Showing 57001 words to 60000 words out of 242549 words

Chapter 20 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3386

da 'ya'yanta ba idan ta kaso auren.

"Faten tsaki nayi miki. In zuba yanzu ko sai anjima?"

"Zuba min sai ki leka wurin Asabe ku gaisa ki zo ki tafi dare na kara yi."

"Baban Ummi zai biyo ya duba ki. Shi zan jira."

"Da ma kar ya wahalar da kansa. Taki wahalar ma ta isa."

Anti Hasiya sai ta mike ba don tana son zuwa dakin Asaben ba. Zamanta zai sa Innayo ta koma nuna rashin son aurenta da kullum ta sami dama sai tayi. Ita kuma ta riga ta karbi kaddararta hannu bibbiyu. Zaman lafiya da aminci suke yi dashi wanda yafi karfin zaman soyayya. Ya girme mata sosai amma yanayin zama ya mayar dasu tamkar aminan juna.

***
Riga da skirt na atampa aka sakawa Qibdiyya da zasu fito bayan Magrib. Ita ta dage wai kayan 'yan mata take so. Iya Kande tayi mata dauri ta kwance ta sake yin nata a cewarta na Iya na tsofaffi ne. Natan ma dai sai dai a gimtse dariya kawai. Tayi abinta Abbati yana ta kwarzanta kyaunta har suka fito.

Kowa da motarsa suka fito daga gidan ita tana ta Munzali shi kuma Abbati yana tasa shi kadai. Daga wurin Asabe zai je gidan Shazali ne ya fara gabatar masa da kudurinsu na daina wannan mummunar alfasha. Shi kuma Munzali zai dawo da Qibdiyya gida.

***
"Salamu alaikum" Anti Hasiya ta sake doka sallama ta biyar a kofar falon Asabe.

Da karfi da alamar kosawa Asabe ta ce "Wai waye ne haka ake ta yi min sallama kamar an biyo bashi?"

Ba don Innayo ce ta turota ba da babu abin da zai kawota. Danne bacin ranta tayi ta ce
"Hasiya ce."

"Wace Hasiyan" ta kuma tambaya a wulakance.

Zuciyarta har wani harbawa take saboda bacin rai. Juyawa tayi za ta bar wurin taji an tura kafadunta cikin dakin.

Asabe dake zaune rashe rashe tana kallo ga farantin da ta dora ledar tsire a kai ta mike tsaye tana gyara zani.

"Meye haka za ki fado..." sai kuma ta kula da wanda Hasiyan take yiwa kallon mamaki bayan ya turota dakin. Fuska ta saki ta kama dariya "Alhaji Munzali sannu da zuwa, sannu da zuwa. Lale marhabin. Ai ban san tare ku ke ba. Ita ma kuma da sai ta ce Hasiya matar Honorable Habun A'i sai nafi saurin daukar haske."

Munzali ya yiwa Abbati irin kallon nan na kaga abin da nake fada maka ko. Duk maganganunsu sun ji shi yasa ma ya turota dakin. Abbati dake dauke da Qibdiyya ya yi dan murmushi kawai.

Anti Hasiya sai ta gaishe ta domin ta basu wuri amma maimakon ta amsa sai ta karkata kai ga Abbati.
"Alhaji Abbati ina wuni? Ya fama da jama'a? Ya kasuwar? 'Yan uwa duka lafiya ko?"

Ran Munzali ya sosu da wannan barar da kai na Asabe da kuma wulakanta Hasiya da tayi.

"Baki ji Hasiya na gaishe ki ba?"

"Au...hankali na ne ya tafi wurin Mariya." Ta janyo Qibdiyya jikinta. Ko daga kai ta kalli Hasiya bata yi ba ta ce "ya mijin naki da yara? Dazu ma naga Salima da Uwani ince dai lafiya."

Wani mamakin ya sake kama Hasiya. Jiya baki da baki ta fadawa Babansu an cire hakwaran Innayo har biyu. Shi kuma ya san da lalurar ma kudi ne da ba zai bayar ba. Bata sani ba yanzu shi ne bai fadawa Asaben ba ko kuwa shaftarta ce da ta saba.

