Showing 249001 words to 252000 words out of 259198 words

Chapter 84 - Rudin Kuruciya Book Complete Original By Ayshercool.txt

ja motar ya bar gidan.

Ita kanta Nana ta yaba tsarin gidan, yayi kyau sosai da sosai, gashi ɓangaren ta ya sha furnitures Abba ya kashe mata kuɗi sosai da sosai.

Ƙarfe takwas na dare sannan aka kawo Farhan, Sadik kuwa be shigo gidan ba se ƙarfe sha ɗaya na dare, kowa ya watse.
Farhan jin abun take banbarakwai, wai yau itace matar Sadik, abun abun mamaki sosai.

Nana kuwa tuni ta canza kaya zuwa na bacci, Sahal yayi bacci tuni, ta nemi guri ta zauna akan gadonta, ta dinga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un a cikin ranta, saboda wani abu da ya tsaya a maƙogwaronta ya ƙi wucewa.

Sadik yai sallama a bedroom ɗinta, ds ƙyar ta iya amsa masa, ya zauna tare da ajiye mata leda manya guda biyu.

Zeyi magana ta ɗora hannunta akan laɓaɓanta tace "Shhh, seda safe Allah ya bamu alkhairi" fafur ta hana shi Magana, haka ya tashi ya ƙyaleta.

Sashin Farhan ya nufa da sauran ledojin, yana yiwa Allah godiya yau Allah ya tabattar masa da mafarkinsa na mallakar Farhan, lallai soyayyar su bata tsaya a iya RUƊIN ƘURUCIYA ba, yana fatan Allah yasa Auren Farhan da yai ya zama kankarar laifin da ya aikata a baya.

Da sallama ya shiga bedroom ɗin Farhan, ta takure guri ɗaya da alama sanyin AC yai mata yawa. Ya rage AC Sannan yaje kusa da ita ya zauna, amma Farhan ta matsa.

Sadik yace "Ikon Allah, yau kuma ni kike gudu?" Shiru tai ba tace komai ba.

Ya cire rigar jikinsa ya bar shirt da wandon yadinsa, yace "yo alwala ki zo muyi salla"

"Bana salla?" Ta gaya masa kanta tsaye, cikin ko in kula yace "ok fine" dan ya lura haryanzu Farhan a ƙule take da shi.

Yaje yai alwalarsa yazo ya gabatar da nafila raka'a biyu, ya ɗakko plate ya juye kazar a kai, ya zauna a kusa da ita tare da yaye mayafin lafayar jikinta amma ta ƙanƙame jikinta.

Shi Sadik dariya ma ta bashi, yace "Bismillah, muci Abinci"

"Naci tuwo a gida, na ƙoshi".

"Tuwo daban kaza daban, kici"

"Ni na ƙoshi" tai maganar tana zumɓura baki.

Be kuma ce mata komai ba, yaci nasa ya rufe sauran, se ƙare mata kallo yake kasancewar ta sha ado da gyara, kuma ta Sunkuyar da kanta.

Da Sadik ya matsa in da take, se ta matsa yai murmushi yace "wani darene jemage be gani ba amaryar? Dama kin dena wannan abun, Sadik ɗin ne dai ba wani ba, kuma Farhan ɗince dai ba wata ba, ki bari mu ɗora a in da muka tsaya mana" yai maganar yana kashe mata ido.


Wata nadama ce ta sake kama Farhan, duk da Sadik ya Aureta amma ta tafka kuskuren biye masa da ta dinga yi a baya.

Be kuma kulata ba yaje ya kashe fitilar ɗakin,yana ta hamdala a zuciyarsa, ganin yai kwanciyar sa yasa ita ma ta ɗosana ta kwanta, dan a gajiye take matuƙa, ta shiga tunane tunane daban daban a cikin zuciyarta har bacci yai awon gaba da ita.

Seda ya tabbatar tayi bacci, sannan ya tashi zaune, ya kwance lafayar jikinta tsaf, skirt ne a jikinta da shirt, ya kunna fitilar wayarsa, ya haskata wata irin soyayyarta da ƙaunarta suna fuzgarshi, ji yake kamar ya maida ita cikinsa saboda so da ƙauna, bacci take sosai har da ajiyar zuciya saboda gajiya.

Ya kashe fitilar, ya matsa kusa da ita ya rungumota jikinsa, yana shaƙar ƙamshin turaren da ke ta shi a jikinta, fatarta tayi wani irin santsi da laushi.

Murmushi yai ta ƙara girma sosai, saɓanin lokacin da ya tafi ya barta.

