Showing 246001 words to 249000 words out of 259198 words
Chapter 83 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
ne? Ko na faɗi ba daidai bane?"
Faruk yace "da dai a bar wannan maganar?"
Nana tace "ba za'a barta ba, ai Magana ce ta gaskiya, a gaskiya a gida a na so ba zamu bari kaje waje ka auro ba, muna da wannan zuƙeƙen saurayi haka, ace a kai waje, gaskiya a'a tunda ana so a gida, shikenan mun maka mata, zan shigar da maganar ku da zarar an gama bikin Besty"
Sumsum Khairat ta miƙe, dan ba ta zata shishshigin da takewa Faruk ana ganewa ba, da sauri ta bar falon, Nana a ranta tace ina sane na faɗi haka, gurin mijina dai ba space wannan ma dan ya ƙallafa ransa ne, ni ba kishiyarki ba amma kin sani a gaba" a zahiri kuma tace. "dan Allah uncle a duba lamarin nan, save the innocent soul of your sister"
Faruk yace "Maman Sahal, gaskiya a tsarina bana son Auren Yarinya, nafi son me ɗan hankali, Khairat tai min yarinta da yawa, kuma ƙanwa kawai na ɗauketa"
Nana tace "haba Uncle, meye aibun Khairat ne?"
Faruk yace "ba ta da kunya, ga shigar banza, ga ta da abokai maza da yawa, kowa friend ɗinta ne, yarinya ƙarama da hak ai be dace ba, and at least yakamata ace ko level 2 ta shiga kan tai Aure"
Nana tace "Yanzu ni ban isheka misali ba? Ni ma lokacin da Besty ya Aureni bani da Kunya Wallahi, ka tambaye shi kaji, ni ga rashin Kunya ga ƙauyanci, duk da dai ƙauyancin nawa ba wani na azo a gani bane, amma gara Khairat tana da tsoro yin rashin Kunyar wasu lokutan, ni a lokacin bana son sa, kasan dai irin takun saƙar da muke yi da shi, amma a hankali da na fara sonsa duk na dena.
Ita mace in dai tana sonka, za tai duk wani abu dan ta burgeka, kuma zaka iya saita ta yadda kake so.
Auren Khairat da zakai ze iya cetota, idan ta shiga Jami'a ma ze zama tana da katangar Aure a Tare Da ita, hakan baze bari ta cigaba da kule kulen mazan da baka so ba"
Faruk yai shiru, yana mamakin yadda Nanan ke tsara magana cikin hikima.
Faruk kawai yai murmushi yace "Hajiya Nana kenan"
Nana tace "Uncle, ka taɓa soyayya kuwa?"
Murmushi yai yace "eh to, bana ce a'a ba na taɓa"
"No gaskiya ba ka taɓa ba, da ka taɓa ba zaka ƙi karɓar tayin Khairat ba, baka da nauyin Soyayar kowa a kanka, zaka iya farawa da soyayyarta, dan Allah kar ka bari ta shiga hatsarin soyayya, soyayya akwai wahala musamman idan kana son maso wani" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin goge hawayenta.
Faruk yace "Subhanallaahi, dan Allah Nana ki dena, ko Sadik ɗin ne yake miki wani abu?"
Tace "A'a, sedai na fara son Sadik a lokacin da be kamata ba, lokacin da ban san akwai wadda take ransa ba, yana da kyakywar mu'amala, kan ka zauna da shi zakaga ya fiye izza, da raina mutane, amma ba haka yake ba a zahiri, hasali kyawawan ɗabi'unsa suka sa na fara son shi, sedai na makara, ina ta ƙoƙarin danne komai ya koma bakomai ba, amma na kasa bana jin daɗin yadda nake masa, amma ba yadda zanyi ne. Ni babban damuwata shine su Mother su dena jin hausinsa, su yi masa uzuri dan so ba shi da linzami. Dan haka uncle dan Allah kar ka bari Khairat ta cutu, idan har ba wata a ranka ka amince da ita dan Allah, tana sonka sosai za tai maka biyayya insha Allah, amma ni zan haɗa lefe kuma haihuwar fari sunana za'a saka, ko na Besty" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi duk da hawaye ne a fuskar ta.
