Showing 252001 words to 255000 words out of 259198 words

Chapter 85 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

yake damunsa, ya sha magani amma abu kamar turi, baya jin magani, yana kwance a ɗaki ya ga wata inuwa tana shawagi a kansa, ya waiwaya amma be ga komai ba, ya yunƙura ya tashi yana waige waige amma ba kowa, ya koma ya kwanta, amma ya kuma ganin inuwar yana ɗaga kai, yaga Farhan a kansa hannunta riƙe da wata bulala, jikinta duk a ƙoƙƙone.

"Ke Farhan meye haka? Meye ya ƙonaki haka?" Ba tai Magana ba ta shiga zuba masa bulalar hannunta, nan ya dinga kurma ihu kamar wanda ake cirewa ido.

Haladu ne ya shigo a gigice yana faɗin "lafiya, menene ya faru?"

Sunusi yace "ita ce, dukana take"

"Ita wa?x

"Farhan ce take dukana da bulala"

Haladu yace "wace irin Farhan kuma?"

Sunusi yace "Wallahi yanzun nan ta bar ɗakin nan" yai maganar cikin ƙaraji.

Da ƙyar Haladu yai tai masa Addu'a, da tunanin ko gamo Sunusi yai.




Duk yadda Sadik yake tunanin lamrin ya wuce tunainsa, dan sosai Farhan ke gudunsa, take nuna masa ba ta sonsa, ita Abbas take so amma ya Aureta, se fama yake da ita, amma babu alamar zata sassauta masa, abun ya bawa Sadik mamaki sosai, Nana kuma tai watsi da su, kamar ba suyi existing ba, idan ya zo in da take shikenan, in be zo ba ba ta damu ba, makarantar ta take tafiya, in aka taso ta tafi gidan Mother ba zata dawo ba se dare.



Ranar da Sadik ze bar ɗakin Farhan, ya ɗaukesu zuwa gidansu, dan su gaida Mother, Nana tana zuwa ta shige bayan mota, ba tare da ta saurare su ba, Farhan ta miƙ hannu ta ɗau Sahal, amma ya dinga ihu ya ƙi yarda, Saboda akwai shi da ƙyuya.

Farhan tai mamakin ganin Nana ta kame a bayan mota, ta basar da su, dan ta Farhan ba ta son Irin wannan zaman da suke da Nana, duk da ita ma Farhan ba me son mutane bace, amma yadda suk zaman kowa da halinsa, ba ta jin daɗin hakan sam.


Ko da suka je gida, suna zuwa sabo direba yai murmushi yana kallon Farhan yace "Allah yayi, Amaryar Sadik Allah ya amsa wannan soyayya"

Farhan ta sunkuyar da kai cikin jin kunya, tana gaida Sabo.

A falo suka haɗu da Abba yana shirin fita, Nana ce ta fara gaisheshi ya amsa cike da kulawa yana cewa ina abokin nasa wato Sahal.

Sega Sadik sun shigo tare da Farhan da Sahal, suka gaida Abba ya amsa ba yabo ba fallasa, yai musu sallama saboda yana sauri ze shiga taro, sedai Abba ya dinga tantamar abunda aka faɗa akan Farhan, saboda a nutse take sosai ba alamar rashin ji a tare da ita.

Mother ce ta fito, ba tare da tasan su Sadik sun zo ba, Nana ta fara gani tsce "ke kuma daga ina haka?" Tana rufe baki ta ga Sadik tare da Farhan.

Turus tai tana bin Farhan da kallo, cikin ladabi Farhan ta gaida Mother, guntun tsaki Mother tai ta cigaba da maganarta.

Se Nana taji ba taji daɗi ba, saboda ta san raɗaɗin irin wannan abun, Sadik yace "Mother ga Farhan na kawo miki"

Mother tace "naganta ai, se a kai yaya?"

"Ai naga ta gaisheki ba ki amsa ba".

"To in amsa ince mata me? Ba dai Aurene ka dage ka je ka Aureta ba, to ga ka nan gata ai, dama na gaya maka ba ruwana da Aurenka ba hannuna a cikin wannan Auren, dan haka kar ka ƙara kawomin ita wai ka kawota gurina bana buƙata"

Dam dam! Gaban Farhan ya faɗi, kenan iyayen Sadik ba sa so amma ya Aureta.

Nana tace "Mother, ai aikin gama ya gama, abu ka ya faru ake ƙinsa, amma ya riga ya faru dan Allah kiyi haƙuri komai ya wu....

