Showing 207001 words to 210000 words out of 242549 words
yake faruwa? Don zamu zo duba Suhaib sai mu fito a haka? Jallabiya ce fa a jikinka. Kalli yadda Shazali ya yi min da riga." Ya nuna masa kayansa da suka dukunkune kamar sun fito daga rami.
Ficewa Munzali ya yi daga motar idanunsa a rufe da bacin rai ya nufi gate din gidan ko kallonsa bai yi ba. Yana fita Abbati ma ya fito. Yana ganin ya daga hannu har ya buga gate din sau daya yayi saurin riko masa hannuwa.
"Munzali meye haka wai?"
"Sake ni Abbati. Ka sakeni in kamo dan iskan yaron nan..."
Gaban Mami Khadija yankewa yayi ya fadi ta damki hannun Lilu a tsorace.
"Muryoyin nan ba na Munzali da Abbati bane?"
Kafin ya iya cewa komai Abbati ya sake yin magana. Ransa a bace yake matuka don duka kafadun Munzali ya riko ya juyo dashi suka fuskanci juna. Zuciya ta tunzura shi ya daga murya yana fada.
"Wane yaro? Sai tambayarka me yake faruwa nake ka ki kayi magana. Me muke yi a kofar gidan nan?"
"Lilu zan kashe."
"Me???" Abbati ya sake shi babu shiri yana yi masa kallon mara hankali.
"Yadda bai iya tausayawa Qibdiyya ba nima..."
Da sauri Abbati ya dora hannunsa ya toshe bakin Munzali sannan ya ce,
"Shi ne? Qibdiyya ce ta fada maka?"
Munzali ya gyada kai hawaye yana zubo masa.
Mamaki ya kama Abbati ya ce "A yaushe? Duka duka sau nawa suka taba haduwa? Kaga zo mu koma gida..."
Zuciya da bata da kashi. A take ta Munzali ta shiga kuncin ganin kokonto a fuskar Abbati. Bai san lokacin da ya fuzge hannunsa daga gareshi ba ya ja baya.
"Nufinka karya nake yi?"
Sassauta murya Abbati ya sake yi saboda ko kadan baya so wani yaji sirrinsu. Da lallashi ya ce,
"Ba haka nake nufi ba Munzali. Wannan maganar tana da girma. Ka zo mu tafi mu fara yin shawara a gida."
Zuciyar Munzali ta kara zuwa wuya. Wace irin shawara kuma zasu yi a gida bayan gasu a kofar gidan da zasu sami Lilu? A tunaninsa jin sunan wanda ya bata Qibdiyya sai ya batawa Abbati rai fiye dashi. Me Abbati yake nufi da nuna sanya akan lalurar 'yarsu? Sai yanzu ma ya tuna cewa tun zuwan Abbati jiya ko sau daya bai tambaye shi waye ya keta mata haddi ba. Wani hawayen ne ya zubo daga idanunsa da suka rine kamar garwashi ya yiwa Abbati kallon takaici. Kallo irin wanda bai taba tsammanin zai gifta tsakaninsu ba.
"Sanin waye ubansu da kayi a yau dinnan bai isheka hujjar yarda da maganata ba? Ko soyayyar da kake yiwa Farha ce tasa kake kokarin kare kaninta ko kuwa don baka san zafin haihu.."
Tsayuwar gaggawa ce ta kama numfashin Abbati da bugawar zuciyarsa. Jikinsa ya hau bari saboda tsananin bacin ran sanin abin da Munzali yake shirin fada. Gumi ne kawai yake zubo masa kamar ruwa ga wani uban sanyi da yake ratsa kasusuwansa. Bai barshi ya karasa maganar ba ya dakatar dashi cikin zafin rai.
"KAR KA SOMA WALLAHI! Kada ka kuskura kayi min gorin haihuwar Qibdiyya don bacin ran da zamu shiga sai ya ninka wanda muke ciki a yanzu"
Munzali kasa motsawa ya yi ko kadan sai idanu da ya kafe Abbati dasu.
Shi kuwa Abbati jikinsa sai karkarwa yake kamar wanda zazzabi ya yiwa mummunan kamu. Bai haifa ba ya sani. Qibdiyya ba jininsa bace wannan ma ya sani. Fargabar da ya shiga ba komai ya janyota ba sai tsoron kada wannan masifar ta zama silar watsewar alakarsu da dan uwansa don ya wuce amini. Zai iya daukar komai banda gorin haihuwarta. Domin da zarar ya fito daga bakin mahaifinta kai tsaye zuwa gare shi, ya tabbata babu sauran zama a tsakaninsu. Munzali ba zai taba yi masa furuci irin wannan a halin rashin sani. Idan ya yi to tabbas daga zuciyarsa ne. Cikin sanyin gwiwa ya juya ya fara nufar motar.
