Showing 147001 words to 150000 words out of 259198 words
Chapter 50 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
ne Jidda ke shigar kirki ta atamfa ko kayan mu na Hausawa, kullum cikin tsukewa take kamar inyamura.
Kwanan Nana tara a gidan dr., Sannan Abba ya zo da daddare, Nana ta dinga murnar ganin Abban.
Har Abban yai ƙoƙarin kira mata su Hakimi su gaisa amma wayar ta ƙi shiga, nan da nan kuma se kuka.
Abba yace "meye na kukan kuma Nana? Jiya naje ƙauye duk suna gaisheki, Hakimi ya bada kilishi Inna ta bada turaruka tace a kawo miki, ki shirya gobe in Allah ya kaimu zaku tafi, da kaina zan raka ku can"
Aikuwa Nana ta sake fashewa da kuka, kamar Abba yace ze kaita in da za'a kashe ta, Jidda ce ta janye ta ɗaki tai ta rarrashin ta, dan ita tasan dama gobe zasu tafi, Dr. Ya gaya mata, bata gaya mata bane dan kar ta ɗaga hankalin ta.
Wasa wasa Abbas yaƙi sallamar Farhan, ya barta a Asibitin sedai kullum se yana duba BP ɗinta safe da Yamma.
Gaba ɗaya zaman Asibitin ya gundure ta, se dai ta kasa dena tunanin abun ƙaunarta wato Sadik, ga damuwar Sunusi hakan ya sa jininta ya ƙi sauka, dan in dai Sadik be dawo ba Aurenta da Sunusi babu fashi.
Yanzu ma Dr. Abbas ne ya shigo da abun awon BP.
Yana ƙoƙarin ɗaura mata tace "Doctor"
Ba tare da ya kalleta ba yace "Na'am Babyna"
Wani Yarrr ta ji, tare da binsa da kallo.
Yai murmushi yace "it sounds like na raina miki hankali ko? I don't mean I love you, i mean you are my daughter"
Ba abunda ya faɗo zuciyar Farhan se Sadik, bakinsa yafi kowane baki iya furta kalmar Baby, ba zata manta lokacin da ya rungumeta yana maimaita Babyna a kunneta ba.
Ba ta dawo daga hayyacinta ba, taji Abbas ya zauna a kusa da ita.
Da sauri ta ja baya daga kusa da shi.
Yai murmushi yace "ba taɓaki zan ba Farhan, zan sallameki ne a yau, naji daɗin yabon da Hajiyata ta dinga miki na tabattar ke me tarbiyya ce sosai, Amma Sadik ɗin nan da yake zuciyar ki, dan Allah ki aje shi aside ki kula da karatun ki da lafiyarki, duk da baki gayan ba nasan alaƙace ta soyaya tsakanin ku, amma kinyi Yarinta da love Crises, ki cire Sadik daga ranki maybe baze dawo gareki ba, tunda har ki kai rashin lafiya be zo ba, Yanzu dai tashi muje, Zan maida ke gida, in Antynki ta zo zata ɗaukar muku kayan"
Jiki a Sanyaye Farhan ta sakko daga kan gadon, tabi bayansa. Tana ta ƙoƙarin gazgata abun da Abbas ya faɗaa, amma zuciyarsa ta kasa amincewa da Sadik ɗinta baze dawo ba, haryanzu tana nan akan cewa be dawo daga ƙauye bane.
Har gida ya kai Farhan, ya kalleta yace "nan da sati ɗaya zanje Zariya yin clearance, zan tafi ƙasashen waje ƙaro karatu, ina fatan idan na dawo in tarar kin manta da komai, karatunki yayi nisa, murmushi kawai tayi ta buɗe ƙofar ta fita.
tana zuwa gida ƙannaneta suka dinga murna, nan da nan maƙota wanda sukaje Asibiti dubiya da wanda ba su zo ba sukai ta shigowa dubata.
Sedai abun mamaki, ko sau ɗaya Umma ba ta kalleta ba balle tai mata sannu, abun ya dinga damunta tana cigaba da jinjina ƙiyayyar da mahaifiyarta ke mata.
Seda daddare kowa ya tafi, ƙannaneta har sun kwanta sannan Umma ta shigo ɗakin Farhan, ta cillo mata wayarta tace "Wayar waye wannan?"
Gaban Farhan yai mummunar faɗuwa, dan ta manta da wayar a ƙasan pillowan ta kwana ranar da abun ya sameta.
