Showing 156001 words to 159000 words out of 259198 words
Chapter 53 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
tafi.
Haka ta ɗau jakarta ta bi hanya itama, ba tare da ta ɗau ko babban hijjabin ta da ta saba sawa ba.
Ji take kamar ta samu wani gurin da babu kowa ta ƙwala ihu da ƙarfi ko ta samu sassauci Amma babu halin hakan. (This is how depression starts, and later on you will see what it leads to)
Yauma akan idon Sunusi Farhan ta dawo, da skirt iya ƙwaurinta, ya matse ta rigar Makaranta duk a ɗame, ga wani ɗan mitsitsin hijjabi, kasa Magana yai sema buɗe baki da yayi yana kallonta dan be taɓa sanin haka Uniform ɗinta na Makaranta suke ba, ga wani irin kyau da sukai mata, dirarriyar budurwa me kyakykyawar ƙira komai nata daidai da jikinta.
Se ya rasa kishi zeyi, ko kuma farincikin ganin abunda ze aura?.
Haka ta shiga gida babu ko sallama, Umma ta bita da kallo, tana zuwa tai jifa da jakar Makarantar ta, ta faɗa kan katifarta.
Adda Maryam tace "yarinyar nan kuwa Lafiya take?"
Umma tace "oho mata"
Adda Maryam ta shiga ɗakin Farhan tana mata Magana, amma Farhan ta ƙi kulata.
"Anya Innar Farhan ba aljanu ne suka kada ita ba, Sannan kalli kayan jikinta wannan ai dole Aljanu ma su shafeta dama wannan watsewar ake makarantar? Wannan ne kayan makarantar ta ta?"
Umma tace "to ni me zance, bani da yadda zanyi babanta ne ya dage se tayi, kuma ni bata taɓa aljanu ba, amma bari Amira ya shigo ya kira Malamin su Sunusi ko Sunusin su zo suyi mata addu'a"
Farhan na jinsu tai musu shiru, amma yadda take ji a ranta idan aka kusakura Sunusi ya zo in da take a halin yanzu, seta masa Illa!.
Abba da su Mother suna kan dining suna cin abincin rana, suna ta hira Faruk se dannan waya yake.
Mother tace "wai ba zaka ajiye Wayar nan kaci Abinci ba, ka ƙi maida hankali, idonka akan waya"
Yai murmushi yace "Am sorry maam, ina ganin wani abune a IG yanzu zan ajiye"
Abba yace "ai matasan mu se fatan Allah ya shirya, amma sun maida waya kamar wani nau'i na ibada, in basu Danna waya ba ba sa jin daɗi"
Faruk yai murmushi yace "Abba kenan, kasan yanzu Komai ya koma kan waya shiya........ Kai!"
Abba yace "ya dai?"
Faruk ya ƙurawa wayarsa ido.
Abba yace "wai menene?"
Faruk ya miƙawa Abba wayar, Abba ya karɓa yana dubawa.
Ɗiffff Abba yai, yan nazarin abunda ya gani a wayar.
Ba tare da yace uffan ba, ya ajiye wayar ya tashi fuuuuuu!
(Me Abba ya gani 🥺🙄🙄)
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Take tsigar jikin Farhan ta tashi, taji kanta yai wata irin sarawa, wani irin sanyi ya shiga Ratsa ta, taji tamkar an ɗora mata dutse a ƙirjinta, zuciyarta ta bushe hawayen ma suka gagara zubowa balle ta ji sauƙi a ranta.
Umma da ke tsakar gida tace "dubu Ashirin da biyar kuma?"
"Eh, sun ta bada haƙuri kin san ba masu ƙarfi bane, sedai yaron akwai zuciyar nema"
"Hakane, Allah ya sa albarka ya kaimu lokacin ya sa ayi damu"
Ya amsa mata da "Ameen"
"Allahumma ajirni fi museebati, wa akhlifni khairan min ha" shi Farhan ta dinga maimaitawa, dan wata irin muguwar tsanar Sunusi take ji tana ƙara ratsata, ji take kamar ta kwashi kayanta ta gudu, da tai ido huɗu da wannan mummunar rana da za ace Sunusi shine mijin da zata aura.
"Why Sadik? Meyasa kai nisa da ni ka bari nake shan wahala haka, come back to me please" tai Maganar tana ƙanƙame pillow a ƙirjinta, tana tura hancinta jikin pillown, tamkar zata ji ƙamshin turaren Sadik a jikin pillown, gashi tai tai tayi kuka, amma kukan ya gagara zuwa sam, se wata irin Azabar raɗaɗi da zuciyar ta ta take mata.