"Innayo ce bata jindadi."

"Allah Ya sauwake. Mariya mu je ciki na baki alawa" ta kama hannun Qibdiyya ta shige ciki da ita.

Gwiwa a sage da wannan wulakancin har a gaban bakon ido Anti Hasiya ta juya ta fita. Munzali ya bita da sauri ya cimmata kafin ta karasa dakin Innayo.

"Hasiya tsaya mana."

Tsayuwa tayi bata juya ba. Dan uwanta ne da ya bata 'yan watanni amma rabon da su hadu ta manta.

Fuska ya saki da ya iso gabanta "saurin me kike yi ko gaisawa bamu yi ba?"

Murmushin da tayi masa mai ciwo ne. Gabadaya jikinsa ya yi wani irin sanyi. Bata ce masa komai ba amma a fuskarta yake karanto damuwarta.

"Don Allah kiyi hakuri. Dukkanku ku yi hakuri akan duk wani rashin kyautawa daga gareni ko Asabe da duka 'yan dakinmu. Laifin namu ne don na san Innayo bata son wannan zaman da muke da juna."

Kwalla ce ta taru har tana barazanar zuba daga idanunta ta ce "Ba komai. Biyonin da kayi ma wallahi naji dadi"

Hannu ya mika ya karbi wayarta yana cewa "kawo in saka miki nambata". Ya fara saka nambar yaga sunansa ya fito "kaiiii, ashe kina da nambata amma baki taba kirana ba."

"In kiraka in ce me?"

'Yar dariya ya yi ya ce "Ki ce kin kira mu gaisa." Nambarsa ya kira domin ya sami ta ta sai yaji ana cewa "your account is too low for this call"

Dama a kunnensa ya kara wayar sai kawai ya wayance don kar ya kunyata ta ya ce babu service mai kyau. Da ka ta karanto masa nambar ya bita har dakin Innayo.

"Munzali kai ne a dakin nan? Hasiya daga cewa ki je ki gaishe da Asabe kin dauko min magana ko?" Innayo ta ce a dan tsorace.

Kunya kamar an zuba masa ruwan sanyi haka yaji. Yanzu ace ganinsa bai haifar da komai ba a wurin matar babansa sai tsoro. Sunkuyar da kai ya yi bayan ya zauna a gabanta.

"Ba haka bane Innayo. Kiyi hakuri don Allah. Na dade bana kyautawa amma in sha Allahu zan gyara. Zan daidaita zumunci da 'yan uwana." Ya dubi Anti Hasiya "taimaka ki karanto min nambobi su Yaya Uwani da kaina zan kirasu. Idan da hali mu hadu a nan ranar asabar mai zuwa. Kowa ta taho da 'ya'yanta. Zan kira ki dai mu tsara yadda abin zai kasance."

Kwallar da ta danne tun farkon maganarsa ce ta sauko. Tana son 'yan uwanta kuma tana kwadayin su yi zumunci da juna kamar kowanne dan uwa. Gasu da yawa amma babu jituwar kirki tsakaninsu da juna tamkar sun hada jini da Malamijo (KU DUBE MU). Mahaifinsu ta dorawa alhakin lalacewar lamuran gidansu. Babu ruwansa da komai na iyalinsa indai zai dawo a bashi abin ci. Ta rasa gane wace irin rayuwa yake yi. Tarbiyar jowa a gidan saitinta daban. Matansa ya kamata ya daidaita tuntuni domin su hada kan 'ya'yansu amma ya bari a daki daya ma ana gaba.

Munzali sai ya matsa ya rungumota a barin jikinsa "in sha Allah Hasiya komai zai daidaita tsakaninmu. Nayi sakaci a baya kuma ina da na sani."

Bambarakwai taji rungumar ta yi murmushi tana kokarin ture shi. Shi kuwa ya rike kafadarta gam yaki saki yana dariya
" 'Yar kauye meye haka? Irinku ne masu rungumar miji sau daya a wata ko?"

