Showing 240001 words to 242549 words out of 242549 words
Tahir kuma ya ce zai tafi da Alh. Sadisu don gujewa kananun magana kamar yadda Mami ta ce. Harda direbobin zasu tafi. Idan suka gama zasu dawo su daukesu su wuce.
Mai aiki ce tayi jigilar kai kayan abincin falo. A ciki kuma ba babba ba yaro an hadu ana bawa Mami Khadija labarin hoton Farha da Abbati. Ita da tayi hoton ma sai yanzu kunya ta rufeta. Dariyar da Mami Khadija tayi ne yasa "Mami sharri ne fa. In akwai su nuna miki."
"Lallai ma Ya Farha. Bari naje na karbo wayarsa" inji Lilu uban gayya.
Suhaib ya janyo hannunsa "dawo gadanga abinci zasu ci"
Falon Mami Khadija ta tura mazan. Su Mardiyya ta saka su aikin hada fruitsalad sannan ta tsare Farha a daki.
"Na jima rabona da ganinki cikin yanayi irin wannan na zallar farinciki Farha." Kai Farha ta sunkuyar. Mami ta cigaba da cewa "bana so ki zura jiki da yawa. Tun haduwar farko na lura Abbati yana da hankali. Na tabbata faruwar wannan lamari ne ya koresu. Kin ji ance basu da komai yanzu. Sai dai nayi imani tunda Alh. Sadisu yake bibiyarsu he has a plan for them. Abbanku ma ya ce akwai abin da ya shirya. Tambayata a nan Farha za ki iya zama da Abbati sabanin yanda kike zatonsa?"
Idan tayi shiru tabbas za ta kwari kanta. Sannan bata kasance cikin masu zurfafawa da naci ba tare da neman zabin Allah ba.
"Ina addu'a sosai Mami. Sai gashi na ganshi a wurin da ban taba zato ba. Indai kin yarda dashi in sha Allah zan iya zama dashi.
Cikin farinciki Mami Khadija ta ce "Alhamdulillah. Abbanku ne ya ce na tambayeki kafin su dawo don yana so a yau a tsayar da magana guda."
Da gudu Farha ta bar dakin saboda kunya. Dakinta ta shiga tayi sallah ta sake gyara fuska. Tana gaban mudubi taji kira ya shigo. Haka kawai jikinta ya bata Abbati ne. Da ta duba kuwa sai taga bakuwar namba. Sake kira aka yi still taki dauka. Sai ma haushi da taji cewa yana da nambarta amma bai taba kira ba. Fitowa tayi daga dakin suka kusa karo da Lilu. A ranta tace dama ya saba rawar jiki idan ya gansu.
"Yauwa dama ke nake nema. Wai ya ce ki fito ku yi zance"
Bakin Lilu ta rufe da sauri ta waiga hanyar kitchen. Ai kuwa masu aikinsu biyu suna wurin kuma sun ji. Ga Sauda da Mardiyya. Sai suka hau yi mata dariyar shakiyanci.
49
Bakin Lilu ta rufe da sauri ta waiga hanyar kitchen. Ai kuwa masu aikinsu biyu suna wurin kuma sun ji. Ga Sauda da Mardiyya. Sai suka hau yi mata dariyar shakiyanci.
Falon ta nufa zuciyarta tana dukan uku uku. Tana yin sallama Abbati ya ajiye cokalin hannunsa ya bita da ido. Munzali ya hada ido da Suhaib sai kawai suka tashi. Ya zo bakin kofa ya juyo ya kalli plate dinsa wanda ya cinye abincin tun kafin shigowarta.
"Abbati ban koshi ba fa. Na dawo na karasa?"
Jinjina kai Abbati ya yi rai a bace. Munzali ya rasa lokacin yi masa haka sai a gaban Farha. Bai san lokacin da harare shi tare da gargadi ba.
"Kada ka bari na tashi Munzali"
"Za ki iya da wannan mafadacin? Ko dai za ki koma ciki ni na karasa cin abincina?" Munzali ya sake zolayarsa kafin ya fita da sauri da Abbati ya yunkura zai tashi.
Kujerar farko idan an shigo Farha ta samu ta zauna. Abbati sai ya ajiye nasa plate din akan tray ya taso ya dawo ta kusa da ita. Yana kallon alamun takura a tare da ita. Ta hade yatsunta tana ta wasa dasu.
"Ya Farha"
Tsigar jikinta tashi tayi saboda yadda tayi kewar sunan a bakin wanda ya furta shi.
"Uhm"
"Ina neman alfarma. Farha-ta nake son magana da ita. Wadda ta sauke min alkawarin da nayi na daukar hoto da ita"
"Me yasa kake nemanta bayan baka damu da ita ba?" Ta furta a raunane.