"Dalla rufemin baki mara zuciya kawai, ke har abada Mijinki baya laifi komai yai daidai ne, amma hakan be hana yai miki kishiya ba ai, sakarya" Nana ta ja bakinta ta tsuke, Farhan kuwa se murza yatsunta take, amma hawaye ne ya cika mata ido fal, Yanzu da Abbas ta Aura da shikenan ba ruwanta da wannan tashin hankali.



Haka suka wuni a gidan nan, babu daɗi sam dan Farhan tai dana sanin zuwa gidan nan, dan ta sha miyagun maganganu a gurin Mother, maganganu na muzantawa, ba tare da la'akari da koma menene ɗanta ne sila ba.



Se bayan sallar isha'i sannan suka koma gida, ko Abincin gidan Mother Farhan ba ta ci ba, ita kanta Nana sam ba ta ji daɗin abunda Mother taiwa Farhan ba sam, duk da ba shiga shirgin Farhan take ba, amma Koba komai Allah ya riga ya ƙaddara Auren be kamata tai haka ba.


Suna zuwa gidan Farhan ta wuce ɗakinta, ta dinga kuka kamar ranta ze fita, saboda wani irin ɗaci da zuciyarta ke mata.

Sadik ya durƙusa a gabanta cikin sigar rarrashi yace "Farhan, nasan abunda mahaiiyata tai miki ba daɗi, amma dan Allah kiyi haƙuri komai ze wuce, watarana se labari".

"Yanzu dan Allah kasan mahaifiyarka ba ta sona amma ka Aureni? Ba ka kyauta min ba ba kai min adalci ba, da ka barni na Auri wani daban da shikenan da duk ba haka ba, amma kana tunanin akwai lokacin da ze zo Mahaifiyarka ta canza ra'ayinta a kaina? Baka kyauta min ba tunda ka shigo rayuwata nake haɗuwa da ƙaddara kala kala, ni haɗuwata da kai ba ta haifarmin komai ba se tsananin nadama da gurɓacewar rayuwa, ina dana sanin haɗuwa da kai, bana son ko ganinka Sadik".

"Farhan, kar ɓacin rai ya sa kiyi kuskure, ina son in gyara laifukana a gareki"

"Ba wani abu da ze gyaru, ka tafi ka bai guri kawai, ni ko san ganinka bana yi, ka cutar dani Sadik da ba saka ba da duk wannan abubuwan ba su faru da ni ba" a sanyaye jiki ba ƙwari, Sadik ya bar ɗakin gaba ɗaya ya rasa abunyi.

Ya daidaita nutsuwarsa Sannan ya nufi ɗakin Nana.


Ya tarar tai shirin bacci, tana shan madara a kofi, ta kalleshi tace "ya dai ya na ganka?" Hararta yai yace "saboda kin sallamani har kin manta yau zan dawo gurinki"

"Aini ban zaci zaka dawo ba, ka koma na ƙara maka wata ɗaya kyauta"


Banza yaiwa Nana,yaje gaban mirror ya cire agogon hannunsa ya wuce toilet, ko da ya fito Nana har ta kwanta, bayanta shima yabi ya kwanta, ya rungumeta ta baya, gaba ɗaya ransa a cunkushe.


Nana tai ajiyar zuciya tace "kamar wani abu na damunka?"

"To Besty ya zanyi? Kowa ya ƙi fuskanta ta, duk yadda nake da Mother ta juyamin baya, kun ƙi yadda Auren nan nawa ƙaddara ce, rabona da ke a shimfiɗa ta watanni uku da wani abu, amma yau in dawo gareki kice wai kin ban wata ɗaya, ya kuke so inyi ne? Da wace kalma zan miki amfani wadda zata tabattar miki da ina sonki?" Ya ƙarasa Maganar cikin tsantsar damuwa.

Nana ta juyo tare da fuskantar Sadik sosai tace "Besty ya zanyi, ka auri wadda kake so dole in ja jikina, kar in fiye maka shishshigi, amma ni kaina bana son abunda Mother tai, amma nasan lokaci ne, tunda Mother ta ƙaunace ni, to tabbas ita ma watarana zata so ta".

"To amma meyasa kuke zama kamar na gaba, ina kallo fa wataran se tai miki Magana ki shareta, bana jin daɗi, kin san in ita ce ba zan taɓa bari ta wulaƙanta ki ba, ke meyasa kike mata haka?"