"Wato kin fara biyewa yaran banza da zasu lalata miki rayuwa ko? Na bawa Huzaifa ya karanta min saƙonnin da ke cikin wayar, duk da shima ɗin ba komai ya karanta min ba dan ya kareki.
Kin bani mamaki, dama tuntuni na fara ganin take takenki, ashe yaron nan dagaske yake wani ne a gefe yana hure miki kunne, har kin san ki dinga gayawa Namiji irin wannan maganganun, ban nunawa mahaifinki wayar ba, amma Ranar Asabar iyayen Sunusi za su zo, watanni uku rak za'a sa Aurenku, a yanzu ma bani da tabbacin in haryanzu ke budurwa ce kar a cuci ɗan mutane, kin bani kunya wallahi kin ɓata wayon ki!
Tirƙashi, WACE RAYUWA NANA DA SADIK ZA SUYI A ƘASAR WAJE? MOTHER ME ZATA SHIRYA DAN RABA AUREN SADIK DA NANA? A WANI BABI FARHAN ZATA KASANCE, ME KUKE TUNANIN ZE FARU NAZIR ZE AURI LILLY KO AKWAI MATSALA?
INA JIRAN RA'AYOYIN KU, BELIEVE ME YOU WON'T REGERET BUYING THIS BOKK 😍😍😍😍
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Gigicewa Farhan tayi, cikin tsananin tashin hankali ta fara tattaro kalaman kare kanta, duk da ba ta da tabbacin kalaman nata za suyi tasiri a gurin Umman na ta.
"Umma, dan girman Allah, Umma ki saurareni dan Allah"
"Rufemin baki, ƙanƙanuwar ki dake, amma kin san munafunci, kin san ki yiwa namiji wannan kalaman, kin cuci rayuwarki, kuma kanki ki kaiwa ba ki min ba, dama dan babanki ya takura se kinyi bokon nan ne, amma dan tani gara ai miki aure"
Ta ƙarasa maganar tare da ɗauke wayar daga jikin Farhan, ta fice daga ɗkin.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ya rabbi Allah ka shiga lamarina, Allah ka kawon mafita"
Take taji ƙirjinta saitin zuciyarta yai mata wani irin nauyi, ta dafe gurin hawaye na fita daga idonta.
"Dagaske Sadik ka barni? Shikenan haka alƙawarin ze tafi a banza, za'a Auramin wani bayan ka koyar dani abu me wahalar sha'ani, ka da sa shukar da ba zaka iya bata ruwa ba? Sadik zuciya ta ba zata iya jure tarayya da wani a matsayin miji ba kai ba, Please come back" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka.
Sadik kuwa sam ya kasa murna da wannan tafiyar, an sai masa sabuwar waya da Komai da Komai, Mother ta shirya masa kayansa da ze tafiya da su.
A ɗaki ta tarar da Sadik, yana shirin kwanciya ta nemi guri ta zauna a bakin gadon ta kalleshi tace "Sadik ina son ka buɗe kunnenka da kyau ka saurareni, ba kai ba Yarinyar nan, ba kai ba shiga sabgarta, tai rayuwarta kai taka ina nan zanyi duk me yuwuwa in ga nai Dalilin da zan kawo ƙarshen Auren nan"
Sadik yace "dama ni me ze haɗani da ita, boarding fa za ai kata ni kuma ina hostel"
Mother tace "Yawwa, ai ni ban san da Wannan Maganar ba ma, shikenan ta kwana gidan sauƙi, babu wani dalili da ze dinga haɗaku ma, ka maida hankali kayi karatunka kaji Auta, na san you are gifted, amma kayi karatu da kyau, idan ka kammal karatu da kaina zan maka Aure irin na 'ya'yan gata, in aura maka wadda kake so, dan wannan yarinyar ba ajinka bace, ba tsarar ka ba ce son zuciya ne kawai na kakannin ka yasa su ka aura maka ita"
SADIK yai murmushi yace "shikenan Mother, Allah ya kaimu in gama makarantar Nagode sosai da kulawar ki My mum"
"Mentioned not dirling, am gonna Miss you so much"
"Me too mom" yai Maganar yana rungume Mother da tuni ta fara hawaye, ƙarshe Sadik ne yai ta rarrashin ta, tai masa sallama ta kashe masa fitila.
