Showing 42001 words to 45000 words out of 259198 words
Chapter 15 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.
19_20
Nana kam zuba ido ta yi ta ga yadda za'a kaya da wannan rigima.
Wandon Prince kuwa tuni ya koma tsumman ƙarfi da yaji, saboda yadda aka dinga sauke tukwane da shi.
Wandon yai baƙi ƙirin ya fita daga hayyacin sa.
Sadik kuwa da ya tafi nasa yawo be dawo ba se wajen sha ɗaya na dare.
Da takeaway ɗin sa ya dawo, dan karma ya shiga cikin gidan su, ya haɗu da Yarinyar da yafi tsanar gani wato Nana.
Ya so ya shiga gidan ya ga wandonsa, amma ya fasa ganin dare yayi, ya wuce part ɗin su.
Usman na kallon sa Sadik ya zo ya wuce, ya shige bed room ɗin sa, ya zauna yaci Abincin sa, yai wanka sannan ya nemi guri ya kwanta, sedai kwanciyar ta sa ke da wuya, yaji yanayin da ya saba ji ya fara bijiro masa, take bacci ya ƙauracewa idonsa, se tunanin Farhan da ya dinga masa yawo a ka.
Duk yadda ya so ya rintsa amma abu ya gagara, se juyi kawai da yake akan gado, ya rintse idanun sa sosai amma ba abun da ya sauya daga yanayin da ya ke ji.
Duk da yanayin da yake ciki, ba ya hana shi murmushi, lokaci lokaci idan ya tuna Wasu daga halayen Farhan, na tsoro da kuma tsananin Kunya.
Abu kamar wasa Bacci ya gagari Sadik, maimakon ya tashi ya ɗau carbi, ko yai salla kawai se ya janyo laptop ɗin sa, ya kunna.
Films ɗin da su Nasir suka tura masa, ya buɗe ya fara kallo da nufin ko ze manta da abunda ke damun sa.
Sosai ya nutsu ya fara kallon film ɗin, kamar wasa film ɗin ya burgeshi yaji yana son ganin yadda za ta kaya.
Da ya gama episode ɗaya idan yai niyyar kwanciya, se yaji lallai yana son ganin me ze faru a next episode.
A hankali Film ɗin ya cigaba da burge shi, Soyayya ce me tsayawa a zuciya tsakanin Jarumin film ɗin da jarumar film ɗin, kasancewar film ne na masarauta, shi ɗan sarki ita kuma baiwa ce a gidan.
A hankali kuma Film ɗin ya fara canza salo zuwa wani abu daban, yadda aka fara bayyanar da abunda ya zarce ƙa'ida.
Da fari ya fara jure kallon cuddling da kisses da ake nunawa, ya dake ya cigaba da kallon, a hankali kuma aka fara zarce wannan matakin aka shiga nuna romance tsakanin jaruman, da yadda yake samar musu da meeting point, a cikin wani lambu, yaje suyi hirar su ta masoya ba tare da kowa ya sani ba, wanda a nan ne a hankali suka fara da kissing.
Series ɗin yai matuƙar burge Sadik, sedai fa kansa ya soma cigaba da wuta, dan baze iya jure abunda yake cigaba da kallo a system ɗin ta shi ba.
Kashe system ɗin yayi ya saketa ta faɗa ƙasan gado, ya dafe kansa tare da cije laɓɓansa na ƙasa, ya firzar da wata iska yace "Subhanallah, Nas why? Meyasa zaku turamin irin wannan Film ɗin?"
A hankali ya tashi, ya tafi toilet yai wanka da ruwa me sanyi, ya dawo da ga shi se boxers ya kwanta.
Wayar sa ya laluba, ya nemo hotunan Farhan da yai mata ɗazu.
He Just stat zooming her beautiful face, seda hoton fuskar tata ya cika screen ɗin wayar ta sa.
Ya ƙara zooming ɗin hoton, kyawawan leɓenta suka bayyana Sosai, da fararen haƙoranta kasancewar ta yi murmushi a hoton.
He just start imagine himself kissing that her beautiful lips.
Ya dinga sauke ajiyar zuciya a jejjere, a hankali ya ajiye wayar ta sa, yai ruf da ciki a kanta, tare da ƙanƙame pillow, yana jin yadda zuciyar sa ke harbawa da sauri, ga wani abu da ke masa yawo tun daga kan sa har ƙafafuwan sa.
A haka bacci yai awon gaba da shi.
