Showing 255001 words to 258000 words out of 259198 words
Chapter 86 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt
miki fyaɗe a bi mana hakkinmu, amma ya tabattar da ba abunda yai miki, sun bugar da ke dan suyi miki fyaɗe, amma hijjabinki kawai ya iya cirewa, da ya tunkareki se ya ji wani irin hucin zafi yana fitowa daga jikinki, kamar ze ƙona shi, haka suka ƙyaleki a gurin ba abinda su kai miki. Kuma nima na tabattar da hakan, tsaf na sameki da mutuncinki, Allah be ɗora miki wahala ba Farhan, da har mu mutu ban san me zanwa Babba in huce ba"
Ta kwantar da kanta a ƙirjin Sadik tana cigaba da hawaye, Shi kansa Sadik wani irin tausayinta ne ke ratsa shi, tabbas Farhan ta fuskanci ƙalubalen rayuwa daban daban, wanda kusan shine sila.
Sadik yace "amma meyasa kike yawon Hotel?"
Tace "Saboda iyayena, da 'yan uwana na shiga damuwa idan na bugu, shiyasa na zaɓi inje Hotel, in da ba wanda ze ganni in yi shaye shaye na in bugu ba wanda ya ji balle ya gani, amma nai dama sanin yadda na gurɓuta rayuwata, saboda shaye shaye sam ba mafita bane, musamman ga ni mace, duk mazan nan da suke bina, suka kashen kuɗi ne, saboda suna sa ran zan amince da su wataran, amma Wallahi ban taɓa zina ba"
Sadik yace "Shhhh, ni zan bada wannan shedar, ni na fara karatun, kuma na dawo na tisa shi na wanke allon" ya ƙarasa maganar yana kashe mata ido.
Wani irin sanyi ya dinga ratsa zuciyarsu lokaci ɗaya.
Can ta nisa tace "Prince, wai dan Allah meye a tsakaninka da Mubarak, da yake ta ƙoƙarin ganin se yai abunda ze ɓata maka, har ya sakoni a ciki?"
Sadik ya ɗanyi shiru sannan yace "Lokacin da aka kawo Mubarak Babba, yana Ss1 ina Jss3, ya zo da zafinsa makarantar, sedai ya tarar gani ƙarami sosai, amma shahararrene ni ana ji da ni, ina da ƙoƙari ina son gayu, kuma ina da sakin hannu sosai.
Se ya fara cewa ina burgeshi yana son yai abota da ni, kasancewar kowa nawane ya sa ban damu ba, muka fara abota da shi, abokina ne shi sosai, sena fuskanci yana shaye shaye, nai ta masa nasiha akan ya dena yana ɓata rayuwarsa ne kawai.
Kwatsam wataran ya zo min da wata mummunar magana, da ba zan taɓa mantawa ba, lokacin daga ni se shi a ajinsu, muna wata game a waya, ba kunya ba tsoron Allah ya gayamin wai sha'wata yake. Da farko ban kawo komai a raina ba, nake masa dariya se daga baya muraran ya nunan buƙatar sa, ashe riƙaƙƙen ɗan Neman maza ne, duk yana da ƙanan shekaru a lokacin, ya sanar min ba wanda ya san sirrinsa se ni, shima wani abokin babansa ne ya koya masa, kuma yake biyansa kuɗaɗe akan hakan, saboda ƙuruciya har sunan mutumin ya gayamin.
Hankalina ya tashi ƙwarai da gaske, saboda mutumin babban mutum ne, ganin ba zan yadda ba yasa Mubarak Babba ya so yai amfani da ƙarfin tsiya, kasancewar ya na da girman jiki sosai, a lokacin muna amfani da ƙararrawa ne ba jiniya ba, dan haka Allah ya temake ni, na ɗau ƙararrawa na buga masa a mararsa, na bar shi a gurin.
Ba wanda na gayawa, amma abun ya tsaye min, na dinga mamaki saboda ni ban taɓa sanin, namiji na ɗan uwansa namji ba, se a wannan ranar.
Mubarak se da yai wata biyu baya zuwa Makaranta, wai ba shi da lafiya, ranar da ya dawo, muka haɗu ya dinga min wani irin kallo da ban gane kansa ba, kawai naji zuciyata ta kasa nustuwa ina komawa gida na gayawa Abba komai.
Aikuwa daga Abba har Mother hankalinsu ya tashi sosai da sosai, Abba yace ba ze yuwu ba, ya shigar da ƙorafi gurin 'yan sanda.