"Ina za ka?"
Munzali ya fada da wata irin murya tamkar ba tasa ba. Yawun bakinsa ma daci yake yi masa saboda masifar halin da yake ciki.
"Ka same ni a gida idan ka aiwatar da abin da zuciyarka ta raya maka."
Yana rufe baki wani adaidaita sahu ya tsaya a gabansa wanda Munzali bai kula da lokacin da ya daga masa hannu domin ya karaso ba. A guje kuwa ya bi bayansa yana kwala kiran Abbati. Da suka ki tsayawa ya durkushe a wajen ya dauki hannu ya dinga dukan goshinsa da cikin tafin. Idan bai yi a hankali ba yana jin yana daf da zarewa. Banda haka me ya kai shi furta wandannan kalamai ga Abbati?
*
Gudun jinin Mami Khadija ya ninku, bugun zuciyarta ya zarce ka'ida. Tashin hankalin da ta shiga ya zarce tunani balle a fade shi. Duk wata kalma da ta fito daga bakin Abbati da Munzali ta sami damar shiga kunnuwansu ita da Lilu. Ma'anar zantukan nasu ya fita dalla-dalla basa bukatar karin bayani.
Daga gabar da suka fahimci inda maganganun suka dosa Lilu ya saki wayarsa a fusace ya nufi gate din. Kunnuwansa sun kurmance, haka nan idanunsa sun makance. Abu daya kawai yake hangowa shi ne hannuwansa a wuyan Munzali a yayinda zai tuhume shi dalilinsa na yi masa sharri.
"Me kake shirin yi? Ina za ka?" Mami ta tambaye shi a firgice lokaci guda ta riko hannun shi domin hana shi bude gate. Sa'arsu daya maigadin ya zaga bayan gidan zai cirowa matar gidan zogale.
Muryarsa tamkar ba tashi ba saboda tashin hankali ya dube ta da mamakin tambayar da tayi masa.
"Baki ji me ya ce ba? Ki barni in je..."
"Kada ka fita" ta furta tana girgiza masa kai.
Shi ma kan ya girgiza kuma sai lokacin hawaye ya sauko masa ya ce "idan ki ka hana ni fita zuciyata za ta iya bugawa Mami. Wallahi baki san yadda nake ji ba. Zan iya mutuwa...Mami ni ba Abbanmu bane. Ba zan taba yarda ko da wasa wani ya jefeni da irin abin da ya dade yana sanyaki kuka akan Abba ba. Kina ji fa akan sanin halinsa aka dogara da cewa ni nayi."
Daga nan bai kuma sauraronta ba ya fita da sauri. Cikin sa'a yana fita ya sami Munzali ya shiga mota kenan har ya tayar. Ba tare da bata lokaci ba kuwa ya zagaya daya barin ya bude.
Kallo daya Munzali wanda idanunsa suka yi masa nauyi saboda tsabar zubar hawayen da suke ya yi masa ya kashe motar. Mamakin karfin halinsa ya ma hana shi cewa komai. Sai Lilu ne da kansa ya ce,
"Ka kaini gidanka. Ka kaini gaban Qibdiyya in ji yadda aka yi na yi mata fyade."
"Kada ka sake ambaton sunanta. Kuma ka fice min daga mota don ban san me zan maka ba."
Wata irin dariya Lilu ya yi yace "kaga nayi kama da matsoraci ne?"
Domin samun damar wanke kansa a gaban Abbati ya fizgi motar a guje. Tashin motar ya faru akan idon Farha, Mami Khadija da Suhaib wanda ya fito yana jan kafa. Sai Prof Zuwaira da suka iso lokacin. Jama'ar gidan da suka biyosu bayan shigar Mami tana kiran Farha duka sun shiga tashin hankali. Da ta bawa Farhan mukullin mota akan su bi bayansu sai da matar kawun nasu ta ce ga direba ko ma mene ne gara wani ya kai su.
"Kiyi hakuri Anti. Idan Allah Yasa wutar ta mutu da kaina zan baki labari. Ki ara min yau ta zama sirrin gidana don Allah." Ta juya ta bawa Prof. Zuwaira hakuri da alkawarin zasu yi magana a waya in Allah Ya yarda.