Wani irin tausayinta ya kama Faruk, tabbas Nana 'yar halak ce, yayi mamamki da Mother tace masa Nana ce ta saka baki, da kuma maganar Hakimi sannan suka amince, yarinyar tana da sadaukarwa, kuma dagaske take son Sadik ba wasa ba, tabbas idan Sadik ya cutar da ita dan yana son wata Allah ze saka mata.
"Maman Sahal, naji dukkan maganganun ki, kuma insha Allah zan san abunda zanyi akan Khairat, and akan mijinki ki dena cewa kina son maso wani, Wallahi Nana Sadik yana sonki, so na gaske kuwa, ai kin riga kin gama da shi tunda har kika nema masa alfarmar a bashi dama yai Auren, wani babban abun burgewa da halayensa shine baya butulci Sadik, ba wai dan ɗan uwama bane no, ba goya masa baya nake ba, amma idan ki kawai Sadik alkhairi bayan shekaru yana sane a ransa, mutum ne me halacci sosai, dan haka ki sawa ranki ƙaddarar junanku ce a tare duk ku ukun, ki duba wani abu na ikon Allah, dokar gidan nan seka haɗa master's za kai Auren fari ma, amma shekarun sa sha bakwai zuwa sha takwas aka aura masa ke, kuka haifi Sahal, yanzu haka se nan da wata uku in Allah ya kaimu ze cika shekaru Ashirin dai-dai, amma kalli mata ta biyu za'a aura masa duk da tsananin zafi da Aƙida ta iyayenmu, amma wani ikon Allah, dr. Da ake cewa ya isa Aure yau kusan shekaru huɗu zuwa biyar da Aurensu ko ɓari matarsa ba ta taɓa yi ba, ni gani kalleni nima haryanzu ban Auren ba, nima idan nayi babu tabbacin in samu ƙaruwa, shine ƙaramin mu Amma Allah ku ya fara bawa ɗa, haka ya isa ya tabbatar miki da cewa rayuwa Allah shike tsarawa bawansa komai, kalli irin ƙiyayyar da Mother ta nuna miki a baya, fafur cewa tai se ta kashe Aurenku kin sani, duk da yadda yake akwai matukar shaƙuwa tsakanin Sadik da Mother, saboda yana sonki yai burus da umarnin ta be sake ki ba, saboda yana sonki, kuma da yake Allah baya ɗorawa bawansa abunda ba ze iya ba, cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya juya komai, Yanzu Mother jinki take kamar ita ta haifeki, kalli yadda yanzu take ta nan nan da ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, Allah yana tare da ke a Kowane hali, kuma albarkacin kin saka baki, ƙanwata ce ke da kika isa da yayanki, za duba maganganun ki akan Khairat"
Nana ta ɗago tana murmushi tana share hawaye tace "Nagode uncle, naji daɗin maganganun ka, sun bani ƙarfin gwiwa, insha Allah komai ya wuce, zan daure zuciyata in dubi Ni'imomin da Allah yai min, in yaƙi sheɗan da kishi".
A daidai nan Sadik ya shigo, ya tarar da Faruk da Nana a zaune, ga Nanan tana share hawaye, wani abune ya soki zuciyar sa ya tsuke fuska yace "ina son magana da ke"
Faruk yace "meye haka zaka shigo ba sallama?"
Nana tace "to ka gayamin a nan mana, naga Ai Yaya Faruk ne kawai a gurin".
"Cewa nai ina som magana da ke" ya faɗa a kausashe.
Tashi tai tabi bayan Sadik, suka shiga wani ɗaki ya kalleta yace "Me yake ce miki?"
Nana tace "shi wa?"
"Faruk"
"Me kuwa yake cemin, hira muke yi"
"Hira kukeyi shine har kike masa kuka yana rarrashinki?"
Nana tace "Haba to meye a ciki, Yayans fa nima"
"Yayanki me amma yana da iyaka, ni kaɗai na cancanci kiyi kuka in rarrasheki ba hurimin Faruk bane"
Nana cikin mamaki tace "Abun harya kaimu ga haka? Yau na fara hira da Faruk? Kasan ma akan me muke magana? Kawai zaka fara yi min faɗa?"
"Bana buƙatar jin koma menene, amma ki sani akwai iyaka tsakanin ki da shi" mamaki ne ya kama Nana, bayan ficewar Sadik, tun kan yai Auren kenan, idan yai Auren kuma wataƙila dukanta ze farayi, amma ai ba yau ta fara hira da Faruk ba, gaba ɗaya se jikinta ya sake yin sanyi sosai.
