Showing 165001 words to 168000 words out of 242549 words
ne uban gayya mai daukar credit din cigaban duka 'ya'yan gidan dole ya karbi lalacewarsu ma. Ta Abbati dai ta fito fili, zuciyarsa kuma tana nan tana raya masa cewa ba shi kadai bane ya fada tarkon shaidan daga zuwa karatu.
"Gashi nan ka kara a kudin asibitin"
Karba kawai Abbati ya yi ya koma ciki ko daga kai ya kalle shi bai yi ba.
Haka suka fita ana ta juyayin wannan lamari na ciwon Baaba Mari da Mal. Sa'idu a cikin gidan. Deluwa tayi nacin har ta saduda aka son jin kwaf.
Habi da Abbati ne kadai masu tafiya tare da mahaifansu. Babban asibitin gwamnatin Dutse suka tafi. Cikin dare sosai suka isa garin. An kuma karbi Baaba Mari an fara bata taimakon da ya dace. Zuwa safiya jikinta ya soma daidaita sosai sai hamdala. Bayan azahar ne da Abbati ya tabbatar an sami kanta yadda yake bukata ya iya dauko wayarsa. Ashe ta shiga silent ba tare da saninsa ba. Missed calls ya gani rututu. Na Munzali sun fi na kowa yawa. Sai na wanda suka nada yake kular musu da ginin plaza. Plazar da sai dai idan gwamnati ta gaji da ganinta ta san yadda zata yi da ita tunda komai na samuwarta haram ne. Na Farha basu fi biyar ba. Ya san lallai ita din ba mai takurawa bace. Tunda ya tafi a irin wannan yanayin kuma bai nemeta ba ta tabbata abin ya girmama. Babu na Hanne ko daya. Dama ita bukata ke sanyata nemansa ko zai yi sati bata ganshi ba.
Wani irin yanayi na shaukin soyayyar da mai yinta ya san bata tafe da cikar buri ne ya shige shi. Abubuwan da ya yi ta gudu a baya game da rasata sun bayyana. Ko yana hauka baya jin zai iya sake komawa gareta. Arzikin da ya zame masa garkuwar neman aurenta ya kau. Yanzu bashi da maraba da almajirin kan hanya mai jiran sadaka. Messages din ta turo masa har sunfi kiran yawa. A kalla a rana ta turo uku. Nasihohi ne da maganganun kwantar da hankali. Zuciyarsa ta sake karaya. Ba don karfin addu'ar mahaifiya ba da jajircewarsa wurin son ya kyautata tuba da ya koma gareta. Zai kirata ya jaddada mata girman soyayyarta da alkawarin aure.
"Allah Ya baki wanda ya fini a wurinsa. Allah Ya cire min kaunarkiba don na daina sonki ba Ya Farha."
Adduar da ya yi kenan iya jin kunnuwansa sai dai Baaba Mari tana ganin motsin bakinsa.
Adadin kiran da Munzali ya yi masa ne ya dakatar dashi daga rufe wayar. Munzali ya san me ya kawo shi gida. Ya san abubuwa marasa dadi dole zasu faru. Ya kuma san cewa zai neme shi da zarar abubuwa sunyi sauki. Babu lafiya jikinsa ya bashi. Bai yi tunanin komai ba ya kira shi tare da fatan ya amsa da gaggawa.
Ringing din farko ma bai gama shiga ba Munzali ya dauki wayar da sauri. Hannunsa yana rawa ya kara wayar a kunnensa. Zazzabi yake mai zafi da matsanancin ciwon kai ya kasa tashi zaune ma balle ya nemi agajin kukunsu a kai shi asibiti ko a bashi magani.
Yadda numfashinsa yake fita da sauti da kuma canjin muryarsa kadai suka ganar da Abbati cewa bashi da lafiya.
"Munzali me ya sameka? Kana ina?"
"Qibdiyya aka yiwa .. "
Sallah Baaba Mari zata tayar daga zaune ba shiri ta katse kabbarar haramarta ta kira Abbati a fusace.
"Abbati. Bani wayar nan!" Ta kalli Habi wadda ta tsorata "bamu wuri". Da saurinta kuwa ta fice duk da tana son jin me ake boye musu.
Tashi Abbati ya yi yaje gabanta ya durkusa sannan ya bata wayar. A wurin ya cigaba da durkuso ita kuma ta kara wayar a kunnenta. Kafin tayi magana Munzali dama yaji kiran da ta yiwa Abbati saboda haka bai yi mamakin jin muryarta ba.
