Showing 183001 words to 186000 words out of 259198 words

Chapter 62 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

nake an fasa ɗaura Auren"

Umma ta janyo Huzaifa gefe tace "ka gayamin tsakani da Allah, ka san ba na wasa da kai ko?"

Yace "wallahi Umma ba ƙarya na ke gaya miki ba, an fasa ɗaurin Auren nan"

"Huzaifa ko dai za'a ɗaura an jima?"

"Wallahi Umma fasawa a kai"

"Amma saboda me?"

Huzaifa yace "Nima ban sani ba, se dai in su Abban sun dawo"


Please manage, bana jin daɗi ne.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.



Not Edited!


Sam Huzaifa ya ƙi gayawa Umma dalilin da ya sa aka fasa auren Farhan, gaba ɗaya hankalinta ya tashi, ga gida a cike da mutane.

Ana haka se ga su Abba sun dawo, Abba ji yake tamkar ƙasa ta tsage ya shige saboda kunya, ya rasa da wani ido ze dubi wannan al'ummar da su ka tara, ga mutane har an fara ƙananun surutai, saboda yadda Sunusi ya dinga miyagun maganganu akan Farhan, wajen ɗaurin Aure.

Wasu daga mutane suka goyi bayansa, cewar suma sun sha gani ana sauketa a mota, kuma falla fallan motoci na alfarma.
Ya yin da wasu suke ƙaryata abun da Sunusin ya faɗa, suna yabon halayen Farhan, ɗin na tarbiyya da girmama mutane.

Su Abba na dawowa, Abba ya wuce ɗakinsa, dan baze iya haɗa ido da mutane ba.
Ba kunya Malam Zakari yai musu bayanin cewar an samu mishkila, da haka an fasa wannan biki, abinci da aka dafa, kowa yaci sadaka, Allah ya zaɓawa yarinya Mafi Alkhairi.

Nan aka shiga salati da salallami, gashi Malam Zakari mutum ne me kwarjini, dan haka aka rasa wanda ze tunkare shi ya tambaye shi dalilin hakan.

Dangin Umman Farhan, sukai kanta da tambayoyi "Maryamu dan me za'a fasa Auren nan? A tara wannan jama'a haka kuma ace an fasa, lallai ku mutan birni ba kwa gudun abun Kunya, mu dai kin san da a garinmu ne, ba za'ai haka ba, mu zuriyar mu ba a taɓa wannan abun kunya ba , se akanki da 'yar ki. Yo koma mene ya faru ai ba a fasa biki ba, a rufa a ɗaura Aure haka nan, amma kawai ace an fasa"

Sosai Umma take kuka, dan ba ta da amsar da zata kare kanta da shi a gurin 'yan uwanta.

Malam Zakari ya shigo yana ƙwalawa Umma kira, Umma ta fito ido duk hawaye.

Yace "ai ba kuka yakamata ki ba, ki gode Allah da Allah be sa an bawa wannan shashashan auren 'ya ba, ina ita Farhan ɗin take? Ta zo muna son ganinta ni da babanta"

Umma ta goge hawaye tace "ta na can a ɗaki, ni ban san abinda ya sameta ba, amma malam meyasa aka fasa auren nan mun tara mutane?"

"Kinga kar ki damu, da wata wahalar gara wata, yaron nan mutumin banza ne mara ɗa'a, muje ina yarinyar take"

Umma na sheshsheƙar kuka, ta wuce gaba ta buɗe masa in da Farhan take.

Ana buɗe ɗakin, ta zabura ta shige cancikin saƙo, ta takure kanta sosai.

Malam Zakari ya ƙarasa shiga ɗakin yana faɗin "Subhanallah, Farhan lafiya kuwa?" Farhan ta ɗago jajayen idanunta, ta sauke akan Malam Zakari, wanda tuni idanun na ta suka juye, kamar harare garke.

"Meke damunki?"

"Ni..Ni ku ƙyaleni dan Allah, du...duuuk ku fita ku barni, ba na son ginin nan ya faɗo mana a ka..... Allah ya sa ma dai, ya faɗo mana a ka, kowa ya huta"

Malam Zakari yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, me Yarinyar nan take haka kamar maye?"

Umma cikin kuka tace "Nima ban sani ba, na kasa gane kan wannan lamari"

Gida kam tuni labari ya ba zu, ya cika unguwa cewar an fasa wannan biki.