"Saboda ina so da kishin mijina, ins ganin ta rage min wani jin daɗi na rayuwata, amma ina tausar zuciyata za dena insha Allah, ba zan sake ba hakan yai maka?"

Sadik ya janye jikinsa daga nata yace "Ni rabu dani, idan na mutu ai duk kun huta"

Ta rungumo shi tace "haba Besty, am sorry ba zamu so ka mutu ka barmu ba, dan Allah kayi haƙuri Bestyna, i miss You sosai"

Yace "serious?"

Ta jinjina masa kai alamar eh, murmushi yai ya sake rungumeta a jikinsa, daga nan suka sha soyayyarsu, hakan ya ragewa Sadik damuwar da yake ciki, dan da gaske yai kewarta.





Farhan kuwa seda ta tabattar yau ba tare zasu kwana da Sadik ba, sannan ta shiga hankalinta, wani irin kishi ya dinga damunta, tare da kewar Sadik ɗin.



Da safe yau Nana tai girki, Sadik ya ƙi zuwa su gaisa da Farhan, ya shareta ya cigaba al'amuransa.
Gaba ɗaya se abun ya dameta, ranar da ze dawo gurinta da safe, ya shigo ɗakinta amma ta ganshi da travelling bag, kallonsa tai saroro tace "ya naga haka?"

"Zan tafi Zariya ne"

"Zariya kuma, me za kai a Zariya?"

Sadik yace "makaranta zan koma, tun kan ai bikinmu nake ƙoƙarin komawa can, Alhamdilillah na samu zan tafi"

Kamar za tai kuka tace "amma meyasa ba ka gayamin ba?"

"Ni da ba kya so, idan na tafi kika dena ganina maybe ki dena jin haushina" be jira me za tace ba, yai waje abunsa, binsa tai da kallo ta kasa furta komai. Can kuma seta bi bayansa da sauri, amma tana leƙawa har ya kunna mota, Nana tana tsaye da Sahal tana ɗaga masa hannu.

Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, gaba ɗaya taji abubuwan da tai ba ta kyautawa Sadik ba sam, shiru tai ta rasa abunda yake mata daɗi, gashi sam ba ta ƙawaye ko wata wadda zasu tattauna akan matsalar tare.




Nana na falo tana son ta ci Abinci, amma Sahal ya hanata, se ƙoƙarin zubar da Abincin yake, yana kai hannu cikin kwanon, Farhan ta fito daga ɗakinta, ta kalli Nana tace "barka da rana"

Nana tace "yawwa barka" daga haka ta cigaba da kokawa da Sahal.

Can Nana tace "Ya salam da wannan Yaron, kai ga babarka can tafi ka bani guri" tai maganar tana nuna masa Farhan, murmushi Farhan tai tana miƙawa Sahal hannu.

Nana tace "maza jeka, ta kai ka gurin Besty, ko gurin Mother maza tafi,yaron tun da ya fara rarrafe ya hana mutane sukuni".

Farhan ta ƙaraso ta ɗauki Sahal, sedai a wannan karon be mata kuka ba, se leƙa fuskarta da yake yi, a taƙaice dai a ranar saboda Sahal su Nana suka ɗanyi magana ranar.

Ranar da Nana zata Makaranta, Farhan tace ta bar mata Sahal.

Nana tace "a'a fa, ze wahalar da ke baya zama guri ɗaya, ga kukan banza da ci, Mother ce take iya masa"

Farhan tace "bakomai zan iya kula da shi" Nana ta tafi makaranta ta bar mata Sahal.


Nana taje ta dawo, ta tarar da Sahal tsaf da shi.



Farhan duk kiran da za taiwa Sadik baya ɗauka, Haka zalika in tai masa message baya replying, gaba ɗaya abun duniya ya dameta.

Ranar da ta cika wata ɗaya cif,ta shirya taje gida, ta turawa Sadik saƙon zata gida, wuni tai a gida, Umma taji daɗin ganin Farhan, tai kyau tai ƙalau da ita, abun mamaki Umman Farhan har da sakin jiki suyi hira sosai.