"Munzali..." Da fada taso kiransa domin ya san duk abin da zata fada ba wasa bane. Sai dai kuma yana amsawa taji tausayinsa ya tsirga mata.
Gaisheta ya yi da faduwar gaba "Baaba ina wuni?"
Bata amsa ba. Sai ma kai tsaye fada masa abin da yake gabanta.
"Don sonka da Allah da ManzonSa (SAW) babu kai babu Abbati indai da gaske tuban kuka saka a gaba."
Tunda Abbati yake bai taba yiwa Baaba Mari musu ba amma yanzu bai san lokacin da ya kira sunanta da karfi ba. Jikinsa ya kama rawa ya sanya hannuwa ya dafa cinyarta.
"Baaba don Allah kada kice haka. Nayi miki rantsuwa da sunayen Allah tsarkaka wallahi bama neman juna. Abotarmu ita kadai ce halattaciyar dangantakar dake tsakaninmu. Domin Allah muke yinta ba don..."
Fuskarta babu annuri ko miskala zarratin amma ga hawaye suna gudu akan nagartacciyar fuskarta. A lokacin da Abbati yake nasa maganganun tana jinsa da kunne daya shi ma Munzali nasa yake yi mata.
Magana yake cikin dakewar murya domin kuwa iya abin da ya rage masa kenan. Mutuwa yake yiwa kansa fata domin yana ganim idan har Allah Ya karbi tubansa to lallai can din zai fiye masa akan rayuwa ba tare da aminin kwarai ba. Ashe alkhairi na karshe da zai gifta a tsakaninsa da Abbati shi ne assasa masa tuban da bai hangowa nan kusa ba. Kamar wanda ake cakawa mashi a kahon zuci haka ya dinga ji a lokacin da yake yi mata magana.
"In sha Allahu zaki sameni mai biyayya a gareki Baaba. Babu ni banu Abbati. Zan tashi daga gidan da nake kafin ya dawo Kano."
"Shi ma ba zai dawo ba. Ku nesanta da juna sannan ku nesanta da dukiyar haram. Sannan ne zaku yi tuba da kyakkyawar zuciya. Wala Allah zaku samu rabauta a nan duniya da lahira."
Kuka ya fashe dashi ba tare da sanin cewa Abbati ma kukan yake mata ba.
"Ki yafeni Baaba. Don Allah kada ki kai karata wurin Allah akan Abbati. Ko naki hakkin na rage ina sa ran samun sauki ko yaya yake a wurin Mahaliccina."
Rufe ido tayi wasu hawayen suka sauko a guje masu zafi.
"Na yafe maka. Allah Ya yi muku albarka."
Abbati na jin haka sai ya ce "Baaba don Allah ki tambaye shi me ya sami Qibdiyyan"
Munazali yaji tambayar da yayi. Wani daci ne ya taso masa daga makogaro har wuya a sanda ya ce
"Fyade aka yi mata Baaba amma don Allah kada ki fada masa. Bata ji ba bata gani ba ta soma girbar shukata tun kafin ta fahimci duniyar kanta."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Baaba Mari ta fada tana jin kamar ciwonta zai dawo. Masifun zamanin nan sun yi matukar yawa.
A gigice Abbati ya ce "mutuwa tayi?"
Da ta girgiza masa kai sai ya ce "Baaba ki bani don Allah ko sallama ne muyi dashi."
Tausayi ya bata ta mika masa wayar sai dai yana karawa a kunne yaji kit Munzali ya katse kiran. Kiransa ya yi amma taki shiga domin kuwa yana katsewar ya kasheta. Ya kuma lallaba ya kashe sauran ukun ma wadanda duka Abbati yana da lambobin.
Da Abbati ya gaji da gwada kiransa ya dubi Baaba Mari tamkar karamin yaro ya ce "kinga ya kashe wayoyinsa."
"Saboda yana son ka shiga sahun masu bin maganar iyayensu."
Bai iya cewa komai ba sai kifa kai da yayi akan cinyarta yana sheshekar kuka. Ita ma nata hawayen take yi saboda nauyin raba wannan abota. A bangaren Munzali kuwa shi ma kwanciya ya yi yana jin yadda hawaye suke gangarawa cikin kunnuwansa.