Har Sadik ya kwanta, yaji wani abu me nauyi ya tokare masa zuciya, wani abu me mahimmanci ya shiga cin zuciyarsa, wata irin damuwa ta baibaye shi, da farko ya danganta hakan da tafiyar da ze da kuma Auren da a kai masa, sedai damuwar da yake ji ko lokacin da aka ɗaura Auren be ji ta ba, ji yake kamar zuciyarsa za ta tsaga ƙirjinsa ta fito, amma ya kasa tuna me ya jefa shi cikin wannan mawuyacin halin haka.
Ya tashi zaune ya dafe kansa, yana jujjuya kan ya na son ya tuna menene wannan abu a zuciyar sa da ƙwaƙwalwarsa ta kasa tuna masa? Amma kansa ya shiga sara masa, the more yake pressing ƙwaƙwalwarsa the more yake jin wani irin ciwon kai.
Ya runtse idanunsa, yana sauraron yadda zuciyarsa ke wani bugu kamar zata fasa ƙirjinsa.
Haka ya lumshe idanunsa, da ƙyar bacci ya ɗauke shi.
Farhan kuwa, jiki a sanyaye taje ta ɗauro Alwala ta tada salla, sedai ta kasa sallar da ta fara karatun sallar se ta rikice, zubewa tai akan daddumar tana kuka, tana faɗin "Ya rabbi, Ya rabbi" a hankali bacci kuwa dama ba ta yi shi ba sam.
Washegari tun da sassafe, Jidda ta sa Nana tai wanka, ta shiryata amma Nana taƙi karyawa se kuka da take.
Se da Usman ya zazzare mata ido, ya sata a gaba sannan ta ci Abincin.
Bayan ta karya suka ɗau hanya zuwa gidan Abba.
Suna zuwa gaban Nana ya shiga faɗuwa, dan a falo suka tarar da Mother ta hakimce tana kallon TV.
Tana ganinsu tai murmushi tana musu sannu da zuwa, amma ta na ganin Nana ta haɗe rai, Nana har ƙasa ta durƙusa ta gaida Mother, amma Mother tai mata banza ta na yiwa Jidda Magana.
Usman kansa be ji daɗin yadda Mother taiwa Nana ba sam, Jidda tace "Mother ashe abun Alkhairin da ya faru kenan, Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya, Amma Mother ai ko walima Yakamata a shirya mana kafin su tafi"
Tsaki Mother tai tace "ke rabani da wannan shiriritar, dan ban ɗau wannan auren wani Auren kirki ba, ya jikin naki ance min baki da lafiya, hankalina ne ba a kwance ba shiyasa ban zo dubaki ba"
Jiki a sanyaye Jidda tace "Jiki da sauƙi Alhamdilillah"
Suna cikin hirar sega Faruk ya shigo shi da Sadik, Nana ta na ganin Sadik gabanta yai mummunar faɗuwa sakamakon kallon da yai mata.
Faruk yace "our runaway bride, shine kuka haɗa baki da Abba ki ka koma gidan Dr. Ko ai shikenan ya kike?"
"Lafiya ƙalau" Nana ta faɗa a Sanyaye.
Faruk yace "Sadik ga amaryar fa, ai kwa gaisa ko"
Wani uban tsaki Sadik yai, ze wuce ɗakinsa.
Dr. Ne ya daka masa wata irin tsawa yace "zo nan, ana maka Magana waka kewa tsaki?"
Mother tace "ya za kai masa tsawa haka, ba dole yai tsaki ba, an samun yaro a damuwa, dole yai tsaki"
Dr. Yace "Mother please, abu Kafin ya faru ake nuna masa ƙiyayya, ko ɗaukar matakin hana faruwarsa, amma wannan ya riga ya faru, karki tsananta ƙiyayya akan lamarin nan daga baya ki zo kiji kunya, ki fita sabgar yaran nan please"
"Ni kake gayawa haka Usman?"
"Mother, I don't mean to say anything bad to you, but Maganar gaskiya ce tunda lamarin nan ya faru kiyi haƙuri dan Allah, ki musu Addu'a"
"Rufemin baki!" Mother taiwa dr. Tsawa.
"Dan ba kai a kaiwa haka ba shine kake wannan maganar ko? Dan kai ka kammala karatu ka samu aiki ka zaɓo matar da kake so ka samu ka Aura, shine shi zaka dinga zare masa ido, dan ba kai aka aurawa 'yar ƙauye ba ko? Aka ɓata career ɗinka da burin ka na karatu ba?".