Se da Farhan tai sallar magariba Sannan ta shirya tafiya gida, ta kusa ƙarshen layinsu ta haɗu da Haladu, Kamar ta wuce amma Haladu yai mata magana, ta tsaya suka gaisa da Haladu, Haladu yace "Farhan, ina miki murnar Aure da ki kai, naji daɗi da Allah yasa shi Sadik dai shi ya Aureki, amma bari in gaya miki wani abu da baki sani ba, Sunusi shine yai miki Asiri da shi Sadik ɗin, ya manta da ke a rayuwarsa gaba ɗaya da duk wani abu da ya shafeki, kuma ya haɗaku da wata aljana wadda ta dinga ingizaki kina abunda kike, So yai ki zama mutuniyar banza abar ƙyama a cikin mutane, amma Aljanar ta gaza tasiri sosai a tare da ke, se akan Sadik shima daga baya da ya ke addu'a, matarsa ta sa yana Addu'a shine Aljanar ta dinga ƙonewa, wannan aljana ce ta dinga assasa miki ɓacin rai,ke kuma seki kasa jurewa se kinyi shaye shaye, yanzu haka duk ta ƙoƙƙone, ta fara zuwar wa Sunusi a siffarki tana nema ta haukata shi, duk da nima na bada gudummawar ɓata Asirin da yai miki, dan Allah Farhan ki yafe masa, ya cutar da ke iya cutarwa, musamman mijinki da be ji ba be gani ba, Amma dan Allah kiyi haƙuri ki yafe masa"

Kan ya gama gayamata, jikin Farhan tuni ya hau rawa cikin kuka tace "in yafe masa kace? Bakomai ni ba zan masa Allah ya isa ba, na bar shi da Allah"

Jikinta na tsuma tai gaba, tana tunanin yadda ta dinga yiwa Sadik wulaƙanci, duk son da ɗokinta da yake, se da ta tunzura shi ya watsar da ita.


Ta koma gida kamar korarriya, ta dinga kuka, kamar zararriya tana Allah sarki Prince ɗina.

Ko Abinci ba ta iya ci ba ranar, sallar isha'i kawai tai, ta saka kayan bacci tana shirin kwanciya, taji kamar motsi a ɗaya ɗakin nata, fita tai ta leƙa taga meye yake motsi. Sadik ta hango kwance, sanye da kayan baccinsa yana waya, ya dawo a ɗakinta ya sauka amma be nemeta ba.

Da sauri ta shiga ɗakin, tana zuwa ta maƙalƙale shi ta fashe da kuka, mamakine ya kama Sadik, ya ajiye wayar yace "ya dai?"

Ƙanƙame shi ta sake yi tana kuka tace "Am sorry my Prince, dan Allah ka yafemin, kayi haƙuri Please"

"Me ki kai min kike bani haƙuri"

"Komai ma na maka, dan Allah kayi haƙuri ka yafemin, ina sonka Prince, i still love you, am just pretending to revenge what you did to me, but am sorry I love you"

Sadik yai murmushi yace "yau kuma soyayyar Sadik aka tuna? An dena fushin da ni ai kince ba kya son ganina" cikin hanzari ta haɗe bakinsa da nata ta zubar da hawaye, ƙanƙameta shima yai, wasu hawaye na zuba daga idonsa ba tare da ya san dalilin yin su ba.

(🫣🫣🫣 Naga abun ya motsa, yau RUƊIN ƘURUCIYA suke ji, dan haka se anjima 🚶🚶)
NA kuɗi ne ₦300 kacal.




Sadik ya zame bakinsa, ya kalli Farhan yace "My love wai ya akayi ne? Duk kamar a birkice kike"

"Da Allah ni dai kayi haƙuri, Wallahi haryanzu ina sonka, ɓacin rai ne duk ya sa na maka abunda nai maka" tai maganar tana hawaye tana sharewa Sadik hawayen fuskarsa.

"Do you mean, you still love me?"

"Yes i do My Prince"

Murmushi yai yana sauke ajiyar zuciya yace "Alhamdilillah, ban taɓa zaton abubuwa za su da sauƙi haka ba, duk da ƙalubalen da muka fuskanta a rayuwa, so ya tabbatar wa da Duniya cewar,ba ruwansa da tsoho ko yaro, kowama kamawa yake yi"

Tace "meyasa ka dawo baka gayamin ba?"

Yace "ai kince ba kya son ganina, shiyasa bana son in kuma Abunda zan ɓata miki rai"

"To kaci Abinci?"

"Naci, Besty ta bani Abinci ya kika baro su Umma"

"Duk suna Lafiya ƙalau, nai missing ɗinka tun da ka tafi nake tunaninka"

Murmushi yai yace "Anya kinyi missing ɗina Kamar yadda nai missing ɗinki?"

