Showing 204001 words to 207000 words out of 242549 words
ga da yadda aka yi yake iya daga kafa ba. Ya dai dawo hayyacinsa da yaga bai fi taku biyar ya rage tsakaninsu ba.
"Abbati..."
A tunanin Abbati maganar da Alh. Tahir zai yi masa ba za ta wuce tuhuma akan 'ya'yansa ba. Saboda haka bai bari ya kai karshen abin da zai fada ba ya ce,
"Babu abin da ya taba mutumcin su Farha a a hannunmu. Ban kuma kawo kaina da niyyar aurenta ba kamar yadda yake a wurin Munzali sai da muka tuba" ya ciji lebensa na kasa wanda yake nuni da karayarsa yayinda ya cigaba da cewa "mun yi nadama, mun tuba har muna shirin barinsu kafin duniya taji a dalilin barazanar da Shazali yake yi mana...amma ban san me yasa Allah Yasa asirinmu ya tono ba a irin wannan yanayi."
"Asirina ne ya tono ba naku ba Abbati. Ni Allah Ya gwadawa IkonSa ba kai ba."
Da sauri ya daga kai ya dubi Alh. Tahir. Shi ma din Abbatin yake kallo. Idanunsa sun cicciko da kwallar da ya manta rabonsa da yinta. Haka ya cigaba da magana jikinsa yana mutuwa da kowacce kalma. A jikin motar ya jingina saboda babu sauran karfi a tare dashi. Ya daure dai ya fada masa cewa maganin bacci ne aka shakawa Qibdiyya saboda haka ya kwantar da hankalinsa zata dawo daidai nan da awa daya ko kasa da haka kamar yadda Comared ya fada masa. Yana ganin yadda Abbati ya shafa fuskarta cike da kulawa. A ganinsa wannan ita ce soyayyar iyaye da 'ya'ya ta gaskiya ba wadda yake ikirarin yiwa nasa ba. Zantukan da suka biyo baya kuwa ya yi su ba a cikakken hankalinsa ba.
"Ban taba tuba ba. Shekara da shekaru Khadija tana kuka tana hakuri dani. Sai yanzu ne ma wani dan dalili yasa ni nadama. Bukatar kawar da wannan dalilin ce ta kawo wannan lokaci. Kafin zuwanka ina tunanin akwai lokaci a gaba da zan sami damar yin hakan in tsufa ya kamani. Ashe lokacin zai biyoni yau? Suhaib ya sani! Farha ta sani!! Lilu ma ya sani!!! Amma hawayen 'ya'yana dana mahaifiyarsu bai sa naji lokacin tubana ya yi ba. Ba don abubuwan da suka faru ba a ciki da yanzu kila na amince anyi..." Karshen maganar nauyi ya yiwa bakinsa dole ya datse zancen.
Kamar saukar guduma maganganun suka dinga shigar Abbati. Farha ta san mahaifinta yana zina? Ko shi ne musabbabin ganin canjin da ya yi a gareta kwanakin baya da Alh. Tahir ya dawo gida suna wurin?
"Ban taba mu'amala da maza ba. Na yau din ma dalili ne" kamar an matsi bakinsa ya fadawa Abbati abin da yasa ya zo Kano yau da kuma dalilin nadamarsa. Wato sanin da Farha tayi cewa yana neman aminiyarta wanda da ace aurenta yake nema kadai ma da sauki.
"Mayafin da ya lullube soyayyar da 'ya'yana suke yi min naso yayewa. Na tabbatar fasa auren Yumna zai iya dawo min da martabata a idanunsu. Ashe Yumna ba ita ce matsalata ba. Ni ne matsalar kaina. Wallahi Abbati ina jin kamar na bude ido naji an shafeni baki daya."
Shi dai Abbati kasa cewa uffan yayi saboda shi ma din mai laifi ne. A nutse dai ya saurari dukkan maganganun Alh. Tahir wanda ya sake dauka a matsayin izina. Babban mutum, mai kudi, iyali, da kima a idanun al'umma ya tasa shi a gaba yana ta sumbatu. Ashe idan basu tuba ba nan gaba suna da rabon ganin rana makamanciyar wannan ko ma wadda ta fita muni.