Shikuwa Sadik kishi ne ya kama shi, dan Nanan ba ƙaramin kyau tai ba, gashi duk in da ta shiga ƙamshin turare take, hakan ne yasa yaji wani haushi ya tokare masa wuya da ya ganta da Faruk.
Sadik ya cigaba da hada hadarsa, groups na 'yan makarantarsu ya ɗauka akan cewa Prince ze angwance da Farhan, kowa da abunda yake faɗa akan Auren nasu, wasu na son barka wasu na tofa abunda ba'a so, wasu suna ba su taɓa ganin Soyayar gaskiya ba irin wadda Sadik yakewa Farhan.
Sadik reception kawai ya shirya zeyi da abokansa, idan aka dawo daga ɗaurin Aure.
Sadik jinsa yake Tamkar ze sauke wani gagarumin nauyi da yake kansa, yakama gobe in Allah y kaimu ne ɗaurin Aure, se wani nishaɗi yake yi, har ze kwanta kawai ya tuna da wani hali Nana zata shiga, shifa ganinta yai kawai da Faruk suna hira yaji haushi, ita kuma ya zata ji, shi da ze tare da wata ya take ji a ranta, nan take nadamar abunda yai mata ya baibaiye shi, tashi yai ya zura rigarsa ya koma cikin gida, yana mitar da suna tare a BQ da ba wanda ya sani ze bata haƙuri, amma yanzu Mother ta hanata zuwa in da yake, wai se sun tare, haka ya tafi yana mita.
Dubawa ɗakin da take kwana yai amma bata nan, ya nufi sashin Mother, da Mother ya fara haɗuwa yace "Mother dan Allah ina Besty?"
Mother tace "ban sani ba"
Sadik yace "Mother Magana kawai zan mata dan Allah"
"Nace maka ban sani ba, ka ɓacemin daga ganina" tunani ya shiga yi ko dai ta gayawa Mother abunda yai mata ne.
A lokacin ya sake jinjinawa ƙoƙarin ta, tabbas kishi babu daɗi sam, ya koma BQ ya kira layinta amma a kashe, daga ƙarshe se haƙura yai.
Yau haka Sunusi ya wayi gari sukuku, kamar wanda aka yashe, ga wani irin ciwon kai da ya tashi da shi, ko sallar juma'a be samu ya halarta ba, unguwar su Farhan shiru, Kamar ba sauran mutane a unguwar, can ya fara jin hayaniya, alamar an dawo.
Haladu ne ya shigo ɗakinsu yana faɗin kai Abu na Allah, Allah me ƙudira sassauya lamuransa yadda ya so.
Sunusi yace "wai meyafaru ne?"
Haladu yace "kan in gaya maka, duk da bani da murya bari in rera waƙar mawaƙin nan Wayeka oho dai da yake cewa "duk yawan rabo, in ba kai kar ka ɗau salon jahili, in rabo ya tsago da kai, kuma abun ya tabbata da kai, Rabbu ne yace se da kai, in seda kai kawai se da kai.
in abun ya zo babu kai, Rabbu ne yace babu kai, in babu kai kawai babu duk duniya ba me sa da kai, Rayuwa wucewa take kawai, Rayuwa mubi a hankali kawai"
"Wai dan Allah ka gayamin meyafaru ka tsaya a kaina, ka saki murya kamar fitar tusa kana waƙa, kamar wani maroƙi"
Haladu yace "koma kamar zubar zawo ce, in dai saƙona ya fita ai shikenan, Allah ne ya nuna ƙudurarsa, yaron da kaiwa Farraƙu da Farhan, ashe shi zata Aura, an ɗaura musu Aure da sadakinsa dubu ɗari Wallahi".
A zabure Sunusi ya tashi zaune yace "wannan ɗan yaron?"
Haladu yace "shi fa, Allah ya nuna maka shike da komai, kai kaga tarin motoci na alfarma a unguwar nan, Allah ne yai yarinyar nan ba ta da rabon shan wahala dan dama sam baku dace ba, shiyasa tsabar taurin kanka da ƙauyanci yasa baka sameta ba.