Innayo bata san lokacin da tayi dariya ba. Dariyar da bata iya karasawa ba saboda banko kofar dakinta da Asabe tayi tana huci.

"Billahillazi huwar rahmanu Bokanki ya yi karya Innayo. Ni? Ni Asabe da raina ki ke neman yi min farraku da d'an da baki san lokacin da nake fadi tashin gina shi ya zama mutum ba?"

Wani irin kallo Munzali ya bita dashi zuciyarsa tana zafi. Bai taba ganin uwar da bata san darajar kanta da 'ya'yanta ba sai ita...sai kuma babar yarinyar nan ta Diamond plaza wani sashe na zuciyarsa ya tunatar dashi.
(Akwai kuskure mai girma ga iyaye musamman mata su dinga gilla karya a gaban 'ya'yansu. Sosai hakan yake taimakawa wurin zubar musu da girma a idanunsu. Mu kiyaye.)


*********
Masu karatu kar ku ga kamar labari yana ta tafiya amma lokaci ba ya ja a cikinsa. Hakan yana faruwa ne saboda yawan jaruman labarin wadanda suke da rawar takawa ba 'yan karo ba. Kuma abubuwan da zasu faru a dan takin lokacin nan suna da nasaba da yadda labarinmu zai tafi a gaba. Sai mun hadu a shafi na gaba da izinin Allah.

#SonSoI just published "13" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/H7FJkqEvQab




UWA UWACE...13


Batul Mamman💖



"Hasiya muje daga waje muyi magana please. Ina so mu tsayar da rana ne a yau dinnan."

Innayo ta kalla da Asabe wadda take shirin hadiyar zuciya. Maganar me Munzali zai yi da Hasiya har yake neman su kebe?

"Bishi ku je. Allah Ya kara muku zumunci." Cewar Innayo tana murmushi. Allah Ya sani har zuciyarta ko Munzali yafi kowa talauci tana maraba dashi da 'yan uwansa wurin zumunci da nata 'ya'yan. Yau idan babu su a raye bata jin ko shi uban gayyar mahaifinsu zai so ace kowa tasa rayuwar yake yi.

A tsakar gidan suka zauna ya sake bata hakuri. Ita mamaki ma ya kashe nata bakin sai murmushi take dokawa. Basu taba zaman hira ba da 'ya'yan dakin Asabe tun kuruciya.

"Weekend dinnan zan yi tafiya da wanda ki ka ganmu tare a dakin Asabe. Aminina ne sosai sosai Hasiya."

Wai Munzali ke fada mata wani abu nashi mai mahimmanci? Lallai duniya inda ranka ka sha kallo. Ita ma zata bashi labarin tata rayuwar kuwa ta ayyana a ranta.

"Allah sarki. Yaya sunan shi?"

"Abbati"

Daga yadda ya fadi sunan ma ta fahimci alakar ba ta wasa bace. Dan tunani tayi ta dago kai tana ware idanu.

"Ba dai wanda Asabe ta taba dukanka akan kana kula shi ba?"

Dariya ya kwashe da ita "ashe kin tuna..oh su Hasiya muguwa...ai na kullaceku lokacin. Kuna kallo tana neman kaini kiyama aka rasa mai cetona."

Ita ma bata san lokacin da ta soma dariyar ba. A nan Abbati ya samesu suka sake gaisawa yana murna da canjin da aka fara samu a rayuwar Munzali tun yanzu.

"Ina Qibdiyyan?" Munzali ya tambaye shi.

"Asabe ta ce idan zamu tafi kaje ka daukota. Ni bari naje wurin Shazali zan sameku a gida."

Sallama ya musu ya tafi. Munzali ya san fada ne Asaben ke ji kuma ba zai bari ta sake raba kansu ba. Ummakati ya tuno ita ma ko a waya sai ayi watanni basu gaisa ba. Kananun ne dama masu damunsa saboda roko da Asabe ta koya musu.

"Wai don Allah bebin da muka zo barkarta ce wannan? Mariya sunanta ko?" Anti Hasiya ta ce tana rike baki.

"Allah wadaran gida irin namu. Yanzu fa babu abin mamaki ki ganta a waje ku wuce juna. Wallahi Baba bai yi ba..."