Duk wata daraja da kimarsa shi da kansa yake jin sun gudu sun bar shi a dalilin haduwarsa da Abbati a gidan nan. Zuciyarsa har lokacin bata huta da kakkarfan harbin da take yi masa a kirji ba. Wace irin masifa ce tafi wannan? Ya aka yi bai ji girman laifinsa ba a lokacin da 'ya'yan cikinsa suka san sirrinsa sai yanzu a gaban mutumin da bai riga ya zama surukinsa ba? Kalmar surukin da ya ayyana a ransa ita ta sanya shi yin wani tunani. Babu bata lokaci kuwa domin tabbatarwa ya nuna saitin jerin wasu motoci guda hudu ya ce,
"Don Allah taimaka ka miko min wayata a cikin mota in kira likitana"
Durkushewa ya fara yi wanda hakan yasa Abbati yin saurin zuwa wurin motocin ba tare da ya tambayi wacce bace cikin hudun. Da d'ai-d'ai ya dinga bin tagogin motocin yana lekawa ko zai hango wayar amma bai samu ba. Ya taba hannun babu wadda ta bude. Ya dawo da sauri ya tambaye shi ,
"Wacce ce a ciki? Duka a rufe suke."
Maimakon ya bashi amsa sai yaji ya ce "Zina bata yarda taci bashi bata biya ba komai daren dadewa. Naji dadi da kunnuwana suka jiye min kalaman tuba daga gareka wanda yanzu na tabbatar baka fadesu domin ka san ina ciki ba."
Yana gama magana cikin gidan ya koma. Abbati ya sake taba jikin Qibdiyya sau daya bayan ya shiga mota ya zauna sannan ya tayar ya tafi.
***
Wani irin ihu Zakiyya tayi da Abbati ya shigo da Qibdiyya cikin falon Munzali tamkar bata da rai. Ya manta ta zo gidan da bai shigo kai tsaye ba. Munzalin ma hankalinsa ba karamin tashi ya yi ba da yaga hannuwanta suna kadawa su kadai.
"Me ya sameta kuma? Tare da Asaben ka daukosu? Ko ita kadai ta biyoka bayan ka ajiye su Innayo?"
Akan doguwar kujerar da Zakiyya ta tashi ya kwantar da ita.
"Maganin bacci aka shaka mata. Nan da. .."ya dubi agogon hannunsa "minti talatin idan bata tashi bane zamu nemi likita"
"Ka kara sakani a duhu. Me yake faruwa ne?" Cewar Munzali yana tattaba jikin Qibdiyya.
"Zakiyya bamu wuri don Allah"
Gyara zama tayi abinta a kusa da Qibdiyya tare da rike mata hannu.
"Gara ma ka fadi ko ma mene ne don babu inda zani alhali akan 'yata zaka yi magana."
"Zaki tashi ko sai na mugun bata miki rai"
Tsawar Munzali ta tsorata ta amma bai kai yadda zata iya bin umarninsa ba. Zai sake magana Abbati ya ce,
"Zakiyya ki dauketa ku je sama ki yi mata wanka. Nayi miki alkawari zaki ji duk wani abu da ya kamata idan na gama magana dashi."
Ba haka taso ba sai dai kuma a yau din Abbati ya yi mata kwarjinin da bata taba gani a tare dashi ba. Tashi tayi da Qibdiyya a kafadarta sai Munzali ya zo ya karbeta. Dakinsa ya kaisu ya fito ya rufe kofar. Da sauri ya dawo ya zauna a gaban Abbati. Shi kuma sai ya kama hannunsa suka fito waje ya bude mota suka shiga. Tafiyar kimanin minti goma suka yi wadda ta dan nesantasu da gida sannan Abbati ya tsaya.
"Ina so ka saurareni da kyau Munzali."
"Don Allah ka daina ja min rai haka. Wallahi kiris nake jira zuciyata ta buga kawai. Me ya faru?"
Tiryan tiryan Abbati ya shiga labarta masa abin da ya faru a daren jiya da yana kwance a asibiti har zuwa yanzu. Kai ya rike wanda yake azabtar dashi da bala'in ciwo da yaji karfin halin Shazali na daukar musu 'ya. Ga kuma bacin ran son tilasta Abbati ya koma ruwa. Murfin motar ya kama ya ji ta a rufe.
"Bude min Abbati. Ina jin nine ajalin Shazali." Ya furta a fusace idanunsa sun kankance sun kara yin jazur.