Sosai Sadik yake jin yadda yai missing ɗinta, farkawa tai daga nannauyan baccin da ya ɗauke ta, ture Sadik ta fara ƙoƙarin yi.

Murya can ƙasa yace "meyasa ki kai min ƙarya?"

"Ƙaryar me nai maka?" Tai maganar kamar za tai kuka.

"Au baki san ƙaryar da ki kai bama ko? To bari in gama fanshe soyayyata da wahal da ni da kika dinga yi, se ki gane ƙaryar da ki kai min"

"Dan Allah Sadik ka rabu dani, ni gaba ɗaya haushinka nake ji, dan Allah ka ƙyaleni".

"Umm, Umm I don't care Baby".
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680





Sosai take ture Sadik da iya ƙarfinta, tana kai masa duka, cikata yai tare da ɗagota tana kallonta, se sauke numfashi take kamar tayi gudu me nisa.

"Farhan me kike nufi ne?"

"Nace maka ka ƙyaleni".

"Saboda me zan ƙyaleki?"

"Ni bana sonka, bana ƙaunarka yaudarata kake yi ka ƙyaleni".
Tai maganar gabanta na tsananta faɗuwa.

Sadik yai ajiyar zuciya yace "Me zanyi wanda ze sa ki yarda dani ne Farhan? Sadik ne fa"

"Ni ka ƙyaleni dan Allah"

"Why?" Yai maganar yana cigaba da abunda yake.

"Stop it please, am not in mood".

Wata miskilar dariya yai iya maƙogwaronsa yace "I know how to turn you on, ko kin manta Prince ne?"

"Sadik am on my period, i told you earlier"

"Meyasa ba kya jin kunyata yanzu ne? Kike min ƙarya yadda kike so".

"Ni ba ƙarya nake ba, ka ƙyaleni nace"

Tana ji tana gani, Sadik yai burus da ita, dama ba wani fashin salla da take, ta gaya masa ne da biyu, na farko tana cikin fargabar abunda ka iya komowa saboda rashin kai budurcinta, abu na biyu kuma haryanzu tana jin haushin Sadik, ga wani irin tsoro da ya baibayeta.

Hankali kwance Sadik yai abunda Allah ya nufe shi da yi, musamman da burinsa ya daɗe yana fata ya cika, mafarkinsa ya zama gaskiya yau ya kasance da yarinyar da ya fara so a rayuwarsa.

Farhan kuwa ta gigita da lamarin, dan ta Sha jini jikinta, ba ta zaci lamarin ya kai haka ba, kukan ma Muryar ta ƙasa ƙasa ta dinga fita, dan Sadik ya bata mamaki ƙwarai.

Fuskarsa ya ɗora akan tata, yana son yai mata Magana, amma ya kasa se sauke mata numfashi da yake a fuska.

Janye ta ta fuskar take ƙoƙarin yi, a hankali yace "Indeed, you are good girl, a promise keeper, Princess your crown will never fall, you will forever remain in the throne, you will remain the queen of my Emirate, inshallah i love You fisabilillah Farhan"

Ita Farhan gaba ɗaya ta kanta take, dan haka ba gane kan wannan surutun nasa take ba.

Sadik ne ya fara tashi, yaje yai wanka ya dawo ya taimaka mata, duk yadda ya so tai magana ba ta kula shi ba, tai masa shiru ta ƙi Magana, sedai babban abunda take tunanin shine, Babba yace sun mata fyaɗe su huɗu, amma ta ji ta garau Ranar, to ya akai taji banbanci sosai haka yau? Ba tace komai ba dai amma se tunanin abun take.

Sadik ya ƙanƙame Farhan, kamar yau ya fara sonta, duk wani shakku da yake ya kau, jinta yake wata ta musamman a zuciyarsa.
First night ɗinsa ya tuna da Besty, cike da shiririta da daru a gurin Nana, murmushi ya saki, dan Nana rigimamiya ce lambar farko.

Da Asuba seda Suka makara, dan haka a gida yai salla ya koma bacci, Farhan kam sanyi take ji sosai, jikinta ya ɗau zafi Sadik ya dinga jera mata sannu, daga nan suka koma bacci.

Se bayan tara Sannan Sadik ya tashi, Farhan kam ko ƙwaƙwƙwaran mosti ba ta yi, baccinta kawai take yi.

Be tashe ta ba yai wanka, ya kintsa cikin ƙananan kaya, ya kalli wayoyinsa dake kashe, ya ɗauka ya zuba a aljihunsa, sannan ya fita kai tsaye part ɗin Nana ya shiga.