Sunusi kuwa se da ya ga da gaske, an fasa wannan Aure sannan ya shiga hankalinsa.

Yace wa malaminsu "Malam dan Allah aje a basu haƙuri, ina son Yarinyar nan Sosai wallahi"

Malam Labaran yace "wallahi ba zani ba , lokacin da nake kwaɓarka akan maganganun da kake ai ba ka saurareni ba, kai ga ka kuturu Sarkin zuciya, ba irin halaccin da iyayen yarinya nan ba su maka ba, amma ka rufe ido ka dinga rashin mutunci kana ciwa 'yar su mutunci, ba dani ba ba in da zanje"

Haladu yace "Sunusi ba tun tau ba, na sha ba ka shawarar ka rage wannan saurin fushin, amma ka ƙi gashi nan a banza ka janyo kan ka,da tuni Allah ya rufa maka asiri,kai wuf da zuƙieƙiyar Yarinyar nan, amma baƙar zuciya da taurin kai ya janyo maka.meye a ciki dan ace ka je kai gwaji, in da kasan ka na da gaskiya ai ba abun damuwa ba ne, kuma kamar yadda suka faɗa, 'yar su ba kalar ƙauye bace, ba zata iya wannan wahalar ta ƙauye ba, ka na da kuɗi ka kama mata gida ka ƙi, gashi nan kaiwa kan ka, sedai nan gaba ka ga wani yana morarta, dan kai dai ta maka nisa wallahi"

Sunusi yace "inji uban wa, wallahi yadda ban Aura na mora ba, ba bu me mora, sedai kowa ya rasa, za su gani ai"

"Za su ga me? Ka ga Sunusi ka ƙyale mu su 'ya ta huta"

"Wallahi Haladu ba me hutawa, yadda aka hana ni Aurenta haka za su zauna da ita, dan ba zan bari kowa ya aureta ba, na dinga ɓata lamura kenan, har se sun gaji sun bani mata ta"

"Amma kuwa ba ka da imani, ba ka da mutunci duk halaccin da su kai maka?"

Tsaki Sunusi yai yace zuba ido ka ga.

Nana ta dawo daga makaranta, ta tarar da Sadik a gida, sedai a fuskar sa kawai ta lura kamar wani abu na damunsa, ko dai duk saboda laifin da nai masa ne? Ta tambayi kanta.

Sallama tai, ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

Tace "Friend na dawo" ba kulata ba balle yai mata sannu da zuwa,haka ta wuce ɗakinta.

A ɗakin ta tarar da kayan siyayyar da sukai jiya a kanti, ba ta bi ta kan kayan ba, ta cire kayan jikin ta tai wanka tai sallar azahar, Sannan ta fito falo.

Sadik yana nan a in da ta bar shi, take Kitchen ta ɗakko bredi, ta dafo tea ta dawo ta zauna.

"Friend ka ci Abinci kuwa?" A wannan karon ma be tanka mata ba.

A karo na biyu cikin damuwa tace "Dan Allah kayi haƙuri, na ga fushi kake da ni, dan Allah kayi haƙuri ba zan kuma ba"
Miƙewa yai ya nufi ɗakinsa, ya bar mata falon, dan ya gaji da jin surutun  ta.

Nana ta shiga damuwa sosai, saboda yadda ta ga gaba ɗaya ya canza, duk saboda abun da tai masa, ba ta zaci abunda tai ɗin ze sa Shi fushi haka ba.

Har dare ba ya shiga harkarta, a ɗaki ya gama wuninsa ko fita be ba, kuma ba ta ga alamar ya ci Abinci ba, shi ko Sadii Bayan haushin Nana da yake ji, harda matsananciyar damuwa da be san dalilin ta ba.

Nana harta fara shirin kwanciya, tai tunani a ranta tace "Ni, Nana idan ya kwana da yunwa duk laifi na ne, saboda ni na ɓata masa rai, amma ai nace yai haƙuri" sakkowa tai daga kan gadonta, ta saka hijjabi ta tafi ɗakin Sadik.
Yana zaune akan gadonsa, yai tagumi da hannu ɗaya ya zubawa guri ɗaya ido ko ƙiftawa ba ya yi.

Tai Sallama amma be amsa ba, kai tsaye ta tafi gabansa, ta durƙusa akan gwiwowinta tace "dan Allah dan Annabi Yaya Sadik kayi haƙuri, ba zan kuma ba, dan Allah ka dena jin haushi na"
Shi mamaki ma ta ba shi, bil haƙƙi har ranta haƙuri take ba shi.

