Showing 57001 words to 60000 words out of 259198 words
Chapter 20 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
ji yai tamkar ya shirya ya tafi gidan su.
Murmushi ya sake yi yana jin yadda shima yake kewarta.
Yana tuna yadda su kai da Mother jiya da yai nata zancen Farhan yaji ransa ya ɓaci, take yaji ze iya ɗaukar kowane risk dan ganin ya samu abunda zuciyar sa ke so.
Se Yamma sannan su Inna suka isa gida, duk da a motar gida suke, Inna ta gaji duba da yanayin jikin girma.
Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, saboda sun koma gida ga Hakimi se taraiyar ta yake yi.
Tabbas Nana ta yi missing ɗin Kakanta, me sonta da kuma ji da ita sosai.
Duk da ta wani fannin ta ɗan ji daɗin zaman birni, amma ta kasa mantawa da baƙin halin Mother da na ɗanta Sadik, mussaman Sadik da ke nuna mata tsana a fili.
Duk surutun Nana da wuri tai bacci, saboda ta kwaso gajiya sosai da sosai.
"Inna wuro kun sha birni, kun barni kamar maraya ba jikata ba ke"
"Hmm mun sha birni kam, Alhamdilillah gashi kuma mun dawo ai"
"Hakane, ya kuka baro min su?"
"Lafiya ƙalau, sedai akwai ƙura fa"
Hakimi ya sake nutsuwa yace "kamar yaya kenan?"
"Ranka ya daɗe, nifa sedai kace na cika ƙorafi, amma maganar gaskiya akwai gyara a gidan Bawan Allah, mussaman Ƙaramin ɗan sa, na rasa wace irin macece Hauwa"
Hakimi yai murmushi yace "ba zaki dena damun kanki akan yaron nan da iyalan sa ba ko?"
Inna ta girgiza kai tacee "ba damun kai bane, ina jiyewa bawan Allah abunda ka iya zuwa ya zo, akan wannan taƙadarin yaron nasa"
"To wai me yai miki ne? Ni kuma kinga nutsuwarsa nake gani, lokacin da naje ɗaurin Aure mota ɗaya muka shiga da shi muka dawo, banga wani abuba tare da shi ba"
"Hmm ni na gani ai, Allah ya kyauta kawai"
Washegari da Safe Sadik ya shiga ɗakinsa da ke cikin babban falo, ya fito daga ɗakin kenan se ga Mother ta fito hannunta ɗauke da wata leda, ta kalli Sadik tace "wai kai uban me a kai maka ne? Ko zuwa gaisheni yau ba kai ba, tun ɗazu Abba yake ta cigiyarka? Meye hakan ka ne, kullum ba ka da aiki se yin abunda zaka jamin laifi gun mahaifinka ko danginsa"
Mamaki ne ya kama Sadik, wato har Mother ta manta abunda ya faru, amma ya basar yace "Mother ba Komai fa, am not in mood ne kawai, amma ba wani abu"
Faruk ne ya shigo da sallama, hannunsa ɗauke da key Yace "Mother gani na shirya, kawo saƙon in kai"
Mother ta ƙarewa Faruk kallo sannan tace "Yawwa dama ba iya kai saƙo ne yasa na kiraka ba, ɗazu da ka shigo mahaifinka na nan, ba damar in maka magana a gaban sa kar yaji haushi"
Faruk cikin rashin fahimta yace "Mother wani abun ne ya faru ne?"