Kai kaga yadda yaron ya ɗau wanka tubarkallah, se haskawa yake kai turaren da yake tashi a jikinsa shi da 'yan uwansa yadda kasan a kamfani, kai abun arziki na masu arziki ne, na matsiyata se Innalillahi wa Innalillahi raji'un".
"Dalla rufemin baki, waye matsiyacin ka bar wannan cika bakin, ka bari ka gani idan zasuyi zaman Auren cikin daɗin rai, har yau har gobe matata ce"
"Matarka ta ina, ba dai jahilci ya ja maka ba? Meye aibu dan ance kai gwaji, kuma ba kama mata gida a birni, ka tsaya kana cin zarafinta, Allah ya ƙara yanzu sedai kaga wani ya mora ba dai kai, ba ɗan cicif daidai ita ga gayu kamar ita ba kai ba , da seka kwana uku baka wake baki ba"
Haladu yasa Sunusi a gaba da cin mutumci, ƙarshe seda su kai faɗa baran baran uwaki ubaki, ga ciwon kai da ya addabi Sunusi.
Gidansu Farhan ya kaure da hayaniya, tare da shewa ana ta rangaɗa kuɗin Sadakin Farhan, ita Farhan duk jin abun take kamar a mafarki, wai ita aka ɗaurawa Aure da Sadik, ikon Allah.
Su Sadik suka shigo domin ɗaukar hotuna, Farhan ta saka farin lace me golden color, shikuma Sadii ya sanya fararen kaya, ya ɗora farar alkyabba me adon golden yayi kyau matuƙa.
Fuskar Farhan ba yabo ba fallasa, kallon Sadik kawai take ji take kamar almara, amma da ta tuna Abbas gaba ɗaya se taji Auren Sadik ya fita a kanta.
"You look so much beautiful, Alhamdilillah yau kin yadda son da nake miki ba RUƊIN ƘURUCIYA bane?" Wata uwar harara ta galla masa, Murmushi kawai yai be kuma cewa komai ba.
Duk da Sadik yana da girman jiki, dan idan aka faɗi shekarunsa wasu har mamaki suke, amma a haka Wasu suka dinga surutun Angon Farhan ɗin yaro ne, kuma a haka yana da mata kuɗi iyayenta suka bi suka ba shi 'yar su, 'yan baƙin ciki kuma na kwanan nan ze sakota dan duk abunda a kai ba dan Allah ba baya lasting.
Mother ta shiga bedroom ɗinta tarar da Nana a kwance ta zubawa guri ɗaya ido, gaba daya Mother tausayin Nana take, ta ƙarasa gaban gadon tace "ya baki tashi kinyi wanka ba? Yanzu 'yan ɗaurin Auren nan zasu dawo, su cika gidan nan ki maza ki shirya, kar a zo a ganki a yanayi na ba daɗi, ki daure bari in sa a kawo miki Abinci.
Nana gaba ɗaya tun da ta fuskanci an ɗaura Auren jikinta yai sanyi ƙalau, dan tun abunda Sadik yai mata akan Faruk gaba ɗaya ta sare da lamarin.
Jiki a sanyaye tai wanka, ta fito tana shafa abubuwan gyaran jikinta, me kwalliya ta shigo tai mata light makeup, ta saka wani danƙareren leshi da Mother ta sai mata, ta fito ras da ita tai kyau.
Mother ta shigo tana faɗin "Masha Allah, kinyi kyau sosai, yanzu abunda nake so da ke, zamu fita falo wasu basu sanki ba, yau zasu ganki, dan Allah ki daure ranki karki bayyanar da damuwarki, ki nuna komai normal kinji ko?"
Nana ta jinjina kai, Sannan tai gaba Nana na binta a baya, da yawa wasu se ranar sukaga uwar gidan Sadik, musamman matan abokan Abba, nan suka dinga yabata suna gata yarinya ƙarama kyakykyawa, lallai Sadik ya more.
Nana kam a nutse take komai, bayan sun gama gaisawa ta samu guri ta kame ta cigaba da sabgoginta.
'yan ajiksu Sadik sunje reception Sosai, suna cewa sun zata gagarumin party ze shirya musu, Sadik yace "da kenan, yanzu an girma, har da ɗa, ai dole a nutsu" har da wasu daga cikin malaman makarantar sunje bikin na Sadik.
