Showing 96001 words to 99000 words out of 259198 words
Chapter 33 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
ba abu ne me sauƙi ba, ya riga yayi matuƙar sabo da Masoyiyyarsa Farhan, yana jinta sosai a cikin ransa, sedai fargaba ta kan shige shi a duk lokacin da ya tuna wai mahaifinta ya mata miji, yana jin wani abu a ransa wanda ya kasa tantance ko menene.
Da safe ba zuwa Makaranta, se ƙarfe goma na safe sannan ya tashi daga bacci, ya tashi ya shiga cikin gida dan gaida Mother.
Tana ganinsa tace "Ahh, Sadik wai me ke damunka kwanan nan ne?"
Sadik yace "me kika gani?"
"Duk ka rame kayi wani iri, ance kun kammala exams amma ba wani alamar farinciki a tare da kai, balle a ɗan shirya maka wani abu na musamman, whats wrong ne my Auta?"
Sadik baya son maimaita magana, ya san koya gayawa Mother damuwarsa ba abunda za tayi a kai, sema wataƙila ƙarshe suyi faɗa dan haka yace "bakomai kawai am not in mood ne"
"Ban gane you are not in mood ba, gaba ɗaya fa ka dena walwala Sadik nifa bana son ganinka a haka"
Cike da shagwaɓa da kuma ƙosawa yace "haba Mother, nace miki fa bakomai am ok, just a little stress, kuma shima saboda exams ne, but i will be ok insha Allah"
"To shikenan, kaje Abbanku ya tashi ka gaishe shi"
Sadik bece komai ba ya nufi sashin Abba, ya tura ƙofar ya shiga da Sallama.
Abba dake shan tea ya ɗago ya kalli Sadik tare da sakar masa murmushi sannan ya amsa sallamar.
"Abba good morning"
"Morning dear, ka tashi lafiya"
"Alhamdilillah"
Abba yace "Masha Allah, director na makarantar ku ya kirani jiya, he tolds me that you wrote your last paper yesterday"
Sadik yace "eh Abba mun gama"
"Masha Allah My Son, Allah yayi albarka ya bada sa'ar jarrabawar, Insha Allah sakamako na fitowa zaka tafi karatun ka, kaje kai zamanka hankalinka kwance, idan ka kammala seka dawo"
"Abba dan Allah, ni dai dama a bar zuwa ƙasar wajen nan a nema min kawai a Nigeria ko a nan Kano ne"
Abba ya kalleshi yace "You Are not serious, Sadik da a zamaninmu shine a kai karatu na gaske a ƙasar nan, amma banda yanzu karatun da zaka kammala a shekara huɗu, se kai shekaru bakwai kana fama abu ya gagara, kullum cikin yajin aiki, yanzu idan kaje can kuwa ba ruwanka da wannan nan da nan ka kammala degree ɗinka, kayi Master's ɗinka a can, sannan ka dawo gaba ɗaya"
Sadik kamar ze kuka yace "Abba wai sena gama masters zan dawo?"
"To idan ka dawo ka zauna me zakayi, ka dinga zuwa mana hutu shiki, ka maida hankali ka gina rayuwar ka, duk da nasan ba zaka bani Kunya ba"
"Abba, ba zanyi Aure ba sena gama Master's ɗin?"
Saroro Aba yai, dan har damuwa ta bayyana a fuskar Sadik ɗin.
"Wace irin maganace kuma wannan Sadik? Guda nawa kake da kake wannan batun, kai ka san nauyin dake hawa kan mutum kuwa idan ya ajiye iyali, guda nawa kake gaba ɗayanka, yayanka ba abun koyi bane a gareka, ya kammala Master's ɗin sa sannan yai aure, ai shi Aure lokacine Ɗan gidan Abba, idan lokaci yayi zaka yi"
Ba fargabar Komai Sadik yace "Abba yarinyar da nake so ba zata jirani tsayin shekaru bakwai ba, kan in Aureta ba, Daddy wallahi ina sonta Sosai" Sadik yai maganar ƙwalla kwance a idonsa.
Abba ya jinjina kai yace "Sadik, kasan dai ba zan maka Aure yanzu ba ko? Kai kanka kasan ba ka isa Aure ba, ina son ka cire wannan tunanin a ranka ka maida hankali akan karatun ka"
"Abba ina sonta Sosai, idan na tafi zata iya Aure ta barni".
Tausayin Sadik ne ya kama Abba, amma ya bar hakan a zunzurutun shirmen ƙuruciya.
