Showing 6001 words to 9000 words out of 259198 words
Chapter 3 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
sosai.
Nazir ya gama faɗansa san ransa sannan ya shiga gabatar da lesson ɗinsa.
Har ya gama karatunsa Farhan kuka take yi, dan sam na ta fahimci komai ba har yai ya gama.
Bayan ya fita wata daga cikin'yan ajinsu wadda ake cewa Lilly tazo ta dafa kafaɗar Farhan, Farhan ta ɗago kanta ta kalli Lilly.
"Ki dena kuka ki rabu da wannan ɗan rainin hankalin kinji, ki dena kuka"
Farhan ta jinjina mata kai alamar to.
Koda aka tashi daga school, Farhan bata jira kowa ba ta silale ta tafi gida, Sadik yaita nemanta be ganta ba, haka ya haƙura ya tafi gida, yana mamakin yadda aka yi ta tafi basu haɗuba.
**********
Gudu gudu sauri-sauri haka ta faɗo makeken tsakar gidan, hannunta ɗauke da jakar makaranta, tana zuwa ba tayi wata wata ba, tai jifa da jakar a tsakar gida, ta faɗa banɗaki.
Dattijiwar dake zaune tana mulmula fura, ta kalli jakar makarantar da yarinyar ta jefar a tsakar gida, ta girgiza kai ta cigaba da aikinta, kusan mintuna biyar sannan ta fito daga banɗakin, ta tsaya a tsakar gida ta shafa cikinta tace "wayyo Allah, fitsari idan ya matseka ba arziki, ina tafe a hanya kamar zanyi hauka, saboda yadda ya matseni"
Dattijuwar ta kalleta tace "zaki zo ki ɗauke wannan jakar da kikayi jifa da ita a tsakar gida, ko kuwa se nayi yaƙi da bakina"
Ɗan tura baki tayi, taje ta ɗauke jakar Tata, ta kai cikin ɗaki ta ajiye, ta cire duk kayan jikinata, ya rage daga ita se dogon wandon makarantar ta, ta fito tsakar gida tana faɗin "Innarmu, wai yau me aka dafa ne?"
Inna ta ɗago zata yi magana, amma taci karo da yadda yarinyar ta fito tsakar gida.
"Nana waike wace irin sha3 ce ne haka? Kalli fa a yadda kika fito, kowane lokaci za'a iyayin sallama a shigo gidan nan, amma kika fito tsakar gida a haka"
Ummi ta ya mutsa fuska ta kalli kanta tace "to ni innarmu me nayi?"
"Dan ubanki baki san kin fara girma bane? Dubi ƙirjinki kin fara ƙigar dangi, amma kin fito a haka bako Kunya, ko 'yar shimi ba ki saka ba"
"Meye kuma ƙirgar dangi?" Ummi ta tambaya cike da wauta.
Inna tace "kin wuce kin nemi riga kin saka, ko sena taso na iskoki a gurin nan, gaɓuwa kawai ba kya ganin yadda ƙirjinki ya tasa? Amma kike yawo a haka? Karki adana su ki bari su fito a wulaƙance, naga alamar idan banyi dagaske ba, haka zakiyi budurci ba kintsi, 'yar butar uwa da kai kamar gwai gwai"
Ummi ta faɗa ɗaki, tana kumbura baki, dan bata son wannan faɗace faɗacen na Inna, Gashi idan ta tashi yi bata rufe komai, haka za tai ta sakin bayani, ko a gaban waye kuwa haka za tai ta sakin zance da sunan faɗa.
"Sarkin faɗa, ke da waye kuma da tsakar ranar nan kike faɗa haka?"
Cewar dattijon da yake shigowa, jikinsa sanye da Alkyabba.
"Dawa zanyi faɗa banda wannan yarinyar, duk gidan nan wake sani magana banda Nana, yarinya kamar ba'ace mata bari, taɓara da iya shege sinƙi sinƙi a cikinta"
Dattijon yai murmushi Yace "haba ke kuwa, takwarar taki guda, Ki dinga haƙuri da ita, yarinyace har yanzu ke kike ganin girmanta, amma yarinya ce ƙarama"
'ko da yarinta, harda iskancinta wani lokacin, bata taɓa jin daɗi idan bata sani magana ba"
Yai murmushi Yace "to yanzu dai ba wannan ba, zuwa wani satin insha Allah, gidan Abdullahi zasu kawo lefen Usman ɗin, ina fatan kina nan kina shiri?"