Ya fuske yace "karki sake zuwa in da nake, ki rayuwar ki inyi tawa, haka kurum kika ɗagamin hankali na dinga nemanki, kuma dan baki da Kunya, kika dinga gayan magana, wai kin barni da mata inje in ta taɓa su ko?"

Ta ɗan tura baki tace "kayi haƙuri, amma ai gaskiya na faɗa maka, se ka je kai ta taɓa mata, alhalin kuma ka san ba kyau, kuma ni haushi nake ji"

Be san lokacin da yai murmushi ba yace "to meyasa kike jin haushin?"

"Bana son a rubuta maka zunubi, Allah ya kamaka"

"Hakane, kina sona kenan?"

Da Sauri ta ɗago kai tace "taɓ a'a wlh"

"To ai kishi na kike"

"Meye kishin?" Ta tambaye shi ta na tsare shi da ido"

Sadik yace "shikenan, tun da ba ki san meye ba, yanzu ke dai burinki in dena taɓa mata ko?" Ta jinjina masa kai da confidence ɗin ta.

Yace "shikenan, ɗakkon wayata akan mirror"

Ba tunanin komai, ta ɗakko ta kawo masa, tana miƙo masa ya sa hannu ya riƙota, ya Ajiye wayar a gefe, cikin zafin nama ya cire hijjabin jikinta,ya kwantar da ita akan pillow, ya ɗora kansa akan ƙirjinta.

Tsoro ya baibaye Nana, tace "Sadik meye haka? Dan Allah ka bari"

Hankali kwance Sadik yace "ai kince in dena taɓa mata ba kya so, ni kuma ba zan iya rayuwa ba tare da nayi hakan ba, kinga se ki maye min gurbinsu"

Cikin rawar murya, da janyo numfashi Nana tace "Wallahi babu kyau, Inna ta hana ni, wallahi tace idan na bari namiji yana taɓani zan lalace, dan Allah ka ɗagani, naji ka cigaba da taɓa matan"

Yai murmushi, tare da saka hannunsa akan cikinta yace "so kike a rubutan zunubin taɓa mata?"

Tana kuka tace "Au so kake a rubuta mana tare ni da kai shiyasa kake taɓa ni, wallahi idan Inna ta san abunda nake kenan, za tai fushi da ni Sosai"
Hawaye take Sosai, Kamar wadda za'a yanka, Sadik yai banza da ita, ya sake kwanciya sosai a jikinta, a hankali yaji yana samun sauƙin wannan damuwar da ke ta ɗawainiya da shi tun safe.
Se da jikin Nana yai laƙwas, bakinta ya mutu, ajiyar zuciya take tana jujjuya ido.
A hankali ya ɗaga ta, ya nufi banɗaki, tana ganin ya shige toilet, ta miƙe ta sakko daga kan gadon tai waje, sedai taji gaba ɗaya jikinta ya mutu, se mita take da ƙananan maganganu ƙasa ƙasa.



A can gidan su Farhan kuwa, Farhan ce zaune tai shiruu, duk da haryanzu a cikin maye take, amma ta na iya fuskantar abubuwan da ke faruwa, sedai ta kasa gane hakane a zahiri, an fasa Aurenta da Sunusi ko kuma mafarki take.
Gefe ga Umma na ta uban kuka, kamar ance mata Farhan ce ta mutu, a ganinta dalilin da ya sa aka fasa Auren, ba wani dalili ne da ya taka kara ya karya ba.
Abba kam ya rasa abunda yake masa daɗi, dan tabbas Farhan maye take a wannan lokacin.

Malam Zakari yace "Umman Farhan, haƙuri za kiyi, duk abunda kika ga ya samu bawa to yana rubuce a cikin kundin ƙaddararsa ne, ki sa a ranki, da ma Allah be ƙaddara mijinta bane"

Cikin kuka Umma tace "Baban Huzaifa, kamar ni ka ɗai na taɓa haihuwar 'ya a rayuwa ta, daga wannan se wannan, yarinyar nan duk wani salo da za ta janyo min abun kunya, da abun faɗa ta sanshi, kuma za ta aikata. Kalli fa maye take Ranar ɗaurin Aurenta, kuma Sunusi ba ƙarya yai ba, na kamata da wayar da saurayi ya bata, zamanta a gidan miji ba shi yafi Alkhairi ba, yanzu ta samu lasisin aikata abun da ta ga dama, na rasa wannan wace irin kangararriyar yarinya ce!"

