Showing 222001 words to 225000 words out of 259198 words
Chapter 75 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
duk a in da ka ajiye ni zan zauna"
Abbas yace "Amma meyasa kika yanke wannan hukuncin haka? Makarantar ki fa?"
"Doctor ina da dalili, makaranta kuma na cigaba a gida ka sedai in ka dena sona"
"Ya ma za'ai in dena sonki, insha Allah zan yadda kika ce, zan turo magabatana insha Allah zanyi Magana da su"
"Angon Farhan" tai maganar da sigar tsokana.
"Na'am Amarayar Abbas" su kai murmushi, suka cigaba da taɗinsu yayin da ƙasan zuciyar ta cike yake da tausayin Sadik.
Abbas kam ya shiga taradaddin yadda ze sanar da Auren da yake son yi ga dangin mahaifinsa, dan ya san dole za suyi bincike akan Farhan, yana tunanin yadda wannan abu ze kasance.
Yaiwa Hajia magana, amma tace ba ruwanta ya tuntuɓi dangin mahaifinsa in sun nema masa shikenan.
Sadik ya kasa gajiyawa da zaryar gidansu Farhan zuwa makarantar su, amma ko sau ɗaya ta kasa ba shi damar yi mata Magana ko kare kansa.
Yau ma yana nan zaune a ƙofar gidan su Farhan, Abbas ya kawo Farhan a motarsa, kasancewar magariba ce ba ta ga Sadik ba, Abbas yai reverse ya koma ƙofar gidan Hajiyarsa, tana shirin shiga cikin gida, taji an janyo ta da ƙarfin gaske.
Turaren Sadik kawai ta shaƙa ta gane shine, wani irin huci yake kamar wani kumurci.
"Dalla meye haka?" Tai maganar a hasale.
"Farhan wai me kike son ki maida ni ne? Mahaukaci? Kullum cikin zaryar gidanku nake ki bani lokacinki kin ƙi, kullum sedai wannan ya ɗauke ki a mota wannan ya sauke?"
"Au ai idan hauka ne, kai baka daɗe a cikin sa ba, kwanan nan ka fara ni shekaru biyu na shafe a cikinsa, kuma ba zan taɓa saurararka ba Sadik, dan Allah ka rabu da ni"
"Ba zan rabu da ke ba, Wallahi kika kuma shiga motar wani duk abunda nai miki ke kika siya"
Tace "ikon Allah, saboda ubana ne kai?"
"Saboda ke mallakina ce, Wallahi na kuma ganinki da wani se na illata shi, kar wannan wawan ya kuma zuwa yace ze ɗauke ki a motarsa na gaya miki"
Fizge hannunta ta tai tace "ba ma ka da kunya Wallahi, kaifa Aure kaje kayi, se ka zo ka takurawa rayuwata, ka fita sabgata dan saura wata ɗaya a ɗauran Aure"
"A ɗaura miki Aure da Sadik ba"
"Allah ya kiyaye, ko hauka nake aka ɗauramin kai se na kwance na yar, mayaudari kawai" yana kallonta haka ta wuce cikin gida.
Sadik be taɓa zaton Farhan tana da irin wannan zuciyar ta kafiya da taurin kai ba, saboda shi sanyin ta kawai ya sani.
Haka nan ya wuce ya tafi gida, da yaje ya tarar tuni Nana tayi baccinta, yai wanka ya nemi guri ya kwanta ya rungume su ita da Sahal a jikinsa, wani irin tausayin su yana ratsa shi, da da ne se ta jira ya dawo ta bashi Abinci sannan su kwanta, amma yanzu har ta gaji da abunda yake yi.
Abbas yaje ya samu wan mahaifinsa da suke cewa Alhaji, ya sanar da shi yana son ƙara Aure, se da yai mita sosai da sosai, akan ƙare ƙaren Auren nan in ba dace a kai ba baya haifara da ɗa me ido.
Abbas yaita lallaɓa shi, da ƙyar ya amince sannan ya tambaye shi 'yar waye kuma a ina take?.