Inna tace "eh ina shiri, naji yace bikin bada tsawo za'a saka ba, ina ga idan suka kawo Kayan, zan bisu se kuma anyi biki, dan bana son yawan tafiyar motar nan"
But Nana dta fito daga ɗaki da ɗaurin ƙirji tace "Alhaji wai waye zeyi aure ne? Wai su wannan ɗin nan na birni?, wanda basa dariya sosai masu tara gashin nan kamar ƙabilu? 'ya'yan kawun nan?".
Dattijon Ya buɗe baki Yace "yayyen naki ne baki san sunansu ba? Se masu tara gashi?"
"Ni a ina zan san sunansu, bayan ba kula mutane suke ba, kuma ma ba zuwa gidan nan suke ba"
Alhaji ya jinjina kai Yace "ikon Allah, lallai wannan abu bemin daɗi ba, Dole a tafi da Nana, kuyi kwanakin Tare, dan ta ga 'yan uwanta sosai"
Ummi tai tsalle tana faɗin "yee, zani birni inje asha bikin 'yan gayu dani"
Inna tai tsaki tace "mara hankali, ai idan kikaje ma kallon kwantacciya zasu yi miki, musamman matar Abdullahi, me wa mutane kallon banza"
Alhaji Yace "ai haka nan za'aje da Ita, rashin zumuncin yayi yawa, ace ba tama san sunayen su ba, shikenan ace yaran nan ko garin nan basa zuwa, balle su shaƙu da 'yar uwassu?"
Inna tace "to ya zamuyi tunda uwarsu bata so? Nace a kai maka furar turakarka ne idan an dama?".
"Eh, a kawomin turaka, ina so idan na sha na ɗan huta, zanyi baƙi da yamma"
Inna tace "to shikenan, Allah ya baka yawan rai, zan kawo insha Allah"
Ya nufi hanyar ɗakinsa, Inna ta tashi, ta wanke hannunta, ta shiga ɗaki, ta tarar da Nana da ɗaurin ƙirji tana shirin Dutse"
"Nana kinyi salla kuwa?"
"Inna ai da sauran lokaci fa"
"To kuma kafin kiyi wanka, ba lokaci yayi ba?"
Nana ta zumɓura baki tace "wai Inna ba nayi wankan nan da safe ba? Shikenan ni kullum cikin wanka kamar wata tarwaɗa?".
Inna tace "kyaci ubanki, lokaci na nan zuwa da za kiyi medalili, wanka ba wataran da asubar fari, koman sanyi haka zakiyi shi"
"Wankan?" Nana ta tambaya cike da mamaki.
Inna tace "ƙwarai kuwa wankan da ki ke gudu, kuma dole ki koyi wanka da tsafta tun Yanzu kina gida, gaba nake jiye miki, kuma Yanzu ki ke girma kina kan tashen balaga, warin jikinki daban ze dinga fita, kuma duk wanda ki ka bari yaji wari a jikinki kin faɗo, ze dena ganin mutuncin ki, kuma dan ubanki na sake ganinki da ɗaurin ƙirji Sena makeki, idan baki alkinta abubuwan nan ba haka zasu fito ba tsari, kiyi 'yan matanci amma nono a zube, kizo kiyi aure ba zasu dinga birge miji ba"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, waike Innarmu kiyi ta faɗan magana ba kyajin kunya"
Inna tace "Naƙi inji kunyar, idan ban gayamiki ba wani a waje zan jira ya gaya miki?, kin tashi kin tafi wankan ko sena zo inda kike? Na watsar da ke"
Nana ta tashi tana bubbuga ƙafa, da takaicin yadda Inna ke sata wanka ba gaura ba Dalili, ta ɗebi ruwa ta tafi banɗaki.
Bayan shigar Nana banɗaki, Inna tace "A kula idan za'ayi wanka, a wanke hammata da kyau, wuya da duk wani lingu....
'innalillahi Inna na haddace wallahi, na haddace ko karatune wannan na iya ke kullum sekin nanata min yadda ake wanka wai?"
'rufemin baki, gara in nanata miki ai, dan banƙi in zuba ruwa in wankeki da kaina ba,wani warin jikin yana faruwa ne daga rashin iya wanka tun a ƙuruciya, in kin gama wankan ga ruwan alumun nan da miski ki shafe jikinki dashi"
Nana ta yiwa Inna banza, dan wannan karatuttukan na Inna basa ƙarewa.
