi yunwa nake ji, jiri ne yake kamani"
"Dan girman Allah kiyi haƙuri, ki lallaɓa ki fito kar Asirin mu ya tonu a gano cikin nan"
"Kaifa kace min ba wanda zece komai akan cikin, kuma yanzu kana faɗar wsni abu daban"
Sadik yace "hakane, amma ai da kunya ace an ganshi yi haƙuri ki tashi muje"
Da ƙyar ya lallaɓota suka fito falon.
Abba yace "Nana, ko akwai matsala ne naga kin koma ɗaki ke kaɗai?"
Nana tai murmushi tace "ba wata matsala Abba"
"To Alhamdilillah, ya zamanku a London ya kasance ya kuma makarantar".
Nana ta dinga amsawa Abba tanbayoyinsa, yana murmushi yayin da Mother ta haɗe rai tai kicin kicin.
Daga baya aka kawo Abincin dare, jalop sphagetti, nan ma Nana ba ta ci ba, aka gama kowa ya watse, Sadik yana son ya kaiwa Nana wainar nan, amma Khairat na falo.
Yana nan a ɗakinsa yana tunanin da suna can, da yanzu yana sa ta aiki tai ta masa hidima kan ta kwanta.
Mother ce ta shigo da sallama, ya amsa tare da faɗaɗa murmushin fuskarsa, ta ƙarasa ta zauna a gefen gadon Sadik, tace "Auta yaya, ina fatan ba wata matsala?"
Yace "matsalar me fa Mother na?"
Tace "game da Auren nan naka?"
Ya ɗan taɓe baki yace "ba wata matsala, me kika gani?"
Ta ɗan yi shiru sannan tace "ban so Auren nan naka ya kai i Wannan lokacin ba, na so tuni kan ku dawo na lalata Auren nan, amma mahaifinka ya kasa ya tsare a kan lamarin Auren nan, amma duk da haka ba zan karaya ba, zan ga abunda yakamata ayi a kai, dan bana ƙaunar Auren nan"
Sadik a ransa yace 'wannan shi ake kira da ihu bayan hari'
Sadik be cewa Mother komai ba, har ta gama surutanta ta tafi.
Tana fita ya leƙa ya ga ba kowa a falon, ya ɗau kwanon nan yaje ɗakin Nana, ya tarar da ita a zaune ta riƙe ciki tana kuka.
"Menene kuma?" Ya tambaya yana leƙa fuskarta.
"Yunwa nake ji"
"To kuma se ki ta kuka, ga shi nan" ya dungurar mata da flask ɗin waina.
Ta ja abunta ta fara ci, ji take nan duniya wannan wainar fulawa ta fiye mata Komai daɗi.
Sadik ya zuba nata ido yana kallonta yadda take aika wainar nan ba ƙaƙƙautawa.
"Ki ci a hankali kar ki ƙware malama"
"Wai kai ina ruwanka da ni ne dan Allah? Ka ƙyaleni mana in ci cikin kwanciyar hankali"
"To seki yi ai"
Se da ta ci ta ƙoshi sosai, sannan hankalinta ya kwanta, ta kalleshi tace "Nagode sosai, Allah yai maka albarka kaji Abokina"
"Kawai kin sani wahala"
"Allah ya baka haƙuri, amma ai wannan ne ya sani" tai maganar tana nuna masa cikin ta.
Sadik yai murmushi tare da shafar cikin nata yace "Husna ina son abunda ke cikin nan naki, fiye da yadda kike tunani"
Murmushi tai masa tace "ka tashi ka tafi, kar a ganka a ɗakin nan"
Yai ajiyar zuciya yace "Nana, zan missing ɗin ki yau wallahi"
Tace "to naji, amma dai ka tafi kaji Abokina"
Da ƙyar Sadik ya tashi ya bar ɗakin nan.
Khairat tayi mamakin yadda Sadik gaba ɗaya ya canza, ba ya shiga harkar ta sam kamar da, yadda suke ɗasawa amma sam tunda ya dawo ba wannan.
Gashi kamar an masa Asiri, sam ba ya fita waje ba in da yake zuwa, kullum cikin zaman gida yake, sedai a takure yake sosai saboda rashin sakewarsa da matarsa, Nana kuma kullum cikin zaman ɗaki take saboda kar wani ya ga cikin nan.
Cikin bacci da daddare Nana taji mutum a jikinta, ta tashi cikin hanzari amma Sadik yace "Shhhhhh nine"
"Friend meye haka, ka kusa danne min ciki fa"
"Am sorry ai ban danne ɗin ba"
"To me kake yi a nan?"
"Ke nifa na gaji ne, haba yau kwananmu tara a gidan nan na gaji da wannan wasan kwaikwayon"
"Ni dai yanzu, dan Allah ka rufa mana Asiri, ka tashi ka tafi tun wani be ganka ba"
"Wallahi ba zan bar ɗakin nan ba se Allah ya kaimu Asuba, na yi magana da Abba, na shirya mana tafiya ƙauye gobe in Allah ya kaimu, zamu gidan dr. Daga nan mu wuce"
Cikin farinciki Nana tace "dan Allah dagaske?"