Babba be san waye mahaifina ba, dan haka aka kamo shi, da shi da uban gidan nasa gaba da Mahaifinsa.
Seda suka kwan uku a gurin 'yan sanda Sannan Abba ya ɗauke ni muka je, aka sa na maimaita abunda ya faru, se da aka gayyato har shugaban Makarantar, Abba yace seya rufe makarantar, a kai ta bawa Abba haƙuri, da ƙyar ya haƙura a nan aka sanarwa da Abba cewa, ai dukan da nai masa a mara, baze taɓa haihuwa a rayuwarsa ba, dama duk ya gama lalata kansa, gurin aikata wannan mummunan aiki, yaro ƙarami da shi, amma yana wannan mummunan aiki, babban abunda ya ban mamaki be wuce yadda daga abokin mahaifin har mahaifin ba su damu da abunda Mubarak ɗin yai ba.
Abna yace se ya ɗaure Mubarak, a kaita bawa Abba haƙuri, shine a kai min iyaka da shi, kuma aka nemi in rufa masa asiri, aka kuma ce muddin aka kuma kamashi da irin wannan laifin se an hukunta shi, akai rufa rufa aka binne case ɗin. Kinji in da gabar mu ta samo asali, yai alwashin yadda nai masa illa, shima se yai wani abu da ze min illa, ban taɓa gayawa kowa ba se ke, kuma a binciken da nai da babansa talaka ne, sanadiyyar ba da Mubarak ɗin da yai ne, ake wannan harkar da shi yai wannan arzikin.
Jikin Farhan yai sanyi ƙalau, tace "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah yai mana tsari da mugayen mutane, thank God da Allah ya tsaremin mijina"
Sadik yace "godiya ta tabatta ga Ubangijin da ya tsaremin mata ta, ba tare da wani abu ya sameta ba"
Su kai murmushi a tare, se wajen azahar sannan suka sake wanka, suka sha kwalliya, suka shiga kitchen tare, Farhan ta kalleshi tace "Prince, dan Allah ka ɗakko min Sahal mana"
Sadik yace "kai gaskiya bana son motsawa daga nan zuwa can in barki"
"Dan Allah ka ɗakko min shi, baka san yadda nake son yaron nan ba ne"
Sadik yace "to kamar yaya kike son babansa?" Yai maganar yana saka fuskarsa a wuyanta.
"Ina son babansa sosai, kuma ina son ɗana ma sosai"
"Ni zakiwa wayo?"
Farhan tace "dan Allah kaje ka ɗakko min shi, Kafin ka dawo na gama girkin" da ƙyar ya iya ƙyale Farhan ya tafi ɗakko Sahal.
Sadik ya tarar Mother ta fita, Faruk ne yake rainon, Sadik yace "kai aka bari da rainon?"
Faruk yace "to rainon Sahal ɗin har wani aikin wahala ne?"
Sadik yace "lallai kam, lallai kuna son Abban nan sosai, gaskiya kaima ka yunƙura mana, mu tarawa Mother yara da yawa"
Faruk yai murmushi yace "kan inyi Aure, na san amaryarka ma ta juye ita ma, ƙarami da kai se kasada".
Kwashewa da dariya Sadik yai yace "kaga ni fa Sahal na zo ɗauka, Farhan ta dameni in zo in ɗakko mata shi".
"To a dinga yi ana tausayawa marainiyar ƙanwarmu, naga akan wannan kake ta rawar kai".
Sadik yace "wai dan Allah waye ya gaya muku bana son Nana? Wallahi ina son ta sosai, kowacce akwai mazaunin da ana ajiye ta, kowacce tana da matsayi na musamman a zuciyata"
Faruk yace "hmmm Allah ya sa, ka san ni tunda Nana ta ɗarsa min son Khairat naji kamar ina sonta, na fara jinta a raina sosai"
Sadik yai murmushi yace "kai amma na tayaka murna, Soyayya ai duniya ce, wanda baya Soyaya da me yake more rayuwa, inji wani mawaƙi"
Haka suka taɓa hira, sannan ya ɗau Sahal ya tafi gida.
A falo suka baje sukai salla suka ci Abinci, suna hira Farhan ta haɗawa Sahal madara ta na ba shi, Nana ce tai sallama a falon, Nana na shigowa Farhan tai saurin tashi daga jikin Sadik.