Kalmar kangararriyar yarinya ta daki zuciyar Farhan, fiye da kima, ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Ummanta, yau ita Umman take dangantawa da kangararriyar yarinya, tabbas ko da ace mafarki take abubuwan nan da suke faruwa, har ta koma ga Allah ba zata manta wannan kalma ba.

"Ashsha, ya kike kamanta 'yar da kika haifa da kangarewa, duk biyayyar da Yarinyar nan take da shi, dan an samu wannan akasin se ki danganta ta da kangara? Kin san meye kangarewa kuwa? Kar ki sake wannan kuskuren, da kika ganta da wayar saurayi wane mataki kika ɗauka? Dan Allah kar wannan abun ya sa ku yiwa Yarinyar nan baki, dan yarinya ce me biyayya a baya, kamata yayi aji meyasa tai shaye shaye, garin yaya a kai ta rasa lokacin da zata sha wani abu se ranar ɗaurin Aurenta, ni anya ma kuwa tana son Yaron nan?"
Daga Abba har Umma ba wanda yave uffan, se ma Umma da tace "shikenan, tun da haka ta zaɓawa kanta, taje ta ƙarata, ga gidan nan ta zo tai ta zama muna jerawa, tana kallona ina kallonta, ai duniya makaranta ce"

Umma ta tashi fuuu ta bar ɗakin, Abba ma bece komai ba ya tashi ya bar ɗakin, haka kowa ya fice aka bar Farhan.

'yan biki duk aka watse, ana ta gulmar ashe ma Yarinyar lalatacciya ce, bin maza take ga shaye shaye tana yi.

Lamarin ba ƙaramin dukan Hajiyar Abbas yai ba, ta yi mamakin yadda aka ce wai Farhan tana shaye shaye, da yake ran ɗaurin Auren ba ta gari, se da yamma ta dawo, kan ta shirya ta shiga gidan su Farhan, har gida aka sameta aka bata labarin abunda ya faru, da yadda aka fasa Auren Farhan ɗin.

Ita kanta Hajiya, ta lura da yadda Farhan ke cikin damuwa, amma iyayenta ba su maida kai, dan gano meye damuwar ta ta ba, su dai kawai su mata Aure, dan haka dama dole ta nemawa kanta mafita, wannan abun dama Abbas yake ta ji, masu irin halin Farhan in damuwa tai musu yawa, a ƙarshe dole su nemawa kan su mafita.
Baƙinciki ya hana Hajiya ko zuwa gidan su Farhan, ta sha takaicin yadda sunan Farhan ya ɓaci, gaba ɗaya unguwa ta ɗauka, an innocent kid like this, gashi mutane ba sa wa kansu adalci, suna hukunci ne da iya abinda idonsu ya gane musu.
Tabbas, ba dan abun ya zo a ƙurarraen lokaci ba, kuma ba tattauna da dangin baban su Abbas ba, da ba abunda ze hana tace a ɗaura da Abbas, dan ba ta yanke hukunci akansu se da sanin dangin mahaifinsu, saboda a tsaye suke a kansu.

Nana ko haɗuwa taƙi yadda suyi da Sadik, suka koma wasan 'yar ɓuya, da ta ji motsinsa a falo, ba zata fito ba.
Jin shiru ya sa ta ɗauka ya fita, yana kallonta ta window ɗakinsa, tan sanɗa, ta shiga Kitchen.
Se da ya bari an ɗau lokaci da shigarta, ta sakankance, sannan ya fito ya risketa a Kitchen ɗin.

Tana ganinsa ta hau ƙwalala ido, ya shiga takowa a hankali, tana ja da baya har suka ƙure bango, ya kalleta yace "Yau ni zan gyara ɗakin nawa?"

Ta tura baki tace "zan gyara, amma se anjima"

"Wace anjima kuma? Azahar ce fa Yanzu, tun safe yakamata ki gyaramin ai.
Amm an gayyacemu cin Abinci da yamma"

Nana ta kalleshi tace "Ni gaskiya ba zani ba"

Yai ƙasa da murya yace "idan naje ni kaɗai gaskiya zan taɓa mata"

Tace "Allah yana kallonka"

Yai murmushi ya sunkuyo daidai da tsawonta, ya sa hancinsa a wuyanta, seda ta saki ludayin da ke hannunta, ta ƙanƙame jikinta, tana jin wani abu da ba ta san menene ba.