Dole kowa ya hakura. Suna kallo Mami ta taimakawa Suhaib suka shiga baya, Farha taja mota da gudu. Kafin ta karasa kan titi ta kira Abbati bisa umarnin Mami. Da yake shima suna tsaye a junction ba a basu hannu ba shi yasa yaji kiran. Ganin sunan Farha ya bashi tsoro ko Munzali ya yi wani abu. Yana amsawa yaji muryar Mami.
"Kwatanta min gidanku"
"Lafiya kuwa Mami?" Ya ce a razane.
" Munzali ya tafi da Lilu."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Kuna ina yanzu? Bari na juyo. Ko dan gari ne zai kawo ku?"
"Mu kadai ne"
Inda suke kawai ya bukaci sani ya ce su jira shi a nan. Tsayuwar minti goma sha biyar suka yi domin ya hadu da goslow a hanyar dawowa. Kafin isowarsa ne Mami ta sami damar sanar dasu Suhaib abin da suka ji ita da Lilu. Hankulansu duk a tashe har Abbati ya iso. Yana zuwa bangaren direba ya nufa ya bude kofar. Farha tayi masa wani irin kallo wanda ko kusa bai bata masa rai ba.
"Ki bashi wuri ya tuka" taji muryar Mami a kunnuwanta.
Ba don ta so ba ta fita ta koma daya barin. Abbati ya dinga tukin 'yan Kano saboda tsoron abin da zai iya faruwa a gidan kafin su isa.
I just published "43" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221354829?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=JWAJxTZASApy6wCWp2SxqyncmVPlR75j0u6mfsma%2FRA4DJkEWK8dcy4Cd6t6X1KPZVzn7xOh%2Bvb%2Fvr04iNZxbfE14IvfhaUcIRPlHUyKV%2BAl3wqSUqBjA8wf8A%2F9Kn7%2B
UWA UWACE...43
Batul Mamman💖
***
Fitar su Munzali ba jimawa su Mal. Inuwa suka iso. Maigadi ya bisu har bangaren Abbati yana yi musu maraba bayan ya rufe gate din. Bai gane Mal. Inuwa da Mal. Sa'idu ba. Amma Habu ba bakonsa bane tunda yana yawan zuwa gidan. Sannan ya hadu da Baaba Mari sau biyu. A wurinsa suka ji cewa Abbati da Munzali basa gida amma Hanne tana nan. Da murnarsa ya dinga kwada sallama a kofar gidan tare da bubbuga dan hannun kwankwasa kofa da yake daga wajen.
Hanne tana tsakar cin abinci taji bugu. Tsaki ta jejjera sun kai goma sannan ta mike ta ajiye plate din da ta gama shakarewa da abinci.
"Waye ne?" Ta ce bayan sautin wani tsakin nata ya karade kunnuwan su Baaba Mari.
A gajiye suke su duka musamman ita da Mal. Sa'idu saboda yanayi na rashin lafiya.
"Iyayenki ne" Mal. Sa'idu ya furta da fada.
Faduwar da gabanta ya yi a lokacin ba na wasa bane. A iya saninta idan ka cire tafiyarsu Hajji bata taba ganin kawun nasu a Kano ba. Mantawa tayi da hannu ta fara cin abinci ta damki hannun kofar ta bude. Da d'ai-d'ai ta bisu da ido har suka shiga suka zazzauna. Habu ne kawai bai biyo su ciki ba ya tsaya suna sake gaisawa da maigadin. Hanne ta rufo kofar ta durkusa ta gaishesu. Babu yabo babu fallasa suka amsa. Na iyaye mazan bai dameta ba sai na Baaba Mari. Tunda suke bata taba ganin ta canja mata fuska daga faram-faram ba. Shi yasa taji gabanta ya soma faduwa ta fara tunane tunane barkatai.
Gauron numfashi da Mal. Sa'idu ya sauke da kyar na ciwon jiki ne yasa ta mayar da hankali gareshi a k'agauce.
"Ina yayan naki"
"Ya fita"
Mal. Inuwa ya ce "ya yi miki bayani akan abin da yake faruwa?"
Kafadarta ta daga da fari alamun ko-in-kula, sai kuma taga rashin dacewar hakan tayi saurin cewa bai yi ba.