Tana jiyo Ummanta tana ta kiran danginta tana gaya Musu, ai an kawo kuɗin Auren Farhan, suna ta murna suna yaren fullanci suna mata barka da arziki.
Huzaifa ne yai sallama ya shigo gidan, dan tun da Umma ta ritsa shi ta sa ya karanta mat saƙonnin cikin wayar Farhan, yake jin kunyar zuwa gidan su haɗu da Farhan, dan lokacin da Umman ta bashi wayar ya duba mata, be san wayar waye ba, dan a saninsa Farhan ba ta da waya, sedai yai nisa a karanta saƙonnin sannan ya fuskanci wayar Farhan ce.
Ɗakin Farhan ya leƙa, ya hangota tayi ruf da ciki akan katifar ta, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin ta ya hargitse, ta dunƙule guri ɗaya da Sauri ya saki labulen yana ambaton Allah, dan be san a haka ze ganta ba, amma kana ganin yadda take zaka gane tana cikin damuwa da tashin hankali, ko ba a faɗa ba yanayin ta ze nuna tana cikin damuwa sosai.
"Ahh Huzaifa har ka zo?"
Yaji Maganar Umma, ya waigo da sauri yace "eh Umma, wai ki bani kayan in tafi da su"
"To Huzaifa, kai ko Allah sanya Alkhairi ma baka mana ba, bayan a gidan ku aka karɓi kuɗin Auren ta"
Huzaifa kawai ya sunkuyar da kai yana murmushin yaƙe, dan kwata kwata ya rasa meya rufewa su Umma ido, suka ga dacewar haɗa Auren Farhan da wannan ƙazamin mutumin me masifar tsiya.
Yana karɓar saƙon da ze karɓa ya tafi, dan ji yake kamar yaiwa Farhan kuka, messages ɗin wayar nan ya tabattar masa akwai wanda take so, ba wannan Sunusin ba, zuciyarta na tare da wani daban, gashi an gaza ba ta damar zaɓen abokin rayuwa, ga katse mata karatu da akayi.
Sadik kuwa tuni yai sabbin abokai, dama shi ba ruwansa ba shi da wuyar sabo idan ya ga dama. Dan ba ko yaushe yake miskilancin ba. har wani group ne da su shi da abokansa, ba ya taɓa ɗaukar littafi yai karatu, abune me wahala yai wannan, sedai abubuwa sun fara caza masa kai daga lokacin da ya fara bin abokai zuwa club, wanda Addinin su da al'adar su ba ɗaya bane, hugging, shaking hands and Even hugging is not something big a gurinsu.
Mussaman da Sadik yake burge 'yan mata, he is young but looking sexy and hot (ba inji ni ba, kun san dai su ba ruwansu faɗa za suyi 🙄🙄🙄) yana da suffa me kyan gaske, mussaman idan ya cire rigarsa ya shiga ninƙaya a ruwa, yana samun masu zuwa su ɗauki hoto da shi.
Mata suje hostel ɗin maza, ko maza suje hostel ɗin mata wannan duk ba wani abu bane normal ne, suna iya haɗuwa su yi wa junansu bitar karatun da a kayi a aji.
Sadik yana iya ƙoƙarin sa, gurin kula da addinin sa, da kiyaye abunda ze kaucewa hanya, amma abubuwa na nema sufi ƙarfinsa.
Hajiya Nana kuwa, ta ɗan fara sakin jiki da Linda, wato room mate ɗinta, idan ta saurara da kyau, tana iya gane abunda Lindar take faɗa, tana yawan tambayar Nana kukan me take yi, idan ta ga ta zauna tana kuka, ko in taga Nana tana salla ta tambaye ta menene wannan take yi haka?
Linda akwai shegiyar tambayar tsiya, yayinda Nana wasu tambayoyin suke bata haushi, dan ba ta san ta ya zata fara gaya mata ba, lokuta da dama se tai mata mixing our Nigerian English da hausa ta bata amsa (lolz 🤭😂).
Linda ta kan gayyaci Nana ta zo suje gurin motsa jiki, ko wasannin Nana tace ba zata ba, saboda ba zata iya shiga ba hijjabi ba, kuma ta lura in dai zata fito da hijjabin nan se ta zama abun kallo a gurin su.