Yana ji ya san ranta ya baci da shirunsa. Dole ya rarrasheta in yana son ta fahimce shi.
"Bana bukatar fada miki matsayinki a wurina. Amma ina so ki sani cewa zuciyata bata taba samun hutu ba tun ranar da na fara ganinki"
"Ta yaya zan yarda bayan kai kadai kake yadda kake so. Lokacin da ka ga dama kawai kake nemana" tayi maganar cikin zubar hawaye.
"Ki yi hakuri. Nayi zaton hakan shi ne mafi alkhairi saboda halin da muka tsinci kanmu ni da Munzali"
Sai ya kara bata tausayi. Ta dube shi da hawayen idanunta "kana ganin ya dace kai kadai ka yanke hukunci akan abin da ya dace ba tare da jin ta bakina ba?"
Idanunta dake cike da kwalla ya fara kallo sannan duka fuskar da kuka ya fara kumburawa. Wani abu mai girma ya sake motsa zuciyarsa. Sonta da burin mallakarta a matsayin matar aure ya mamaye tunaninsa. A cikin nutsuwa ya ce mata,
"Kiyi hakuri Ya Farha. Farha-ta. My Angel. Zan iya kiranki Angel ko?" Ya marairaice murya.
Da wadannan kalaman ya tarwatsa tunaninta. Zuciyarta ta kara cika da tsaftatacciyar soyayyarsa.
"A'a" ta bashi amsa kai tsaye.
"Me yasa?"
"Saboda ban sani ba ko nan da kwanaki kadan zan sake nemanka na rasa"
Murmushi ya yi ya ce "na hakura. Zan jira ranar da za ki kirani da kwatankwacin wannan sunan. A lokacin na san kin shirya karbar Abbati."
Dan muskutawa ya yi ya ce "Zamu iya magana a gaggauce kafin su Abba su dawo?"
Da ka ta amsa. Abbati ya dauko mata zancen abin da ta sani. A kasan zuciyarsa yana bakincikin boye mata ainihin labarinsa. Sai ya tuna cewa ko babu tsoron rasa soyayyarta bai kamata ya dinga kwayewa kansa baya ba. Takaicinsa sai ya rage na sanya mahaifinta da duk masu son rufa musu asiri yin karya.
"Rayuwata ta koma baya. Bana ajin irin mazan da suka dace su kiraki matarsu. Wannan ne dalilin da yasa ban kara nemanki ba"
"Angel" ta ambata a can ciki don da kyar ma yaji. Cike da annashuwa kuwa ya kalleta.
"Na'am"
"Kada ka sake guduwa!"
Daga haka ta tashi ta fita. Ba jimawa Munzali ya shigo. Sai kuma su Alh. Tahir suma suka dawo.
Fitar da Munzali ya yi yasa Sauda ta kira masa Mardiyya. Sun sami wuri sun zauna ya yi amfani da rufin asirin da babanta ya musu ya fada mata duk abin da ya faru. Ba tare da jan zance ba ya ce,
"Baki cancanci soma rayuwar sadaukarwa da kuruciyarki ba. Zan cigaba da kasancewa tare dake a matsayin dan uwa. Amma ina so ki cigaba da normal rayuwarki har muga ikon Allah"
Kuka yaga tana son yi ya ce "kada mu yi haka dake. Ba datse alakarmu nayi gabadaya ba. Ina bukatar lokaci. Bayan abin da ya faru da Qibdiyya yanzu zamu daidaita da mamanta. Ki yafe min bacin lokacin da nayi miki"
"Nagode Ya Munzali" Mardiyya ta kirkiro murmushi. Karancin shekaru basu sa ta kasa fahimtarsa ba.
Su hudu suka zauna a falon. Alh. Tahir ya fara da tambayarsu game da 'ya'yansa. Kai tsaye Munzali ya ce ya janye.
"Bayan duk abin da ya faru ina ganin ya dace na dawo da matata da muka rabu. Zan cigaba da daukar Mardiyya kamar kanwata. Allah Ya kawo musu miji nagari.
"Kai fa Abbati?"
Kai a kasa ya fada musu yana son auren Farha amma ba yanzu da bashi da komai ba. Ya kuma san cewa ta jira shi ba karamin son kai bane. Rasata kuma is not an option.
Manyan dariya suka yi. Sun riga sun gane halin da yake ciki. Alh. Tahir ya ce idan ya je gida ya bawa mahaifinsa nambarsa don ya kira suyi magana. Sauran abubuwan da yake tsoro kuma Ya barwa Allah.
Da suka tashi tafiya Mami ta sake fitowa. Su Suhaib ma har mota suka zo, Farha ce kadai bata fito ba. Kunyar da rashinsa yasa ta iya ajiyewa dazu ita ce ta dawo bayan samunsa.