Abbas ya gaya masa, Alhaji yace "na gane mahaifin yarinyar, na san shi farin sani mutumin kirki ne, wata mu'amala ta taɓa haɗani da shi, zamuje insha Allah daga nan ai binciken da duk Yakamata"
Abbas yace "Alhaji ai ba se anyi wani bincike ba tun da kasan mahaifin ta, kuna kace mutumin kirki ne, itama ta na da kirki"
Alhaji yace "in baka da hankali mu muna da shi, ɗan yau ka haife shi ne baka haifi halinsa ba, dan haka zamuyi bincike tashi kaje" jikin Abbas yai sanyi ƙalau, haka ya baro gidan Alhaji, dan yasan muddin binciken su ya gano halin da Farhan ke ciki, bayan hana shi Aurenta se sun ci masa mutunci tsaf.
Abun mamaki Farhan ta ɗan saki ranta a kwanakin nan, bata yawan ƙunci da damuwa kamar baya da Sadik ya ɓacewa duniyar ta.
Sedai duk da haka yanzu ta ƙauracewa zaman gida, dan sosai take son t nesanta kanta da Sadik, in dai zata cigaba da ganinsa, to tabbas zata iya kasa Auren Abbas, kuma hakan tamkar ta saka alkhairi ne da sharri.
A samarinta ta saka Alhajin nan ya kuma kama mata ɗaki, a wani hotel ɗin, ta koma can abunta, Abbas ya kaɗa ya raya akan ta koma gida, fafur taƙi kuna taƙi gaya masa dalili, abun ya dame shi matuƙa, in dai zeje ze tarar da ita ita kaɗai, be taɓa kamata da wani a hotel ba, amma dai zaman hotel be dace da ɗiyar kirki ba, amma Farhan tai burus da shi, tai zamanta.
Amir ƙanin Farhan har mamakin wannan uban naci na Sadik yake yi, yana ganin kwata kwata ba shi da zuciya, musamman duba da yadda Farhan ɗin ke masa wulaƙanci.
Kamar yadda Alhaji ya alƙawartawa Abbas, sunje neman Auren Farhan, kuma har sun saka ranar da zasu kawo kuɗin Auren, sun nemawa Abbas izini, kuma an bashi.
Watanni uku Alhaji ya saka, dan a cewarsa baze biyewa Abbas ba, dan be ga abun gaggawa a lamarin ba.
Abba ya dinga murna tare da Addu'ar Allah ya tabbatar da wannan lamarin, kar ya watse kamar yadda aka dinga zuwa neman Aurenta abun na watsewa, saboda yanayin rayuwar da take yi.
Sam Farhan ta kasa murna da batun kawo kuɗin Auren, ba ta zumuɗi sam, ta rasa dalili, ƙasan zuciyar ta na ƙoƙarin gaya mata har yanzu tana son Sadik, amma ta dage ta cire wannan tunanin a ranta.
Yanzu ma ta fito daga wanka, ta na sanye da doguwar riga a jikinta, tana zaune tana duba litattafnata, dan haryanzu akwai son karatu a tare da ita, makaranta ce kawai ta fita daga ranta gaba ɗaya.
Turo ƙofar ɗakin a kai, ta zuba ido, dan ganin waye haka ya zo mata ba izini ba komai.
Seda ta buɗe baki dan mamaki, ya akai Sadik ya gano in da take.
Ya ɗan tsura mata ido sannan yace "kina mamakin yadda a kai nasan in da kike ko?"
Haɗe rai tai tace "kaga kar ka zo ka samun ciwon kai, ka tafi ka bani guri"
Bece mata komai ba, ya nufi kan dressing mirror ɗin da ke ɗakin, ya kwaso magungunan da ke kai ya zuba a aljihunsa, ai da sauri ta miƙe ta nufo shi, cikin haɗe rai tace "ka ajiyemin kayana malam"
"Na ƙarfi ne ki ƙwata" yai maganar shima ransa a haɗe.
Shiru tai tana huci tana kallonsa.