Ba ta bedroom ɗin, ya zauna yana jiranta, wani dadaɗan ƙamshin humra ne ya daki hancinsa, Nana ce sanye da wasu English wears masu matuƙar kyau da duka amshi jikinta sosai, ta shigo hannunta riƙe da kofi, sedai kallo ɗaya za kai mata ka san ba tai bacci ba, idanunta duk sunyi wani iri.

Zuba mata idanunsa yai, har ta ƙaraso ta zauna tace "Ina kwana?"

Be amsa ba se kallonta kawai da yake, yai ajiyar zuciya yace "kin tashi lafiya?"

Tace "Lafiya ƙalau"

"Kin karya ne?"

Nana tace "Eh"

"Me kika ci"

Tace "Abinci mana"

"A ina kika samu Abincin?"

"Na sha cornflakes, ga Abinci can an kawo daga gida"

"Besty meyasa ba kya tausayin kanki ne? Shayarwa fa kike ya za'ai wani cornflakes ya riƙe ki? "

"To ai ya fara cin abinci, ni Abincin ne baya kaina"

Be ce mata komai ba yaje kitchen, ya tarar da Manyan warmers, kunun gyaɗa a teaflask, se soyayyan dankali da ƙwai a flask ɗaya.

Ya zubo dai-dai cikin Nana, ya koma ɗakinta, ya sata a gaba ya takura mata, ya dinga bata a baki da kansa, cikin kulawa Kamar ba wanda yake da sabuwar Amarya ba, se da ya tabattar ta ƙoshi sannan yace "Yawwa yanzu Sahal ze samu Abinci sosai shima, ki dena min wasa da cikinku in ba baka ba za muyi faɗa, wai ina Sahal ɗin ma yake?"

"Da aka kawo Abinci, Mother ta saka aka tafi da shi"

"Kai Mother dai na fuskanci so take mu bar mata ɗan nan, kuma ba wanda zan iya bawa, bari ajima inje in ɗakko shi"

Nana tace "to in dai kaje ni dai ba ruwana, bance a ɗakko shi ba"

Bece komai ba ya miƙe ya fita, sashin Farhan ya koma, ya tarar ta tashi har tai wanka ta canza bedsheet, ta zauna tana shafa mai a jikinta, sam ba ta san yana nan be fita ba, da Abincin da aka kawo ya shigo, yace "Princess, barka da safiya"

Kamar ba ta ji ba tai masa shiru, ya ƙara so gaban mirror yace "kina jina fa, amma ki kai min shiru, kawo in tayaki shafa man"

"A'a Nagode, tai maganar tana karɓe robar man, ta gama shafa manta ta ɗau kayan sawarta ta shige toilet, shi dariya ma ta ba shi.

Ta fito cikin riga da skirt na atamfa, se kare jikinta take saboda yadda kayan suka matsteta, aikuwa ya zuba mata kyawawan idanunsa, se wani haɗe rai take wai ita a dole dole a kai mata ta Aureshi ta dena son sa.

"In kin gama ɓoye ɓoyen, seki zo mu karya"

"Ka ci naka, in ka fita naci nawa" ta bashi amsa.

Sadik yace "Ina zan fita in je, ina da zankaɗeɗiyar Amarya a ɗaki, ba in da zani muna tare tip da tire, soyayya zamu sha".

"Se dai ka sha da matarka ba ni ba, ita ke sonka se kuyi ba dani ba"

"To ke yanzu ina ruwanki da mata ta? Kuma kema ai mata ta ce" neman guri tai ta kwanta, ta share Sadik.

Tana kwanciya Sadik be jira komai ba, shima ya bi bayanta kan gadon yace "Ai ta kwana gidan Sauƙi Beb, na gane abunda kike nufi"

Wani uban tsalle tai ta sakko tana haki, yai dariya yace "kin raina ni Farhan, hmm to ko ki zauna ko kuma ni in zo in sameki"

Haka Farhan ta zauna, Sadik ya dinga bata Abincin nan da kansa, tana karɓa idonta har da guntun hawaye.


Sha biyun rana ƙannnen babar su Farhan da wasu 'yan uwansu suka zo gidan, bayan sun gaisa da Sadik ya fita ya bar gidan.

Suka kawowa Farhan miya da akai mata, ta sha nama, ga Nono kaya guda da suka kawo mata, da su kayan daddawa da kaɗin miya, Adda Hafsa tace "Ina abokiyar zaman naki ne mu gaisa, mu yau zamu koma"

Farhan tace "nima ban san in da take ba"

"Kamar yaya baki san in da take ba?"