Ƙawayen Linda kan kawo mata ziyara ɗakin su, suyi ta kallon Nana, suna mata magana amma tai banza da su sema tace "in ku mayu ne Yakamata ku ƙyaleni haka, se wani kallona kuke kamar an kawo muku buranya, dama ance haka kuke ce mana bururruka, banzaye zabiyai kawai, kuma ai munanan ne daga me ƙaton leɓe se me zanzana da cin zuma a haƙori, masu kyan kawai ake nunawa a TV"
Da yake basu sa me Nana take cewa ba, sedai su bita da ido, ta ƙare musu zagi tsaf ba su san me take cewa ba.
A hankali kuma Nanan ta fara gane turancin, dan har tana iya mayarwa, yadda Lindar zata gane.
Har su kanyi hira koma Linda ta gayyace ta suje suyi karatu a Library.
Sam Linda ba ta nunawa Nana ƙyama, mussaman da taji ance 'yar Afrika ce Nigeria ta na son Sanin abubuwa da yawa a game da Afrika especially Nigeria, shiyasa take yawan yiwa Nana tambayoyi, duk da Nanan ba bata amsa take ba.
Abubuwa da dama na bawa mamaki game da rayuwar yaran turawa, ko laifi su kayi ba a fiye tsawatar musu ba.
Watarana anyi karatu a aji, Malamarsu Nana tai mata tambaya, gashi ta san amsar tambayar amma ta kasa bayarwa, saboda tunanin yadda zata haɗo turancin tayi, kawai se 'yan ajin suka kama yi mata dariya ganin yadda tai wiƙi wiƙi da ido, tana tura baki, wani irin takaici ya kama Nana, kawai ta fashe da kuka, ga mamakinta se taga hankalin malamar ya tashi tana ta bata haƙuri tana rarrashin ta.
Nana ta fuskanci ana bawa ra'ayin ɗalibai mahimmanci sosai da sosai, ga ba duka ba zagi a harkar koyarwar ta su.
A hankali Nana ta fara sabawa da su, ta dage sosai tana ƙoƙarin mayarwa idan a kai mata turanci.
Yanzu tana hira da Linda sosai, dan bayan Lindar ma har wasu ƙawayen tayi, amma ɗabi'arta ta yawo da hijjabi na nan ba ta dena ba.
Mutane na ta shigowa yiwa Umma Allah Sanya Alkhairi yayin da a unguwa ake tayi da su, wai wannan 'yar yarinyar za'a aurawa Sunusi, wasu sukace Asiri yaiwa iyayenta, wasu suce ita yarinyar ce yaiwa Asiri take son shi, kowa da abunda ze faɗa.
Hajiya ma ba a barta a baya ba, Wajen zuwa yiwa Umman Allah Sanya Alkhairi, sedai se da tai ƙorafi tace "Umman Farhan, meyasa za'a aurar min da Farhan yanzu, tayi ƙanƙanta kuma karatun ta fa?"
"A'a ba haka bane, kin san sha'anin rayuwa da kuma yanayin yaran namu na zamani, kamata yai da sun kawo ƙarfi a kauda su"
"Hakane Maganar ki, amma ai ki godewa Allah, kinga Farhan nustsatsiyar yarinya ce, ba ruwanta da hayaniya irin ta yaran zamani, wallahi ki gode Allah amma yaran zamani suna kangarewa son ran su, amma kinga ke taki a nutse take kamar ke kika zaɓowa kanki"
Umma a ranta tace 'wannan ɗin ma dan ba ki san halinta bane'
A fili kuma tace "hakane, amma lokaci ne, idan yazo se anyi"
"Haka yake, amma ze bar mana ita ta ƙarasa karatun ko? Dan ba wanda yasan abunda Allah ze sa ta zama nan gaba"
"Eh yace ze barta, ai ba wani ne a nesa ba fa, Sunusi ne"
Hajiya tace "wane Sunusin?"
"Yaron nam dai Sunusi, Almajirin Malam Labaran"
Hajiya tai galala tana kallon Umma tace "Wannan baƙin yaron me doguwar ƙeya?"