Jidda ba ta ga abun tada jijiyar wuya da Mother ke yi ba, sema tausayin da Nana ta bata, dan se kuka take, abun da tausayi a dinga nuna maka ƙiyayya a gabanka, ana goyon bayan a wulaƙanta ka.
Jidda tace "Nana, ta shi ki shiga ɗaki kafin Abba ya dawo" sannan ta maida hankalinta kan Mother tace "Dan Allah Mother kiyi haƙuri, gaskiya ba a kyauta muku ba, amma dan Allah kiyi haƙuri"
"Ƙyaleni Jidda, wannan mijin naki be san yakamata ba, ban san me Sadik yai masa ba da yake takura masa haka"
Dr. Ze magana, Jidda ta girgiza masa kai alamar yayi shiru, yayin da Sadik se cin magani yake yana hura hanci.
Shi Faruk dama takaici ne ya hana shi Magana gaba ɗaya.
Nana kam a ɗakin ma takurewa tai, ta dinga kuka tana tunanin tun a nan kenan, ina ga in sunje can in da ba kowa, Allah kaɗai ya san irin zaman da za suyi.
Khairat ce ta leƙo ɗakin da Nana take, ta kalleta tace "kwaɗayayyiya kawai 'yar ƙauye, hadda kukan munafunci nan kuwa ƙasan zuciyarki murna kike"
Nana ba tace mata komai ba, se kuk kawai da take, dan ba ta da lokacin Khairat a yanzu.
Kusan awa ɗaya da zaman Nana a ɗaki, Jidda ta shigo tace "Nana ta so mu raka ku airport Abban ya dawo"
Jiki ba ƙwari Nana ta taso, tana ta goge hawaye, Jidda ta rungumota Zuwa falo, Sadik ya rungume Mother yana kuka tana kuka, Allah sarki Nana ita babu me rarrashin ta, Jidda ce take ta bata haƙuri ta na mata Nasiha.
"Zaka zo ka wuce ne, ko kuwa in ƙyaleka ka fasa karatun, in ya so uwarka tai romonka ta cinye?" Abba yai maganar a fusace
Mother tace "Amma dai ai ka bari in sallama da ɗa na"
"Ba abunda ya dameni bane, ya zo ya wuce in ba haka na tafi, wallahi se dai ki nemi kuɗinki ki biya masa"
Mother har mamakin yadda Abba ya koyi masifa take, Sadik suka fito harabar gidan, suka shiga mota ɗaya shi da dr. Da Faruk, Abba kuma suka shiga ɗaya shi da Jidda da Nana da Khairat.
Suna tafe Dr. Yace "kai Sadik, dan kut..... Bar ganin a gaban Mother muke ɗazu na ƙyaleka, wallahi ka kula da kanka, idan ka sake ka cuci Yarinyar nan Magana ta dawo kunnen Abba ka san matakin da ze ɗauka ba ze maka daɗi ba, kuma in da zakaje ba idon kowa a kanka, dan haka kaji tsoron Allah ka kula da addinin ka"
Shiru Sadik yai Kamar ruwa ya cinye shi, yana ta kallon gari, yau kusan wata biyar kenan rabon da yabi wasu guraren, kuma gashi daga yau ze tafi wata Duniyar se dai in ya zo hutu kuma.
Khairat da ma gulmace ta sa ta biyo su Nana rakiya, Jidda ta rungume Nana a jikinta, kamar ƙanwarta tana mata faɗa ƙasa ƙasa yadda ba me ji se Nanan.
"Yanzu idan Sadik ya dawo yana sonki, ai kema zaki so shi ko?" Jidda tai maganar a kunnen Nana.
Nana ta girgiza kai alamar a'a.
"Yarinya zaman Aure ya wuce tunaninki, amma idan kina son ya dena miki masifa ku zauna lafiya, kinga yadda nake wa dr. A gida? Kema haka zaki dinga yi masa"
Nana a ranta tace "taɓɗijan, wallahi ba zan zama 'yar iska ba, bayan Inna ta hana maza su taɓa ko hannu na, in na dawo taga na zama 'yar iska ai seta koreni'
"Ya naji kinyi shiru, ko ba zaki iya ba?"
Nan ma shirun Nana tayi, Jidda tai dariya kawai tana ɗan dukan bayan Nana alamar rarrashi.
Ƙarfe ɗaya suka isa Airport, kasancewar jirgin ƙarfe biyu zasu hau, ya sa suka tsaya su kai salla, suka ci Abinci banda Nana da tabi ta takura kanta.