Seda Sadik ya makara sallar Asuba, dan be kwanta da wuri ba, ga tarin mafarkai barkatai da yai tayi.
Ya tashi yaje yai wanka yai sallar Asuba, ya koma bacci.
Se wajen tara da rabi Sannan ya fito falon su dan yin break fast.
A falon ya tarar da Faruk shima yana karyawa, ya nemi guri ya zauna yana ta wani ciccin magani, kamar wanda aka tursasa yai wani abu da baya so.
Faruk ne yace "naga wani wando a gurin Khairat, tace min naka ne, wandon yai kyau sosai"
Se yanzu wandon ya faɗowa Sadik a rai yace "Eh jiya aka kawo shi, se na shiga gidan yanzu zan nemota ta bani"
Faruk yace "good" daga nan ba wanda ya kuma cewa komai, Sadik ya ɗebi Abincinsa ya koma gefe.
Farhan kuwa da ta koma gida, kyakykyawar ajiya ta yiwa lambar Prince, ta na yi ta na murmushi idan ta tuna yadda ta ganshi cikin manyan kaya, ba ƙaramin kyau yai mata ba.
Haka ta ƙarasa wunin ranar cikin annashuwa da farinciki, lokaci lokaci ta kan ɗakko takaddar da ya rubuta mata lambar sa, dan jin ƙamshin turarensa da ke jikin takaddar.
Da safe kasancewar ba makaranta, yasa Farhan ta kammala ayyukanta na gida gaba ɗaya, ta koma ɗakinta tana karyawa.
Umma ce da Abban ta zaune a tsakar gida suna karyawa, can Abban Farhan yace "jiya yaran nan da suka kawowa wannan Yarinyar katin gayyata, 'ya'yan Alhaji Abdullahi me turare ne fa"
Umma tace "Ikon Allah, ina ta samo yaran wannan mutumin?"
"Ahh makaranta mana, kin manta makarantar da take yi ne?"
Umma tace "ban manta ba, ni dai ina fatan ta kammala Makarantar nan Lafiya a aurar da ita, dan ina jin tsoron cuɗanyar su ita da yaran masu kuɗi"
"Haba ki zama me kyautata mata zato mana, mun san tarbiyyar da muka bata ai, kuma ni yaran na gansu a nutse, ba rawar kai shiyasa na bar yarinyar ma ta shigo, kuma ni da ki kai zancen ta gama Makaranta a aurar da ita se ki ka tunanin da batun Yaron nan Sunusi"
Umma tace "Wane Sunusin kenan?"
"Sirikin ki mana, Wannan ba barbaren yaron, babban Almajirin malam Abbas. Na yaba da hankalin Yaron sosai, Malam Abbas ɗin ne da kansa ya zo min da zancen ya na son in bawa Sunusin Auren ta, ni kuma na gamsu da nustuwar yaron, nace masa ba damuwa amma ya bari ta ɗan ƙara girma kan ayi Magana"
Umma tace "Alhamdilillah, Allah ya tabattar da Alkhairi, tana gama wannan Makarantar se ayi Magana, Allah ya tabattar da Alkhairi"
Ƙosan da Farhan ke taunawa a bakinta, tafi ƙarfin mintuna tana kokawa da shi amma yaƙi haɗiyuwa, ji tai gaba ɗaya test ɗin bakinta ya ɗauke.
Gaskiya Sunusi be mata adalci ba, gaisawa ce da girmamawa tsakaninta da shi, dan me za'ai mata haka?
Gaba ɗaya, ba ya cikin tsarin ra'ayinta, ba ta san me ake ji a so ba, se akan Prince ɗinta, gashi ɗan gaye me aji, gashi me kyau, ina zata kai Sunusi, ga baƙi kamar an rina shi, ga tsagu a fuskarsa kamar ƙwarya, seya shafe sati yana saka yadi ɗaya, dama batun gayu babu shi, sedai Sunusi akwai haddar Alqur'ani me girma, dan gwani ma ake cema sa, da ka yake Rubutun Alqur'ani.
Ya san Alqur'ani sosai da sosai, sedai bayan ilimin Alqur'anin nan babu na hadisi, babu na fiqihu, amma idan ya zauna ze iya gaya maka adadin ayoyi na kowacce sura a cikin Alqur'ani, sau nawa Allah ya ambaci kowane Annabi, sau nawa sunayen Allah suka zo a Alkur'ani, adadin sunan Allah nawa ne a Alqur'ani da in da aka ambace su, duk da ka yake irin wannan abubuwan.