Cikin tausasa lafazi Sadik yace "Farhan meyasa baki da tausayi ne? Ko iya sintirin da nake miki, ya isa ki sassauta min ki kwantar da hankalinki ki saurareni, nasan na miki laifi amma ki sani da bana sonki, ds Wallahi ba zan dawo gareki ba, haryanzu ina sonki Farhan, dan Allah ki saurareni"
"Kana sona da kenan, amma banda yanzu"
Ya ƙarasa gabanta, ya kamo hannayenta yana kallonta yace "Farhan dan Allah ki sassauta min idan ba so kike in rasa raina ba"
Kawai ta fashe da kuka tace "wai ya kake son in yi ne? Me kake nema a gurina, na ɗora rai a kanka amma ka yaudareni, a haukana na sakankance zaka dawo ka Aureni, a lokacin da nake tsaka da neman ɗauki, soyayarka na barazana ga rayuwata, amma ka yanke alƙa dani ba tare da ka sanar dani dalili ba, haka na haƙura da son yiwa iyayena biyayya in auri wanda ba na so, soyayyarka ta hanani sukuni da nustuwa, na fara neman maganin da ze mantar da ni kai, wanda iyayena suka zaɓamin ya bi ya ɓatamin suna yana cewa ni mutuniyar banza ce, ko da yake hakane,. Lokacin soyayyarka ta rufemin ido, ina iya sakin jiki kai min koma menene saboda son da nake maka, aka zo aka fasa Aurena ranar ɗaurin Aure, ya cigaba da bina da sharri kala kala a gari.
Katsam na tsinci labarin kayi Aure Sadik, bayan duk alƙawarurrukan da kai min, kai Aure ka barni, ba amo ba labarinka, ta yaya ba zan shaye shaye ba, ka koyamin abubuwa masu wuyar mancewa da ƙuruciyata, ba abunda nake kewa, banda tausayawarka da daɗaɗan kalamanka na yaudara, na saba da kwanciya a jikinka, ƙamshinka da barkwancinka lokaci ɗaya ka yanke wannan alaƙa da ka gina, sannan duk a garin in samu mafita miyagun abokanka suka min fyade suka lalata min rayuwa ta.
Duk wanda ya zo neman Aurena, se Sunusi ya ɓata, Mubarak babba bayan cin zarafina ya kirani da ƙasƙantacciya mara amfani saboda bamu da kuɗi, shiyasa na yadda in nemi kuɗi in rama abunda yai min.
Sadik me yai saura da kake da shi wanda zaka gayamin menene?" Tai maganar cikin ƙaraji.
Lumshe ido yai, yana jin yadda magananunta suke tasiri a cikin zuciyar sa.
A hankali yace "ban san da wani suna ya dace in kira kaina ba, amma duk sunan da kika kirani, mayaudari maƙaryaci duk na cancanci hakan.
Farhan na so ki tun ban san menene son ba ma, kuma na shirya yadda zan rayu da ke, amma har kullum shi bawa ba shi yake da kansa ba, Allah ke tsara masa komai nasa.
Farhan kakanni na ne suka Auramin ƙanwata Nana a cewarsu zuwana ƙasar waje karatu nikaɗai hatsari ne, na sha gayawa iyayena ina son Aure, amma suka dinga dankwafeni, suna min kallon yaro, hakan ya bawa kakannina damar Auramin Nana, ba tare da sun tuntuɓi ko ina da wadda nake so ba.
Ban sani ba ko hakacewa nai Farhan, amma lokaci ɗaya da ke, da makarantar mu, da abokaina Wallahi kamar an min formatting na manta komai, haryanzu na kasa gano dalilin yadda a kai haka ta faru da ni, na manta da komai a shekarun nan ko da wasa, ban iya tuna kowa da ya shafi makaranta da rayuwar da nai a cikin ta ba".
Ture shi tai tace "ai dole ka manta mana, tunda kai Aure, ka barni a wahala"
Matsawa ya sake yi daf da ita yace "idan ma hakane, mahimmancinki da soyayyar ki a gurina yasa na sake dawowa rayuwar ki a karo na biyu, in nemi afuwarki kuma in sake neman soyayarki, duk da nasan soyayyata haryanzu tana nan a tare da ke"
"Kar ka yaudari kan ka malam" tai maganar ranta a haɗe.
"Hmm, ba yaudarar kai bane ba Farhan, sannan zan nunawa Babba ke mace ce me tsabar daraja da kima, duk wanda suka ci zarafinki sena ɗau mataki a kansa, kuma ni a haka nake sonki Farhan, zan Aureki ina sonki Wallahi"
"Se kuma kayi, dan an sa min ranar Aure, saura watanni uku, kuma ko ba'a sa ba ba zan Aureka ba".
Be damu ba yace "zan zo neman Aurenki, ba ki da mijin da ya wuce Sadik, ki rubuta ki ajiye wannan, and magana ta gaba, ba zaki min asara ba, shaye shaye yana kawo illa ga ƙwayoyin haihuwa, ban sani ba ko da yarana a cikin ki, dan haka na hana shan wani abu daga yanzu, dama saboda ni kike sha, to gani na dawo.