Inna ta damawa Hakimi furarsa, ta shiga kai masa, ta tarar dashi yana dariya, ta kalleshi tace "lafiya naga kana dariya?"
Yai murmushi yace "dariya nake miki keda jikar taki, kina takura yarinyar nan da yawa fa"
Inna tace "a'a ba takura bace, gara in gaya mata ai, duk da Allah be taɓa bani 'ya mace ba, amma ni ban yadda se an sawa yarinya rana, sannan a dinga gaya mata ƙabali da ba'adi ba, tun tasowar yarinya ya kamata a dinga koya mata yadda zata kula da kanta, da yanayin Rayuwar Aure"
Hakimi yai murmushi yace "eh to hakane, amma ai Nana tayi ƙarama da yawa, da wannan karatuttukan naki"
"Taɓɗijan, kai kake ganin tayi ƙanƙanta, ba tayi ƙanƙanta ba, ba dan karatun boko ba, ai da yanzu idan ba'ayi aurenta ba, ana nan ana shirin hakan, kuma karkayi mamaki suna tattaunawa a junansu, yaran zamani ka kallesu kawai, gara in horata da nawa karatun, da wanda za'a karanta mata a waje ta ɗauka"
Hakimi ya jinjina kai yace "hakane kam, naga zasu yi hutun makaranta, shiyasa nace ki tafi da Ita bikin nan, wallahi ina jin banƙin cikin rashin raɓata da jikokina basa yi"
"Ka dena damun kanka fa, ita uwar yaran nata halin kenan, yaranta baza suzo ƙauye ba, dan haka ka haƙura ka bar mata yaranta, shi shine ɗanmu kuma yans zuwa inda muke, meye na damuwa dan yaransa basa zuwa?, Baga Ummi nan Allah ya baka ba"
Ya ɗanyi shiru Yace "na tabatta da baban Ummi na raye ba yadda ze hana yaransa zuwa inda muke, kin sanni da ƙawa zucin yara, Allah be bani su da yawa ba, duk ya karɓe abunsa, ina ƙaunar yaran nan, irin son da nakewa mahaifinsu, haka nake sansu"
Inna tace "ni dai nace kayi haƙuri, ka maida komai ba komai ba, Ummin nan kawai in Allah ya bamu yawan rai, seka ga ta haysyyafa, ta cika mana gida da jikoki"
Hakimi ya jinjina kai Yace "wai, idan ba wani ikon Allah ba, ina ni ina ganin 'ya'yan Ummi, 'ya'yan jika fa?"
"Eh mana 'ya'yan jikan, ai abun na Allah ne, kai dai Allah ya baka tsawon kwana me amfani Saraki"
Yai murnushi, yana jin daɗin yadda matar tasa take masa addu'a, ko kuma yi masa kirari.
Inna na nan zaune tare da megari, seda ya kammala shan furarsa, ya kwanta sannan ta fito daga turakarsa, tana zuwa ɗaki ta tarar da mutuniyar tata, tana cin Abincin rana.
"Yawwa ta Nana, gaki nan fes dake se ƙamshi kike, haka ake son mace a ganki kullum cikin gyara, ga kayanki can na islamiyya an goge miki, idan kin gama seki shirya ki tafi Makaranta"
Nana tace 'to Hajiya Inna"
Shirye shirye suna ta nisa, na bikin Usman, Sadik ma yana ta nasa shirin, dan yana son ya gwangwaje da bikin nan, zasu yi shagali sosai shida friend's ɗinsa.
Yauma yaje school sedai har ya shiga aji be samu ganin abar ƙaunarsa ba, ana fitowa break ya tafi ajinsu Farhan, sedai ya tarar bata nan.
Cikin takunsa na isa ya shiga cikin ajin, ya kallesu Yace "ina Farhan?"
Lilly tace "Ana fita break ta fita, bamu san inda ta tafi ba"
Be kuma cewa komai ba ya fita, yana tunanin ina ta shiga haka? Tun jiya be sake ganinta ba.
Ita kuwa bayan wani aji taje tai zamanta, dan karma su haɗu Sir Nazir yai mata faɗa, koya kira babanta, sedai sam itama zuciyarta a takure take, tana son ganin Sadik ɗin nata.