Duk da fankar ɗakinta na ta uban gudu ta na bada iska, Amma ita wata irin zufa takeyi, sam ta kasa samun nutsuwa.
Ummanta kuwa cigaba su kayi da hirarsu, yayin da Farhan kuwa ta shiga cikin zullumi da damuwa, dan ita a duniya yadda take ji a zuciyar ta, idan har ba Sadik ba, ba zata iya auren kowa ba.
Duk da ana yawan faɗa mata Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai, kuma babu lallai ya Aureta, amma ita yadda Sadik ɗin ke nuna mata ba ta jin ze kasa Aurenta, Amma idan aka haɗa ta Aure da Sunusi an gama cutarta, yanzu ta san ciwon kanta, ta gane menene so meye daɗin sa, sam zuciyarta ba zata iya karɓar Sunusi a matsayin mijin Aure ba!.
Sadik kam cikin gida ya shiga, yana zuwa ya tarar da Inna a falo Nana na kusa da ita, da sauran ma'aikatan gidan da ke ta shige da fice, da fara shirin karɓar baƙi, dan saura kwana biyu a fara biki, gidan a cike yake da mutane.
Sadik na ganin Inna ya ɗan ɓata fuska dan baya son damuwar tsohuwar nan, amma ya basar ya ɗan risina yace "Ina kwana?"
Inna ta ɗaga kai ta kalli Sadik, ta ɗan yi murmushi me cike da ma'anoni tace "lafiya ƙalau ka tashi lafiya?"
"Lafy ƙalau" ya amsa tare da miƙewa ze tafi.
"Su sauran jama'ar ɗakin ba zaka gaishe su bane?"
Haushi ne ya kama Sadik, ita dai tsohuwar nan ba ta san zaman lafiya kwata kwata, tun da dai ya gaisheta meye na wani seya gaida sauran mutanen ɗakin?"
Juyowa yai ya tsurawa Innan ido amma yaƙi magana.
Nana kuwa zuciyarta se dukan bakwai bakwai take, tana fargabar kar ya gano waitar da tai masa.
Ana haka sega Mother ta fito, akan Sadik ta fara sauke idonta tace "Sadik har ka tashi da safen nan haka?"
Inna ta kalli Mother, kusan ƙarfe goma na safe, amma tana kiran har ya tashi da safen nan.
Sadik cikin shagwaɓa yace "Mother, ina wandona?"
"Wane wandon?" Ta tambayeshi cikin rashin fahimta.
"Wanda Khairat ta baki ko ajiyemin" ya bata amsa.
Mother tace "A'a ba ta bani komai in ajiye maka ba, ni yaushe rabon da in sa Khairat a idona ma?"
Sadik yace "jiya fa nace za'a kawomin saƙo ta karɓa ta baki ko ajiyemin"
"To ni ba ta bani ba, kuje can ku ƙarata"
Sadik ya ɗan fesar da iska daga bakinsa yace "yau a nan gidan ta kwana?"
"A'a a gidansu ta kwana, amma nasan anjima kaɗan zasu zo"
Be ce komai ba ya jinjina kai ya bar falon.
Inna ta ɗago ta kallesu kawai ta girgiza kai.
Nana kam cikinta ya fara ɗurar ruwa, dan idan Asirinta ya tonu ta shiga uku.
Nan ta ga sam ba ta kyauta abun da tayi ɗin, be kamata ace tayi haka ba, duk da a ƙule take da Sadik da Khairat tayi hakan ne dan huce takaicin wulaƙancin da suke mata, amma kuma se taji gaba ɗaya ba ta kyauta ba.
Wajen ƙarfe sha ɗaya Khairat suka zo gidan, ita da 'yan gidansu, se iyayin yawon karɓar ɗinki da zuwa gurin Saloon take yi, gaba ɗaya ta manta da batun ajiyar Sadik.
Kamar an jefo shi se ga shi ya kuma dawowa, ya tarar da Khairat ɗin a falo, ita da wasu 'yan uwansu zasu koma gurin tela, Mother na musu sautu.
"Malama ina kayana?" Shine abunda yace da Khairat ba tare da ya kula kowa ba.
Tana ganinsa gabanta ya faɗi, dan gaba ɗaya ta manta, se kuma ta ga kamar ta bawa Mother ai.
"Na bawa Mother tun jiya"
"Na tambayi Mother ai, tace baki ba ta ba, ina kika ajiyemin kayana?"
Mother tace "Ni baki bani komai ba"
Nan Khairat ta shiga wulƙita idanu, dan gaba ɗaya ta manta da batun wandon nan ta shiga sabgar ta.