Ƙarfe biyu jirgin su ya ɗaga, sedai Sadik yana ji a jikinsa ya bar wani abu me matuƙar kusanci da shi a Nigeria, amma ya kasa tuna ko menene.
Nana na kusa da kujerar Abba, Sadik kuma na ta bayansu, sam Abba yaƙi kula Sadik a Abunda Abban be taɓa yi ba, ya share Sadik tsawon kwanaki ba tare da ya kulashi ba, komai girman laifin da yai kuwa.
Abun duniya ya addabi Farhan, Rana zafi inuwa ƙuna, Umma ta ƙara watsi da lamuran Farhan fiye da da.
Hajiya ta shigo sake duba Farhan a gida, tana ta tsokanar ta wai babanta yace ta duba masa idan ta fara ƙiba.
Hajiya tace "Umman Farhan, wai ni ko dai haryanzu jikin ne na Farhan, naga duk ta ƙara zubewa bayan fitowar ta daga Asibiti, ta rame sosai tayi duhu"
Umma tace "A'a ai taji sauƙi sosai"
"Ai ni na ga ramar tayi yawa ne, yarinya me garin jiki tubarakallah amma duk tabi ta rame, ni gani nai kusan har gara tana Asibiti, amma yanzu ta rame sosai"
Umma tace "kuma kimga ta na shan magungunan ta"
"Hakane, to Allah ya ƙara Afuwa"
Nan Umma ta ku ma yiwa Hajiya godiya sosai, sannan Hajiya ta tafi.
Farhan kam ta yanke shawarar komawa Makaranta ko ba ta gama jin sauƙi ba, dan da ta cigaba da zama tana ganin ɓacin rai a fuskar Umman nata, gara ta koma Makaranta ta dinga tafiyar da mafi yawan lokacimta a can, ta samu ta dinga rage zafi.
Su Nana an sauka lafiya, sedai tun daga airport ta ga akwai banbanci tsakanin gida Nigeria da ƙasashen ƙetare, ba karonta na farko kenan ba da hawa jirgi, an taɓa zuwa da ita umara tana yarinya sosai, tana da burin sake hawan jirgi, amma da yake ba daɗi ne ya hau da ita jirgin ba, ko murna ba tayi da hakam.
Ko ina fitule ne a birnin kamar rana, saɓanin gida Nigeria, wani gurin da haske wani kuma babu.
Wani baƙin Bature ne ya zo da mota, ya ɗauke su daga airport ɗin.
Da alama sun san juna da Abba, dan suna haɗuwa suka gaisa, suka fara hira, Sadik ya gaishe shi, Nana kuwa tai shiru tana kallonsu, dan yadda Abban ya jiya harshe yana turanci shima Kamar Bature.
Wani gida mutumin ya kaisu, sedai gidan girmansa yayi yawa, ga mutane burjik a gidan suna shiga suna fita, wannan motar ta shiga wannan ta fita, a taƙaice dai Hotel ne, da yake Nana ba ta san ya abun yake ba ta ɗauka gida ne.
Wani ɗaki suka shiga, falo da bedroom biyu, Abba yaiwa Nana umarni da ta shiga ɗaya daga ɗakunan, shi da Sadik kuma suka shiga ɗaya, Mutumin nan yai musu Sallama ya tafi, har Abinci duk an samar a ɗakin.
Suka fara rama salloli ta hanyar yin ƙasaru, Abba ya sa Nana a gaba taci Abinci sosai, ko ta kan Sadik ba ya bi da Nana yafi damuwa.
Bayan ta gama ci ya kalleta yace "to Nana, gobe in Allah ya kaimu da safe, zanje in kai ki Makarantar ku, a in da zaki zauna, ina me miki Nasiha da kiji tsoron Allah, na san ke me Addini ce ki kula da kanki, kiyi karatun ki, karki wasa da Addini ko kuma al'adar ki, sannan kiyi taka tsantsan kibi dokokin su, kin san nan ba Nigeria ba ce.
Ki nutus kiyi karatu da kyau kinji 'yar gidan Inna, duk abunda kike buƙata akwai in da zakije ki faɗa a makarantar za'a kirani a waya muyi magana, in munje duk za'a nuna miki Insha Allah, ni dai fatana kiyi karatu da kyau kinji?"
Nana tace "to zanyi in Allah ya yadda"
"Yawwa Allah yai miki Albarka, maza tashi kije ki