Showing 48001 words to 51000 words out of 242549 words
ko mamakin halayyar uwardakinta yanzu.
"Ayi hakuri dai. Na kamawa Gaji ne saboda baki da ...."
Da hannu Zara ta dakatar da ita "ni ba surutu na tambayeki ba. Ga leda nan a kasa ki miko min."
Da azama ta dauko ledar ta mika mata sannan ta fita daga dakin. Tana zuwa bangarensu na masu aiki suka tuntsire da dariya. Duk sun san bakar kyuya da son jiki irin na Haj. Zara. Ko kadan bata son motsa jikinta a dole ita matar Alhaji. Komai sai mai'aiki tayi mata. Ba komai bane dalilinta na yin haka illa son nesanta kanta da tunawa da asalinta. Ba za ta ce ga wani lokacin kirki da Innayo ke zama da suna gida. Kullum ita ce karshen bacci kuma farkon tashi kuma har yau bata huta ba. Ita kuwa za ta mori arzikin mijinta son rai. Ba don shi din ma ba mai son bada kudi bane da ta fi haka fantamawa. Tsarin Alh. Unais shi ne wadata iyali da duk kayan jindadin rayuwa amma kafin su ji kudi hannunsu sai a dade. Da yake amaryarta ta fito daga gidan arziki ko kadan bata damu ba. Ita kuma girman kai da gudun asali sun hanata nemawa mahaifiyarta agaji. Aurensu da wata biyu mahaifinsa ya fitar da zakka. Da kansa ya tambayeta idan babu laifi a bawa Innayo duk da ya kula ba wani damuwa tayi da ita ba.
"Allah Ya sauwake. Sai kace almajira? Ko so ka ke 'yan uwanka su cigaba da raina ni?" Ta zauna a kusa dashi "don Allah kar ka taba karbar komai ka kai gidanmu. Idan zance ya zagayo ni ce darajata za ta zube a idanunsu."
Haka take zaune duk abin da take so indai bai saya ba bata yarda ta tambaya. A haukanta duk ranar da ta tambaya zai zama kamar ta amince ita din 'yar talakawa ce. Wata rana zai iya goranta mata ko kishiya ko wani a danginsa.
Ledar zazzage a gefenta ta karewa kayan ciki kallo. Turaruka ne da suka amsa sunayensu har guda goma.
"Ga turaruka ki zabi biyar ko kuma ki zuba duka a akwatin zuwa asibitin. Bana so ko da wasa a dauki dana ace anji wani abu ba kamshi ba"
Ta tuna kalaman Alh. Unais lokacin da ya ajiye ledar da zai fita kasuwa. Daya bayan daya tabi ta fesa domin tantance kamshinsu. Ta gama ta shafa cikinta tana murmushin jindadi. Sai yanzu a haihuwa ta shida da ake jira ko yau ko gobe likita ya tabbatar musu da cewa da namiji ne. 'Yan matanta biyar na kishiyarta uku. Alh. Unais ya kwallafa rai akan samun namiji. Tun cikin yana wata hudu da aka fada musu mene ne yake bata kulawa ta musamman. Babu abin da ta nema ta rasa. America ma yaso kaita haihuwa amma Hajiyar Fatakwal mahaifiyarsa ta hana. A cewarta lokaci ne na nunawa dangi ya sami magaji. Idan sun bar kasar dokin dan zai iya raguwa a zukatan dangi.
Abubuwan alkhairin da Zara ta samu a tsukin lokacin ita kanta bata san adadinsu ba. Ga dan Adam da son idan yana cikin farinciki ko samuwa ya sami mai taya shi murna. 'Yan uwanta da ta wofintar take kewa sosai. Su take son burgewa su tayata murna amma da kunya ta fara binsu yanzu. Uwani ce dama suke mu'amala to ita kuma rokon tsiya gareta. Ga aiki ga albashi amma kullum kiran babu da tambayarta abubuwa take.