"Munzali ka daina magana irin wannan" Abbati ya ce dashi a tausashe.
Kallon takaici Munzali ya bishi da shi yana taune labbansa.
"Wacce iri ya kamata in yi? Fatan alkhairi zan masa ko me? Da ka amince fa? Da shegen ubangidan nasa ya taba Qibdiyya fa? Da me zan ji? Da me zan ji??" Karshen maganar muryarsa karyewa tayi sakamakon hawayen da ya soma bin fuskarsa.
"Idan kana irin wannan abin bana jin zan sami kwarin gwiwar karasa maka labarin nan."
Idanunsa fayau kamar fanko ya dubi Abbati ya ce "ina jin ka. Har akwai wani mummunan labari da zai kara tayar min da hankali makamancin wannan?"
Abbati bai bar komai ba game da haduwarsu da Alh. Tahir da kuma abin da Innayo ta fada masa na Ayaah da Suhaib. Sai ga Munzali ya kasa cewa komai sama da bude baki da rufe shi. Mamaki da kaduwarsa suka ninku dari bisa dari da ya fada masa abin da Innayo ta ce Suhaib ya yi na taimakon Ayaah. Da kuma wayarsa da Farha.
"Tabbas akwai kudurin Allah a cikin haduwarmu da iyalin nan. Ka duba kaga alakarmu da 'ya'yan gidan, da haduwata da babansu wanda ba don shi ba kila da Allah kadai Ya san halin da zamu shiga yau. Sannan ga taimakon tsare mutumcin Ayaah da ...
Yana cikin magana kawai yaga Munzali ya zura hannu ta gabansa ya bude lock. Hakan ya bashi damar bude bangarensa ya fita da sauri ya zagaya ya bude shi.
"Fito in tuka"
"Ina zamu je?"
"Don Allah ka fito. Wannan labarin ya bude min tunanina akan abubuwa da dama"
A zaton Abbati tunanin Munzali ya tafi daidai da nasa akan ganin akwai abin da Allah Ya yi nufi da Ya hadasu da mutanen nan. Bai san cewa a nasa lissafin ya kara gaskata cewa lallai Lilu ne ya bata masa 'ya ba.
***
Anti Hasiya da kanta ta hada kayan Abbas dana Honourable na tafiya asibiti. Ranakun farkon aikin ne zai dinga kwana. Daga nan kuma sai dan mai bin A'i ya cigaba da kwana. Larai ce ta dage bata yarda ya nemo mai kwana da jikanta ba a cikin danginsa. Mutanen da basu iya taimaka musu da hatsi ba a lokacin da komai ya jagule masa. Ita ma Anti Hasiya tayi na'am da shawarar. Ta san yaron ba zai kuskura ya yi wasa da lafiyar dan uwansa ba ko don gudun fadan kakarsa. Sun gama ta kira Innayo ta fada mata karfe nawa duka zasu rankaya asibitin. Ba za su dawo gida ba a cewarta sai an fito dashi.
"Inji waye ya ce ba za ku dawo gida ba? Ke fa na lura ganin kanki kike yi daidai da kowa" Honourable ya ce yana mai daure mata fuska da wasa bayan ta gama wayar. Tuni ta gano korafin nasa bai rasa nasaba da cikinta ba.
"Don Allah kada ka koroni gida wallahi fargaba ba za ta barni ba"
Illolin zaman asibiti da yanzun nan ya tattarasu a kansa saboda rashin son ta wahala ya shiga jero mata. Daga karshe ya hada da rarrashi.
"Hasiya bana son mu yi sakaci da taki lafiyar. Allah bai hana ni 'ya'ya ba kuma nagode Masa akan wannan ni'ima. Hakan bai hana ni kwadayin son ganin irin da zaki haifa min ba."
Murmushi ta bige da yi don ta riga ta san cewa ya gama cin wannan yakin. Da lokacin tafiya asibitin ya yi baki dayansu suka tafi aka rufe gida. Larai ma iyalanta a asibitin suka riskesu.
***
Ba karamin dadi Suhaib yaji ba da zuwan su Mami. Abin da bai saba yi mata ba ma ya dinga yi lokacin, wato raki da shagwaba. Damuwa da kulawar da take nuna masa ne bai gaji da gani ba. Ko yaya ya motsa kafar sai ya ce wash. Ita kuwa jiki na rawa ta dinga ambaton sannu, ko ta ce a koma asibiti. Mayafi ta yafa ta riga kowa mikewa tana cewa gara dai a je ayi x-ray a kafar. Matan gidan dasu Farha suka taru suna yi mata dariya da suka fahimci yana yi ne da gangan.