Mother tace "eh wani abu me ya faru, zaman kakarku a gidan nan, da wannan fitsarariyar yarinyar naga kana wani rawar kai, kana wani shishshsigi da neman suna, to let me tell you something, wallahi idan ma wani abu kake tunani game da Yarinyar nan gara ka cire shi daga ranka, ka maida hankali akan karatunka kar ma du fara tunanin wani abu ne a tsakanin ku suyi tunanin liƙa maka ita, ba zan amince da 'yar ƙauye a matsayin sirikata ba, dan naga su ba abunda suka saka a gaba banda Aure Aure, ko Aure za kai kafi ƙarfin wannan 'yar ƙauyen"
"Ohh my God Mother, what are you trying to say? Me nayi da ya nuna ina son Nana, idan alaƙata da Khairat be sa an kirata da Soyayya ba me ze sa alaƙata da Nana ya zama soyaya, wannan 'yar ƙaramar yarinyar, You know i just love female sister that's all, ban san meyasa kike zargin wani abu ba, she's a sister to me ina sonta saboda ita kaɗaice 'yar uwamu a ɓangaren Abba that's all, amma in kinji haushi ne am sorry for that, amma ba abunda kike Tunanin bane"
Duk haƙurin Faruk da alama yaji haushin maganganun Mother, Yain da Sadik shi abunda ya dame shi be wuce yadda Faruk ma me shekara kusan Ashirin da biyar ake cewa ya maida hankali akan karatu ba, balle shi da be ma cika shatakwas ba.
Gajeren tsaki ya ja ya bar Mother da Faruk a falon.
Mother ta dafa kafaɗar Faruk tace "am sorry my Faruk, ba na faɗa ne dan in ɓata maka rai ba, na faɗa ne dan in saka a hanya, ka maida hankali akan karatun ka ka zama wani abu a rayuwa, duk harkar matan nan shirme ne kawai, mutanen ƙauye da sunga kana nan nan da ita se suce zasu haɗa ku Aure da ita, But don't mind, zo ka kaiwa Mummy kayan nan"
Faruk be kuma cewa komai ba, ya karɓi ledar hannun ta, yai waje ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Farhan duk damuwa ta isheta, duk a takure take sosai, tana son sake ganin Sadik ko ta kirashi a waya, amma ta rasa yadda za tai ta kuma samun waya ta kirashi, haka nan take jin kamar zuciyarta a takure take rashin Sadik ɗinta, saura 1 week a koma school, amma ji take tamkar Shekara guda ya rage a koma makarantar.
Sadik yawonsa ya tafi, amma wajen tara na dare ya dawo gida, a falo ya tarar da Mother da Abba ga kuma Faruk suna kallo.
Abba ya kalli Sadik yace "kai daga ina haka?"
Sadik yace "na raka Salman ne gidan kakar su an aike shi"
"Mamanka ta san ka je rakiyar?"
Mother tace "A'a Abba ai naga abokinsa ne, kuma suna fita tare dama meyasa kake tambaya?"
Abba yace "bana son yawan yawon nan ne, gara ya zauna a gida yai karatu"
Sadik be ce Komai ba ya wuce ɗakinsa da ke cikin falon yana mita aƙasan ransa boko boko boko, an kasa fahimtar halin da mutum ke ciki se batun wata boko"
Ya ƙarasa Maganar yana rufe ƙofar ɗakin, ya jingina bayansa a jikin ƙofar yana sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya taka ya zauna a gefen tangamemen gadonsa, wanda yafi na BQ girma da kyau, ya ƙurawa system ɗin sa ido, yana jin kunnawa ya ci-gaba da kallonsa, amma yana tuna halin da ze iya shiga a dalilin cigaba da kallon.
Miƙa hannu yai ya ɗakko remote ɗin TV dake kan fridge ya kunna, canza tashoshi yake yana neman wadda ze kalla.
Ya daɗe yana caccanza Channels, miƙewa yai da niyyar rufe tagar ɗakinsa, ya hango Mother kwance a jikin Abba, suna kallo yana bata popcorn a baki, su dai sam basa girma suna bawa junansu kulawa duk da shekaru sun fara ja, amma Mother ta kan maida Abban kamar ɗan shekaru talatin, basa ɓoye Soyayyar su ko a gaban yaran su ne.
Sakin labule kawai Sadik yai a hankali ya furta "When, When will you understand that am also human being?"
Ya koma ya zauna yana cije lips ɗin sa na ƙasa.
Farhan a hankali ta lallaɓa ta shiga ɗakin Umma, ta tarar Umman tuni tayi bacci, cikin sanɗa ta ɗau wayar Umma ta fito daga ɗakin.
Ta sa wayar a silent ta tafi ɗakinta.