Ba don taso ba ta tashi ta bude wasu akwatuna da suke shakare da sutura sababbi marasa dinki. Ciki harda na barka da take samu na haihuwa da kuma na wurin mijin da abokansa. Tunda hannunta a kame yake irin na Alh. Rabi'u ba kasafai take kyauta ba. Idan barka ta tashi kuma mijinta yana saya ya bata ta kai. Wasu lesuka ta dauko masu tsada amma wadanda aka ci yayinsu kimanin shekaru shida da suka wuce lokacin haihuwarta ta hudu. Komai na akwatin ma na barkar yarinyar ne wadda bayan haihuwarta tayi rashin lafiya. Shi yasa bata diddinka kayan sosai ba. Guda hudu ta zabo za ta bawa Innayo, Hasiya, Salima da Maimuna su dinka su saka ranar sunan danta. Tana zuba su a leda ta tuno bala'in Hasiya ta karo atampa daya za ta karawa Innayo da ita. A kalla babu mai rainasu wannan karon ba kamar sunan 'ya'yanta na baya ba. Haihuwa ta biyar da kanta ta ce musu babu taro don kawai kada a maimaita irin na da. Basu zo ba kuwa aka ci suna aka watse. Kowa ya yi cigiyar danginta sai ta ce Innayo ba lafiya.
Wayarta ta janyo ta kira Uwani bayan ta kwanta saboda bata jurar aiki. Lokacin kusan rabin awa kenan da rabuwar Innayo da Uwanin a cikin asibitinsu. Ranta duk a jagule saboda rashin nutsuwar da ta saukar mata sakamakon rashin kyautatawa mahaifiyarta. Ganin wayar Zara sai ta saki ranta ta dauka da murmushi.
"Haj. Zara ikon Allah. Matar Alh. Unais uwar Maryama."
Zara ta murmusa "duk ni kadai Yaya Uwani?"
"Kin isa ne kanwata."
Uwani ta saba yi mata bambadanci saboda kwadayin samun wani abu a jikinta bata san irin zaman da take ba.
"To ni dai ya ku ke?"
"Lafiya kalau. Muna nan zamu fara shirye shiryen tafiya Saudiyya. Allah Ya yi Hajjin bana mun amsa kira."
Dan yamutsa fuska Zara tayi saboda bata son yawan surutu kuma ta san shi Uwanin zata yi mata.
"Na tayaki murna. Allah Yasa ayi maqabuliya."
Uwani ta murmusa amma da dukkan gaskiyarta ta ce "Amin. Zan zo karbar 'yan riyalan da ku ke dawowa dasu dai."
"Hala kin manta na fada miki watan nan zan haihu?"
Jin kamar ranta ya baci Uwani ta kwantar da murya tana tambayarta lafiyarta. Basu dade ba fushin ya gushe Zara ta labarta mata tanadin da maigidan yake yiwa haihuwarta.
"A Afficent za ayi suna. Ya biya kudi ko da sunan ya kama rana daya da masu biki zai biyasu kuma ya kama musu wani wurin. Ni abin da yasa na kira ki dama kaya ne za ki zo ki karbarwa su Innayo"
Fadin maganar ya yi daidai da shigowar Hajiyan Fatakwal falon Zara. Isowarta garin kenan ta taho bangarenta ta duba ta taji tana waya. Zama tayi a kujerar da tafi kusa da kofar dakin tana dan danna kafafunta da zummar jira ta kammala.
"Bana so wannan karon su zo a tsummokara ayi ta kallonsu."
Uwani tayi 'yar dariyar kalmar tsummokara sannan ta fada mata zuwan Innayo din asibitinsu.
"Wai ciwon hakori take kuma na ce muje a duba taki."
"Kar ma ki damu indai ciwon hakori ne da kanta za ta nemeki. Ba ma dole su yi ciwo ba. Ni kaina wallahi ina kyamar kalar hakoran nan nata." Zara ta fada tana bata rai.
"Kin san da ciwon sai da ta karbi dubu hudu a hannuna. 'Yan gulmar abokan aikina suka dinga tambayar wace na bawa kudi ni kuwa na ce matar makocinmu."
Haushi ya kama Zara. Ko me yasa Innayo ta auri mutum irin mahaifinsu bata sani ba. Hatta sauran 'yan uwanta tana bakincikin yadda suka auri talakawa. Ba dole su lalace ba. Ace maza ba za su fita su nema yadda masu kudi suke yi ba. Kalaman Uwani basu dameta ba bare su bata mata rai.
