Showing 1 words to 3000 words out of 242549 words

Chapter 1 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3340

Wattpad: https://my.w.tt/YJ8zpAc3a8




1


UWA UWACE...


Bismillahir Rahmanir Rahim

Batul Mamman


SANARWA: Ina mai bawa masu jiran wannan littafi hakuri game da canjin da zaku gani a tare da labarin. Wasu dalilai sun sa na canja tsarin labarin sabanin yadda na fara shafin farko watannin baya. Allah Yasa mu amfana da darussan ciki Ya yafe min kurakuran da ajizancin dan Adam ba zai barni na tsallakesu ba. Amin



Shimfida



KIRIKASAMMA, JIGAWA
1983


Nishi take mai kama da gurnani saboda tsananin ciwon da take ji. Ko da wasa bata taba tsammanin ciwon nakudar da mata ke yawan fada ya kai haka ba. Mace ta kasa gane a wace duniyar take. Idan ba ta kama bakinta ba sai dai ka ji tana sumbatun da basu da kan gado. Addu'a kuwa bata san nawa ta kama ta saki kafin ta kai karshe ba. Yau Kulhuwallahu, Falaki da Nasin da ko cikin bacci basu bace mata ta kasa kai karshen ko daya. Sai ta karanta ayoyi biyu a nan ta kama wata. Halilala ma da kyar take cijewa ta kai karshe. Iska take furzarwa akai-akai ta baki ta hanci. Ashe shi yasa Malamin makarantar darensu ya ce duk wadda ta rasa rayuwarta wurin haihuwa tayi shahada. Ladanta daya da wanda ya rasu a wurin yaki. Mahaifiyarta ce ta fado mata a rai a wannan yanayin.

"Allah Ya jikanki Inna. Inna idan na yi miki laifi ki yafeni. Innata bani da kamarki duk fadin duniya." Ciwo na tasowa ta ce "Inna ki ceceni."

"Allah dai Ya ceceki Mari kada ki yi sabo mana."

Ba da niyya ba ta kalli idanun surukarta Inna Mairo cikin radadin ciwo ta ce "kin san irin ciwon da nake ji ne Inna Mairo? Nan..." ta nuna mararta "...ne yake rabewa gida biyu. Yanzu kema a haka ki ka haifo Inuwa?"

Dan murmushi Inna Mairo tayi saboda sanin cewa Mari ba a hayyacinta take ba. Ita da ta sha wannan wahalar sau goma sha uku sai dai ta bada labari.

Wani irin ciwo ne ya damki mara da bayan Mari ta kai hannu ta cafko hannun Inna Mairo. Gani take kamar ba za ta tashi ba saboda azabar ciwo.

Harira unguwae zoman ta sake danna gefe da gefen cikin sannan ta kuma lekawa. Kai ya taho amma da alama hanyar tayi masa kadan. Sabuwar rezarta ta dauko ta ce da Inna Mairo ta matso kusa da tochilan ta haska mata da kyau. Acibalbal din da aka kunna bata da hasken da zai wadaceta tayi abin da ya kamata.

Mari ciwo bai barta taga abin da ake shirin yi mata ba. Harira ta saka tochilan din a cikin dankwalinta ita kuma Inna Mairo ta rike hannuwan Mari. Rezar ta dan kara a jikin wutar acibalbal din ta dauke ta danna kowane gefe a jikin zaninta. Ji ka ke kit-kit ta kara Mari ta hagu da dama. Wannan izaya bata da kalmar kwatance. A kan ce mata basu ganewa idan an karasu saboda ciwon nakuda amma Mari kam taji komai.

Budar bakinta za ta yi ihu wani nannauyan nishi ya taso mata. Da dan sauran kuzarin da ya rage mata ta cije baki tayi nishin. Hamdala Harira tayi tare da karfafa mata gwiwa akan ta kara wani domin ga kan jariri nan ya kara turowa gaba. Ta daddage tayi kuwa sai ji tayi an canyara kuka irin na sabbin haihuwa bakin duniya. A take ta nemi wannan azababben ciwo ta rasa sai son ganin abinda ta haifa.

"Sannu Mari. Sannu da kokari. Allah Ya raya shi Ya baki lafiyar shayarwa." Inna Mairo ta furta tana share mata gumi.