Ta turawa Sadik message kamar haka "Barka da dare, kwana da yawa ina fatan kana lafiya"
Wayarsa tai ƙara alamar saƙo ya shigo, ya kai idonsa kan wayar, yai ajiyar zuciya sannan ya janyo wayar, ya duba yai tozali da saƙon Farhan.
Hannu yasa a sumarsa yai murmushi, ya kwanta sannan ya kirata a waya.
"Dama idonka biyu ba kai bacci ba?"
Sadik yace "ke zan tambaya ba ki bacci ba?"
Farhan tace "eh nayi tilawa ne, na ɗakko wayar Umma na kiraka"
Yai murmushi yace "gaba ɗaya na koma kamar mara lafiya, saboda bana samun ganinki da jin muryarki"
"Nima haka ai"
"Dagaske kinyi missing ɗina"
"Umm" ta bashi amsa.
"Ok i understand, ya jikin naki?"
"Ni meya sameni?"
"Ba kince min kina ciwon ciki ba?"
Farhan tace "wallahi har yanzu yana min kaɗan kaɗan, wasu lokutan idan ya far sena dena duk abunda nake sedai in kwanta"
"Amma baki je Asibiti ba?"
"No ai ya dena"
"Karki min wasa da lafiyar ki Farhan please" ya ƙarasa Maganar muryarsa da rauni.
Farhan tace "lafiya kuwa, naji muryar ka na rawa?"
"Farhan Aure nake so" ya faɗa mata kai tsaye ba wata kunya ko shakka.
Jin maganar tai a bazata, wai Aure yake so se taji abun wani banbarakwai.
Shiru tai ta kasa Magana, Sadik yace "is sound somehow to you ko? Ban san a ya zan miki bayani ki gane ba, Farhan zanyi duk me yuwuwa in ga na Aureki nan kusa ba a nesa ba Insha Allah, ki kwanta kiyi bacci, dare yayi have a nice dreams Cwthrt"
A hankali ya ajiye Wayar ba tare da ya katse kiran ba, wayar Farhan ta bi da kallo, ta na maimaita abunda ya faɗa a ranta, cikin sanɗa ta tashi ta maida wa Umma wayarta, ta ajiye ta dawo ta kwanta, tana cigaba da jujjuya maganar Prince.
Kwanci tashi asarar rai, sati ya zagayo aka koma Makaranta, domin cigaba da gwagwarmaya ta neman ilimi, wanda ba'a samunsa da sauƙi, amma duk da haka a gurin neman ilimin Akwai bambanci me tazara tsakanin yaran talaka da na me kuɗi.
Farhan uniform ɗinta a goge suke tsaf, se murna take za'a koma Makaranta, wanda a zahiri ba komawa makarantar ce ta sata farinciki ba, haɗuwa da Sadik take ta ɗoki.
Shima nasa ɓangaren yana cike da shauƙin son ganinta, da kuma abokan karatunsa.
Ɗaliban sunji daɗin sake haɗuwarsu a zangon karatu na gaba, saboda akwai shaƙuwa ta mussaman a tsakanin ɗaliban.
Yana tsaye a cikin abokansa a gurin Assmebly tun daga nesa ya hangota ta shigo makarantar, ta cire ƙaton hijjabin jikinta, ta bar na makarantar da suka kasance tsangalallu.
Ta ƙara ƙiba tai fresh da ita, ta ƙara cika kayan makarantar nata, sosai alamun girma ke sake bayyana a tare da Farhan ɗin.
Be san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba, tare da lumshe idanunsa.
Guri ta samu ta tsaya a cikin 'yan ajinsu, ba wanda ya kulata se Lilly da ta miƙa mata hannu su gaisa.
Farhan ta miƙa mata suka gaisa, Lilly tace "An dawo lafiya"
Farhan tai murmushi tace "Lafiya ƙalau Alhamdilillah"
Nasir ne ya taɓa Sadik yace "dan Allah karka cimye Yarinyar nan da wannan idanun haba, wannan kallo haka"
Be ce Komai ba se cigaba da murmushi da yayi.
Har aka kammala Assembly ba ta gano shi ba sam, tai ta rarraba ido amma ba ta ganshi ba.