Na dena lallaɓa ki ko kina so, ko ba kya so zan Aureki Farhan dan tabbatar wa da Duniya soyayyar mu ba RUƊIN ƘURUCIYA bace, saboda so ba ruwansa da ƙuruciya".
Mamakin ƙarfin hali irin na Sadik take yi, harya juya ze fita ya dawo ya kalleta yace "kar kuma in sake ganinki tare da wannan farin mutumin, da koma waye suke zuwa gurinki, ki gaya musu ke matar Aure ce, matar Sadik ce idan suka cigaba da bibiyarki kuma, Wallahi se na yiwa mutum illa, kuma ki tattaro kayanki ki bar Hotel ɗin nan ba zan miki dole ki bar nan yanzu ba, amma Wallahi na kuma ganinki a hotel, kafin in gaya miki matakin da zan ɗauka bari in tuna baya, let's remember our first kiss". Kan tai Magana ya rungumota jikinsa, ya fara kissing ɗinta so deeply.
Lumshe ido tai, tabbas ta tuna first kiss ɗinsu, a gurin birthday ɗinta, she so much Miss him, ji take tamkar ta rungume shi, itama ta mayar masa, amma tuna yadda ya gujeta yai Aure har da ɗa, ya sa ta fara mutsu mutsu za ta ƙwace, ba ta tsinke da lamarin Sadik ba se da taji ya zuge rigarta, kokawa suka shiga yi, ta saka kuka tana girgiza masa kai tace "ba ka da hankali ne me kake yi haka?"
Ya cire rigar da ga ita se underwears, ta rurrufe jikinta, take hawaye ya wanke mata fuska, be damu da abunda yai ba, ya sa hannun sa ya fizge nata daga kare jikinta da tai Sannan ya kalleta yace "ko da tsiya, ko da tsiya tsiya in dai ina numfashi ke tawa ce, ba zan cigaba da lallaɓaki kina wahal da ruhi na da gangar jikina ba, ke har ma da matata da ɗana ba, ba jikinki nake so ba, zuciyar ki nake so, da jikinki nake so ba zan Aureki ba bayan wasu sun riga sun..... Se kuma ya datse zancen ya ɗora da
"Wallahi, Wallahi idan na kuma ganinki a hotel, i will sleep with you there, tunda abunda kike so kenan, ki ke zaman banza a hotel kina tara ƙarti"
Sosai Sadik ya bata tsoro, jikinta se rawa yake yi, a ranta tace 'wai ba jikina kake so ba, Sadik na sanka kamar yunwar cikina" amma a zahiri ko motsi ta kasa se hawaye.
Se kuma ya lumshe ido yace "kin ƙara girma da kyau sosai princess, am sorry na saki kuka, ban sanki da gardama ba, amma ƙwaya duk ta canza min ke, amma daga yau insha Allah se kin dena sha, tunda gani na dawo, sa rigarki muje ki ci Abinci in kai ki gida".
Ta ɓoye tsoronta ta dake tace "ka fita ka barmin ɗaki, kace ba jikina kake so ba amma kai min tsirara, ka fita ka bani guri"
Murmushi yai be kuma cewa komai ba ya fice.
Yau wani irin nishaɗi Sadik yake yi, sedai yana tunkarar gida gabansa ya shiga faɗuwa, saboda be san ta ina ze ɓullowa lamarin a gida ba.
Tunanin yadda Sadik ze sake tunkarar iyayensa da batun yana son sake ƙara Aure kuma ya baibaiye shi, dan ya san abune me wahalar gaske su amince, na farin ma da ya akayi balle ya sake zo musu da wannan sabuwar maganar.
Nan fa tunani ya sake komawa Sadik sabo.
Yau Abba ya zo hutun ƙarshen wata da yake zuwa, sedai shima ya lura da canjin yanayin Sadik, sedai be ɗau abun da mahimmanci ba, saboda yasan halin Sadik ɗin wasu lokutan ba gane kansa ake yi ba.
Sedai abun ya ɗan dameshi, ganin ita kanta Nana duk tana cikin damuwa, wadda ita kanta ba ta san tana da damuwar ba.