Farhan tace "to ai ni tunda na zo ban ganta ba"

"To shi mijin naki be haɗaku ya muku nasiha ba"

Farhan ta jinjina kai, Adda Hafsa tace "dama abunka ds harkar yara, gayyar shirirta wataƙila ma be san anayi ba"

Bayan azahar sukace zasu tafi, sukaiwa Farhan sallama tare da yi mata nasiha sosai, sukai mata sallama suka tafi.

Daga Nana har Farhan ba wadda ta kuma fitowa, balle wata taga wata.

Se magariba Sadik ya dawo, a zatonsa suna ta yin baƙi ne, part ɗin Nana ya fara zuwa, hannunsa ɗauke da Sahal, ya ajiye Sahal sannan yace "Besty, zamuyi dinner a falo tare gaba ɗayanmu, zan gabatar muku da juna".

Idan Sadik ya gani daidai wani mugun kallo Nana ta watsa masa, ji tai kamar tace ba zata fito ba, amma tai shiru bata faɗa ba.

Itama Farhan da ya je gurinta, haka su kaita artabu da ita, tsiwa kala kala, wadda be taɓa saninta da ita ba.

Bayan sallar isha'i yace mata "muje falo, zaki gaida uwargida na"

Yamutse fuska tai, ba tare da tace komai ba, ji yai kamar yai dariya, amma ya haɗiye, suka fito ƙaton falon tare, Sadik ya nufi sashin Nana, yana Addu'a, dan mutuniyar ba sauƙi hukuma ce se da rarrashi.

"Sarautar mata, ke muke jira fa"

Tace "Me za'ayi?"

"Kin manta maganar da mukai ne?"

"Dan Allah ni ka ƙyaleni, ba se naje ba"

Sadik yace "karki ɓatamin rai Please, tashi muje" ya ƙarasa maganar yana saɓa Sahal a kafaɗarsa yai waje.

Nana ta wani sake karkace ɗaurin kallabinta, sannan ta biyo bayan Sadik.

Farhan na ganin Sahal ta fara murmushi, yaro tubarkallah lafiyayye, kai da ganinsa ka san akwai kulawa, ƙato da shi, fari tas me yawan suma a ka baƙi ƙirin, ko ya ya yamutsa fuskarsa se dimples ɗinsa sun lotsa, Sahal kyakykyawa ne yaron sosai.

Sadik na ƙarasowa Farhan ta miƙe tana murmushi, tana son ta karɓi Sahal, Sadik yace "mara kunya, kince ba kya so na, amma kina wa ɗana dariya zaki ɗauke shi, to ba zan bayar ba nima"
Saroro tai tana kallon Sadik, tace "dan Allah ka bani shi"
"Ba zan bayar ba, ba kya sona kike son ɗana?"

Nana ce ta fito ta same su, sedai tana fitowa suka haɗa ido da Farhan, sunawa juna kallon sani, a take gabansu ya faɗi, kowacce tana ganin anya 'yar uwatta ba ta fita komai ba.

Nana ta fara janye idonta, ta samu guri ta zauna, ta maida idonta kallon wani gurin, tana kaɗa ƙafafunta.

Sadik yace "bari mu fara da Addu'a, Besty yi mana addu'a"

Nana tace "ai kai yakamata kayi"

Be kuma tanka mata ba kar suyi faɗa, yai addu'a sannan ya fara bayani.

"To Dukkan yabo da godiya sun tabatta ga ubangijin talikai, buwayi gagara misali, wanda ya haɗa dukkanin mu ƙarƙashin inuwa ɗaya ta Aure. Dukkanin ku ina alfahari da kasancewar ku a ƙarƙashina matsayin matana, wadda kowacce dan ina sonta ne nake tare da ita, babban fatana da roƙona a gareku be wuce dan Allah ku haɗa kanku ba, kar a samu wata ɓaraka da wani daga waje ze shigo ciki ba. Ku haɗa kanku ku bani damar in muku adalci, Nana ke ce Uwargida amma Farhan gaba take da ke, amma matsayinki na uwargida yana nan baze canza ba, Farhan kece ƙarama amma gaba kike da Nana, a bata girmanta a matsayin ta na uwargida na Please, Besty ga amanar Princess ɗina, Princess ga amanar Besty na nan, dan Allah ku haɗa kai ku zauna lafiya" har ya gama ɓaɓatunsa ba wadda ta tanka masa, dan Nana ma kashingiɗa tai akan kujerar tana shilla ƙafarta a hankali, rabin hankalinta akansa rabi akan tunani.