"Kar mu fara aikin alheri da aibata iyaye. Shi Baba sai dai addu'a kawai."

"Da Asabe ma..."

"Da Uwani.."

"Da Mahe (kaninsa wanda Asabe ke cewa sune magadan Alhaji Rabiu)"

"Da Zara."

"Da duka ahalin Laraba (babarsu A'i)"

Wata dariyar suka yi. Gidansu kamar ba gidan mutane ba. A gabanta ya tura mata katin waya na dubu biyar ya ce ta kira duka 'yan uwan nasu suyi shawara. Idan asabar ko lahadi ta sama tayi musu duk su hallara a gidan da 'ya'yansu.

"Allah Ya kara budi Ya kuma kyautata zumincinmu." Cewar Anti Hasiya.

"Amin"

"Dan dauko min Mariyan in dauketa. Ya ma naji kuna kiranta?"

"Qibdiyya" ya ce da murmushi.

Asabe tana ta masifa ya dauko 'yarsa ya kai dakin Innayo wurin Anti Hasiya. Yarinya kuwa tuni ta ware saboda Hasiya tana da son yara. Kafin ya fita Honorable Habu ya shigo suka gaisa. Innayo bata nuna halin ba saboda farincikinta na soma gani hadin kan 'ya'yansu. Fatanta Uwani da Zara ma su bada hadin kai.

Da Abbati yaje wurin Shazali ya fada masa bukatarsu nuna masa ya yi babu komai har ya ce zai bisu bikin nadin saurautarsa. A badini kuwa ya hau lissafin asarar da zasu tafka da kuma kalubalen da ka iya biyo baya. Manyan 'yan siyasa da masu kudin da suke mu'amala dasu ba yarda zasu yi su rabu haka ba. Gani zasu yi kamar dama turo su akayi ko kuma sun gama sanin sirrinsu zasu tona musu asiri. Rabuwar sam ba za ta zo yadda suke tsammani ba.

***

Tunani da zubar hawaye sune suka taya Mami Khadija kwana. Bata san kulle kullen da Alh. Tahir ya yi ba tun a jiyan sai washe gari da misalin karfe takwas na safe. Farha ya aiko kiranta amma sai ta kasa tashinta ganin yanayin yadda take baccin. A inda tayi sallar asuba bacci ya dauketa a zaune. Komawa tayi ta sanar da Abbansu tana bacci sai ta tarar da'irar kakaninta da abokan Alh. Tahir duk a falon. Gabanta ne ya fadi, da gani ba lafiya. Gaishesu tayi ta koma dakin ta taso ta.

Tsabar ta rude ma harda hawayenta. Nata hankalin har yafi na uwar tashi wai amma a haka take kokarin kwantar mata da hankali.
"Mami ki kwantar da hankalinki ki shiga falon a nutse. Kin san komai kaddara ne. Naga Mama da Baban Kawo tare da Yakumbo. Kuma su Lilu suna dakinsu kowa lafiyarsa kalau." Zuwa yanzu jikinta har karkarwa yake "Mami harda Yakumbo fa. Me zai kawosu gidan nan da sassafe haka?"

Mami Khadija ta murmusa da ta fahimci inda zancen ya dosa "ki kwantar da naki hankalin kuma kar ki yarda ke ko wani cikin 'yan uwanki yazo falon Abbanku."

Idanu kamar su fado saboda tsorata Farha ta ce "Mami ko dai sakinki Abba ya yi?"

"Wuce ki fadawa yayanku nace" Mami ta furta da dan karfi don ta tsorata ta.

Tare suka fito Farha ta ruga dakinsu Suhaib ta fada musu kai tsaye tare da sallama. Tayi sa a kuwa kowannensu da suturarsa. Lilu lecture gareshi da karfe tara shi kuma Suhaib yunwa ce ta tashe shi.

"Are you crazy?"

Suhaib ya ce fuska a hade. Ya hana kannen nasa mata shigo musu daki babu sallama kamar yadda ya hana Lilu shiga nasu kai tsaye. Hawayenta ya gani ya cillar da wayarsa ya mike daga kan gadon.

