Showing 99001 words to 102000 words out of 259198 words
Chapter 34 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
beautiful, and at the same time kina da innocent soul kina da hali me kyau shiyasa nake ta kula, bana son wani ya ƙwace min ke, dan Allah Farhan ki dinga mana Addu'a, Allah yasa kar a rabamu, Allah ya tabattar mana da Alkhairi a tsakanin mu"
A zuciyarta tace "Ameen" Amma a fili tai shiru.
"Farhan ba ki ce Ameen ba, ko ba kya sona ne?"
Noƙe masa kafaɗa tayi.
Yace "ok faɗi Ameen in ji"
"Nifa na faɗa a raina" tai maganar a shagwaɓe.
"Ni ban ji ba ki faɗa inji" yai maganar yana kwaikwayon muryarta.
"Uhmm ka bari"
"My Lovely baby, wannan shagwaɓar taki is killing me"
Ya ɗakko wata leda, cike da kayan ciye ciye na chocolate yace "ungo ke na siyowa wannan"
"Ta ya zan shiga da Wannan gida? Idan aka ce a ina na samo fa?"
"Kice mijinki ne ya baki, ai ba a shiga tsakanin miji da mata"
Zare ido tai ta kalleshi.
Yaxe "eh mana, tunda ke dai baki da wayo, ga jakar Islamiyyar ki nan ga ƙaton hijjabi, kisa a ciki mana"
Ba ta san yawan yi masa musu, dan haka ta karɓa tace ta gode.
Islamiyyar da Farhan ba taje ba kenan, ta zauna suka cigaba da hirar su a mota.
Seda lokacin tashin su daga Islamiyya yayi sannan yace bari ya rakata bakin layin su.
Suka fito daga motar, ya rakata har bakin layin, sannan ya juya ya tafi.
Zuwan Sadik duk ya mantar da ita wata damuwa da take ciki.
Sedai ta na zuwa gida ta fara fargabar kar a gane ba taje makaranta ba.
Da daddare ta tura ƙofar ɗakinta, ta ɗakko wayar nan, ta saita komai a silent.
Tana cikin saitawa se ga message ɗin Sadik "Hi sweetheart, kinyi bacci ne?"
"No banyi bacci ba, ya kaje gida?"
"Lafiaya ƙalau Alhamdilillah, meya hanaki bacci har wannan lokacin?"
"Thinking of someone very important to me"
"Wow, who is that lucky?"
"Youuuuuuuu"
Abun mamaki, Farhan ta zage suka dinga hira kamar ba ita ba, da yake ba a gabansa bane, ta dinga tura masa saƙonnin soyayya.
Har kusan ƙarfe ɗaya na dare, sannan su kai sallama, ta je ta ɓoye wayar.
Sedai bayan sunyi sallamar Sadik ya shiga aikin nasa na tunani, kullum sake jin Farhan yake a cikin zuciyarsa, sedai ya kasa tuna menene mafita akan wannan lamarin, ya rasa ta ina ze fara samun mafita, ga tafiya zeyi Gashi yasan ko giyar wake ya sha, Babu yadda za'ai Farhan ta jira shi tsawon shekaru bakwai ba tai Aure ba, ga ƙudurin iyayenta na son Aurar da ita da zarar ta kammala Makaranta, gashi ya rasa goyon bayan iyayensa akan abinda ke damun sa.
Lilly kam tai ta ɗar ɗar ko Mamanta za tai noticing wani canji a tare da ita, amma taga sam mamanta ba ta fuskanci komai ba dan haka Kamar wasa, Lilly da Nazir suka koma suka jone kamar yadda suke a baya.
Sema sake samun kusanci da su kai da juna fiye da baya.
Farhan ta cigaba da zuwa Makarantar ta, wasu lokutan da wayar take tafiya makarantar, idan an fita break ta ɗau wayarta ta samu wani gurin, suyi ta waya da Sadik.
Yau kamar yadda ta saba tai wayar ta gama, zata koma aji taga Mubarak Babba ya zo makarantar, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, dan yace in dai yana raye seya rama marin nan da tai masa.
Aka tashi daga Makaranta, ta kasa ko fitowa daga aji saboda tsoron ba ta san meze mata ba.
Da ƙyar ta samu ta fito daga ajin, tana waige waige da niyyar ta samu dama ta gudu gida, yau take sake ganin Ranar Sadik a makarantar nan, duk abunda ze faru ba wanda yake raɓarta saboda a na tsoron sa.