"Bestyna, ko kina da abinda zaki tofa?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Magana fa nake, nace ko kina da Magana?" "Babu"ta faɗa a taƙaice.

Ya kalli Farhan yace "Princess ke fa, do you have anything to say?"

"Babu" itama ta bashi amsa.

Sadik yace "Madalla, ga Abinci nan ku sakko muci Abinci".

Nana tace "Nikam na ƙoshi, a ci lafiya"

Sadik yace "meyasa?"

"Ka san bana cin abincin dare, saboda ban son in ƙiba".

Farhan wani dumm taji, tana tunanin ko dai magana Nana ta faɗa mata, dan ita 'yar duma duma ce.

Sadik be sam wani Nana ba ta cin abincin dare ba, tsabar kishi ne da iskanci kawai.

Be kulata ba, yace Farhan ta zo taci, ba ta wani ci ba, ta koma gefe tana kallon Sahal da Sadik ya kwantar da shi yana bacci.

Seda suka gama, Sadik yace "bari in kai mata Sahal, ina dawowa.

Yaje ya iske Nana har tai shirin bacci, ya ƙare mata kallo, Sannan yace "Haba Nana, Yakamata fa ki kula, kar kishi ya sa ki abunda zaki zubar da kimarki a gurin ta da wuri, she's very kind and simple, meye abun cewa wai ba zaki ci Abincin dare ba dan kar ki ƙiba?" Saboda cusa haushi, setai kamar ma ba ta san da ita yake ba

Fizgota yai tana fuskantar sa yace 'ba da ke nake magana bane? Wai yaushe kika zama haka ne? Shikenan ban isa in magana ba se ki rainamin hankali, kina ji ina miki Magana, se lalaɓaki nake amma kina buntsurewa ya kike so in yi da raina Nana? Da me zanji? Fushin su Mother ko kuma abunda kike min?"

Kuka ta fara yi masa, abunda Sadik ya tsana, kuma sanin baya son kukan yasa daga taji ya matsata se ta fara kuka.

"Me nai miki kuma kike min kuka?" Yai maganar a sanyaye.

"Ba kaine kake min faɗa ba"

"Haba Besty idan banyi faɗa ba ya zan miki? Duk kin bi kin ɗagan hankali na kasa samun nutsuwa saboda halinki"

"To ni me nayi?" Tai maganar cikin sigar shagwaɓa, jikin Sadik yai sanyi ya fara bin bakinta da kallo, se tura shi take tana kuka.

"Allah ya shiryeki, da rikicin gangan"

"Ni ka cikani bacci nake ji"

"To Allah ya bamu alkhairi, kwanta in lulluɓeku"

Ta kwanta ya ja musu bargo, sannan ya kashe musu fitila ya tafi sashin Farhan.

Farhan har ta ƙule, daga zuwa kai Sahal, yaje yai zamansa aikuwa taji haushi, ta nemi guri ta kwanta.


Yana zuwa ɗakinta ya ga ranta a haɗe har ta kwanta, bece mata komai ba kuma be ƙudurci yai mata wani abu ba ya ƙyaleta, saboda ya ga yadda ta haɗe rai.






Khairat ta fito daga ita se rigar bacci, kanta ko ɗan kwali babu, zata fita babban falo neman aunda zata ci, tai kiciɓis da Faruk yana shigowa, wata kunyarsa cea kamata, dan tun lokacin da Nana tai wanan Maganar take jin kunyarsa.

"Ina zuwa?" Ya tambayeta yana kallonta.

"Kitchen zani, ina jin yunwa ne"

Yai gaba yace "follow me" ba musu tabi bayansa, be tsaya da ita a ko ina ba, se a gaban mudubi, yace "look at you, kalli rigar jikink kaki babu ɗan kwali, kuma kin san haryanzu da sauran mutane a gidan nan, amma zaki fita a haka, am very jealous, idan har kina sona dagaske kina son mu shirya, to gaskiya ki dena yawo a haka"

Kunya ce ta kamata kamar ta nutse ta sunkuyar da kai, tun da Nana tai masa magana akan Khairat, ya fara jinta a ransa, kuma yana tausayin yadda take son sa.

"Oya, aje a canza kayan nan maza". Tace "to".





Sunusi yana kwace yana fama da kansa, Wani irin matsanancin ciwon ka ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login