Ya dafa Sadik yace "Sadik, RUƊIN ƘURUCIYA ne ke damunka, kana tafiya karatu ya ɗauke naka hankali zaka manta da ita, sannan ina kai ina wata Soyayya? Shirmen ƙuruciya ne kawai, ka cire ta daga ranka ka fuskanci rayuwar ka kaji ko?"
Sadik ya jinjina kai jikinsa a Sanyaye.
Abba yace "yawwa my son, Allah ya baka ilimi me amfani, matso kusa dani muyi breakfast tare"
Sadik ya girgizawa Abba kai yace "na karya"
Ya miƙe jiki a Sanyaye, ya bar part ɗin, ɗakinsa na BQ ya tafi, jikinsa har rawa yake saboda tsabar damuwa.
A falo ya wuce Faruk, yana shirin fita.
"Sadik lafiya kuwa?"
Sadik be amsa masa ba ya wuce ɗakinaa, yana zuwa ya faɗa kan gadonsa, ya ɗora pillow a kansa kawai yaji hawaye ya fara bin fuskarsa.
"Sadik tashi muyi magana, meye haka kake ne?" Yaji muryar Faruk a kansa.
Sadik ya tashi zaune, sedai abunda ya bashi mamaki be wuce yadda yaga hawaye a fuskar Sadik ba.
Take hankalin Faruk yai mummunan tashi, saboda mutum ne me matuƙar son 'yan uwansa.
"Sadik meke damunka ne, ka ɗagan hankali fa"
"Faruk dan Allah ka gayamin meyasa kuke cewa soyayata RUƊIN ƘURUCIYA ce? Na gayawa Abba abunda yake damuna, amma shima yace min RUƊIN ƘURUCIYA ce, meyasa kuke cewa hakane?"
Faruk yace "Sadik, ba ka ajiye batun nan ba ko? Ni da kai na gaya maka komai, kuma nace maka lokaci ne, zaka dena jin duk abunda yake damunka"
Shiru kawai Sadik yai, Faruk ya cigaba da ƙoƙarin kwantar masa da hankali, amma sam baya jin abunda Faruk ɗin yake faɗa, har yai ya gama ya bar ɗakin.
Yana cikin tunanin ne, Wayar Sadik ta far ringing, be ko duba waye ba ya ɗaga ya kai kunnensa.
"Wato kai dan ka riga mu graduating har ka fara ja mana aji ko? Ji muka fito muka nemeka muka rasa, ana can ana ta celebrating muna nemanka muyi maka spraying kuɗi, amma muka neme ka muka rasa gaba ɗaya"
Nasir ne yake ta wannan cakwaikwaiwar da ba Komai Sadik ɗin yake fahimta a cikin maganganun nasa ba.
"Sadik kana jina kuwa?"
Sadik yai ajiyar zuciya yace "ina jinka mana"
"Amma shine kai mana banza? Wallahi har mun fara missing ɗin ka"
Sadik yai murmushi yace "kune za kuyi missing ɗina?"
"Wallahi Sadik dagaske nake, gaba ɗaya yau ajin ba daɗi baka nan, ko salama ba ka tsaya munyi ba jiyaka tafi"
Sadik yace "na tafi kai mata ta gida ne shiyasa"
"Lallai Sadik, yanzu yarinyar da ka haɗu da ita a 'yan watannin nan har ta fiye maka mu da mu kai shekara da shekaru tare?"
"Kowa matsayin sa daban a gurina"
"Bakomai, yaushe zaka shigo ne?"
"Daga gama makarantar se in fara zuwa, se an kwan biyu tukuna, bana son in zo ta shiga damuwa"
Nasir yace "Lallai, abun anku babba ne Sadik"
Sadik yace "ƙwarai kuwa, zamu bawa wanda suka ɗau lamarin namu wasa Mamaki"
Nas yai dariya yace "ai shikenan"
Su kai sallama Sadik ya kashe wayar ya cigaba da tunanin sa.
Ya barwa zuciyarsa ze jarraba cire Farhan daga rayuwarsa ko da gaske ne da ake cewa ba sonta yake ba, RUƊIN ƘURUCIYA ne kawai?
Sir Nazir kuwa tun da abun nan ya faru, kusan kwanaki uku amma damuwa da masa yawa, hakan ya bawa ciwon zama sosai a jikinsa, ga ciwo ga damuwa, hawaye sosai yake idan ya tuna aika aikar da ya tafka, be san wani irin hukunci ze fuskanta ba, ko zata je ta faɗa azo a kama shi, ko ba zata faɗa ba be sani ba.
Kasa jurewa yai, ya ɗau wayarsa ya kira layinta, beyi tsammani ba yaji ta ɗaga wayar.