Nana ba ta nuna taga wani abu ba, ta zauna tana cire safarta, Sadik yace "Sannu da zuwa besty, ya school ɗin?"
"Alhamdilillah" shine kawai ta faɗa, ta cigaba da abunda take.
Farhan tace "Sannu da zuwa"
"Yawwa Sannu da gida, ɗakko Sahal ku kai kenan, Allah ya sa be takura miki ba"
Farhan tace "A'a ai uwa ba ta gajiya da ɗanta".
Nana tai murmushi tace "lallai kam"
Sahal kuwa ƙoƙarin rarrafawa yake ya tafi gurin Nana.
Nana ta miƙe tsaye tace "kai daga daowowata zaka fara wani kuka a ina ka sanni".
Kuka Sahal yake, a lallai se yaje in da Nana take.
"Kai lallai ma yaron nan, ga madara nan an baka ka sha ka ƙoshi, amma se ka zo ka addabamin, aikuwa ba ka isa ba" tai maganar kamar ta na yi da sa'anta.
Sadik yai murmushi yace "Allah ya shiryeki Besty, ya nunan lokacin da zaki girma"
Sahal ya biyota da rarafe, ta ɗau jakar makarantar ta da gudu, tai part ɗinta.
Ba Sadik ba Farhan kanta abun dariya ya bata, ta tashi ta ɗakko Sahal tana rarrashinsa.
Abunda yake bawa Farhan mamaki, Sahal ma Besty yake ƙoƙarin kiran Sadik da Nana, a gwarancimsa na yara.
Farhan tace "wannan sunan shi Daddy kaji ko" tai maganar tana nuna masa Sadik.
Sadik yace "ai yaron nan ba yadda ban ba yace Daddy ya ƙi se besty yake so shima ya dinga cemin".
Farhan tai dariya tace "to ai ku ɗin ne kamar yayyansa ba iyayensa ba" Sadik yace "Lallai kin ci mu wasa".
Rayuwar gidan Sadik ta cigaba da tafiya, yana iya ƙoƙarin sa gurin ganin kowacce ya kula da ita daidai da buƙatar ta, Farhan ma ta koma Makaranta, dan ita har taje Ss3, Nana kuma na Ss1, shi kuma yana zuwa ABU zariya, duk ƙarshen wata yake zuwar musu, sedai sam haryanzu Mother ba ta maraba da Farhan.
Soyayyar da Farhan ke nunawa Sahal, da kuma zuwan da Inna tai, tai musu nasiha sosai yasa Nana fara sakkowa daga kishin da take, Inna ta nuna musu su haɗa kansu su zama kamar 'yan uwa, se rayuwa ta fi yi musu daɗi ganin hakan ya sa ita ma Farhan ta sassauta na ta kishin.
Sadik baya nan yana makaranta, Farhan ta na ta rashin lafiya, Nana ce ta lura da hakan tace "Nikam Mummyn Sahal lafiyarki kuwa, duk kin rame haka".
Farhan tace "Wallahi besty zazzaɓin dare nake, ga ciwon ciki na rasa abunda yake min daɗi".
Nana tace "Ai ba kya zauna da ciwo ba, bari in wa Sabo direba waya, ya zo muje in rakaki Asibiti" Farhan ba tai musu ba, sedai suna zuwa Asibiti, gwajin farko aka ce ciki ne da ita, har watanni biyu.
Ita Farhan ma kunya ce ta kamata, Nana kuwa tausayi Farhan ɗin ta bata, Saboda ta san ɗawainiyar ciki akwai wahal, tun da suka dawo gida kuma laulayi ya saka ta a gaba, koma a ci se amai, Nana ce keta ɗawainiyar kula da Farhan, har mamaki abun ya dinga bawa Farhan, Nana ba dai tausayi ba.
Nana ca ta sanarwa Sadik halin da ake ciki, murna Kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha.
Ranar da ze dawo, Nana tace "Princess be kamata ya dawo ya ganki a haka ba, duk kinyi wani iri, ki wanke gashin ki, se in miki stretching.
Haka kuwa aka yi, ta gyarawa Farhan kai, ta sakata a gaba akan Lallai ta ci Abinci, ba ta son a haifo musu yaro ramamme.
Suna cin abinci Nana na bata labarin zaman London da sukai, da irin wautar da ta dinga yi, musamman lokacin yace ta sha Nonon karya.