***
Ko akwai, ko babu, indai dangi suna da yawa kuma da hadin kai to kuwa da wuya idan uzurin juna ya tashi a ji kunya. Cikin 'yan watannin nan da aka sami wadatar farinciki da kyautata zumunci a gidan Alh. Rabi'u, 'yan uwan sun dauki juna da matukar mahimmanci. Abu ya zo akan gaba. Za ayi bikin Ummita da Murja. Kowa ya zage damtse. In baka yi bani wuri. Da talaka da mai kudi babu wanda bai kawo wani abu domin a saka a dakin amaren ba. Abdulkarim yaso sakar musu kudi sosai amma sam Honourable yaki yarda. Wanda aka yi ma ya isa. Kada su zama marasa tunani. Sannan dole su kiyaye mutumcin 'yarsu.
Munzali ne ma ya dinga jin ba dadi. Zasu aurar da 'ya'ya amma duk abin da ya saya rabin kudin Abbati ne ya bashi cikin wanda Alh. Sabi'u ya basu.
"Banza, akan haramtacciyar dukiyar kake ta kunkuni tun jiya ko? Idan kana so sai na kai ka inda aka sakaya Shazali ku gana"
Kukan kura Munzali ya yi ya tashi zai cakumo shi sai ga Qibdiyya ta shigo.
"Daddy me za ka yiwa Papa?"
"Maballi ne ya shake shi zan gyara masa" Munzali ya ce da sauri.
Abbati da Asabe dake zaune a falon nata suka kwashe da dariya. Tare suka fito daga gidan da Asabe da Innayo a bayan mota. Sai Qibdiyya akan cinyar Munzali. Abbati ya jasu zuwa wurin da ake taron kamu.
Taro ya yi kyau sosai. Da aka bukaci uwar amare ta fito domin kai 'ya'yanta kan shimfidar da aka tanada domin kamu duka 'ya'yan Larai sai cewa suka yi Uwani taje. Ta tashi cikin farincikin da bata taba ji ba ta rungumosu a jikinta har wurin. Da ta dawo ta zauna Hasiya ta dan tabota ta ce,
"Metiron kuka kika yi ne?"
Uwani ta maka mata harara bayan ta karewa wajen kallo ta tabbatar babu wanda yaji.
"Bani da lokacinki yanzu. Nan da wata biyu zaki ga Metiron Uwani a gabanki ra'ayil aini."
Jikinsa Hasiya tuni ya yi sanyi. Tsokanar da ta fara ta hadiye ta tsurawa katon cikinta kallo. Can dai ta kasa daurewa ta riko hannun Uwani.
"Don Allah da ciwo sosai yadda ake fada? Taba wuyana ki ji. Wallahi zazzabi ke neman kamani"
Uwani ta tuntsire da dariya. DJ na cewa uwar amarya ta fito ta janyo hannun Hasiya filin rawa tana jujjuyata. Innayo ta kallosu su biyar, da su Ummakati da Fati duka suturar jikinsu iri daya, sun yi kyau. Karo na farko da wani zai gansu ya ce jininsu guda.
Cikin aminci aka yi taro aka gama. Washegari daurin aure. Ranar ne kuma Suhaib da Lilu suka zo. A masallacin daurin auren suka hadu dasu Abbati. Munzali ya yi murna da suka karbi gayyatarsu.
"Ba dole ba. Idan naki zuwa Ya Farha da Ya Suhaib zasu iya tsireni" Lilu ya ce yans dagewa Abbati da Suhaib gira.
Munzali ya ce "ban gane ba. Abbati dai na san an gama da zuciyarsa. Suhaib ne dai sai ka bani haske"
" 'Yarka ce Ayaah"
Munzali sai murna. Suhaib ya ce to dai gaskiya kada su bata masa show. Su yi shiru a jira su daidaita.
"Ashe a jaririn mataki kuke. To ga Romeo nan sai ka tambaye shi satar amsa" cewar Munzali da shakiyanci.
"Allah Ya tsareni da zama Romeo. Shi da bai dorar da soyayya ba. Ka dai kirani ...."
"Wa?" Suhaib, Lilu da Munzali suka tambaya.
Abbati ya tashi ya barsu yana cewa duk basu da kunya sun raina shi.
***
Da kaiwa baki abinci Munzali ya samu ya tura Ayaah wurin Suhaib. Tayi kwalliya mara hayaniya wadda ta fiddo da kyawunta. Tray din hannunta lemuka ne da ruwa a kai. Tana tafe wurin da Munzali yace mata ya bar mota tana yangar 'yan mata. Suhaib ne kadai a motar yana ta dariyar yadda take fama tura baki a dole kayan sun mata nauyi.
" 'Yan mata na tayaki ne?"