Ita Baaba Mari ta riga ta san za a rina. Komai dangane da zaman Abbati da Hanne ba bakonta bane. Mal. Sa'idu ne ma yanayin nata ya dan bashi mamaki har ya kai ga tambaya.
"Wane irin zama kuke yi da dan uwan naki ne?"
Hanne na jin haka ta jinjina kai da cije lebe. Zuciyarta ta raya mata kila auren Abbati aka yi da 'Yashshafa shi ne iyayen suka zo da kansu don kada ta tada balli. Ido a rufe kuwa ta ajiye tsoronsa a gefe ta soma kuka da fadin maganganu.
"Haihuwa ta Allah ce ba ni na dorawa kaina ba. Tuntuni Baaba Deluwa take son amfani da hakan domin ta hada shi da 'Yashshafa..." Ta sake fashewa da kuka tana jan hanci "ashe sai da ku ka hadasu" 'yar karamar dariyar farinciki tayi da ta tuna wani abu wanda kuma bata barwa cikinta ba "Sai ta shirya, yadda na san ko zan hadiyi Al'Qur'ani ba zan kaffara ba cewa babu soyayyata a ransa na rantse har gwara ni akanta. "
"Bana son zancen banza. Me ya kawo zancen karin aure kuma?" Cewar Mal. Inuwa domin katse soki burutsun Hanne wanda zai iya janyo mata mummunan hukunci a wurin Mal. Sa'idu.
Shi kuwa gogan hannu kawai ya dan daga yace masa ya barta "yaran nan duk abin da suka yi basu da laifi. Tun farko na riga na fahimci zaman nasu babu armashi sai dai ban yi tunanin kawo musu maslaha ba. Idanuna sun da son ta zauna domin maganar abin da ya wuce a baya kada ta sake tashi."
Cikin tashin hankalin tsoron tabbatuwar hasashenta Hanne ta waro idanu tana cewa "Maslahar ce tasa ka bashi 'yarka?"
Rashin da'arta ya kara bawa Mal. Inuwa haushi ya daga hannu kamar zai kai mata mari.
"Za ki rufe mana baki ko kuwa? Idan auren aka yi masa ke kin isa ki kalubalancemu ne? Ko ruwa baki iya bamu ba sai surutan banza. Ko baki auri Abbati ma na zata zamu ci darajar zama yayyen mahaifiyarki"
'Shikenan! Ta tabbata an cikawa 'Yashshafa burinta. Yanzu Gwaggo Deluwa za ta yi yadda take so da Abbati. Karshenta ma tasa ya saketa' tunanin da yazo zuciyar Hanne kenan. A fili kuwa mikewa tayi cike da fitsara domin yau dai babu sauran tsoron Mal. Sa'idu a ranta ta ce
"Da kuna kaunar mahaifiyata da baku sa anyi min irin wannan kishiyar ba" idanunta akan Mal. Inuwa ta kara da cewa "irin wannan biyayyar da kake yiwa Baba Sa'idu wallahi sai...."
"Ke! Hanne? Baki san su waye a gabanki bane?"
Babu wanda ya kula da shigowar Habu sai da ya yi magana. Furucin nasa muguwar harara ya janyo masa daga Hanne. Ta dube shi sama da kasa ta tabe baki.
"Harda su kaza a cin danko? Idan ma kana tunanin kai wa Yaya Abbati gulmar abin da na fada ne to ka kwana da sanin cewa ko sakina ya yi ni ba zan saku ba. Wallahi zama daram a gidan nan ni dashi mutu ka raba."
Alamun tsoro ne ya bayyana a fuskar Mal. Inuwa ya dubi Baaba Mari da damuwa "Kina ganin abin da yarinyar nan take yi kuwa? Ko tana da mutanen boye ne bani da labari?"
Bahaushe ya kan ce a juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe. Baaba Mari da bata tanka musu ba ko kadan sai yanzu ta daga kai ta ce "uhmm?" alamun bata ma san me suke yi ba. Yau da ace babu matsalar da ta kunno kai a rayuwar Abbati da har dariya sai tayi domin ko surukarsu wato mahaifiyarsu Mal. Sa'idu da tana raye bata taba yi masa magana irin haka ba. A gidansu kam shi kadai ne ya isa, ragowar jama'ar 'yan bin umarni ne kawai. Sai gashi da ranta da lafiyarta ba a labari ba taga mutuwar bakin Sarkin gida Mal. Sa'idu. Yana zaune gurum ya kasa cewa uffan sai girgiza kai kawai da yake yi.