Sadik yana kallon reaction ɗin ta, yace "Mijinki yaro da shi, amma se....." Se kuma yai shiru yana wani miskilin murmushi.

"Abincin ze ƙone fa" ta faɗa a daƙile.

Shiru yai bece komai ba, ji tai abun nasa yana zarce hankalinta, ta dage iya ƙarfinta ta kurma ihu, a gigice ya cikata yace "meye haka?"

"Wallahi ni ba 'yar iska ba ce, da zaka dinga min irin wannan abubuwan'

Tsaki yai a ransa yace "wannan kwantacciyar Yarinyar ba ta san abunda ya halatta a aure ba ne?"

A fili yace "karki wuce ƙarfe huɗu ba ki shirya ba, idan ba haka na tafi ba zan dawo ba se gobe in Allah ya kaimu"

Ita Nana dan ya tafi ya kwana ba damuwar ta bace, dan yanzu ta saba da zaman kaɗaici, jin yace idan yaje ze taɓa mata ne ya sa ta ƙuduri se ta bishi.

Ƙarfe huɗu ta shirya suka fita, wani katafaren gurin cin Abinci sukaje, gurin ya haɗu Sosai da sosai.

Wani ɗaki ya ja Nana suka nufa, a nan ta tarar da Abokansa da suka taɓa zuwa gidan su, nan suka shiga gaisawa, abun takaici har da Matam duk se da Sadik ya bi ya gaisa da su.
Nana se hararsa take, amma yaƙi ko kallonta.
Nan wasu suke tambayar sa, wannan me aikin ta sa ce, yace tsokanar ta yake Ranar, amma ƙanwarsa ce, suka miƙawa Nana hannu dan su yi musabuha, aikuwa ta miƙa wa wanda ya miƙo mata hannu suka gaisa, na biyun ma har ta kai hannu za su gaisa, Sadik ya sa nasa hannun ya kalleta cikin masifa yace "ba ki da hankali ne? Da auren naki kike gaisawa da maza?"

"Kai ma da Aurenka kake gaisawa da mata?" Tai maganar tana murguɗa baki.

"To ni da ke ɗaya ne?"

"Eh mana, da biyu ne, kai kake cemin 'yar ƙauye ai, gara in abunda zan waye"

Sadik ba ya son su raba abun faɗa a cikin jama'a, dan haka ya ƙyaleta, ya ƙwafeta  a ransa.

Suka dinga yaba kyan Nana, suna cewa tana da kyau, har wani abokin Sadik yana cewa, akwai yiwuwar in ya tashi Aure, ya zo Nigeria ya samu mata, dan ace suna da Black beauties kamar Nana.
Sadik kasa cin Abincin yai saboda takaici, Itama Nana ba ta saba da cin abinci a gaban mutane ba, dan haka ta kasa sakewa ta ci.

"Ke tashi mu tafi" y faɗa a kausashe.

"Ni gaskiya ba zan tafi yanzu ba, daga zuwanmu se tafiya"

"Wallahi se kin tashi, tun da baki da man kai, tsabar rashin mutunci kike gaisawa da mazs, a gabana shashasha kawai"

"Ikon Allah, na ga kai ka fara yi ai, kuma gaisawa ce fa kawai, ai kai na gani kina yi"

"Za ki min shiri, ko se na ɓarar da kanki a nan gurin?"

Wata yarinya ce a cikin su ta ke tambayar su lafiya kuwa?.

Sadik yace lafiya ƙalau, tafiya za suyu.

Nan suka shiga tambayar meyasa za su tafi yanzu.

Sadik yace wani uzuri ne da shi a gida, dan haka za su tafi.

Mussaman saboda nasarar da Sadik ya samu suka shirya wannan cin abinci, amma Sadik yace tafiya ze yi.

Suna tafe a hanya yana wa Nana masifa kamar ze maketa, ita kuma se ƙunƙuni take, ta na harare harare.






Abubuwa fa sun ƙara damalmalewa Farhan, dan ba cinya ba ƙafar baya, dan a maimakon fasa Aurenta da Sunusi ya sata a farinciki, sema sake shiga cikin wata damuwar da tai.
Dan bayan ƙwayar ta saketa, ta gane duk abubuwan da suka faru gaske ne, Abba ya dena shiga harkarta gaba ɗaya, yai watsi da ita, dama Umma ba a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login