Sosai suke dariya, ta dinga bawa Farhan labarin yadda Inna take sata a gaba, akan kula da kanta da yanayin rayuwar da tai tare da kakanninta.
Se taga jikin Farhan yai sanyi, Nana tace "meyafaru, ko na faɗi abunda ba kiji daɗinsa ba?"
Farhan tace "A'a, kawai dai kin tunan wani abu ne, ke gashi ba ki rayu da iyaye ba, amma kin samu kyakkyawar kulawa, Besty har ga Allah ni na ajiye batun wani kishi, ban ɗauke ki kishiya ba, se 'yar uwa shiyasa zan gaya miki wani abu da ya shafi rayuwata, kinga ni ga uwata ga ubana, amma mahaifiya ta sam bata damu dani ba, har gara ma yanzu akan da, kinga Inna itama ba fulatana ce, amma kimga halayarta ta sha bamban da ta Ummana, abubuwa da dama ban san su ba, har sonake in ga mutum da mamansa kamar ƙawaye, kinga Inna ta tsufa, Allah ya maye miki da Mother, rashin kulawar uwa ba daɗi" Nan ta ɗan ɓincinawa Nana wani abu na daga Rayuwar ta.
Nana arhar hawaye, kawai ta kama kuka, ita ma Farhan ba ta da zaɓin da ya wuce tai kukan, Sahal ya tsaya yana binsu da ido.
Sadik ne yai sallama ya dawo daga makaranta, amma ya tarar da su a zaune suna kuka, se yai turus, ya ƙaraso yana tambayar su ko Lafiya.
Nana tace "bakomai hira muke"
"To kuma hira se ku hau kuka, wace irin hira ce haka?"
Farhan tace "Sirrinmu ne ai, ba se kaji ba"
Sadik yace "iyeee, to Allah yasa ba laifi nai muku ba, kalli kun sa ɗanku a tsakiya kuna kuka, wannan abun kunya da yawa yake. Yai maganar yana ɗaukar Sahal da jin daɗin yadda ya gansu.
Babban abunda ya ƙara burgeshi shine yadda Nana ke kiran Farhan Princess ita kuma take kiranta Besty, hakan yai masa daɗi ƙwarai da gaske.
Lilly kuwa a ss2, tai graduating, Kamar yadda Mummynta ta bata shawara, haka ta amince dan ba ta son sake aikata abunda za tai dana sani kamar yadda take yi a yanzu, dan haka ta bi shawarar Mummynta don Auren wancan soja shine rufin Asirinta.
Gashi ya manyanta, amma sonta yake kamar ze haɗiyeta dan so da ƙauna, dan haka ta amince ya kawo kuɗi aka tsayar da Ranar Aurensu, yayin da Sir Nazir yake can gidan yari.
Khairat ma Faruk ya kai kuɗin Aure, an saka rana tana yin Candy za'ai biki, tare da walimar graduation ɗin ta.
Ya haɗa lefensa na gani na faɗa, Sadik yace su shirya suje su gani.
Farhan se fartabar zuwa gidan su Sadik take, saboda Mother har kashedi tai mata, akan kar ta ƙara zuwar mata gida.
Se dai yau ma bata canza zani ba, dan tunda sukaje Mother tai mata wani irin mugun kallo, musamman da ta ga alamar ciki a jikin Farhan, ta dinga zazzaga mata masifa da baƙaƙen maganganu, Nana da Faruk na niyyar su dakatar da ita, amma suma ta ƙare musu, ba shiri Farhan ta miƙe ta nufi hanyar fita, Sahal ya bita yana kuka, ta sa hannu ta ɗauke shi tana share hawaye ta tafi.
Nana ma kuwa ta saka kuka, har da sheshsheƙa, Mother ta buɗe baki tana kallon ikon Allah, da mamakin sakarci irin na Nana.
Nana tace "dan Allah Mother ki dena zaginta, Wallahi tausayi take bani, bana jin daɗin hakan, tana da kirki sosai".
"Rufen baki, ko in zo in mangareki shashasha, wannan ɗaukar ɗan naki da take ne yasa kike wannan rawar kan"
Sadik da ke zaune Mother tai faɗanta ta gama, har Farhan ta tashi ta tafi bai motsa ba, shi kansa Faruk be ji daɗin abunda Mother tai.
"Kai kuma dama baka kake so, ga mata nan ka tara, yau Wannan da ciki gobe waccan da ciki shine babban burinka, kaje kai tayi".