"Nace ko tana da mutanen boye ne?" Mal. Inuwa ya sake nanata tambayarsa.
Baaba Mari ba shi ta bawa amsa ba. Hanne da ta soma cewa garau take tana tsaka da son murguda baki domin cikar tsiwar ta dakatar.
"Ya isa haka Hanne. Abin da kike gudu ba shi ya faru ba. Dalilin zuwanmu ya zarce batun kishiya ko sakin aure."
Yanayin nutsuwa da haibar Baaba Mari a lokacin da tayi maganar saukarwa da Hanne wata irin kunya da jin nauyi tayi. Ta kalli iyayen nata maza ta sunkuyar da kai da fargabar me zai biyo baya. Ita kanta bata san me ya shiga kanta ya bata karfin gwiwar sakin baki haka ba. Kokarin durkusawa ta soma bada hakurin gaggawa take yi suka ji ana kiran sunanta da karfi da bugu kamar za a balle kofar gidan.
***
Sai da aka kwashi kusan minti goma da Zakiyya taji karar tada mota sannan Qibdiyya ta soma mutsu mutsu. Da sauri kuwa ta kai hannu domin ta dagata sai gani tayi ta soma buge-buge da ihu tana cewa "ka kai ni wurin Daddy na"
Firgicin da ta gani a tattare da ita ya bata tsoro ta tsaya ta kare mata kallo da kyau bayan ta rirrike hannuwan.
"Qibdiyya bude idanunki nice. Mummy ce"
Tarrr ta bude idon ta tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji. Ba shiri ta kai 'yan hannuwanta ta rungumo mahaifiyarta tana fashewa da kuka.
"Mummy ki boyeni kada ya sake tafiya dani."
"Waye?" Zakiyya ta tambayeta tana waige waige a dakin.
"Wanda ya gudu dani ya boyeni a gidansa jiya, kuma ya dokeni."
Tsoro ya sake kama Zakiyya. Gabanta na faduwa ta fara tariyo yadda Abbati ya shigo da ita gidan. Kamar an zabureta zuciyarta ta tsinke da mummunan tunani. Irin tunanin da yake zuwa kan kowace uwa a yayinda taga danta ko 'ya cikin yanayi mai cike da ayoyin tambaya. Babu bata lokaci ta dage mata siketa ta kai hannuwanta wadanda tsoro yasa suka yi sanyi kalau ta dubata. Wata irin gigitacciyar kara ta saki da ta tabbatar da abin da tayi zargi ya sami 'yarta. A lokacin bata ma iya tantance yanzu aka yi ko ya dade ba. Abu daya ne dai ta fahimta. Tabbas an raba 'yarta da darajarta tun bata san me duniya take ciki ba. A haka ta sabata a kafada ta fito a guje tana kiran Munzali. Da bata ganshi ba ta kira mahaifiyarta tana kuka amma ta kasa fadin me ya faru. A haka tayi hanyar gidan Abbati tana kiran Hanne.
***
Hanne dasu Baaba Mari babu wanda bai tako zuwa kofar gidan ba saboda karfin kiran da tashin hankalin dake tattare da muryar. Tana bude kofar Zakiyya ta fado ciki bata kula da kowa ba ta kama kokarin bude jikin Qibdiyya.
"Zo ki gani Hanne. An cuceni. An cuci ni Hanne"
Hannunta taji an rike kafin ta kai ga bude jikin. Ta juyo a birkice suka hada ido da Baaba Mari. A lokacin ta kula da mutanen dake cikin falon. Ta san kowa tunda suna zuwa Kirikasamma sosai a lokacin da take auren Munzali. Hawaye ne ya sake jika mata kumatu ta dora hannun Baaban a jikin Qibdiyya.
"Baaba Mari duba ki gani. Allah Yasa ni din ce ban gani daidai ba"
"Daukota mu shiga ciki"
Hanne ce ta dauko Qibdiyyan suka shiga wani daki a kasa aka bar su Mal. Inuwa da tunani.
***
Sai da ta gama shirinta tsaf wanda bai wuce wanka da mulka basilin ba ta nufi dakinsa. A kwance ta same shi ya yi shame-shame a kasan fanka yana jan minshari. Duk shige da ficen da aka dinga yi a gidan tun safe akan batan Qibdiyya ko a jikinsa. Ranta ya sake baci ta cije lebe ta kai hannu