Haka aka gama ta tafi aji tana tunanin ko ya dawo yau oho.
A timetable period ɗin farko, Sir Nazir suke da shi.
Ya shigo ajin suka miƙe tsaye suka gaishe shi, kan ya basu iznin zama ya dinga bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo, ya ɗan tsurawa Farhan da ta sunkuyar da kanta ido, kan daga bisani ya janye idonsa zuwa kan Lilly.
Ta ɓalle botiran jacket ɗin ta, ana ganin ta cikin, gashi Masha Allah ta zama budurwa ita ma, duba da yanayin girman jiki na yaran masu kuɗi, ita ma ta fara cika.
A kausashe yace "Fatima, Allah ya dawo damu ko, close your jacket my friend"
Ɗan tura baki Lilly tayi, sannan ta sa hannu ta rufe botir ɗin rigar ta ta.
Haseena ta waigo ta kalli Lilly, ta sunkuyar da kai tana dariya ƙasa ƙasa, yai musu umarni suka zauna.
Daga bisani yai musu maraba da dawowa sabon zango, yai musu Nasiha sannan ya ɗora musu da lectures na ranar.
Kasancewar double period ne be fita daga ajin ba, se break yana fita Haseena ta kalli Lilly tace "to ƙarama 'yar air, daga dawowa zaki fara sa bawan Allah a gaba"
Lilly tai murmushi tace "gani ba taɓawa ba asarar ido"
Haseena ta ƙara samata da "taɓawa ba tafiya da shi ba asarar hannu"
Lilly tace "dan ubanki hauka nake zan tsaya a taɓa, ba wannan maganar sedai in ta gwara kan mutum"
Yasmin da ke ƙarasa kwafar note tace "za kiga ba me taɓawa, naga kin ƙaro wulaƙanci har wani chestout ki ke yanzu"
Lilly tace "to ke ya kika gani?"
Farhan na jinsu, amma ba ta ko motsa ba, ta cigba da danna carbin hannunta.
Ƙamshin turarensa ne ya mamaye mata hanci, tana ɗaga kai ya zauna daf da ita a hankali yace "shine ko ki neme ni ko? Anya kinyi missing ɗina kuwa?"
Murmushi tai tace "Ai na duba a gurin Assembly ban ganka ba, nayi zaton baka dawo ba"
"Meze hanani dawowa inga amaryata, ni tun lokacin da kika shigo na ganki ai, Kinyi ƙiba sosai, me Ummana take baki ne haka?"
Wani daɗi ne ya cikata jin yace Ummansa, ko ba komai yai mata kara ya girmama Ummanta.
"Tuwo take bani"
"Nima zan zo ta dinga bani gaskiya, karki fini ƙiba"
Ƙaramin tsaki Haseena ta ja tace "ban taɓa ganin munafukin mutum kamar wannan Farhan ɗin ba, ba wanda ta kula amma ga yadda take wata dariya"
Lilly tace "to ke da shi ɗaya ne, abunda ke jikinki shike jikinta akan me zata sakar miki fuska? Dalla ku tashi mu tafi muyi order Abinci"
Wani irin baƙin ciki ne ya cika zuciyar Haseeena, da ƙara tsanar Farhan fiye da baya.
" 'yar me kyau na, nayi kewarki sosai fa"
Sunkuyar da kai Farhan tai tana murmushi, tana jin daɗin hirar da yake mata.
"Tashi muje ki rakani wani guri"
Ba musu ta tashi suka fita daga ajin tare, sedai kamar tsautsayi suna fita sun fara sakkowa daga bene, sega Nazir na hawowa ya dinga bin su da wani irin kallo, kamar haɗin baki suka basar da shi suka wuce.
Shop ta raka shi, ya sai mata kayan ciye ciye kala kala, se dai da farko ƙin karɓa tayi, seda ya ɓata rai, sanna ta karɓa.
Seda ya rakata har ajinsu, sannan ya tafi nasu ajin, ta zauna ba daɗewa taji tana jin fitsari, dan haka ta miƙe ta tafi banɗakin mata da benen, dan ba ta son sake sauka daga benen.