"Ni dai ki zo ki karbar musu su dinka da wuri don wallahi INA JIN KUNYAR NUNA INNAYO A MATSAYIN MAHAIFIYATA. Duk ta tsufa fiye da shekarunta. Rannan da muka je da su Maryam fa tana kiransu kin zuwa suka yi. Da muka fito Mas'uda harda amai kuma duk akan fatar jikinta da kalar hakora. Daki sai wani bashi bashi ni kaina da kyar na dinga hadiyar yawu."
Hajiyan Fatakwal mamaki kamar ya kasheta a zaune. Tuni ta manta da matsar kafa ta kasa kunne da kyau tana ji. Kalaman karshen ne suka tunzurata ta tashi ba shiri ta bankada labulen dakin ta shiga. Ba shiri Zara ta katse wayar ta tashi tarbarta harda su runguma.
"A'a kar ki kuskura ki tabani" cewar Hajiyan Fatakwal tana ja da baya "ina naga mutumcin da zai sa ki kaunaceni da zuciya daya tunda ki ke kunyar nuna uwar da ta haifeki."
Baki daya jikin Zara sai ya hau rawa. Hajiyan Fatakwal kuwa ta dinga surfa mata ruwan bala'i.
"Da wannan mummunar zuciyar a kirjinki ki ke haifa min jikoki? Wannan ba don nima a tsaye nake ba kila da Unais ne zai ce shi ma yana kunyar nuna ni."
"Hajiya don Allah ki yi hakuri" Zara ta furta a hankali tana kuka. Kukan tsoron kada surukarta ta tsaneta ko tayi mata iyaka da daular gidan.
"Wa? Ni? Ai ba ni zaki bawa hakuri ba."
Ficewa tayi tana mamakin wannan abu. Ka haifi da a cikinka ya dinga cewa yana kunyar kasancewarka uwa gareshi. Tabbas ta sani wasu iyaye matan suna abin da zai sa 'ya'yansu gudunsu musamman hali mara kyau. Amma wannan fa zancen kalar hakori da yamushewar fata take yi. Bangaren da take zama idan ta zo gidan ta tafi tana ta juya zancen a zuci.
***
Anti Hasiya ta tarar da Innayo ba yadda take saboda ciwo. A daidaita sahun da ta shigo ko tsayuwa bai gama ba ta diro saboda sauri.
"Hajiya kudinki dari biyar."
Sai a lokacin ta ankare da yadda ta fito daga ita sai waya babu jaka. Salati ta soma yi shi kuwa zai fara tijara Innayo ta taso da kyar ta mika masa dubu daya cikin kudin da Uwani ta bata. Chanji ya mika musu ya tafi yana surutan samari marasa kunya.
Ido cike da kwallar kumburin fuskar Innayo Anti Hasiya ta ce "Da kudi a hannunki ne? Na manto jakata garin sauri."
Abin da take dashi ta nuna mata sai Anti Hasiyan ta ce bari ta kira Uwani tazo.
"Kyaleta Hasiya. Bana ma son ganin likitan a wannan asibitin."
Anti Hasiya bata matsa mata ba ta ce "to bari na ranci kudi a wurinta sai mu wuce asibitin Nasarawa."
Suna haka sai ga wayar Honorable ya kira ya fada mata ta manta jaka. Da ta gaya masa halin da Innayo take ciki ya ce zai turo Ayaah ta kawo mata tunda asibiti dole sai da kudi.
"Ka ce ta wuce Nasarawa sai mu hadu a can"
Sai da ta gama wayar ta tambayi Innayo me Uwani tayi mata ganin har lokacin tana kwalla. Da kyar ta iya fada mata tana zubar da hawaye. Zuciya na zafi ta juya ta tambayi wani hanyar wurin karbar haihuwa ya nuna mata. Innayo na kiranta taki tsayawa. Salama tayi a wurin ko amsawa ba ayi ba ta banka kai ciki.
"Uwani Rabi'u nake nema" ta ce da wata 'yar matashiyar Nos a hasale. Teburin nurses din take duka da hannunta irin na wanda hakuri ya yiwa karanci
"Metron Uwani tana break sai anjima za ta fito."
Anti Hasiya kawai sai ta daga murya "Uwani Rabi'u. Uwani..."
Shiru tayi bayan katse wayarsu da Zara tayi tana son gaskata ita ake yiwa wannan kiran na rashin girmamawa ko kuwa.
"Uwani..."