Da sauri ya tashi zaune yana faɗin "Fatima ya jikin ki?"
Maimakon tayi Magana se sheshsheƙar kuka da take.
"Lilly dan Allah ki saurareni, kuskure ne mun riga munyi amma dan Allah....
Be ƙarasa maganar ba ta sake rushewa da kuka, wanda yake bayyanar da tsantsar damuwa da take ciki.
Kasa magana yayi daga ƙarshe ya katse kiran, wasu hawayen dana sani suka shiga zubo masa, shima yana da ƙanne mata, ƙannensa tara mata wasu an musu Aure wasu ba suyi ba, amma yau ace shine yai zina da 'yar da da yayi Aure da wuri, da ya kusa haifarta.
Wani irin dana sanin zuwa makarantar nan ya sake baibaye shi, tun yana jami'a mata suke bin sa, tun yana da ƙananan shekaru ma kan ya shiga jami'a, Amma babu wadda ta taɓa cin galaba a kansa se Wannan tatsitsiyar yarinyar ɗalibarsa.
Sosai ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro, damuwa da dana sani suka haɗu suka sake baibaye shi.
Kewa ta fara damun Farhan, na rashin abun ƙaunarta a kusa da ita, shikenan yanzu idan aka fita break bata da gurin wanda za taje suyi hira, sedai kullum ta na aji, wataran sedai ta kwanta tayi kuka, dan ba ƙaramin kewar Sadik ɗin take ba, gashi yai mata alƙawarin ze dinga zuwa yana ganinta, amma yau sati guda da barinsa makarantar bata ƙara jin ɗuriyarsa ba.
Har abunda ya faru ya faru, Lilly ta warware Mummynta ba ta dawo daga garinsu ba, ta koma Makaranta dan zaman Gidan damuwa yake ƙara mata.
Sedai tun da ta koma kallo ɗaya za kai mata ka san ta canza sosai da sosai, dan duk ta wani koma so silent.
Yasmin ce ta fara lura da hakan tace "wai Lilly meke damunki ne? Kince mana baki da lafiya, amma na ga duk kin koma wata iri, baki da kuzari, ko dai duk dan Nazir ba lafiya ne?"
Lilly ta girgiza kai tace "A'a, ni ba abunda yake damuna"
Haseena tace "kinga yadda ki ka rame Kuwa? Kin rame sosai gashi kin koma wata saliha, waima meya sameki ne?"
Kallonsu tai suna daga cikin wanda suka dinga ingiza ta duk me afkuwa ta afku, gashi ta rasa mutuncinta amma su suna tare da nasu.
Tace "Ciwona ne ya tashi kawai, ga Mummy ba ta nan, shiyasa duk abun yai min yawa haka"
"Eyya sannu Allah ya baki lafiya"
Ta amsa musu da 'Ameen"
Class rep ne ya shigo yace "Lilly, yau kamar haɗin baki, mutumin naki ma se yau ya dawo aiki, yana kiran ki a Office ɗin sa"
Gabanta ne ya faɗi, dan ko haɗa ido ba ta sake son yi da Nazir, Haseena tace "Yawwa muje ma, ni ina da Matsala a test ɗinsa yai min ƙwauron maki"
Lilly ba ta son su fahimci wani abu, dan haka ta tashi jiki babu ƙwari suka fita ita da Haseena.
Tun da suka shiga Office ɗin idonsa na kan Lilly, wadda kallo ɗaya za kai mata ka ga duk a hargitse take.
"Sir ya jiki?" Haseena ta faɗa tana kallonsa.
"Alhamdilillah" ya faɗa a taƙaice.
Haseena ta fara masa magana akan test ɗin ta, amma ya kalleta yace "can You please excuse us?"
Haseena ta kalli Lilly, ta kalli sir Nazir taga yadda fuskokin su ke ɗauke da damuwa.
A hankali ta janye jikinta ta fita daga Office ɗin.
Nazir ya kalli Lilly, cikin sanyin jiki yace "Fatima zauna muyi magana"
Girgiza masa kai tayi alamar ba zata zauna ba.
Miƙewa yai a hankali yaje ya kulle Office ɗin, ya dawo ya tsaya a gabanta, ya zubawa kyakyawar fuskarta ido, wadda take ta koma jawur saboda kuka.
Cikin rauni da karaya yace "Am sorry please, ban San meyakamata in ce miki ba, but..
Kasa ƙarasa maganar yai, ganin yadda jikinta yake kyarma saboda kuka.