Kunya taji ta lullubeta da ta tuna cewa ba don dan ya fito ba sakon tsinuwa da Allah Ya isa ta shirya bata domin ta isar ga Inusa maigidanta.

Harira ta nade jinjirin a zani ta mikowa Inna Mairo. Da saurinta ta mika hannu za ta amshe shi hannun ya yi 'yar kara. Fuskar Mari wadda ta dago kai tana son satar kallon dan nata ta kalla tayi murmushi ganin Marin ta kawar da kai gefe.

"Da dai korafin karya min hannu zan miki amma na fasa. Dauke shi ku ji dumin juna kafin na dawo."

Da hannu Mari ta rufe fuskarta mai dauke da murmushin da ya gagara buya. A hankali ta bawa Inna Mairo hakurin rikon da tayi mata wanda da alama ya janyo mata rauni. Wani murmushin ta sake yi mata sannan ta tashi domin dora ruwan wanka tana murza hannun da take jin ya yi mata nauyi. Tana tausayin matar dan nata saboda ta tashi marainiya mara gata a wurin danginta. Shi yasa bata yarda an tafi da ita wankan jego ba lokacin da matar kawunta ta matsa akan hakan.

Harira ma fita tayi aka bar Mari da jaririnta. Sai da ta tabbatar babu sawunsu a kusa ta matso dashi kirjinta ta rungume. Hannunta yana dan rawa ta bude fuskarsa da kyau. Hawaye taji ya ciko idanunta saboda kaunarsa da ta shigeta farat daya. Bata jin za ta iya hada shi da kowa sai dai idan a gaba ta sake haihuwa. Tunanin kadai sai da yasa tsigar jikinta tashi da ta tuna halin da take ciki mintuna kadan da suka wuce. Addu'a tayi masa ta neman tsari da kariya tare da albarkar rayuwa. Kafin a fara shigowa dakin har ta gama kissima rayuwarsa har aure. Burinta ya zama da nagari abin kwatance. Ya yi ilimi mai zurfi irin wanda taga ana yi a birni lokacin da take aikatau kafin tayi aure. Idan so samu ne ma ya zama babban likita ko lauya.

"Dinkin nan zan zo in cigaba in tara kudin siya maka duk abin da za a nema a makaranta na karatun."

Ta fada masa kamar yana fahimta. Guda ta jiyo ta tabbata yanzu duka matan gidan sun sami labarin haihuwarta. Yanzu dakin zai cika duk da asuba ce da matan 'yan uwan mijinta da sauran kannensu da basu yi aure ba. Ajiye jaririn tayi da sauri kar a ganshi a hannunta a kirata mara kunya. Can kasa kamar mai yi masa rada tayi magana tana murmushin tsananin farinciki da jindadi.

"Bi'izinillahi sai kayi arabi da boko. Kayi sauka sannan kayi digirin digirgir irin na dan Hajiyar da na yiwa aiki."

Rana na soma fitowa ruwan wanka ya yi zafi. Matar kanin Malam wato kawu ga mijinta Inuwa ce ta zaga bayan gida da ita inda za'ayi mata wanka. Jaririn kuma saboda hannun Inna Mairo da alama ya sami gocewa ko targade sai matar wan Inusa ce tayi masa wanka. Tana murnar rabuwa da ciwon haihuwa ashe akwai wani a gaba. Ruwan wankan da zafi sosai ake yarba mata darbejiyar da take ciki. Tun tana daurewa har ta hada da ihu. Ciki da baya sun sha matsa da dannawa. Bayan an gama wankan ta miko mata wani kwabi da kyallen kunguzu. Kallon kwabin da yafi kama da lalle tayi ta tamutsa fuska.

"Me zan yi dashi Gwaggo?"

Idan bata yi da gaske ba take taken Mari ba za ta saka ba saboda haka ta amshe ta ce yaba mata da kanta. Lalle ne aka kwaba da kauri da wani garin magani aka cusa mata. Mari sai gumi kawai take yi na wahala da ciwo. Bayan an gama sakawa kuma aka toshe wurin da kyallen kunzugu sannan aka bata zani ta daura.