'Kamar Hasiya'
Da sauri ta fito ai kuwa ta hango Hasiyan ta hade girar sama da ta kasa. Take takenta ta san indai ta kyaleta sai ta zubar mata da mutumci a wurin. Ga abokan aikinta sun firfito jin gulma.
"Muje waje Hasiya" ta kama hannunta za ta ja ta taji ta coge.
"Ba inda zani. Kudi za ki bani na kai Innayo asibiti."
Daure fuska tayi saboda ta san cewa ta bawa Innayo kudi ita ma Hasiyan sarkin nuna tafi kowa jinkai ba sai ta kawo ba.
"Wata ya yi nisa ba..."
Da yatsa Anti Hasiya ta nunata "wallahi ki ka kira min babu sai na tara miki mutane a wurin nan."
Kirjinta ta nuna tana kokarin danne fushinta kada su yi fada a wurin "Hasiya ni fa yayarki ce."
"Indai ke yayata ce to lallai Munzali (sakonta ne a haihuwa) da su Fati (wadanda suka hada uwa da marigayiya A'i ma yayyena ne)" ta kare maganarta da jan tsaki mai sauti.
Kasa kasa da murya Uwani tayi, dan kada a ji. Ta kula gaba daya yawancin abokan aikin kamar su matso inda suke dan tsabar son jin gulma.
"Ni kike gayawa magana Hasiya?"
Hasiya ta ce "dake nake Uwani. Kinga ki dauko kudi ki bani na kai Innayo asibiti idan kuma ba za ki bayar ba sai na ranta a wurin abokan aikin ki."
Uwani na jin haka ta sha jinin jikinta dan ta san ba ko shakka wannan ba karamin aikin Hasiya bane aikata abun da ta fada. Da sauri ta dauko jakarta, ta zaro dubu biyar ta mika mata. Hasiya ta karba ta jujjuya su cike da takaicin hali irin na yayarta.
"Indai dubu biyar ce nima ina da abin da ya fita, don na yi fitowar gaggawa ba na manto jakata a gida. Ki bani dubu goma, da zarar na koma gida zan aiko miki kudin ki in sha Allahu."
Haka Uwani ba yadda ta iya ta zaro wasu biyar din ta bawa Hasiya, tana so ta jaddada mata ita bashi ta bayar ba kyauta bane, amma kuma tana tsoron ta tabo Hasiya kada tayi mata tsiya a gurin nan. Haka nan ta hakura ta hadiye zancen a ranta ta juya da niyyar barin wurin. Batayi taku uku ba Hasiya ta kasa hakuri da wannan halin ko in kulan nata. Sautin muryarta a karye ta ce mata
"Yanzu Uwani ba za ki zo ki ko kallon halin da take ciki kiyi ba?"
Kafin ta bata amsa ta fice abinta ta nufi inda ta baro Innayo. Wasu a cikin abokan aikin Uwanin har sun riga su yin gaba, suna kallon inda Hasiya ta nufa suka ga ta riko Innayo nan suka fara kuskus. Daya daga cikin su wacce Innayo ta fara tambayar Uwani lokacin da ta zo asibitin ta ce,
"A'a wannan ba matar nan bace ta dazu da ta zo neman Metron Uwani?"
Hasiya ta juyo ta kalle ta, ta ce "mata kuma? Ita matron din taku bata gaya muku alakar su ba kenan."
Uwani ta cika tayi fam, ranta ya gama kai kololuwa wurin baci. Shike nan an kwaye mata baya a idon makiya.
Ita ko Nos da zakuwa ta tce "a'a bata fada mana ba."
Hasiya ta dubi Innayo taga kiris ya rage ta fashe da kuka. Girgiza mata kai take yi don tayi shiru gami da yafito ta da hannu tazo su tafi.
"Ba ma tafi ba Innayo ga abokan aikin 'yarki suna son saninki" ta matsa jikin Innayo din ta dafa kafadarta "ga MAHAIFIYARMU. Uwani yayata ce uwa daya uba daya."
"Ban gane ba fa. Ke da wa kenan?"
Daya daga cikinsu tai mata tambayar cike da mamaki.
Hasiya ta ce "ni da matron din ta ku mana." Ta cuna Uwani da baki. Ta juya tai tafiyar ta.
Nan ko wuri ya kaure da salallami, suna tafa hannuwa,mata an samu abun da ake so.