"Nayi mana" tai maganar cikin sigar shagwaɓa.

Da haka dai yau an sha Soyayya me tsayawa a zuciya, soyayya wadda aka sha gwagwarmaya kafin a cinma nasara a cikinta.

Washegari Nana har ta gama shirin ta ba su fito ba, dan haka ta shirya Sahal, ta kaiwa Mother shi daga nan ta tafi makaranta.

Se wajen sha ɗaya na safe, sannan Farhan ta tashi ta sama musu abunda za su karya, bayan sun karya ɗinma tana maƙale a jikin Sadik, duk da haryanzu tana jin nauyinsa, wannan kunyar ta ta tana nan.

Sadik ya shafa bayanta yace "Wai ni meye sirrin wannan soyayya da tattalin da ake tai min ne? Gaskiya naji daɗi sosai, kuma ina sae baki haƙuri akan abubuwan da suka faru".


Farhan tace "ni yakamata in baka haƙuri, saboda baka da laifi, nima ɗin dan nai fushi ne cikin rashin sani, amma na sha wahala sosai da sosai, na rasaka a lokacin da nake tsananin buƙatar ka, ka ɓacewa duniyata se jin labari nai a gari wai kayi Aure, ga Auren dole da akai shirin yi min a gida, Auren ya zo be yuwu ba, ya dinga bi yana ɓatamin suna a unguwa, ga damuwa da tsananin soyayyar ka suka ƙi barina, hakan yasa na kasa jurewa, sheɗan yai tasiri a kaina, na kasa tawakalli na fara shaye shaye, katsam abokanka kuma sukai min fyaɗe, gaba ɗaya duniyar tai min zafi, na dinga attempting in kashe kaina in huta".

Sadik ya nisa yace "Farhan, ban san ya akai kika bar tunanin tsawon lokaci ba, ko da wasa ban taɓa zaton zaki iya barin raina ba, ko da na minti ɗaya bane, haryanzu na kasa gano ya akai abubuwa suka faru da ni a haka?"

"Prince ba laifinka bane" Nan ta bayyna masa abubuwan da Haldu ya gaya mata jiya.

Jikin Sadik ya ɗau rawa, idanunsa su kai ja yace "Me mu kai masa ze mana haka? Akan wani dalilin? Kalli yadda yai silar tagayyara rayuwaki ya sa ki wahala, to Wallahi ba zan bar shi ba, sena ɗau mataki"

Farhan tace "saboda me? Bayan Allah yai mana komai, duk da sharrinsa da yadda mutane suka dinga cewa Ruɗin ƙuriciya ce, yanzu dai na ga shi Allah ya ƙaddara munyi Aure ba, ka manta da shi kawai dan Allah, mu fuskanci rayuwar mu, Se dai abunda ya faru baze gogu daga rayuwata ba, haryanzu ina jin kamar ban wa Abbas adalci ba, a lokacin da kowa yake ƙyamata, a lokacin ya dinga bina yana lallaɓani yaga ya rabani da shaye shaye da bin Hotel, haryanzu ina baƙin cikin baƙin fentin da naiwa kaina, sedai a shekaruna ba kowa ze iya ɗaukar ƙaddarar da ta riskeni ba, ga fyaɗe da Babbab yai min shi da abokansa"

Sadik yace "Ƙarya yake,ya faɗa ne da ya cuzguna min, ba abunda sukai miki".

Tace "ya akai ka sani, bayan se da suka bani ƙwaya, suka bugar da ni ban tashi farkawa ba, se washegari".

Sadik yace "baki ji banbanci ba, da waccan Ranar da Ranar da aka kawoki gidana ba, ke a tunaninki da sun miki fyaɗe su huɗu zaki iya tashi ma? Ko kin manta yadda kika dinga...

Be ƙarasa ba ta toshe masa baki, hawaye na bin fuskarta a lokaci guda ga murmushi tace "tabbas, ranar ni banji komai ba, akwai banbanci amma dan Allah da gaske kake, ba suyi min komai ba?"

Sadik yace "ba abunda su kai miki, ai naje na samu Mubarak ɗin, har mashayar su, nai masa duka, sedai hakan be min ba, na koma na saka 'yan sanda suka kama shi, kuma aka ritsashi aka sameshi da hodar iblis shi da Nas, na saka aka matsamin shi, dan inji da gaske ne sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login