*
Gari ya waye yau ta kama litinin. A garin Kaduna Mardiyya da Sauda sun shirya sun tafi makaranta. A Kano ma Ayaah tana shirin tafiya tasu makarantar. Dukkaninsu suna aji shida ne a makarantar sakandire. Kwanaki kalilan suka rage su fara jarabawar NECO. Ayaah bata sami damar yin JAMB ba sabods rashin kudi amma su sunyi.
Kunun tsamiya Ayaah ta damawa Anti Hasiya kafin ta fita. Tana sanye da farin dogon wando da shudiyar rigar da ta kawo mata har gwiwa sun sha karin guga. Fitina irin ta dalibai rigar ta kamata tsam sai ka rasa yadda ma take iya numfashi.
A gaban Anti Hasiya ta durkusa da flask din kunu tana tambayarta ko ta zuba mata kafin ta tafi makaranta.
Yamutsa fuska Anti Hasiya tayi saboda rashin dadin baki. Jikinta gabadaya babu dadi ta rasa gane a wace duniyar take. Tunda aka sallamota ta kasa tabuka komai a cikin gidan. Daga amai sai kwanciya. Ita ce zazzabi ita ce ciwon kai. Honourable kansa ya zama kamar mai jinyar. Hasiya ita ce zuciyar gidansa. Matar rufin asiri ce wadda baya fatan ya shiga cikin sahun mazaje masu butulcewa a lokacin samu. Shi da yaransa duka rige rigen kyautata mata suke yi. Ga Abbas an sanya ranar aikinsa nan da sati hudu. An hado shi da magunguna kuma ana ganin amfaninsu. Sai da ta gama yi mata fadan dinkin rigarta wanda bata san lokacin da aka tsuke shi ba da kashedin tana dawowa yau ta bayar a budeta sannan ta bata amsa.
"Kadan zaki zuba amma ki matsa min lemon tsami a ciki"
Ayaah ta fiddo ido waje ba shiri da taji abin da ta ce.
"Tsamiyar ta fito fa yadda kike so. Don Allah ki hakura ki sha a haka."
"In kin tafi ma Murja zata bani, gara ma ki saka min kawai."
Rabin wani dan karami Ayaah ta matse mata sannan ta dauke ledar lemon tsamin ta tura a jaka akan idon Anti Hasiya.
Ita kuwa ta marairaice mata saboda tsamin kadai ke taimaka mata ta sanya wani abu a cikinta.
Murja da ta zama raguwar karfi da yaji saboda tsabar tausayin halin da antinsu take ciki ta taso za ta duba jakar Ayaah ta dauki lemon tsamin. Ayaah ta galla mata harara tana kankame jakarta. Cikin fushi ta ce no
"Tunda ba ke za a haifawa kanin ko kanwar ba ai gara ki bata tasha ta haifo mai yamushasshiyar fata irin na Altine. Kin manta yadda muka dinga tsoron daukar dan saboda kamaninsa da tsofaffi?"
Murja ta ja tsaki "sai aka ce miki lemon tsami ne ya busar masa da fata?"
"Idan ma dai ba shi kadai bane wallahi kika bata bayan na tafi makaranta ban yaf..."
Anti Hasiya bata san lokacin da tayi murmushi ba.
"Ya isa Ayaah ba ma zan sha ba kada Allah Ya isan ta bini nima."
Duk sai suka yi dariya har Ummi da ke wankin wake. Bayan fitar Ayaah shiru Anti Hasiya tayi tana mai al'ajabin kudurar Ubangiji. Watanni biyu da suka wuce idan ance Ayaah zata sauko daga dokin da ta hau su zauna lafiya zata karyata. Sai gashi cikin lokaci kankani da ta dage da addua da kuma bin shawarwarin Salima komai ya sauya. Ko yanzu sai dai tayi ta hamdala ga Allah. Rayuwa kam tayi juyin alkhairi dasu. Zuwan Minister Abdulkarim ya kawo musu canji a rayuwa. Abbas ana sa masa rai da samun lafiya. Kan 'ya'yanta kuma a hade yanzu sannan uwa uba wannan gagarumar kyauta ta samun ciki.