Abba da ya shigo Yanzu ya shiga tambayar Lafiya kuwa, ya gansu jingum jingum ga Nana na ta uban kuka.
Sadik ya tafi gaban Mother ya durƙusa yace "Mother, idan rabuwata da Farhan, ze sa ki samu kwanciyar hankali, insha Allah daga nan idan na bar nan, zan sawwaƙe mata, dan ba ta cancanci a cigaba da maita haka ba saboda ni, amma kan nan bari in faɗa muku dalilin da ya sa na dage, na Auri Farhan duk da ba kwa so, ban sani ba ko zaku fahimce ni, Mother Farhan Yarinya ce ta gari me tarbiyya wadda kowa ze so haɗa zuriya da ita, sedai ni da tarbiyya tai min ƙaranci na kutsa rayuwarta, na liƙe mata se da ta fara sona, Mother zina ce kawai ban aikata a rayuwata ba, na tafka ta'asa iri iri......
Nan ya fayyace labarin soyayyar su da Farhan, ba ɓoye komai ba, har rayuwar da tai bayan rabuwarsu, zuwa Aurensu a yanzu, ya ɗora da cewa "a yanzu haka Mother na fara tara zuriya,kuma nasan duk abunda ana aikata akan ɗan wani se anwa nawa, na auri Farhan saboda ina sonta, kuma saboda ina fatan Aurenta ya zama silar Allah ya yafe min kuskuren da na tafka, idan baki ysdd6ba kuma ku tambayi Sabo direba ya san wasu abubuwan, amma tun da ba kya so, zan rabu da Farhan, in dai hakan ze zama masalaha" ya ƙarasa Maganar hawaye na zuba daga idonsa.
Gaba ɗaya ɗakin yai tsit, saboda abun ya bawa kowa mamaki da tausayi, asje Sadik ne ƙwallon se a hankali, shine silar komai.
Nana ta taso ita ma ta zo gaban Mother ta durƙusa tace "Mother na, ke uwace, kuma ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, be kamata mata 'yan uwanmu su dinga shiga matsala saboda mu ba, bayan muna iƙrarin ciwon 'ya mace na 'ya mace ne ba, dan Allah a karo na biyu, ina nemawa Abban Sahal alfarma, dan Allah kiyi 6ya rayu da Mummyn Sahal, tabbas gaskiyar ki me ɗa wawa, son da takewa ɗa na da kyawawan halayenta ya sa nake sonta nima.
A wannan gaɓar nice ƙaddararsu da na raba wannan Soyayya, dan haka be kamata kowa ya goyan baya ba, ina son Sadik, amma ina kwatanta kaina idan ni na tsinci kaina a matsayin da Farhan take, dan Allah Mother karki bari Auren nan ya mutu, dan girman Allah"
Kuka Nana take sosai tana riƙe ƙafar Mother.
Abba ya nisa yace "Allah sarki Nana, halinki irin na marigayi Hakimi, ya yadda ya rasa na sa farincikin saboda wani ya samu, shiyasa ya samu soyayyar mutane.
A karo na biyu kenan tana nema maka alfarma, lokacin da kake neman Auren nan, haka ta saka gwiwowinta a ƙasa akan mu bari kai Auren nan, a karo na biyu tana nema maka wata alfarmar, tabbas idan ka wulaƙanta Nana, kanka ka wulaƙanta.
Abba "ya za'ai in wulaƙanta ta, wallahi Abba ina son Nana, so na gaske"
Abba yace "kaje kar ka rabu da matarka, Allah ya kyauta ya tsare gaba, ya ƙara haɗa kanku"
Mother kiyi magana, Sadik yai maganar yana kallon Mother.
Mother tace "Ai kuma ba ni da ta cewa, ai ban san haka abubuwan suka gudana ba, Allah ya kyauta"
Abba yace "ɗau matarka ku tafi gida"
Sadik ya sa Nana a gaba suka bar falon, suna tafe a mota, ya kasa magana, se riƙe hannunt da yai cikin nasa, yana jin wani irin sonta a ransa, ga wat kima da ta ƙara yi a idonsa.
Sukaje gida suka tarar Farhan, ta hsɗa Akwatinta, abun tausayi ta goya Sahal a bayanta, zata tafi.
Da sauri Nana ta karɓe Akwatin, Sadik yace "Ina zaki?"
Cikin kuka tace "gida