"Ina miki ƙarya ne?"
"A'a ba kamin sedai tsoratani da sani tashin hankali wasu lokutan" murmushi su kai tare yana sake rungumeta.
(Asuba tagari, in da rabon Mother ta kama Sadik kuma ba ruwana lolz😂😂)
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Bin su sa ido Mother ta cigaba da yi, gaba ɗaya Nana ta ƙanƙame jikinta, saboda tsabar kunya.
Tabbas wannan cikin na Nana ko yanzu ta haife shi ba abun mamaki bane ba, amma tana me ba ta san da cikin ba duk wannan kwanakin da su kai a gidan?.
Babban abunda ya ƙara ƙular da Mother be wuce yadda take ta banbami tana masifar Sadik ya rabu da Yarinyar ba, yayi ƙanƙanta da Aure, ashe kallon biri take masa yana mata na ayaba.
Jiki a sanyaye Mother ta janye jikinta, ta bar ɗakin jikinta ba ƙwari dan ta rasa wane tunani Yakamata tayi, ta nufi sashinta.
Nana kam gaba ɗaya a rikice take, ta rasa abunyi gaba ɗaya se kuka take, Sadik yace "to kukan me kike kuma? Ai gara ma da Allah ya sa taga cikin hankalinmu ya kwanta da fargaba"
Nana ta gaza cewa komai yace "ko in kamaki in maida ke kan katifar?"
Nana ta girgiza masa kai alamar a'a.
Ya rungumota yana ƙoƙarin share mata hawayen dake bin fuskarta amma ta ƙwace tace "kai ba ka gudun abun magana, idan Mother ta kuma dawowa fa?"
"Karki damu ba zata kuma dawowa ba"
Mother ɗakinta ta koma tana safa da marwa, tama rasa wanda zata gayawa maganar, wayarta ta ɗakko da hanzari ta kira Mummyn Khairat, tai sa'a kuwa ta shiga.
"Har kin isa gida ne? Naga kiranki" cewar Mummy bayan ta ɗaga wayar.
Mother tace "hmmm na isa, na tarar da abunda ya bani mamaki na marasa abun Magana"
"Me kenan?"
"Hmm kin san matar Sadik ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe?"
Mummy tace "wane Sadik ɗin wai?"
"Sadik dai nawa, ina ta fafutukar yadda zan kashe Aure ashe kallona kawai yake, naje na tarar da su tare, da uban ciki a jikin wannan Yarinyar"
Mummy tace "iko se Allah, kinga dr. Da suke ta nema Allah be basu ba, se wannan da ba'a bawa Auren nasu mahimmanci ba, ohh Sadik da ɗa"
Mother tace "Abun ya ɗauren kai, Sadik haryanzu gani nake kamar jiya na haife shi, guda nawa yake?"
"Hmm ke dai ki gode Allah da yasa Auren a kai masa, in ba haka ba da wani zancen ake ba wannan ba, ki shirya karɓar jika kawai"
Mother tai ajiyar zuciya tace "mhmm, se anjima kawai" ta kashe wayarta, ta riƙe ƙugu tana sake juya lamarin, Sadik ɗinta za'a haifawa ɗa Allah me iko.
Haka ta wanzu tana wannan salallamin, har bayan isha'i Abba ya dawo, ta gabatar masa da Abinci, ta koma gefe tai zuguum.
"Madam ya dai? Meke faruwa ne?"
"Yallaɓai meye ma be faru ba?"
"Ok, to in da hali a gayamin wanda ya farun na ganki wani iri kamar a cikin damuwa"
"Abba, do you know you are welcoming your grandchild very soon?"
Abba yai murmushi yace "Alhamdilillah, Masha Allah"
"You don't even ask from who?"
Abba yace "ok, i ask?"
"Matar Sadik fa, ciki ne da ita a kowane lokaci zata iya haihuwa"
Abba yace "Ikon Allah, Lallai Autana an girma"
Mother tace "Are you not even suprised? Sadik guda nawa yake?"
"Ba abun mamaki bane ba ai, duba da iyaye da kakanni da ƙananan shekaru suma suke Aure"
"Yallaɓai, Sadik fa ba Faruk ba, so Sadik can impregnent this little girl? Abun ya ɗauren kai yara ƙanana, Sadik guda nawa yake?"
Abba yace "yanzu kin gane dalilin da yasa kakkaninsa su kai masa Aure? Da fari irin tunaninki ne da ni, ni kaina naga baiken Auren da akai masa yayi wuri da yawa, amma tunda naga hotonsa da 'yan matan turawa rabin tsirara, nasan ze aikata hakan, na yanke shawarar haɗe su guri ɗaya da matarsa"
Mother ta dafe kai tace "ya ilahil alamin Sadik fa, and how can that girl endure the hardship of labor?"
Abba yace "da ta fara se a kaita Asibiti, su sun san abunda ya dace suyi, yanzu seki tuntuɓe su, kiji cikin watanni nawa