"Leƙe leƙen me kike? Gani nan a bayan ki, dama ai dan ke nazo"
A razane ta waiwayo taga Mubarak Babba, a tsaye ya zura hannayensa a cikin aljihun wandon sa.
Razana tayi taja ta tsaya tana kallonsa.
"Ke da kin ɗauka da wasa nake da nace sena rama marin da ki kai min, ko a zatonki ƙarya nake da nace sena samu abunda nake so a tare da ke?" Yai Maganar yana takowa gabanta, ita kuma tana ja da baya, har ta kai bango.
"Yanzu ai gaki, ba wannan shashashan da kike taƙama da shi ze tare miki, ba abunda zan miki a yanzu, saboda nan be dace da gurin ɗaukar fansa ba, amma ko a jima ko a daɗe zamu gauraya, ina nan akan bakana, sena ƙetara abunda Sadik a kasa ƙetarawa"
Yai maganar yana dariya da ƙoƙarin kai hannunsa fuskarta.
"Kai Mubarak meye haka?" Da sauri Mubarak ya waiwaya, yaga Amin.
Amin yace "meye haka kake ƙoƙarin yi ne?"
Babba yace "ina ruwanka da abun da nake ƙoƙarin yi? Ina taya kaya ne"
Amin yace "kaga Mubarak dan Allah ka bar wannan maganar, duk matan da kake bi a ciki da wajen makarantar nan be isheka ba, wannan dai ita Sadik ya ƙallafa rai a kai, dan Allah ka bar masa kayarsa, ka bar ganin baya makarantar, kasan halinsa ze iya nemoka wallahi"
Mubarak yace "wallahi tunda na ƙyasa sena ɗana, kaima kasan bana ɗora raina akan abu in janye, and I will show her" yai Maganar yana kallon Farhan da ke zazzare ido.
Amin yace "wannan amanar Sadik ce, ka nemi wata dai banda wannan, in ba haka ba kaima akwai sister ɗinka a school ɗin nan semu far mata"
"Kutmar, karka kusakura wallahi kar kayi wannan gangancin" yai maganar yana nuna Amin.
Amin yace "Ashe ba daɗi kake lalube na wasu, ai iya wuya Sadik namu ne, idan muka bari a kai masa ɓarna bamu kyauta ba, Farhan wuce kiyi tafiyarki"
Farhan har da haɗawa da gudu ta bar cikin makarantar, ƙirjinta na dukan uku uku. Da godewa Allah ta tsira daga sharrin Mubarak.
Farhan duk lokacin da suka so haɗuwa da Sadik, se su haɗa meeting point lokacim tafiyarta Makarantar dare, su shiga mota su yi hira sannan ya tafi.
Gefe guda kuma tana ta fama da Sunusi, kasancewar sa mutum me nacin tsiya, wanda ba ya zuciya, yayi burus yaƙi nunawa Farhan yana jin haushin rashin saurarsa da take.
Wasa wasa kusan kullum se Mubarak ya zo Makarantar nan, duk da ba uwar da take kawo shi, sedai zuwa yiwa Farhan barazana, gashi ta kasa gayawa Sadik saboda buyagin sa.
Yau fitsarar Babba tasa har ajinsu Farhan ya bita, tana zaune tana solving Maths, 'yan ajinsu ana can gurin raye raye da support, kasancewar juma'a ce, seji tai Mutum ya zauna a kusa da ita.
A zabure ta miƙe tsaye, amma ya tare mata hanyar fita.
"Dan Allah ka rabu dani" ta faɗa muryar ta na rawa.
"Yarinya kenan, haryanzu baki yadda da abunda na faɗa ba kenan, idan so nake zan iya sawa a kamo min ke, inyi yadda na ga dama da ke, sedai sonake a karan kanki zaki amince dani*
Yasa hannu ya matse mata kumatunta da ƙarfi.
Taɓa ta yake da hannun sa, tana buge hannunsa tana kuka, tana neman hanyar fita, sukaji an daki ƙofar ajin da ƙarfi.
He was very shocked da ya ga Sadik, dan tunda suka kammala jarrabawa, Sadik be sake shiga makaranta ba.
Be tsaya ba ya janyo Mubarak ya ɗura masa wata irin Ashariya.