Ayaah na adaidaita sahu wayarta ta dauki ruri. Lokuta da dama tafiyar kafa take yi kusan mintuna talatin a hanya zuwa da dawowa. Yanzu kuwa kudin mota na sati aka bata wannan satin. Mamakin mai kiranta da sanyin safiyar nan me ya kama ta. Cikin aljihun wandonta inda ta boye wayar ta zura hannu ta lalubota. Dama ta tafi da ita ne domin kawarta ta saka mata fim. Sunan Dani ta gani baro baro a jiki. Gabanta ya yi mummunar faduwa da ta tuna haduwarsu ta karshe. Amma abin da yafi tsaya mata a rai kuma ya sanyata tsorata bai wuce fuskar wannan saurayin da taji kannensa sun kira shi da Ya Suhaib ba. Ta shaida irin bacin ransa lokacin da Dani yake neman tabata. Tayi ta kokarin hana kanta tunanin abubuwan da suka faru ranar sai gashi wannan wayar ta dagula mata lissafi.
Wani kiran ne ya sake shigowa wancan na tsinkewa. Numfashi ta sauke da karfi sannan ta amsa. Cikin kwantacciyar muryar da ya saba hillatarta da ita ya yi magana. Sai dai wannan karon fushi ya nuna mata.
"Baby ni zaki kai gidan kakanninki ki wulakanta?"
Daburcewa tayi ta ce "wulakanci kuma Dani? Me nayi maka?"
"Au tambayata ma kike yi? Don na bude miki cikina kin san sirrin gidana shi ne kika kira yayanki yazo ya wulakantani. Me ya hanaki tsayuwa kiyi masa bayanin alakarmu banda kina min kallon dan iska?"
Gabadaya hankalin Ayaah sai ya tashi ta soma bashi hakuri. Ya dinga ja mata rai har sai da direban adaidaita sahun ya dan waiga ya kalleta saboda jin yadda take magiya.
A gadarance Danliti ya ce "Abu daya ne zai sa na hakura Baby. Zan zo makarantarku na daukeki anjima ki zo ki gaishe da Mummy"
Da murnar ganin rikicinsu yazo karshe Ayaah ta ce "ta dawo ne?"
"Ta dawo kuma na fada mata komai game dake. Tana son ganinki ne domin gobe ta yiwa kawunnai na magana. Wikent (weekend) dinnan sai su zo su ga Baba asa mana rana."
Dan jim Ayaah tayi kafin ta ce "yanzu makaranta zanje kuma gaskiya Anti Hasiya ba za ta yarda na bika ko ina ba."
"Matar da kika ce bata sonki."
Ita ta fada masa da bakinta amma da ya maimaita sai da taji mugun haushi. Yanzu kam uwa ta dauki Anti Hasiya kuma ba za ta yarda wani ya fadi maganar batanci akanta ba. Kwalla taji a idanunta ta daukesu da yatsanta. Danliti tuni ya gane zuciyarta a karye take. Hakuri kawai ya bata ya cigaba da dorata a keken bera.
"Ban san me nayi miki wanda ya dauke duk wata daraja da girmana da kike gani ba a baya. Ni dai alfarma nake nema ko daga makarantar ne ki zo muje taga zabina. In Allah Ya yarda nan da sati biyu ko ba ayi biki ba na tabbata an daura mana aure"
Sunan makarantar ta bashi tare da fada masa yadda zasu hadu idan an fito break karfe goma da minti arba'in da biyar.
Goma daidai Suhaib yana cikin wani gareji a unguwar Na'ibawa wanda ya dace da kwatancen da Danliti ya yi masa. Wani Dan bumburutu ya samu ya kai shi wurin tun daga gadar da zata sada bako da farkon garin Kano daga titin Zaria. Garejin nasu sananne ne saboda kusancinsa da babban titin fita gari. Matafiya da yawa suna tsayawa ko a dauko musu makanike daga nan. Bayan ya sallami yaron da ya kawo shi ya karasa wurin ma'aikatan da suka yi da'ira ana ta mayar da zance da wani Alhaji.
Sallama ya yi musu sannan ya ce "Don Allah Danliti nake nema."
Kusan mutum hudu a tare suka ce masa ya fita. Wani ne ya kara da cewa,
"Kaima wani abu ya hadaka dashi ne?"
"Eh" Suhaib ya ce kai tsaye ganin kowa ya zuba masa ido da alamun bacin rai.
Taron sai ya karkato ya hada dashi inda a take yaji rigimar da ake yi. Motar da ya gama gyarawa ya dauka ya sanar da abokinsa na garejin wai budurwarsa ce bata da lafiya a makaranta shi ne zai je ya kaita gida.