Riƙo hannayenta yayi a cikin nasa "dan Allah Lilly ki yafemin, ki rufamin Asiri"
"You ruin my Life, ka cuci Rayuwata"
"Na sani, kuma ba kowa nai ba kaina nayi wa, amma ki bani damar wanke laifin da na aikata, ina da ƙanne Mata idan a kai musu nima ba zan ji daɗi ba, idan na nemi Aurenki a gidanku za'a bani?"
Turus tai tana kallon Nazir, dan ta san abune me wuya, dan iyayenta basa ƙaunar talaka mussaman mamanta, amma ita harga Allah tana ƙaunar Nazie duk da wannan abun da ya gifta a tsakaninsu.
"You mean zaka Aureni?"
"I mean it Lilly, na ɗauki abunda ya faru tsakanin mu a ƙaddara, amma in zaki iya Auren talaka kamata, ina sonki a hakan tunda dama aini nayi kuskuren"
"Na yadda, na amince in dai zaka Aure ni"
"Shikenan, tunda mun tsaya akan wannan yarjejeniyar, mu zama masu riƙe sirrin junan mu, kuma muyi ƙoƙarin kaucewa faruwar hakan a gaba"
Ta jinjina masa kai tace "insha Allah, ba zan gayawa kowa ba"
"Yawwa my love" suka rungume juna, yana ɗan shashafa bayanta alamar rarrashi (🙄🙄 anyi ba ai ba kenan).
Farhan kam shirun da taji babu ɗuriyar Sadik yasa ta fara karaya, da fari ji tai kamar taje ajinsu ta tambayesu shi, amma ta fasa, dan 'yan ajin nan nasu se a hankali, yanzu za su iya kawo mata maganar banza.
Sadik ji yake kamar bashi da lafiya, zuciyarsa se azalzalarsa kawai take akan son ganin Abincin ruhinsa wato Farhan, amma yana son tabattar da gaskiyar batun da ake masa akan Farhan ɗin.
Farhan kam ta fara sarewa, dan in dai ta tuna da shi se tayi kuka, tana Addu'a Allah yasa yazo ta ganshi.
Tana cikin tunanin sa Umma ta ɗaga labulen ɗakinta tace "kije kinyi baƙo"
Farhan tace "to"
Umma na juyawa Farhan ta ɓata fuska, dan ta san ba ze wuce wannan mannannen bawan ba, wato Sunusi duk abunda take masa na ƙin yi masa Magana idan ya zo, be sa ya fahimci in da ta dosa ba.
Ta saka hijjabinta ta fito, aikuwa shiɗin ne ba wani ba, tana ganinsa taji kamar ta koma gida da gudu, dan ko ƙaunar ganinsa ba tayi.
"Barkanki da wannan lokaci ya furen zuciyata"
Idan akwai abunda Farhan ta tsana be wuce wannan banzayen kalaman ba da yake faɗa, dan sam basa burgta sema ƙara ɓata mata rai da suke.
Ya sake cewa "ina fatan kin wuni lafiya cikin aminci kamar ni"
Farhan a ranta taji kamar tace "A'a cikin tashin hankali na wuni" amma ta dake, da yake wulaƙanci ba ya cikin ɗabi'arta.
Tace "dan Allah ko zamuyi sallama, zan tafi makarantar dare kar in makara"
Sunusi ya gyara tsaiwa yace "Amma ai kya bari mu gaisa ko?"
"Ai naga mun gaisa, idan na makara za'a iya dukana a makaranta"
"Eh to kuma hakane, amma ba kya iya jure bulalar malam saboda ni ba?"
Ba ta san lokacin da tsaki ya kufce mata ba, dan ji take kamar ta zabga masa mari.
Tace "kaga se an jima, Makaranta zan zo in tafi"
Ta juya ta koma cikin gida zuciyarta na mata wani irin tafasa.
Tana shig gida Umma tace "harya tafi ne?"
"Eh ya tafi, lokacin tafiya makaran yayi"
Umma tace "naga se takwas kuke shiga, yanzu kuma bakwai da kwata"
Farhan tace "eh dama zuwa yai kawai mu gaisa, kuma yai min Sallama ya tafi"
Umma tace "shieknan, Allah dai ya tabattar da al'amrin nan, ayi ai Auren nan kowa ya huta, dan da babanki ze Amince tun yanzu a karɓi kuɗin asan da ƙwaƙwƙwarar magana"
Farhan ɗakinta ta shiga tana ba Ameen ba a ranta.
"Ya Allah karka tabattar da wannan lamarin, Addu'a iyaye ga 'ya'ya ba ta da hijabi a gurinka, Allah ka tabattar min da Alkhairi, Amma Allah ka rabani da wannan sunusin bana son sa, Allah kai ka ɗai zan iya gayawa, kai kayi unarni da bin Iyaye, ina musu biyayya daidai gwargwado, ya Allah ka rabani da wannan bawan"
Haka taita Addu'a, muryarta ƙasa ƙasa tana goge hawaye.