Umma se taji ba daɗi abunda Hajiyar ta faɗa, amma ta maze tace "ba ruwana sirikinki me dai"
Hajiya tace "Ni ko me Farhan ta gani a jikin wannan tsotsatstsen mutumin? Haba Umman Farhan dan Allah, kyakyawar bafullatanar Yarinya me tarbiyya kuma a rasa wa za'a bawa se wannan"
Umma tace "kayya, banda abunki Hajiya, ai albarka ake nema a aure, su kyawawan, ko masu arzikin nawa aka aura amma Auren beje ko ina ba? Kuma naga ai shima mutum ne yaron, kuma gashi nutsatse ne"
"Eh albarka ake nema a aure tabbas, amma gaskiya wannan haɗin be ba, kowace ƙwarya akwai abokiyar burminta, amma shikenan Allah ya Sanya Alkhairi ya sa ayi da mu".
"Ameen ya Allah, dama addu'a dai ita ce"
Hajiya na shirin tafiya, Farhan ta shigo daga Islamiyya, tana tafe sannu a hankali kamar ba ta taka ba.
Tana ganin Hajiya tai murmushi tare da gaida Hajiyan.
Seda Hajiyan ta ƙare mata kallo cike da tausyawa, sannan ta amsa tace "Ashe kuma abun Alkhairi ya samu, to ubangiji Allah ya sanya Alkhairi ya kaimu lokacin"
Farhan tai murmushin yaƙe, tare da ƙoƙarin danne wani irin ɗaci da ya taso daga ƙasan zuciyarta, yake ƙoƙarin fallasar da zunzurutun damuwar da ke cikin ƙirjinta, ta hanyar kwaranyowar hawaye, ta nufi ɗakinta.
Kasancewar ba ta salla, har a kai sallar magariba ba ta fito daga ɗakin ba, se da akai sallar isha'i sannan ta fito ta tafi makarantar dare, sedai ta layin da Sadik yake ajiye mota tabi, ji take kamar za ta ganshi, sedai gurin wayam, ba motarsa da yake tursasata ta shiga ko yace ze ɗagata ya sata motar, mussaman idan su kai faɗa.
Duk da wasu abubuwan da suke a cikin motar ya saɓawa ƙa'ida, amma makauniyar soyayyar da ke cin ranta da kuma RUƊIN ƘURUCIYA ya sa take mantawa da hakan ta biyewa Sadik.
Barandar wani gida ta samu ta zauna, ta haɗa kai da gwiwa ta na wata irin sheshsheƙa, ga hawayen kirki yaƙi ya fito se ajiyar zuciya da take ta jerawa.
"Dan Allah Sadik ka dawo, zuwa yanzu zuciyata tayi rauni, ba zan iya jurewa ba Komai ze iya faruwa da ni, ina kewar ka Sadik"
Makarantar da ba ta je ba kenan, se da tai kuka me isarta, lokacin tashi yayi Sannan ta taho gida.
Tana cikin wannan yanayin, ta shiga ɗaki ta kwanta, akai sallama wai Sunusi yana nemanta, kuma Umma ta bada amsar tana zuwa.
Tai shiru a ɗaki, seda Umma tai mata Magana Sannan ta tashi ta fita.
Kamar yadda ta saba, tana zuwa ta ja guri ta tsaya, ta ɗauke kanta.
Yai murmushi yace "Amarya ba kya laifi, yanzu kin yadda kin zama tawo ko?"
"Allah ya kiyaye, idan wannan tunanin kake tun wuri ka dena, har Gaban Abada ba zan taɓa zama taka ba"
"Zancen banza kenan, ai tunda mahaifin ki ya riga ya karɓi kuɗin Aurena da ke, ai aikin gama ya gama, fatiha kawai tai mana saura, baɗi i yanzu in da rai da lafiya kina nan kin haihu ko kin kusa"
Wani irin kallon banza taiwa Sunusi, muddin ta aureshi ba abunda ze hanata shan guba ta mutu, tai saurin kauda wannan tunanin daga ranta, dan sheɗan kar yai tasiri a zuciyar ta.
"Dan Allah ki kwantar da hankalinki, wannan ɗan yaron da kike biyewa ba Aurenki ze ba, dan ba sonki yake ba, Yaushe rabon da ya zo in da kike, ni ɗin ne dai nine me sonki" yai maganar yana dariyar mugunta.
"Ko Sadik ya zo in da nake, ko be zo in da nake ba, zuciyata da tasa abu guda ne, da zasu kasance da juna har ƙarshen rayuwa, kuma babu wani namiji da ze taka matsayin da Sadik ya taka a zuciyata"
Nan da nan Sunusi ya fusata, yace "Ni kike gayawa haka? A gabana kike zancen wani sakarai?"