Gaban Suhaib ya yi muguwar faduwar da bai san ainihin dalilinta ba.
"Don Allah waye ya san inda zan same shi?" Ya kara da cewa "me yace sunan budurwar?"
Abokin masa da aka tsare yana bada amsa kamar shi ne Danlitin ya dan jinjina kai kafin ya ce "baby dai naji yana ta cewa. Amma kafin ya tafi ya kira wani abokinsa da suke yawan zuwa nan tare Rabilu ya ce masa wai yau zai rufe shafin Ayaah. Sai dai gaskiya ni ban san abin da yake nufi ba."
Kwatanta irin rudanin da Suhaib ya shiga ba zai misaltu ba. Su kansu mutanen wurin sun tsorata da yanayinsa. Musamman da ya ce,
"Ku san yadda zaku yi ku hadani dashi kafin ya cuci yarinyar mutane domin wallahi idan ya taba mutumcinta gabadayanku sai na daureku."
Hargaginsa bai basu damar binciken ko shi waye ba. Suturarsa da motar da yazo da ita sun ishesu amsa. Dan garejin nasu da bai taka kara ya karya ba basu ga mai kwarjinin ja da Suhaib din ba. Shi ma kuma mai motar da Danlitin ya dauka yabi bayan Suhaib ya ce kararsa zai yi. Saboda haka nan da nan wurin ya kacame ana tattauna yadda za a same shi tunda yaki daukar waya kafin ya ida nufi.
I just published "36" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1106315246?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=%2FLt7cLBxCRjebLsBmlyCxirOQgEcocfxDAt12Yz5fTsGj3B%2BnR2rWBg4fLQ5qQ7JSNGYb7aSCF5dRDpjzrAlyImKmw8hPKZYgskdQUUwjuHe%2B4YjRcBozvRpvA2rlViA
UWA UWACE...36
Batul Mamman💖
Addu'ar samun rahama da kyakkyawan makwanci ga iyayen 'yan uwa da muke tare. Sisters Teema (mahaifi), Hadiza Yauri (mahaifi) da Hashal (mahaifi da 'yan uwa maza uku). Allah Ya jikansu da rahama Yasa sun huta.
***
Da sallamar da ya san babu mai amsawa ya murda hannun kofar dakin. Fitila a kunne take da alama cikin sauri aka manta ta. Ga kaya watse a ko'ina. Riguna ne da wanduna harda kwalaban turare na jiki da na kaya. Salihi ya yi ajiyar zuciya ransa duk babu dadi. Da kunnuwansa yaji Mubashir yana waya da abokinsa suna shirya yadda zasu fita party shadayan dare. Bai yi masa magana ba domin yana son tabbatarwa kansa Mubashir din zai je ko kuwa. Fitar da ya yi niyya ya fasa ya zauna a gidan ba tare da sanin dan nasa ba. Goma da rabi kuwa sai gashi ya fita daga gidan da sand'a a zatonsa babu kowa sai Ummule da ta dade da kwanciya.
Wata leda mai kyau Salihi ya gani a saman tebur din da Mubashir yake ajiye tarkacen makarantarsa. Ya dauka ya bude yaga sababbin takalma kala biyu da risit din sayayya. Abin da aka kashe na sayayyar ya girgiza shi. Bill ne na dubu casa'in da yan canji a sayayyar kaya. Shi dai bashi da kudin da zai iya bashi ya yi sayayya mai tsada haka. To a ina ya sami kudin?
A dakin yayi zaman jiransa har bacci ya kwashe. Goshin asuba ana tsaka da kiran sallah sai gashi ya shigo da sand'a. Rufe kofar yayi da sauri ya murda mukulli sannan ya kwantar da bayansa a jikinta yana ajiyar zuciyar tsira.
"Allah Ya soni Baba bai tashi ba"
"Ko kuma ni Ya soni da na kwana a dakinka ba."
Wani wawan juyi Mubashir ya yi a matukar razane yana kokarin murda mukullin kofar ya fita amma ya kasa. Ilahirin jikinsa babu inda baya ji yana rawa.
"Juyo ka dubeni Mubashir."
Maimakon ya juyo sai ya cigaba da kokarin fita har Salihin ya tadda shi inda ya juya masa baya. Hannunsa dake rike da mukullin ya