Jijiyoyin Kan Sadik duk sun ɗaɗɗaga, idonsa yai ja ya kalli Mubarak yace "kai dan baka da mutunci ka rasa wadda zaka bi se abunda nace nawa ne? Tunda muka bar makarantar nan ka fara bibiyarta ake gayamin, dan na ƙyale banyi Magana ba shine kake son zarce gona da iri, an gayamaka a banza zan bar makarantar nan in ƙyaleta? I already put my CID on her, me tai maka kake bibiyar ta? Ko abunda ke tsakanin mu ne ya shafe ta?"
Sadik yai maganar yana hankaɗa Babba.
Mubarak yafi Sadik girma sedai Sadik ya fishi siffar ƙarfi.
Ya kalli Farhan a fusace yace "dan me kika ɓoyemin yana bibiyar ki? Yanzu ba dan an sanarmin ba nazo da shieknan komai ze iya faruwa? Farhan why?"
Kasa Magana tai se kuka da take.
Sadik ya kuma kallon Mubarak yace "wannan shine magana ta da kai ta ƙarshe, kar ka kuskura abunda ke tsakanin mu ya shafi Farhan na gaya maka"
Mubarak yace "Ai kowa yaci tuwo da ni miya ya sha, ka rubuta ka ajiye idan har ina raye, sena wulaƙanta yarinyar nan, tunda ita ce abunda ka ɗora ranka a kai"
Sadik be kuma cewa komai ba, ya fizgo Farhan da jakarta, sukai waje yana huci.
A mota suna tafe se kuka take, "malama ki rufen baki, yanzu ba dan an gayamin yana bibiyar ki ba da komai ze iya faruwa, kin san halin Yaron nan kuwa? Meya haɗaki da shi ma tukuna?"
Cikin kuka Farhan ta gayawa Sadik Komai, haka ya dinga mata faɗa yace duk lokacin da aka tashi ze zo ya dimga ɗaukarta, kuma ya na da masu yi masa CID a kanta a cikin ajinsu ba a wani guri ba.
Haka ya kaita gida, sannan ya tafi.
Farhan ta tsorata da lamarin Babba, amma ta rasa meye a tsakanin Sadik da Babba, saboda wasu lokutan tana ganinsu tare, kuma shi Babba yana zuwa sha'anin Sadik sosai, amma meye a tsakanin su haka?.
Abba yana zaune a falo, yana kallon labarai, Mother na masa hira.
Faruk ya shigo falon da sauri.
Abba yace "Jarumin maza, saurin me kake haka? Ya akayi?"
Cikin damuwa Faruk yace "Abba, yanzun nan aka kirani a waya daga gidan Hakimi, wai ba shi da lafiya, an kira wayar ka ba ta shiga, kusan sati biyu kenan ba shi da lafiya"
Da sauri Abba yace "subhanallah, ai idan ina can layina baya shiga, amma ya akai ba'a kira gidan nan an faɗa ba?"
Faruk ya kalli Mother, ya ɗauke kai Yace "Abba, ance min an kira wayar Mother an gayamata, amma ba wanda yaje duba shi a gidan nan, ni da na sani zanje"
Abba ya kalli Mother yace "Yanzu Hauwa har a kiraki mahaifina ba lafiya, ba kije kin duba shi ba, ba ki tura wani daga yaran nan ba, kuma in dawo ki kasa sanar min?"
Wani Mugun kallo Mother taiwa Faruk sannaan yace "Wallahi ban zaci abun ya kai haka ba, da mu ka waya cemin sukai kawai zazzaɓi ne ke damunsa, aka kwan biyu na kuma kira aka cemin jikin da sauƙi, shiyasa ban gaya maka ba"
A fusace Abba yace "ya isa haka, dattijo kamar wannan ba lafiya, ai yafi ƙarfin ace is not that serious, ko daya ke tunda ba mahaifinki bane ai dole kice haka nagode" ya tashi ya bar mata falon ransa a matuƙar ɓace.
Mother ta dawo da idonta kan Faruk tace "Sannu mara mutunci, ka tunzura shi yamin masifa hankalinka ya kwanta kaji ko, saboda tsabar rashin mutunci maimakon ka bar maganar a iya an kiraka ance ba shi Da lafiya, shine har da gaya masa ai sun gayamin ban gaya masa ba"
Faruk yace "Mother ba haka bane, yanzu shi Abba se suga lafinsa, da aka kira aka faɗa kinga da koni kin aika naje na duba shi ai kinga da abun baze zo a haka ba"
"Dallacan rufemin baki, sakarai kawai shiyasa nafi son Auta ai, da Shine da babu yadda za'ai yaimin wannan shirmen da kai min"
Faruk ya girgiza kai yace "ai ko baki faɗa ba dama nasan ni ba sona kike ba, kinfi son Sadik, amma yadda muke ƙaunar ku haka shima yake ƙaunar su, Mother ba zaki ji daɗi ba ace yai koke ko Abba wani ba lafiya, amma ba wanda ya zo kanku a cikin mu, hakan ai ba daɗi but am so sorry Insha Allah ba zan sake aikata hakan ba"
Ya juya ya bar falon.