Tare suka fito tana taku da kyar zuwa daki. A haka aka ce ta shayar da jaririn bayan ko zaman kirki ta kasa. Haka aka cigaba da yi mata kwabin lallen nan na tsahon kwana shida sai ta nemi tsagar wurin karin ta rasa. Ciwo ya hade tsaf ya warke (don Allah kada wacce ta gwada).

Ranar suna jariri yaci sunan kakansa Auwalu aka yi masa lakabi da Abbati.

***

DALA, KANO
1985


Kukan ya ishe shi. Idan ya bari suka kara minti biyar a dakin yana da tabbacin zai sami tabin hankali. Bai so Innayo ta karbi girki daga yin arba'in ba. Jiya ma haka suka kwana jaririyarta Hasiya tana ta canyara kuka. A fusace yasa kafa ya haureta tana baccin da ana gani za'a gane cewa a gajiye take likis. Da yake muryar Hasiyan ba karfi gareta ba shi yasa bata ji kukan da ta shafe mintuna tana yi ba.

"Dalla can malama tashi ki dauki 'yarki."

Bugun ya shigeta sai dai kukan da ta ji ya dauke zafin dukan. Hannu ta kai da sauri ta lalubi 'yarta cikin hasken farin watan da ya ratso ta tagar dakin. Rarrashinta tayi nata idanun suna yi mata yajin bacci ta soma shayar da ita. Jin yarinyar tana ta ajiyar zuciya yasa ta jin babu dadi a ranta. Maganin mura ta sha ya saka mata nannauyan bacci ga kuma gajiyar aikin da tayi.

"Baiwar Allah kin dade kina kukan nan da alama ban ji ba. Ayi hakuri" ta kare maganar tana shafa mata kai.

"Mtsew" Alh Rabi'u ya buga tsaki.

A cikin duhun dakin ya tashi ya lalubo wandon kayan da ya dawo dasu daga kasuwa ya saka hannu a aljihu. Sautin sulalla na karo da juna Innayo taji ta kalli bangaren da yake tsaye.

"Alhaji idan wani abu kake nema bari ta gama na kunna maka fitilar kwan. A duhun nan ba ganin..."

Kasa karasawa tayi ganin ya nufota. Duk da ba ganin fuskarsa take yi ba amma ta fahimci ransa a bace yake. Hannunta ya kama ya zube mata sulallan da bata san ko nawa bane.

Da kakkausar murya ya yi mata magana cikin fushi.
"Gashi nan na saya sai ki tashi ki koma dakinki."

Sam bata fahimce shi ba.
"Me ka saya?"

Daurewa ya yi saboda dare ya raba ya bata amsa ba tare da ya kara daga sautin muryarsa ba.

"Kwananki na saya Innayo! Ki dauki 'yarki ku koma dakinki. Zan dinga biyanki daga yau har ki kara wata arba'in din."

Hankali a tashi ta fara tambayarsa laifin da tayi masa. Lokacin kuma Hasiya ta zabi ta sake bare baki tana kuka. Kan Innayo har wani sarawa yake saboda rashin isasshen bacci da gajiya. Wuni take a gaban murhu ga fama da yara. Biyar nata har jaririyarta ga kuma hudu na matarsa ta farko da ya saka shekara biyu da suka wuce.

A yanzu su biyu ne a wurin maigidan nasu Alh Rabi'u kuma ita ce matsayin uwargida. Amaryar tasa Asabe ma ta dan kwana biyu tunda haihuwarta biyu yanzu. Iyakarsu da shi ya aunawa maigirki hatsi ga icce jingim a gidan. Sauran abin da za'a hada da hatsin a tayar da abinci kuwa sai dai mace ta nema. Asabe ko wata bata cika ba ta fitittike ta nemi ya raba musu girki. Kowacce tayi nata. Wadda miji ke hannunta ranar tayi da shi. Ita da ta zo cin arziki gani tayi sadakinta ma idan bata yi wasa ba a cefanen ciyar da 'ya'yan koshiyoyi zai kare. Haka kuwa akayi. Ya amince ya raba ya bar masu 'ya'ya da wahala. Bayan rabuwarsa da uwargidan taki daukar ko guda cikin 'ya'yanta. Har yau basu san me ya hadasu ba amma ko tantama laifin ba zai wuce nasa ba. Mahaifiyarsa ya kaiwa yaran da fari yayansa ya ce bai isa ba. Ga tsufa da tayi ga sanin halinsa na son banza. Jibge mata su zai yi sai an ganshi. A dole ya dawo dasu gidan ya rabawa matansa. Asabe tayi tsalle ta dire a gaban yaran ta ce ba za ta dauki ko daya ba. Tausayi suka bawa Innayo ana rabonsu a tsakar gida kamar ba mutane ba ta karba ta hada da nata. Zancen irin wahalar da take sha wurin ciyar dasu ma bai taso ba.