Tana shiga ta ga was 'yan ss3 a ciki, da alama kamar ba su da gaskiya, ɗaya ta mata tsawa tace "ke me kike a nan!"
"I want ease myself" Farhan ta faɗa fuskarta ɗauke da tsoro.
Wata daga cikin su tace "dena mata tsawa, budurwar Prince ce fa, a kanta yanzu ze tayar miki da jijiyar wuya, dan ban manta zagin da yai min akanta ba"
"To ina ruwana, yi abunda zakiyi ki fita, tana Magana da wata maƙalalliyar muryata, tana turanci kamar baturiya, saboda iyayi"
Ɗayar tace "don't you see she's Fulani girl, i just like her she's beautiful and innocent, I want her to be my lover"
Farhan ba ta gane me suke tattaunawa ba, taga Anshigo da Nasreen toilet ɗin, an rirriƙeta tana ta uban gumi. Tabbas ba zata taɓa manta fuskar Nasreen ba, dan a duk lokacin da ta ganta ba abunda take tunawa se yadda ta gansu ita da George.
Farhan ba ta son su kuma yi mata Magana, dan haka ta shiga ɗaya daga toilet ɗin tai abunda za tai ta fice.
"Wayyo Allah na zan mutu! Na shiga uku zan mutu, ku taimaka min dan Allah!!!"
THIS IS JUST THE BEGINNING!!!
DOMIN GYARA SHARHI KO SHAWARA
Ayshercool.
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
RUƊIN ƘURUCIYA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Writer of
WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)
_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_
⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️
SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.
27_28
Tsoro ne da fargaba suka ziyarci Farhan, jin wannan ihun haka, ba tare da tayi fitsarin ba a razane ta leƙo, aikuwa ta ga jini na zuba sosai a jikin Nasreen, wadda ta riga ta haɗa uban gumi kamar tayi gudu.
Take Farhan ta sake birkicewa, ta tsorata ainun ganin wannan uban jini, kamar an yanka rago.
"Ke da kin san baki iya abun ba kika je kika fara, gobe ma kya kuma ai, se ki shiga taitayinki, in kin san zaki yawon ki, seki ɗau mataki ba ki bari abu ya faru haka ba"
Suka cigaba da caccakarta suna mata mita, ita kuwa Nasreen se jujjuya kai kawai take, ita kaɗai ta san azabar da take sha.
Can wata tace "seki gode Allah, tunda Allah ya rabaki da wahala cikin ya faɗi"
Gaban Farhan yai mummunar faɗuwa, Suf Farhan ta silale ta bar banɗakin jikinta yana tsuma, gaba ɗaya ta birkice, ba ta taɓa ganin jini me yawan haka ba.
Abunda ya sake ɗaure mata kai, be wuce yadda taji ana cikin ya faɗi ba, to ciki ya faɗi kamar yaya? Ta yaya cikin mutum ze faɗi?.
Jikinta se tsuma yake ta tafi ajinsu, ta nemi guri ta zauna ta kifa kanta a benci, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin lugude kamar zata faso ƙirjinta ta fito.
Haseena ta kalli in da Farhan take ta ja uban tsaki, tace "Idan za'ai taro na 'yan makarantar nan be kamata a dinga gayyato 'yan alfarma ba, ga bikin yayan Prince da mukaje, yadda wata taje yarkace yarkace kamar wata 'yar ƙauye, taɓɗijan Ni wallahi da bikin gidanmu ne ta zo korarta zanyi wallahi"
Gaban Farhan farhan ta ji wani dumm a ƙirjinta, dan ta san tabbas da ita Haseena take, taji zafin Abinda Haseena ta faɗa amma ba ta damu ba sosai, sakamakon tasan eh dagaske ita ɗin ba 'yar kowa bace akan su. Ita abunda ta gani yau yafi komai ɗaga mata hankali nesa ba kusa ba.
Yauma Meena lesson kawai ake, amma ba wani ganewa take ba, dan tunda ta zo take maye, ƙwayar da ta sha daren jiya ba ta gama sakinta ba.
Taslim ta kalleta tace "Ke Meena, ki dena shan abun nan in zaki zo school,