"Ki yi zamanki Mami tsokanarki kawai yake yi." Cewar Farha bayan kowa ya fita daga dakin an bar uwa da 'ya'yanta.
Kan Suhaib ta shafa cike da kulawa ta ce "idan ma karyar ciwo yake babu ruwanku. In yana so yau har goyo zamu yi."
Lilu da Farha basu san lokacin da suka sake kwashewa da dariya ba. Suhaib kuwa pillow ya dauka ya kare fuskarsa yana cewa,
"Haba Mami a gaban yara ki ke kiramin goyo don su raina ni?"
Daure fuska tayi cikin wasa ta ce "Kai ba a gaban yaran ka ke ta wash-wash ba saboda samun wuri?"
'Yan uwansa ya kalla suna ta dariya ya wulla pillow din saitinsu "Da daya daga cikinsu ne ba za ki ce suna yi don samun wuri ba"
Sai da suka gama zolayarsa ita da Farha da Lilu sannan ta dawo gefen gadon ta zauna. A ranta take kara jin cewa tabbas haihuwa kyautace daga falalar Ubangiji. Duk tarin bacin ran da babansu yake haddasa mata da ta kebe da yaranta sai ta manta da wanzuwarsa. Murmushi ta sakar masa tare da mika masa wayarsa.
"Saki ranka ka kira wadda tayi nasarar canja min kai daga sarkin zafin kai zuwa wannan Suhaib din dake gabana."
"Ummmmm"
Lilu da Farha suka fitar da sautin shakiyanci a tare. Mami babu bata lokaci ta nuna musu kofa tana shan kunu. Ficewa suka yi ana jiyo dariyarsu. Sai da suka rufo kofar sannan ta ce,
"Ayaah ce ko?"
Kallon rashin fahimta Suhaib ya yi mata ya amsa da cewa "tayi me?"
"Ta taba zuciyarka har kake yi min abin da ban taba gani ba tun tasowarka."
Kai ya shiga sosawa irin na marasa gaskiya "nifa babu komai a tsakaninmu"
"Sai ka dage ka gina abu a tsakanin naku kafin wani ya riga ka."
"Kai Mami..." Suhaib ya furta a kunyace yana kawar da kai. Da kafarsa kalau take ma da ficewa zai yi daga dakin a guje.
Zuciyarta tamkar an zuba ruwan sanyi ta dube shi ba tare da alamun wasa ba.
"Suhaib ka cinye kuruciyarka wurin dauke damuwata da kulawa da 'yan uwanka. Shi yasa ba ka san wasa ba balle yadda ake yinsa. You were too serious. Yau gashi Allah Ya amshi addu'ata. Da kan ka kake kirkiro wasa a tsakaninmu ba tare da ka san kana yi ba. Na san ba zai wuce haduwarka da niece din Munzali ba. Kana sonta ko?"
"Mami sa'ar su Sauda ce fa. Yanzu
take shirin gama secondary school"
"And so?"
Kada kai ya yi yana dariya ya ce "wannan hirar tayi min nauyi Mami a canja wata"
"An canja Suhaib. Ai ni yarinyar nan ta gama min komai. Allah dai Ya rabaka da sharrin late-comer. Idan ka tsaya wasa labari zai sha bamban."
"Allah ma Ya kiyaye"
Sai da maganar ta fito ya kama bakinsa. Karo na biyu kenan da ya fadi kalmar nan garera akan Ayaah. Tare suka yi murmushin farinciki. Mami ta sake dubansa, shi ma sai ya nutsu da ya gane magana take son su yi. Wayarta ta mika masa daidai sakon da ta turawa Abbansa. Ya karanta sau daya ya ajiye wayar a sanyaye ya ambaci sunanta
"Mami?"
"Na taba yunkurin neman sakin har sau biyu amma iyaye suka hana ni. Sai dai wannan karon kamar yadda na tura masa text dinnan to in sha Allahu babu gudu babu ja da baya."
"Su Yakumbo zasu amince?"