Duk cikin su ukun nan babu me biyayyar Faruk, shi dr. Dama ba magana yake ba, ko laifi yai maka sedai baƙin ciki ya kashe ka, in zaka kwaɗa shi ka cinye da faɗa wai ya ɓata maka rai, baze ma nuna maka yasan da shi kake ba balle ya baka haƙuri.
Sadik kuwa ƙeƙe da ƙeƙe me ba'a tursasa shi, idan yai laifi kai masa faɗa ma se yai zuciya, koma ya bar maka gurin gaba ɗaya, baya son tashin hankali sam, shi ko laifi yai yafi som ai masa nasiha akan ai masa faɗa.
Faruk ne kawai ko yayi laifi ko beyi laifi ba, dan a zauna lafiya zece ayi haƙuri, sam baya son yaga ya ɓatawa wani rai ace yayi laifi, sedai idan aka fusata shi kamar wuta haka yake, baya sakkowa ta daɗin rai.
Duk da son da akewa Sadik a gidan, amma Abba yana wa Faruk so na musamman, saboda sanyin halinsa da rashin son hayaniya.
Yau kowa a ɓangaren sa ya kwana daga Abba har Mother, dan yayi fushi sosai ga fushinsa ba sauƙi sam, Mother ta rasa in da zata sa kanta.
Faruk ya koma sashinsu, ransa a ɓace ya tarar da Sadik da wayarsa a hannu, yana cin bredi.
Messages ɗin Farhan yake kallo tana ba shi haƙuri, amma yaƙi tankawa dan soyake ya nuna mata yaji haushin ɓoye masa abu da tayi.
Messages ɗin ta na ban haƙuri kala kala, amma yaƙi reply.
Faruk yace "Autan Mother, Hakimi ba lafiya fa, ashe tun kan Abba ya dawo Hakimi ba shi da lafiya"
Sadik ya ɗago ya kalli Faruk yace "Allah ya jiƙansa" ya maida hankalinsa kan wayarsa.
Faruk ya buɗe baki yace "dan ubanka ce maka nai ba shi da lafiya, amma kace Allah ya jiƙansa"
"Ohh sorry, na zi cewa nai Allah ya sawwaƙe"
Gaba ɗaya Faruk ya lura, hankalin Sadik na kan wayarsa, dan haka ya ƙyaleshi kawai.
Farhan ganin Sadik yaƙi kulata duk tarin messages ɗin da tura masa yasa ta haƙura, ta tabattar yayi fushi ne sosai haka, abunda be taɓa yi mata, yai fushi da ita haka.
Ƙarfe bakwai na safe Abba ya shirya tsaf, da nufin tafiya ƙauye gurin mahaifinsa, yana ƙoƙarin fitowa ne sega Mother ta shigo, ta kalleshi tace "Yallaɓai dan Allah ka tsaya ko breakfast kayi seka tafi"
"Bana buƙata" Abba ya bata amsa a taƙaice.
"Dan Allah kayi haƙuri, ka karya kan nan gama shiryawa semu tafi tare"
Be bata amsa ba ya raɓata ya wuce, ta biyo shi tana masa Magana, Amma yaƙi saurarar ta.
Bawan Allah, Yana fita harabar Ajiye motoci, yaga Faruk ya shirya harya fito da mota.
Abba yace "Faruk ya dai?"
Faruk yace "Abba ai nasan yau zakace zaka, shine kawai na shirya da wuri na fito da mota, yanzu dama nake sa ran shigowa cikin gidan, inji da Yaushe zaka tafi in bika"
Abba yai murmushi yace "to shikenan, mu tafi kawai na shirya"
Ya buɗewa Abba mota ya shiga, ya zaga ya buɗe motar shima ya shiga sannan yace "Mother semun dawo"
Ya fara jan motar sannu a hankali suka bar gidan.
Wani marurun takaici ya tokarewa Mother rai, saboda tsabar abu da rashin hankali irin na Faruk, wannan ƙungurmin ƙauyen yabi mahaifinsa, abun takaicin ma wai shi ze ja motar har can, ta ja ƙaramin tsaki ta juya ta koma.