Sadik yana zaune yayi shiru, Meenal ce ta zauna a kusa da shi, Tare da ɗan dukan cinyarsa tace "Babban yaro, what's wrong ne? Ka wani yi shiru"
Cikin damuwa ya ɗan lumshe idonsa ya buɗesu, sannan Yace "Farhan na nema na rasa, naje har ajinsu bata nan, kuma ita bata zo nan ba"
"Shine ka zauna kai wannan shirun haka? Lallai yarinyar nan ta kama zuciyarka fiye da yadda kake tunani"
Yai murmushi Yace "ke dai bari kawai, yarinyar ta musamman ce, komai nata abun burgewa ne, I can't do without her"
Meenal tace "Ranar daka bar makarantar fa?"
"Zan bita har gida mana"
"Hmm Sadik manya, banda abun so dai, banga me ka gani a jikin wannan Farhan ɗin ba, ita gata bata wani cika mace ba"
Sadik yai murnushi sannan Yace "Ni idona sun gane min abunda naku idon baya iya gani, ku kuke ganinta ƙarama, amma ni nasan me nake gani"
Yai maganar yana lumshe idanunsa.
Meenal ta kalleshi tace "Allah me iko, kaga ni dai dan Allah yi mana ordern Abinci, yunwa nake ji wallahi"
Sadik ya zaro wayarsa yana faɗin "bari inyi, kuma fa nima yunwar nan nakeji, amma banga zuciyata ba, ban sani ba itama taci ko bata ciba, ba zan iya ci ba"
"Can ta nannaɗe muku kai da ita, ni dai dan Allah yi mana"
Seda aka kunna jiniya, kowa ya koma aji, Sannan Farhan ta fito daga inda ta ɓuya zata koma aji, zuciyarta nata raya mata taje ajinsu Sadik ta ganshi, amma ta danne zuciyarta ta tafi ajinsu.
A bayan wani aji ta hango wani malami, yana kissing ɗin Tasleem ta ajinsu Sadik, nan da nan mamaki ya cikata jikinta ya ɗau rawa, abun ya bata mamaki sosai, Malami da kansa yake haka shi da ɗalibarsa, ta shiga ajinsu cike da tunanin abunda ta gani.
Ta zauna a gurin zamanta tana tunani, Lilly tace 'Farhan, ina kika shiga ne? Prince Sadik yazo nemanki fa'
Maimakon ta bata amsa se dai murmushi kawai da tayi Mata.
Koda aka tashi, cikin gaggawa Farhan ta ɗauki jakarta, dan ta gudu gida kafin Su haɗu da Sadik, sedai tana fita harabar makarantar tai karo dashi.
Mazewa tayi niyyar yi ta fece, aikuwa ya riƙo hannunta cikin hanzari ya kalleta Yace
"meye hakane Farhan? Kamar kina guduna ne 'yan kwanakin nan lafiya kuwa?"
Farhan ta ɗan haɗe rai cikin shagwaɓa tace "Nika cikani meye haka?"
Sakin hannuta yayi, tare da shan gabanta Yace "tun jiya fa nake nemanki ban ganki ba, ko laifi nayi miki ne?"
"Ni ba abunda kayi min, kawai ka dena bina".
"Wace irin magana ce wannan haka?"
"Ka dena bina ko zuwa inda nake kawai, Sir Nazir yace ya kuma ganinmu tare ze kira babana"
Nan da nan annurin Fuskar Sadik ya ɗauke, ya canza fuska jikinsa har rawa yake ya kalli Farhan Yace "dama shine dalilin da yasa kike guduna? Waye Nazir? Me akai akayi shi? Farhan wai so ƙaryane? Zaki fara wahal dani dan ina sonki? Ina ruwansa damu, meye nasa a cikin soyayyar mu, idan sonki yake ya fito Ya faɗa mana in bar masa ke, kuje kuyi dashi, nafi ƙarfin Wulaƙanci Farhan, karki sa zuciyata ta yanke hukuncin da zesa mu cikin dana sani nida ke".
Nan da nan ido ya dawo kansu, babban abinda bata so kenan, wannan saurin zuciyar da zafin rai na Sadik, gashi ta kasa Magana, ga idon mutane da yai yawa a kansu.