"Da Allah kadai na dogara. Shi ne Ya haramta zama tsakaninmu. Allah ne shaidata ban taba kusantar kowa a waje ba. Na killace kaina da taimakonSa. Kuma nayi imanin zai taimakeni akan kudirina."
Hannunta kawai ya rike yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Ba don rabon haihuwarsu ba da wannan baiwar Allah bata zauna ta kwashi bakinciki irin wannan ba.
"Na rasa kalmar da zan yi amfani da ita domin kwantar miki da hankali Mami"
"Kayi mana addu'a ni da ku Allah Yasa hakan alkhairi ne a garemu baki daya. Zaman da ake ta cewa nayi domin ku bai amfana komai ba sai tonon silili. Farha da Lilu na fada maka sun san komai. Da ace na tafi tun kuna yara da har yanzu kuna ganin mutumcin Abbanku. Akwai ciwo a dan da zai san mahaifinsa yana yawo a waje. Har gara mata akan dan cikinka."
Kwalla ce ta zubo mata Suhaib ya soma bata hakuri. Lokacin kuma Farha ta bude kofar saboda ta manta wayarta. Halin da ta riskesu ya daga mata hankali. Da sauri ta shigo tana kukan da ta riga ta gane musabbabinsa.
Wayar Danliti dake gefensa Suhaib ya budo ya mikawa Mami.
"Kinga sakayyar Allah. Ki daina damun kanki. Gara mu tafi kafin muma wata rana dattin ya shafemu."
Da ta karanta irin kazaman chats din Danliti da Jiddo bata san lokacin da ta kankame Suhaib da Farha ba.
"Kada ku kusanci zina. Wallahi a cikinta akwai tozarci da kaskanci. Ko da raina ko babu don Allah kada ku yarda shaidan yaci galaba akanku. Ba zan yafewa duk wanda ya aikata ta ba cikinku."
Suna cikin wannan yanayin Prof. Zuwaira aminiyar Mami Khadija ta kirata. Sai a kira na uku bayan ta saita kanta ta iya daukar wayar.
"Dr. Khadija kun iso?"
"Eh, a nan shadaya tayi mana."
"Kin ganni mun gama shiri zan bar Kanon yanzu ni kuma. Kwatanta min gidan sai na biyo na duba d'ana kafin mu wuce"
Cikin yaran gidan Mami ta samu aka turawa Prof. Zuwaira text na kwatancen gidan. A falo suka hadu da kowa ana taba hira. Suhaib kuwa zamansa ya yi a daki ya dauki wayarsa yana jujjuyawa. Muryar Ayaah yake son ji tana tsiwar nan. Har zai kira ya tuna ta ce babansu ya karbe mata waya. Komai tsaya masa ya yi da tunaninta. Anya zai iya barin Kano bai ganta ba?
Waya Mami ta cigaba da yi da Prof. Zuwaira inda take kara yi mata kwatance saboda sun kasa gane layin. Ta nemi Lilu domin ya fita hanya bata gan shi ba. Sauran yaran cikin gidan duka mata ne.
"Gidan shi ne mai bakin gate a close din. Bari na fito waje kila ku hango ni"
Tashi tayi ana cewa ta bari a tura wata cikin yan matan ta ce babu komai. Da wayar a kunnenta ta taho bakin gate din suna waya da Prof. Zuwaira. Zuwan Lilu ne ya taimaka wurin saukaka musu. Location dinsu ya turawa Prof. Zuwaira ta whatsapp din Mami. Ba jimawa kuwa sai ga kiranta ta ce layi daban suka shiga amma yanzu zasu juyo. Tare suka tsaya jiran isowarsu a bakin gate ta ciki yana ta tsokanarta wai zamani ya canja waye yake zaman cewa a bi hagu a karkata dama.
***
Saboda mugun gudun da Munzali yake saura kadan ya wuce gidan Kawunsu Suhaib sannan ya farga. Da sauri ya taka wani wawan burki sai da taya tayi kara sannan shi da Abbati suka yo gaba kamar an hankado su. Cikin fushi kuwa Abbati ya hau shi da fada.
"Lafiyarka kuwa Munzali? Wane irin tukin ganganci ne kake yi?"
"Kira Farha ka ce mata ta turo Lilu ya zo ya shiga damu."
Abbati ya kalle shi a tsanake ya adana bacin ransa domin son fahimtar inda matsalar take.
"Me