Ƙarfe huɗu Mother tace azo wasu su raka Nana kan a kai amarya, Sadik ya shiga cikin hada hada sosai, ƙarfe biyar ya sauya wasu haɗaɗɗun kayan, ya shigo cikin gidan, ana ta tsokanar sa, ya wuce ɗakin Mother in da aka gama shirya Nana, yanzu wani material ne a jikinta, me wasu duwatsu kallo ɗaya Sadik yai mata yasan dauriya kawai take, tayi kyau matuƙa.
Ya shiga bedroom ɗin ya kalli wasu cousins ɗinsa yace "A bamu guri zan ga matata"
"Ikon Allah, lallai Sadik yanzu mu kake kora, wai kai magidanci?"
"Eh ya ranku?" Suka fita suka basu guri.
Se uban ƙamshi yake, ita ma Nanan haka se zuba ƙamshi take yace "Ina ɗa na?"
Nana jiki a sanyaye tace "ina ga yana gurin dr. Ko Anty Jidda".
"Idan ya ɓata a taro kya samo mana wani, tunda zuwa yanzu kin manta labor room" Sunkuyar da kai tai tana wasa da dogayen yatsunta.
"Besty, shekaranjiya na miki laifi, Mother kuma ta hanani shigowa, kawai kishi ne ya kamani ranar a kanki, amma kiyi haƙuri dan Allah"
Nana tace "ya wuce".
Ya ɗago haɓarta tana kallonsa, ya haɗe bakinsa da nata, seda ya shanye jambakin bakinta tsaf, sannan ya cikata, ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko wata leda, ya cire mata yari da sarƙar kunnenta, ya ciro na zinare ya sakamata, saboda tunda ya fara hidimar bikin nan, ba abunda ya ɗauka ya bata.
Ya kamo hannunta ya ɗaura mata abun hannu, Sannan ya saka mata zobe yace "ba zan gaji da baki haƙuri ba, Nasan ni me laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki yi haƙuri Nana, Kamar yadda nai miki alƙawari, insha Allah zanyi iya yina gurin kamanta muku adalci, Sannan ki tayani da addu'a in cika alƙawarin da nai wa Hakimi, Besty kina da wata kima a idona da duk juyin zamani ba zan zama butulu a gareki ba, ina sonki Husna, ki sa a ranki ƙaddarar mu ce a haka"
A hankali ta murza zoben hannunta tace "Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya" ta ƙarasa maganar hawayen da take maƙalewa suka fallasa zuciyarta.
Ta kai hannu zata goge hawayen, amma Sadik ya riƙe hannun yace "Cry besty, you deserve to do so, i know is painful cry Besty, amma ki tausayamin kar hawayenki su zame min fitina a rayuwa, Allah baya son hawayen Maraya" ta ɗaga ido tana kallon Sadik da shima idanunsa suka cika da hawayen.
Ta sa hannu ta goge nata hawayen tace "mayar min da jambakina da ka goge min" tai maganar cike da son basar da yanayin da suke ciki, ta ƙara da tabattar da Sadik baya son damuwarta musamman ta zubda hawaye.
Yai murmushi ya ɗakko jambakin yace "wanko fuskar, sena sa miki" taje ta wanke fuskar ta dawo, ta shafa hoda ya saka mata jambakin, ya buɗe ledar da ya shigo da ita, ya ɗakko alkyabbar mata, me matuƙar kyan gaske ya saka mata, ya ɗakko mata takalminta ta saka, Sannan ya riƙo hannunta suka fito shima sanye da tasa.
Suna fitowa matan ɗakin suka dinga rafsa musu guɗa, wasu na musu video ya dinga ratsawa da ita zuwa ɗakin Abba, Abba yana tare da wasu abokan nasa, Abba yai musu Nasiha da fatan alkhairi, akai ta musu Addu'a sannan suka fito.
Mummyn Khairat tace "Kai Sadik kufa muke jira, zamu rakata".
Sadik yace "Mummy kuje, ni zan taho da ita"
Mummy tace "yau kuma Soyayar uwargida ce ta motsa"
"Ai kullum soyayarta a motse take a raina"
A harabar gidan se da a kaita musu hotuna, sannan ya saka Nana a mota, Faruk yace su tafi ze kawo Sahal, Sadik ya