"Kai ne sakarai ba shi ba, ni mallakin Sadik ce, ba zaka taɓa samu na ba, kuma yadda ka dage kake ƙoƙarin Mallaka ta ta ƙarfin tsiya bayan ka san bana sonka, kaima Allah ba ze ji tausayin ka ba, Allah ya saka min, ba zan taɓa bijirewa zaɓin iyayena ba, amma zan dawwama ina maka Addu'a Allah yai maka abunda kai min" tana gama maganar cikin huci fuu tai gida.
Be taɓa zaton Farhan na da baki haka ba, ba ta taɓa masa rashin kunya Kamar haka ba, maganar ma ba son yi take ba, amma yau ta wanke shi tsaf ta nanata masa ba ta son shi.
A hankali ya fara jan silifas ɗinsa, ji kake sharaf, sharaf, sharaf ya nufi makwancinsu.
"Baban Soyayya, anje gurin amaryar ne?" Haladu yai maganar yana dafa kafaɗar Sunusi.
"Bari Haladu ina cikin damuwa wallahi"
"Damuwar me kuma, kai daka kusa zama Ango?"
"Bana tunanin Aikin da nai akan Yarinyar nan ya kamata, yauma ta sake jaddada min ba ta sona, wancan yaron take so"
"Too, ikon Allah abun be kamata ba kenan?"
"Alamu sun nuna hakan" Sunusi yai maganar cikin damuwa.
"Aikuwa ina tunanin ita ma ba haka take zaune ba, dan haka seka sake sabon shiri".
"Hakan za'ayi Haladu, zan sake shiri dole kan bikin nan, dole ta fara sona"
"Gaskiya ne, se ka bada himma"
Ɓangaren Lilly ma, abun duniya ya isheta sosai, yadda babanta yaci mutuncin Nazir ba ta ji daɗi ba sam, ta ƙallafa rai akan ze mata aure kamar yadda ta buƙata, amma ya watsa mata ƙasa a ido, gashi a yadda take ji gaskiya ba zata iya rabuwa da sir Nazir ba.
Gaba daya kunyar yadda zata tunkare shi ma take ji.
Ta kirashi ba adadi, amma yaƙi ɗagawa ta tura masa tarin saƙonni, nan ma ba wanda yai mata reply, ta whats app ma duk be duba messages ɗin ba balle yai mata reply.
A ɓangaren sa kuwa, yaji zafin abunda mahaifin Lillyn yai masa sosai da sosai, ta wani ɓangaren kuma yaji gara ma da akai haka, shikenan ya huta ba shi ba Auren Lillyn, kowa se ya kama gabansa.
Amma da yake Allah ba Azzalumin sarki bane, se wata irin soyayya da ƙaunar Yarinyar suka sake shigarsa, kwana biyu da ba ya amsa wayarta ma, jinsa ya dinga yi kamar a prison, Tabbas shigowar Lilly ratuwarsa ƙaddara ce.
Tabbas rabuwa da ita ba abu ne me sauƙi ba, dan sunyi sabo ba ƙarami ba, ga kusanci da suke da shi da juna.
Se da ya jera kwanaki biyu, ba ya zuwa makarantar, abun ya ƙara damun Lilly Sosai da sosai, se a rana ta uku sannan ya zo, ranar shi ze shiga ajinsu first period, kallo ɗaya tai masa ta san ba ya cikin walwala, dan ransa a haɗe yai lesson ya fice ko in da take be kalla ba.
Yana fita da 'yan mintuna, ta bi bayansa ta tarar da shi yana marking papers, yana ganinta ya haɗe rai sosai ya cigaba da abunda yake, ta ja kujera ta zauna.
Ba tare da ya kallet ba yace "can You Please excuse me, i have something to do now"
"Korata ka ke?"
"Me ze sa ba zan koreki ba, haka shine masalaha ai"
"Amma ai ba ni nai maka laifi ba, babana ne"
Ya ɗago ya kalleta yace "amma ta sanadin wa akai min, ok dama kin gayyace ni gidanku ne dan a ci min mutunci, a ci zarafina? Kin san mahaifinki ba ze amince ba kika sa naje ya min wulaƙanci?"
"Dan Allah ka fahimceni, wallahi be nuna min ze maka haka ba, kawai yace min yana son ku gana ne, wallahi ban san haka ze ma ba, ni kaina banji daɗin abunda yai maka ba dan Allah kayi haƙuri"
"Naji na