Hasiya na tafiya daya ta yiwa Uwani kallon mara hankali duk da kasa take da ita.
" Matron kika ce mana matar makocinku ce."
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ta iya cewa a zuci saboda kallon mujiyar da wanda ya isa da wanda bai isa ba ke jifanta dashi.
Su kuwa juyawa suka yi kan ka ce meye wannan kusan kowa ya samu labarin abin da ta yiwa mahaifiyarta. Wadanda suka ga Innayo cikinsu sun fahimci bata son asan cewa mahaifiyarta ce duba da yadda take. k
Kana ganinta kaga mutum dake fama da talauci daga yanayin jiki har sutura.
Hasiya kuwa kai tsaye asibitin Nasarawa ta dauke ta suka wuce. A take aka cire mata turame biyun dake azabtar da ita. Anyi mata allurai an kuma bata magunguna. Har suka kammala suka koma gidan can Dala babu Ayaah babu dalilinta ballantana ta kawo mata jakarta da ta manta a gida.
Kunun gyada mai dadi Hasiya ta dama mata ta sha da kyar.
"Ki barni haka ya isa" Innayo ta ture cokalin da ta kawo bakinta.
Tayi kicin kicin da fuska kuwa.
"Allah sai kin kara." Sai kuma ta soma mita "Haka kawai kina fama da ciwo ki kasa fada min?"
"Da ki ka zo din me ki ka yi banda kunyata 'yar uwarki? Na dauka kin fi kowa jin maganata amma ina...kina kallo ina cewa kizo mu tafi ki ka ki sai da ki ka amayar da cikinki. Mece ce ribarki?"
Hasiya ta saki murmushi "ai kuwa ni ce da riba. Yau an yi jana'izar girman kan Matron Uwani a Sir Sunusi." Sai kuma ta yi dariya ganin Innayo tana murmushi "banda abinki ma dai Innayo meye na damuwa. Ni da nake son ki bani hadin kai mu fara bincike."
Sai da ta kashingida akan gadon da autar tata ta karkarde ta gyara sannan ta ce "na me?"
"Neman 'yarki ta fari. Ina tsammanin wannan Uwanin dai musanyen asibiti ce."
"Kaniyarki"
Fadin Innayo tana son yin dariya ciwo ya hana. A cikin zuciyarta ta dinga rokawa Hasiya albarka tare da fatan ganin zuri'arta. A gefe daya kuwa kukan zuci take yi. Bata san da me ta ragi Uwani da Zara ba da suke gudunta saboda arziki. Ashe wahalar duk da tayi daga ciki har aurar dasu aikin banza ne? Ita Uwani ke kunyar nunawa duniya. Akwai Allah!
***
Irin kwalliyar da Ayaah ta sha ta zuwa asibiti kai jaka sai ka rantse gidan biki zata je. Bikin ma na masu kumbar susa ko 'yan karya. Idan ka ganta ba za ka ce tana tare da damuwar rabuwa da masoyinta Rabeel ba. Ga haushin Babansu ya rasa wanda zai aika kai kodaddiyar jakar Anti Hasiya sai ita.
"Idan nayi aure naga mai iko dani sama da mijina" ta fadawa kanta ta.
Tun fitowarta wani saurayi da ake kira Dangwarzo da suke harka dasu Rabilu ya kira Danliti a waya. Dama a sanadiyarsa Rabilun ya hadu da Ayaah duk da bata taba sani ba.
"Malama Ayaah sai ina" ya ce bayan ya iso kusa da ita.
Yatsina fuska tayi tana fatan kada Allah Ya kawo wanda ya santa ya gansu tare. Ta tsani Dangwarzo tsana mai girma.
"Sai inda ka aikeni."
"Maida wukar ba fada ya kawoni ba. Saukata kenan daga adaidaita na hango ki." Ya nuno mata wani cikin abokansu zaune a cikin dan sahu yana tazar kai "idan sauri kike ki shiga wancan abokina ne direban ba sai kin biya ba."
Kamar ta ce a'a sai kuma ta tuna ya ce ba sai ta biya ba. Tana faman rangwada da zuba kamshi taje ta shige ta fada masa inda zai kaita. Tafiyar minti biyar suka yi ya kira waya yana maganar da bata fahimta ba.