"Nufinka bani da girki har sai mun kara wasu kwanaki arba'in din?" Ta tambaye shi da mamaki.

"Ashe kin fahimta ki ke wani neman ba'asi." Shimfidar Hasiya ya tattaro mata "tashi ki tafi bacci ne a idona. Kuma ki kwantar da hankalinki ba wai Asabe zan baiwa kwanakin naki ba. Kukan nan ne kawai ba zan jura ba."

Maganganunsa sun bata mata rai amma ta daure taki bashi amsar da za ta sa taji sauki a zuciyarta. Tashi tayi jiki ba kwari ta fice ya kada kai a wurin ya kwanta.

Kamar kullum washe-gari karfe bakwai a bakin murhu tayi mata da goyon Hasiya. Da safe 'yar tsala take sayarwa da kuli-kuli. Da rana kuma dambu. Daidai lokacin tasowar yara daga islamiyya kuma tayi danmalele. Don ciniki kam sai dai tayi hamdala. Kudin ne dai duk yawansu basa isarta. Yara tara ne a gabanta da ita kanta cikon ta goma. Ga kudin laraba ga sayen abinda ba a rasa ba na boko.

Ta sallami yaron karshe da bokiti cike da 'yar tsala da zai kai kasuwa taga fitowar Asabe daga dakin Alh Rabi'u da danta a hannu. Suna hada ido ta gatsina fuska gami da murguda mata baki ta shige dakinta. Bata bi ta kanta ba ta sauke tandar ta dora ruwan wanka. Yaran gidan duka sun tafi makaranta sai wadda ta yaye tana bacci a daki.

Alh Rabi'u ta gani ya fito cikin shirin tafiya kasuwa. Dauke kai tayi kamar ba za ta yi masa magana ba saboda haushin abin da ya yi mata, sai kuma dai ta daure ta ce,

"Sannu Alhaji."

Da yake ba shi da gaskiya sai ya hau sababin borin kunya.
"Na dai biyaki kin kuma cake kudin bare ki ce an ci amanarki."

Zama tayi akan tabarma ta kwanto goyonta kafin tayi magana cikin rashin jindadi.
"Wani abin kaji na ce?"

Hannuwan babbar rigarsa ya nade fuskar nan tasa a hade. Bai so haduwarsu ba shi yasa ya zauna a daki niyarsa sai ta bar tsakar gidan ya fito. Daina jin motsinta da suka yi ne tasa shi cewa Asabe ta duba musu. Ita kuma don ta tura mata haushi ta fito sai ya zata ta gama suyarta ta shige daki ne.

Muryarsa a sama tunda ya san yaran masu wayo suna makaranta yake mata magana.
"Banda fitina ma irin taki Innayo daga yin arba'in ringidi-ringidi kin kwaso jiki kin dawo turakar maigida..."

Maganganunsa a take suka fara tunzura ziciyarta domin ta fahimci ci mata mutumci yake son yi. Kalamansa na gaba basu bata damar yin wani tunanin kirki ba sama da zubar da hawaye.

"...karfe takwas da rabi don bala'i duk kin saka yara bacci kin taho dakina ke mai girki. To magana ta gaskiya ni ba zan dinga kwana da wannan yarinyar tana yi min kuka ba." Ganin tana ta zubar da hawaye yasa shi cewa "Idan arba'in din ne baki son maimaitawa sai ki dinga barinta a dakinki ko ruwa A'i ta dinga bata. A shekarunta yanzu yaci a ce za ta iya kulawa da jinjinya."