"Shikenan, tunda kin fifita decision ɗinsa aka abinda zukatanmu ke so, kije Nagode sosai da kika bari zuciyata tai zurfi a sonki, na sakankance kema kina sona, ashe nayi kuskure"
Tasleem dake gefe tace "shege Prince, akwai kalamai dole ya sace zuciyar yarinya ƙarama"
Ganin yadda ransa ya ɓaci sosai, yasa Farhan sake dirircewa, cikin muryarta me sanyi tace "Ss..Sadik. wallahi"
"Karki gayamin komai malama, kije na bar masa ke, ya kwaɗaki ya cinye"
Fuuuu yai gaba, bebi ta kan jakarsa daya baro a aji ba, ya nufi inda motarsu take ya haye.
Farhan kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu, dan a duniya bata son ɓatawa Sadik rai, dukda bata ta taɓa ɓata masa rai ba, amma taji ba daɗi yadda ransa ya ɓaci haka.
"That's good, na gaya miki muddin na kuma ganinki da yaron nan, sena gayawa mahaifinki, wannan yaron dai ba aurenki zeba, ze ɓata miki lokacine kawai da rayuwa".......
Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
RUƊIN ƘURUCIYA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Writer of
WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)
_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_
⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️
Page 3&4
Waiga wa Farhan tayi ta kalli Sir Nazir, dake tsaye yana mata Magana, ji tayi tamkar ta shaƙeshi, saboda shine silar da yasa ta janye wa Sadik, kuma ga abunda tai yasa ran Sadik ɗin ya ɓaci.
Abunda be taɓa zato ba, yaga Farhan ta galla masa harara, irin up anda down ɗin nan, tai gaba abunta, tsayawa yayi cak ya zuba mata ido harta ƙulewa ganinsa.
Sadik kam a ɗakinsa na BQ ya tsaya, yana zuwa ya cire belt ɗinsa yai jifa dashi, ya cire neck tie ɗin wuyansa na makaranta ya jefar, ya cire rigar itama yai jifa da ita, ya faɗa kan gadonsa yai ruf da ciki, zuciyarsa na wani irin zugi, dan gaba ɗaya idonsa ya rufe, wata irin muguwar tsanar Nazir yaji tana ratsa shi, gefe guda yana ganin laifin Farhan da ta biyewa Nazir ɗin.
Befi mintuna sha biyar da kwanciyar tasa ba, Yayansa Faruk ya shigo ɗakin Sadik, ya kalli Sadik yace "Kai, Lafiya kuwa? Meke damunka kalli yadda kayi watsi da kayan makarantar taka fa, koba lafiya ne?"
"Lafiya ta ƙalau" ya bawa Faruk amsa a taƙaice.
'ban yarda lafiyar ka ƙalau ba, kaga yadda idonka yayi ja kuwa?"
"Budurwata ce ta ɓatamin rai"
Zaro ido Faruk yayi Yace "What? Budurwa fa kace Sadik"
Sadik ya tashi zaune Yace "eh, ko ban kai inyi ba?"
"Ni na isa ince baka kai ba? Ka kai harka wuce ma Autan Mother, dama mates ɗinka ne suka zo, suna son ganin ka naga da alama ko gida basu je ba, dan jikinsu da uniform"
Sadik Yace "kace musu su shigo"
Faruk ya juya ze fita yana kallon Sadik, kamar yayi dariya wai ɗan wannan jaririn yaron ne yake da budurwa, harta kai ga ɓata rai, ko uwar me yake gaya mata oho?"
Nasir ne da Aminu Manyan abokan nasa suka shigo bedroom ɗin.
Nasir Yace "mazaaaaa, Yanzu ɓacin ran ne yasa ka tafi ka bar school bag ɗinka a school?"
Sadik ya ɗanyi tsaki Yace "ƙyale ni kawai, ni bata jaka nake ba, raina ya ɓaci sosai, na rasa me nayi wa wannan banzan coper ya sani a Gaba, se kace ni kaɗaine ɗalibi, ko kuma nika ɗaine nake soyayya a makarantar nan?, duk ya samana ido, har yana wa Farhan barazanar ze kira mahaifinta, ita kuma ta fara guduna, to idan ya kira babanta ma me zece masa? Meye laifin zuciyata dan ta kamu da son Farhan? Ni nafi zargin anya ba sonta yake ba shima?"
Aminu ne yai wata irin shewa Yace "Oh my God, gayen nan kana burgeni Wallahi, dole ka tafi da zuciyar that innocent beb, ka iya kalamai, manyan yara a school suna crushing akan ka, amma ka dage kace kai se Farhan, that little baby, gashi ka koya mata son ka"
"Bana tunanin Farhan na sona fa, bata taɓa gayamin tana sona ba fa"
Nasir Yace "ka gane,