Cikin zafin rai Sadik ya daka mata tsawa "ina wandona malama?, ina miki magana amma kin tsaya kallo na"
"Am..wallahi Sadik ni kamar Mother na.."
"Dalla rufemin baki, wallahi sekin nemo min abuna, daga cewa ki karɓi abun ki bawa Mother ta ajiyemin seki ɓatarmin, a haraba fa naga ledar kamfanin wandon tana yawo, duk in da yake ki nemo min abuna na gaya miki"
Duk Wannan bala'in a gaban babar Khairat ɗin Sadik ke zazzaga mata, ba ta ido ba Komai haka ya rintse ido yana masifa.
Mother tace "Kai dai ka cika rashin haƙuri, Khairat kiyi tunani ina kika ajiye masa?"
Khairat da idonta ya cika da ƙwalla tace "I can't remember, na zata na baki ne, kuma yan...
"Wallahi sekin nemo min, na gaya miki gobe in Allah ya kaimu zanyi amfani da shi, ki nemomin kayana kawai, careless girl"
Nana kam se hailala da salati take, kar a ɗago wannan ɓarnar da tayi.
Sadik kam yana uban huci, haka ya bar falon.
Mother tace "ohh ni Hauwa'u Allah ya shirya min Auta, Khairat kiyi ƙoƙarin tuna in da kika ajiye masa wandon nan dan Allah kar ya zo ya kuma ɗaga mana hankali.
Jiki a sanyaye Khairat tace "wallahi Mother na zaci na baki ne, wallahi na manta yadda nai da wandon"
Sadik na fita yaci karo da abu akan baranda, abunda ya ɗau hankalin sa shine tambarin kamfanin wandon fa yai siyayya.
Tsayawa yai, yasa hannu ya ɗago wandon, aikuwa Tabbas shine, ya yi duƙun duƙun, da alama anyi goge goge da shi ha baƙin tukunya a jiki.
Wani abune ya soki ƙirjin sa, nan da nan jikinsa ya ɗau rawa.
A fusace ya koma falon yana wani irin huci, yana shiga ya jefawa Khairat wandon a jikinta.
Da sauri ta kauce, kasancewar yadda wandon ya koma tsumma, ya fita da ga hayyacin sa.
"Wannan shine abun da na baki ajiya, aka mayar da shi haka ko?"
Mother tace "ba dai wannan ne wandon ba?"
Tabbas shine, amma ya akai haka ta faru ya koma haka.
Cikin kuka Khairat tace "wallahi ban san yadda akayi ya zama haka ba, nasan a cikin ledar sa yake.
Mother ta ɗaga wandon, ba shi da maraba da tsumma.
Inna da tun ɗazu ba ta tanka ba se yanzu tace "Wannan ai tsumma ne, shine wandon da ake ta rigima a kai?"
Talatu me aiki tace "Ai wandon sabone"
Inna tace "wannan ɗin, amma na ganshi duk a yayyage? Ya za'ai sabon Wando a yage haka kamar na mahaukaci"
Duk da halin da Nana ke ciki na regeretin, se da tai dariya jin abunda Inna tace, duk yadda ta so riƙe dariyar ta kasa, ta miƙe ta bar falon tana darawa.
Sadik kuwa ji yai tamkar zuciyarsa ta tsaga ƙirjinsa ta fito.
Mummy tace "Khairat baki kyauta ba gasky, careless ɗin ki yayi yawa, nawane wandon Ni se in biya kuɗin wandon?"
Wata uwar harara ya gallawa ƙanwar mahaifiyar tasa yai waje yana fidda numfashi.
Inna ta girgiza kai, ganin yadda suke ta wani lallaɓa shi yana fizgar kai, sam ba ɗa'a.
Ita kuwa Khairat fashewa ta sake yi da kuka.
Mother ta janyota tana rarrashin ta, suna mamakin yadda a lamarin ya faru.
Farhan kam abun duniya ya hanata sukuni.
Tunda taji zancen Sunusi ko Abincin kirki ba ta iya ci, bacci ma gagararta yake yi, saboda tsabar damuwa.
Ba ta san meyasa iyayenta haryanzu suke rayuwar mutanen da ba, meze sa kawai ai mata miji ba tare da neman yardatta ba, shikenan an mata shamaki da kawo kowa tace ta na so.
"Yaya tunanin me kike ne?"
Muryar cousin ɗinta Huzaifa taji, wanda ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi.