Ido sharbe da hawayen bakincikin wannan terere da ya yi mata kuma a kunnuwan Asabe ta ce "yanzu Alhaji kayi min adalci kenan? Ka dakeni kuma ka hanani kuka. Ita Asaben ba goyo gareta ba?"

"Ban san kina kishi da namijin da ta haifa min ba sai yanzu. Yaro dan wata biyar da an kwantar dashi baka sake jin kukansa sai gari ya waye. Wai ma da ki ke zancen adalci ke shi kika yi min da kika haifi mata har biyar?"

Zancen kenan kullum! Ita da babarsu A'i sun haifa masa 'ya'ya mata. Asabe ma ta farkon ta mace ce cikon ta goman matan. Na shadaya ne ya fito namijin da ake muradi.

Idan ta biye masa ita zai cigaba da konawa zuciya a banza. Tashi tayi ta shige daki ko amsa bata bashi ba. 'Ya'ya mata Allah Yaso bata kuma ta gode. Sake kudurin ganin ta inganta rayuwarsu tayi. Idan ta kama ta kara wata sana'ar za ta kara. Burinta a rayuwa su ginu su zama mutanen da sai dai a rabesu a sha inuwarsu. Ta yarda ita kadai ta gama shan wahalar rayuwar duniya indai 'ya'yanta za su jidadi a gaba.

***
BARNAWA, KADUNA
2000

Zazzage akwatin da ta ajiye akan gadon tayi ta sake bin kayan ciki daya bayan daya tana jerawa a nutse. Tafiya ko da unguwa ce mara nisa tana da wani abu guda, sai mutum ya bincika kayansa sau goma kafin ya bar gida amma yana zuwa inda zai je sai ya tuna wani abu mai mahimmanci da ya manta. Hayaniyar yaranta ta ji daga falo da alama fada suke yi. Ba sai an fada ba kusan kodayaushe suka yi fada mai laifin daya ne.

"Lilu zo nan"

Ta daga murya tana kiran danta na uku. Bai zo din ba kamar yadda tayi tsammani sai ma ambaton "sai na rama" da yake yi cikin kuka. Sanin halinsa na rashin kunya yasa ta tashi da kyar saboda nauyin ciki ta bisu falon. Babban mai suna Suhaib akwai saurin fushi. Farha mai binsa sarkin tsokana. Sai Khalil da kowa yake kira Lilu mara kunya, ga taurin kai da saurin kuka.

"Allah nagode Maka" ta ce tana kallon yadda suka hargitsa falon kamar gidan mahaukata. Abubuwa kalilan ne a muhallinsu na asali. Yaran na ganinta suka shiga taitayinsu don sun san hali. Tana sonsu tana tattalinsu amma bata yarda da sakarci ba. Cikin hikima ta iya bi dasu duka da halayensu. Idan kayi abin fada ko duka kuma baka tsira. Khadija mace ce mai zafin nama da sanin ya kamata. Idan suka yi kiriniyar ta gama fadan sai ta koma gefe tana yi musu addu'ar shiriya. Fatanta kowannensu yana girma halinsa mara kyau yana raguwa har ya barshi gabadaya. Yanzu ma sulhu tayi musu ta kuma ja kunnen Farha akan tsokanar kaninta saboda raini da ya gama shiga tsakaninsu. Falon ta sake kallo sannan ta cira kafa ta taka kitchen ta leka ta dawo.

"Ina Nasima?"

"Ban ganta ba." Yaran suka hada baki wurin fada.

A falo ta bar 'yar budurwar mai aikin nata tare da yaran ta tafi sake hada kayan tafiya asibiti. So take ta tabbatar komai yana ciki kada ayi irin na haihuwar Lilu. Sai da aka gama shirya yaro babu shawul babu zanin nade shi saboda tana tsakar nakuda ta hada kayan.

"Ku taso ku kwashe tarkacen kayan wasanku kafin na kira Nasima ta zo ta share falon."

"Wash Mami hannuna..." fadin Lilu yana yarfe hannu.

Hade rai tayi tun kafin tayi magana ya mike tsaye "tashi makyuyaci. Idan aikin baki ne naka yafi na kowa tashi. Amma da an ce za a more ka sai ka dinga langabewa."

Fita tayi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login