Bata kula dashi ba sai murya taji. Dama kuwa ta gama fushi don ya ce mata ba zai zo bikin ba. A saman boot ta ajiye ta murguda baki cike da shagwaba.
"Bana so."
"To tsayuwar me kike a nan?"
"Saurayina nake jira" ta amsa tana waige waigen baya.
Suhaib ya dauki lacasera mai sanyi ya bude ya sha kadan sannan ya ce "Har ya bani tausayi"
"Wa?"
"Saurayin naki mana. Zai kwashi tsiwa. Gashi ma ba sonsa kike ba?"
Ayaah ta daure fuska. Fushi take dashi maimakon ya bata hakuri ya zauna tsokanarta.
"Inji wa yace bana son sa?"
"Inji wanda kike so"
Kusan faduwa Ayaah tayi don dama inda take tsaye dan tudu ne mara fadi.
Sannu Suhaib ya ce mata da ta gyara tsayuwa a gefensa.
"Na zata kin fara sona ne fa kamar yadda na dade da sonki"
Kunya da farinciki suka rufeta ta ce "Ni wallahi..."
"Ke me?"
"Me yasa kace ba za ka sami zuwa ba?"
"You are not serious. Amsar abin da na fada miki kenan?"
Rufe idanu tayi da tafukan hannunta ta ce "kunyarka nake ji"
Girgiza kai ya yi don ba haka yake son ji ba "ya batun amincewa ko babu? Dazu Baba yake fada min ya dage bikinki sai yaron da ya zaba miki ya dawo daga cirani."
Yana kallonta duk ta fara rikicewa
"Kin tuna ni kuma kin ce kada ma nace ina sonki a baya ko?"
"Lokacin ma fa wasa nake? Kace masa..."
Dariya taga yana yi shi yasa ta kasa karasa magana. Yana kiranta ta dinga sauri ga takalminta mai tsini.
****
A yau cikin hukuncin Allah aka daura auren Auwal (Abbati) da Farha, Munzali da Zakiyya da kuma Suhaib da Haajara (Ayaah). Bikin ya zo wata biyu daidai bayan Hasiya ta haifi santaleliyar 'yarta wadda aka radawa suna Aisha kamar yadda Innayo ta roka.
Anyi biki na masu ilimi da aji. Alh. Sadisu ya tsaya tsayin daka a matsayin uban angwaye. Iyayensu basu da abin cewa sai godiya da addua.
Kamar yadda ya yi alkawari ya basu aiki a jikinsa. A gefe guda sun soma kasuwanci kuma suna ganin alkhairi. Sun kara gaskata zancen da ake cewa Na Allah baya tabewa. Rabon kwado kuma baya hawa sama.
Zakiyya dai auren a bazata yazo mata. Munzali wanda yake jin zai iya sadaukar da komai domin Qibdiyya ya je gidansu wata daya kafin bikin ya yi magana da Gwaggo Lami. Ya fada mata taja kunnen Zakiyya saboda ko kusa ba zai dauki sakaci da rayuwar 'yarsa da wasa ba. Daddy kuma wanda ya koma hostel saboda tsangwamar Gwaggo da kiyayyar da Zakiyya ke nuna masa ya ce a fada masa ko da wasa kada ya yi gigin zuwa inda yake da sunan ganin yayarsa. Bai kulleshi ba saboda kawai yana ganin shi ma mai laifi ne.
A gefe guda ya auna yaga da wahala idan ya auro wata ba za ta gorantawa Qibdiyya wataran ta ce kanin babarta ya bata ta ba. Ya kuma san wannan abin ne yasa Abbati cewa ya dawo da Zakiyya.
Kafin magariba amare duk sun shiga dakunansu. Gidan Abbati yana Farm center, na Munzali yana Lodge road. Dukkaninsu cikin gidajen hayan Alh. Sadisu wadanda suke apartments ya basu daidai su zauna. Ya nuna musu cewa lokaci kuma ya yi da zasu koyi rayuwa su kadai domin samun damar kulawa da iyalansu.
Ayaah kuma Kaduna aka kaita. Gidanta babu nisa da na Mami Khadija. Shima na Alh. Tahir ne. Suhaib ya yi mata alkawarin cigaba da karatu kamar kannensa.
SHEKARA KWANA
Baaba Mari, Innayo, Asabe da Mami Khadija suna zaune a tsakar gidan Alh. Rabi'u. Yau ake yinin bikin Salima da wani abokin Alh. Unaisu.
Baaba Mari tana dauke da Maama (Khadija) 'yar wajen Suhaib da Ayaah. Akan cinyar Innayo kuwa Auwal din Munzali da Zakiyya ne. Mami Khadija kuma ta goya sarkin rigima Sa'id din Abbati da Farha. Asabe kuma tana ta kai kawo wurin kaiwa baki abinci.
UWA UWACE...
Tammat Bihamdulillah