Abba ne ya kalli Nana, da ke zaune a babban falo, gefenta Sahal yana bacci, ya zauna a ɗaya daga kujerun falon ya kalleta yace "Nana, meke faruwa ne daga ke har Sadik gaba ɗaya na kasa gane muku, duk kunyi wani iri ko akwai matsala ne?"
Nana ta girgiza kai tace "A'a"
Abba yace "A'a, kar ki ɓoyemin komai, baki san fuskar ki ta nuna bane?"
Kawai ta fashe da kuka, Abba ya barta tayi tayi, sannan yace "ina jinki"
Mother da tazo wucewa tace "lafiya take kuka?"
Abba yace "Abunda nake son ji kenan"
Nana ta share hawayen fuskarta tace "Abba, ni na kasa gane kansa gaba ɗaya, na tambaye shi idan wani laifin nayi masa yace A'a, gaba ɗaya ya dena kula da mu kamar da, har gara Sahal yana ɗaukar sa, amma ba ya wuni a gida, wataran se dare munyi bacci yake dawowa, na tambaye shi menene yaƙi gayamin, ko Abinci ba kullum yake ci ba"
Mother tace "Aikam nima nayi iya yina, akan ya gayamin meke damunsa amma fafur yace bakomai, ni kaina na lura da hakan a tare da shi, duk ya canza"
Abba yace "ki dena kuka, zan zauna da shi inji ta bakinsa, ki dena kuka kinji yarinyar kirki, dama haka auren yake ai"
Yaita rarrashinta yana kwantar mata da hankali.
Se da aka kwana biyu da maganar da su kai da Nana, Sadik yaje gaida Abba a sashinsa, Abba ya dinga jansa da hira, daga baya yace "kai ya akayi ne gaba ɗaya ka canza fa, gayamin meke damunka ne?"
Sadik ya ɗan sosa kai yace "bakomai Abba".
"A'a da komai mana, yanayinka ya nuna, don't forget that we are friends, so you can share your problems with me, to see if I can help"
Sadik ya ɗanyi shiru yana nazari, tabbas wannan shine right time, da Yakamata yaiwa Abba Magana.
Ya kalli Abba sannan ya ɗan gyara zama yace "Abba, ina son in ƙara Aure ne!!!.
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680
Abba ba tare da ya kalli Sadik ba yace "You must be crazy"
Sadik ya gyara zamansa yace "Abba am serious, wallahi da gaske nake dan Allah ka bani goyon baya, ina son ƙara Auren nan"
"Shut up!" Abba yai masa tsawa.
"Kwata kwata yaushe kai Auren, ko ka manta da ya kai Auren fari, kawai seka zo kace zaka ƙara Aure, saboda baka da hankali"
Sadik ya marairaice yace "dan Allah Abba ka fahimce ni"
"Ba zan taɓa fahimtar ka ba, wai tsaya ita wadda kake tare da itan, me ka rasa a gurinta ta ina ta gaza gayamin ina jinka"
"Abba Wallahi ba abunda Nana tai min, tayi iya ƙoƙarinta a kaina, idan nace zan butulce mata ko in cutar da ita Allah baze barni ba, amma Abba akwai dalilin da yasa nak......
"Kai dalla rufen baki, tashi ka bani guri"
Kamar Sadik ze kuka yace "Abba dan Allah ka saurareni"
"Ka fita ka ban guri nace" Abba yai maganar cikin tsawa, haka Sadik ya tashi ya fita gwiwa a sanyaye.
Nan abubuwa suka sake sha masa kai, ya rasa mema Yakamata yayi.
Haka nan Farhan ta tsinci kanta da tattara kayanta, domin barin Hotel ɗin nan, dan tana shakkar Sadinya aikata abunda yace, tunda har yai rantsuwa, to ze iya aikatawa.
Ta tsinci kanta cikin wani nishaɗi tun bayan sumbatar da Sadik yai mata.
Mother ce ta shigo kawowa Abba Abinci, tana mitar yadda ta sa aka kira me gyaran solar amma be zo ba, se inji aka kunna, sam taga hankalin Abba ba ya kanta.
"Yallaɓai lafiya kuwa?"
Abba ya girgiza kai yace "kin san me ɗanki ya zo min da shi?"
Mother tace "wanne daga cikin 'ya 'yan?"
"Ɗan Autan ki"
"A'a seka faɗa"
Abba