Murmushi ta yi tace "ba abunda nake tunani"
Ya kalleta yace "ba wani nan, kin san tun yaushe na shigo, ina ta magana kinyi shiru, na shigo Umma ma bata nan"
Farhan tace "Kaga ni ba wannan ba, dan Allah wayarka da kuɗi a ciki?"
"Eh da kuɗi, amma ba yawa me zaki da ita?"
"Waya zanyi yanzu zan baka"
Ya sa hannu a aljihunsa, ya ciro wayar duk screen ɗin wayar ya tsatsage, wayar ta sha jiki, ya miƙa mata yace "kuma ki ka cinyemin kuɗi sekin biyani, minti ɗaya da rabi na baki"
Murmushi tai tace "godiya nake gwani Huzaifa"
Abba na son a kirashi gwani, saboda a duniya ba shi da burin da ya wuce haddace Alqur'ani.
Yace "kai kin sa naji daɗi sosai, in Allah ya yadda se na wuce ki a hadda"
Farhan tace "bari fa, na riga na wuce ka"
Murmushi yai ya fita yana faɗin, 'aikuwa zan baki mamaki"
Bayan ya fita, ta fito tsakar gida ta duba, ta ga Umma bata nan ta fita.
A hankali take tafiya kamar mara gaskiya, ta je ta duba ɗakin Abba ta tarar yana bacci, ta koma ɗakinta ta kulle ta saka sakata.
Litattafanta ta zazzage, ta ɗakko lambar Sadik, jikinta na rawa saboda rashin sabo, gani take kamar ana kallonta.
Jiki na rawa ta kwafi lambar ta sa, ta danna kira.
Sadik na kwance ya yi ruf da ciki, zuciyarsa na ta tafasa akan asarar da Khairat tai masa, wayarsa ta hau ringing.
Wani dogon tsaki ya ja ya ɗauke kansa da ga kallon wayar.
Tai ringing harta katse be ɗauka ba, gaba ɗaya se taji ba daɗi, amma se tai masa uzurin ko yana wani abun ne.
Ta tattare litattafan, ta mayar cikin jakarta, ta maida jakar ma'ajiyarta.
Taita dakon ko Prince ze biyo wayara, amma shiru.
Ba ta gaza ba ta sake kiran layin nasa, a fusace ya fizgo wayar ya ɗaga cikin masifa yace "Wai waye ne?"
Cikin sanyin muryarta, me sigar shagwaɓa tace "nice fa"
Wata irin ajiyar zuciya ya ja, tare da lumshe idanunsa, ba tare da yace komai ba.
"Ka na ji na kuwa?"
"Ina jinki Princess, ina tattaro kalaman ban haƙuri ne, na rashin ɗaga wayarki da farko, sannan kuma nai miki shouting, bari in kira ki"
Ya katse kiran, sannan ya kirata, seda ta kuma leƙawa tsakar gida ta ga ba kowa, sannan ta koma ta zauna ta ɗaga wayar.
"Ina fatan an karɓi ban haƙurina" yai maganar cike da kasala.
Ɗan tura baki tai tace "naji muryarka wani iri, meke damunka?"
A shagwaɓe yace "Princess ɓatamin rai akayi zanyi kuka"
Dariya Sadik ya bata tace "Subhanallah, kuka kuma?"
"Eh mana"
"No, sorry kar kayi kuka, kaifa namiji ne kuka ai se mata"
"Khairat ce ta ɓatamin rai"
Tace "am sorry ni ban tambayeka ya kuka je gida ba?"
"Lafiya ƙalau, wandon nan da na siya, aka kawo nace ta ajiyemin ta bari akai mopping da shi, wai an zata tsumma ne"
Kwashewa da dariya Farhan tayi, dan sosai ya bata dariya.
Cikin dariya tace "to ai ba kowane yasan wannan wandon gayu bane, abu duk a yayyage"
"Au haka zakice ko? Shikenan"
"A'a kayi haƙuri kasa wani"
"Ai raina ya gama ɓaci, sena hukunta ta akan abunda tayi"
"A'a dan Allah kayi haƙuri, tsautsayi ne"
"A'a wannan ba tsautsayi bane, za ta gane kurenta"
"Dan Allah kayi haƙuri mana"
Sadik yace "ko zan haƙura se nayi tunani, duk da ita ma ina sonta, duk wadda Allah ya bani a cikin ku ina so, sedai na fi son ki, da ke ki kai laifin da tayi ba abunda zan iya"
Ɗif Farhan tayi taƙi magana, Sadik yace "ya dai