Sadik ƙarfe goma ya tashi kamar yadda ya saba tunda ya gama makaranta, wayarsa ya fara ɗakkowa ya duba messages ɗin Farhan, murmushi yai, tare da kissing ɗin message ɗin yace "ina sonki Babyna, amma dole ina nuna miki rashin jin daɗi na akan laifin da ki kai min" ya ajiye Wayar ya shiga yai wanka ya fito ya tafi sashen Mother.
Yaje ya tarar da ita a zaune tayi shiru, an kawo mata breakfast amma ba ta ci ba.
"What's up Mom, Good morning"
Ajiyar zuciya tai tace "ka tashi kenan?"
"Eh Mother, wai na ganki somehow worried, meke faruwa ne?"
Nan ta gaya masa abunda ya faru, da yadda Abba da Faruk suka tafi ƙauye.
Sadik yace "to Mother meye abun damuwa a nan? Zaki zauna ki ƙi cin Abinci?"
"Bari Sadik, nasan da kaine ba zaka min wautar da Faruk yai min ba, saboda tsabar shirme ya san halin babanku da ɗaukar zafi amma yaimin wannan kwaɓar haka, yadda kasan in mangare shi wallahi, yaita abu kamar ƙaramin yaro, wai a nan ya kammala degree ze koma masters, amma yai ta abu kamar wani mara wayau"
"Easy Mother, ni wallahi idan kina masa faɗa haushi nake ji, bana son inji kina masa faɗan nan wallahi"
Mother tace "Au goyon bayansa kake?"
"A'a ba goyon bayansa nake ba, kawai dai bana som in ga ana ɓata masa rai ne, duk da nima wasu lokutan yana ɓatamin rai, amma haƙurinsa ne yasa yake ban tausayi, dan nafi sonsa akan wannan dukun dunkun ɗin"
"Waye dunkun dunkun ɗin?"
Sadik yai murmushi yace "ba kowa, amma dai na ari bakins na bada haƙuri, dan Allah ayi haƙuri a dena mai faɗa, ji nake kamar ni akewa"
Mother tace "to me ɗan uwa, nima ina son abina ai, dan duk ya fiku hankali"
Sadik kawai ya girgiza kai yace "Mother kina da abun mamaki, bari in zo in karya"
Ya fara haɗa kayan tea da suke gaban Mother ya fara karyawa, ya barta da tunani.
Farhan Alla Alla take a tashi, Sadik ya zo ɗaukarta ta kuma bashi haƙuri, sedai direba ya turo ya ɗauke ta shi be zo ba, ji tai kamar tace ba zata bishi ba, amma gudun karta kuma wani Laifin yasa ta bishi ya kaita gida.
Abba wajen ƙarfe goma na safe suka isa.
Sedai jikin Hakimin da sauƙi, amma dai yayi rama sosai da alama ya sha jiki.
Inna tace "Allah yayi ka zo kenan Hakima ta barka ka zo duba shi?"
"Inna ba haka bane, bana gari ne, shiyasa kuma itama ba ta da lafiya wallahi ban sani ba"
"Eh ai dama ba za saka sani ba, tunda da ka dawo baka damu da kazo in da muke ba, ni ban damu lallai seka zo ba ma, ai ko ta waya ka kira kaji yadda muke, Abdullahi ka kiyaye ni fa"
Abba ya kwantar da kai ya dinga ba da haƙuri.
Faruk yace "Inna na Nana ne?"
Inna tace "ta tafi Makaranta, se anjima zata shigo"
Inna tai ta yiwa Abba faɗa, Faruk ya koma kusa da Hakimi ya ɗauki man zafi ya dinga shashafa masa a bayansa zuwa hannayensa, yana mammatsa masa yatsunsa cike da kulawa da tausaya wa.
Hakimi yace "Anya ba za'a bar min wannan mutumin a nan ba, ya iya jinya fa" yai maganar cike da zolaya.
Abba yace "ko Asibitin cikin gari za'a tafi da shi a duba shi sosai?"
Hakimi yace "A'a, ga ƙaton Asibiti nan da ka gina mana, akwai kayan aiki sun min duk abunda ya dace, dama hawan jini ne, kuma sunce ya sauka Yanzu Alhamdilillah"
Faruk yace "Ai can akwai ƙwararru fiye da nan, ka bari mu tafi da kai kawai, kaga daga nan semu riƙe ka,