Takwas saura mintuna, ta saka hijjabinta na makarantar dare, ta shafa turaren humra me sanyin ƙamshi, ta shafa ta ɗau jakar Islamiyyar ta, daga tsakar gida kawai ta iya cewa Umma na tafi, ta sa kai ta fita.
Jefa ƙafarta kawai take, tana share hawaye lokaci lokaci, ba zato ba tsammani, kamar daga sama wai anwa wada ƙwace,se ji tai an janyo hijjabin ta ta baya da ƙarfi ta faɗa jikin mutum.
Ware murya tai za ta ƙwala ihu, kasancewar ba kowa a lungun, ammma yadda ya toshe mata baki ya hanata yin hakan.
(Mubarak Babba 🥺)!
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Ƙamshin turaren sa ne ya fahimtar da ita waye.
"Matsoraciya kawai, komai seki fara ihu"
Ture hannunsa tai, ta ƙwace tana tura baki.
Fitilar wayar sa ya ɗakko ya haska fuskarta yace "ya naga kamar ma kuka ki kai"
Yana faɗan haka kamar ya tuna mata, se ga wani hawayen na zubowa.
"Farhan lafiya kuwa?"
Cikin shagwaɓa tace "ba kaine ba, kace zaka dimga zuwa ka ganni, amma tunda muka rabu ranar ba ka sake zuwa ba, se damuwa nake".
Murmushi Sadik yai yace "nima ai a cikin damuwar nake, tunanin ki ya hana ni sukuni, nayi tunanin zaki kirani a waya ma, tunda kince in ba ke kika kirani ba kar in kira ki, na ɗanyi rashin lafiya ne.
Kuma yau tunda na tashi na kasa nutsuwa, ganinki kawai nake son yi, na daɗe a gurin nan ina sa ran ganin wucewar ki, in samu in ganki"
Ta sauke numfashi tace "to kaji sauƙi?"
Yace "Alhamdilillah, na warware kina lafiya dai ko?" Ta ɗaga masa kai tace "lafiya ta ƙalau, kawai ganinka nake son yi"
"To ba gani ba nazo, ko dai haryanzu fushin ne?"
Ta girgiza masa kai sannan tace "Mu bar nan gurin kar wani ya ganmu a gayawa Abba.
Yace "ok, mota na ta titin bayan layin nan, muje can ba Wanda ze ganmu"
Tace "Makaranta fa zani"
"Ba daɗewa za muyi ba, ganinki kawai zanyi seki tafi"
Tace "to"
Ta bi Sadik zuwa Mota, suka shiga gaban motar da yake motar me tint glass ce, ba me ganin su, ya kunna musu fitilar motar.
Ya dubeta yace "ya makarantar?"
"So boring duk ba daɗi"
Yai murmushi yace "nima fa ji nake dama ban gama yanzu ba, wallahi ba ki ji yadda kewarki ta dameni ba, gashi ke ba waya ba balle mutum ya neme ki a waya"
"To ya zanyi tunda ba'a bani ba?"
Sadik yace "da yadda za'ai" yai maganar tare da sa hannu a aljihunsa, ya ɗakko sabuwar waya me madannai(keypad) ya miƙa mata.
Ta sa hannu ta karɓa tana kallonsa.
"Ki ɓoye wannan, akwai layi a ciki, duk lokacin da kika samu dama ki kirani, amma ba zan iya jure yin nesa da ke sosai, ba tare da ko jin muryarki ba"
Farhan tace "Tsoro nake ji, kar a ganta a gida fa"
"Ki ɓoyeta Farhan, in da ba wanda ze gani please, ina missing ɗinki Sosai" ya ƙarasa maganar yana marairaice murya.
Tace "shikenan, zan ɓoye Allah yasa kar a ganta ɗin, idan aka ganta ban san ya zanyi ba*
"Babu ma wanda ze gani insha Allah, ki kwantar da hankalinki kinji my wife"
"To Allah yasa kar a gani ɗin"
Yace "Ameen, ko tex ne se ki dinga yi min, my lovely"
Farhan tai murmushi tana jujjuya wayar.
"Kinga ba dan a ɓoye na baki wayar nan ba, ai da Babbar waya zan sai miki ta manyan yara"
"Manyan yara, ai kune manyan yara nikam ba babbar Yarinya bace"
Sadik yai dariya yace "Babbar yarina ce ke Farhan, you are very