"Ya Suhaib wani abu na shirin faruwa...."

Muryarta da sauri-sauri ta dinga fita wurin fada musu abin da ta gani.

"Taso min Mardiyya da Sauda." Ya ce yana yin hanyar kofar dakin.

Bayansa tabi Lilu yana take musu baya. Da kansa ya bude dakin yana kiran kannen nasa. Duk tsoronsa bai wuce kada abin da za a tattauna a falon ya fito har ya shiga kunnuwansu ba. A firgice yake da gudun halin da zasu shiga idan suka san waye mahaifinsu. A duniya bai ga wani abu mai saurin zubar da mutumcin mai mutumci ba sama da zina. Bai san me yake faruwa ba amma ya san da maganar Maminsu na son su koma nata gidan.

"Ku tashi Lilu zai kai ku gidan Mama."

"Maman fa tana falon Abba na ce maka" Farha tayi saurin fada.

"Na sani. Ku tafi zan biyoku nima."

Gardama Farha da Lilu suka so yi masa ya jugo garesu a birkice. Sauda da Mardiyya ba ganin haka suka tashi duk da basu san me yake faruwa ba suka saka hijabansu.

"Ya Suhaib please ka yi min bayani."

Farha ta ce da rawar murya. Ita fargabarta bata wuce tunanin ko Mamin ce tayi laifi ba.

Gyara yanayin fuskarsa ya yi domin ya kwantar musu da hankali baki daya.
"Ku daina damuwa ba wani abu bane" yana fadin haka suka hada ido da Lilu wanda ya tabbatar idan bai basu gamsasshiyar amsa ba yaron zai fara tone-tone. Dan murmushi ya yi sannan ya ce "Kun san Abba ya gama gini zamu tashi daga nan. Ita kuma Mami ta riga shi farawa ita ma ta gama nata. To shi ne take so ita ta koma wanda ta gina ba na Abban ba."

Gabadaya a tare fuskokinsu suka sauya zuwa yanayin da yake fatan gani.

"Fadan da babu ruwanka dadin kallo ne dashi" Lilu ya furta yana dariyar shakiyanci.

Harara ya samu daga Sauda ta ce "Fadan su Mamin ne da dadin kallo Ya Lilu?"

"Idan ba dadin kallo ba me zan ce? Mu dai babu wanda zamu ce zamu shigarwa tunda matsayinsu daya. Kuma na tabbatar miki suna shiryawa sai masu shiga fadan sun ji kunya."

Farha da bata yi saurin yarda kamar kannenta ba ta nisa ta ce "wai kun manta yadda ta shigo daki jiya tanata yi mana fada. Ni nawa ma yafi na kowa" ta karashe maganar da raunin murya.

Suhaib ya yi saurin kawar da tunaninta da cewa "tun jiyan fa suka fara rigimar. Ni na zata ma a lokacin zai fadawa su Mama. Anyways mu zauna a nan don kun san Yakumbo tana ganin mun fita zamu sha fada."

"Yaran zamani ba kunya..."

Suka hada baki suka fada cikin salon kwaikwayon kakar tasu.

*
Da cikakken confidence Mami Khadija ta shiga falon da sallama. Dogon hijabi ne mai hannu har kasa ta dora akan kayan baccinta. Suna hada ido da Alh. Tahir ya kawar da nasa saboda kwarjinin da tayi masa. Dan tabe baki tayi ta wuce gaban Yakumbo ta gaisheta. Fuska a gimtse ta amsa mata. Bata nuna damuwa ba ta matsa gefen Mama (mahaifiyarta).

"Rike gaisuwarki tunda har kin yi girman zama 'yar kanki."

Motsa baki tayi za ta bata hakuri Baba ya katseta ta hanyar nuna mata yatsa "baki isa ki bijerewa umarnina ba matsawar kina amsa sunan 'yata wallahi. Wato kin fara shiga cikin manyan matan dake zaman kansu sun hure miki kunne. Da hankalinki da ilimin addini ki ke neman rabuwa da miji akan abin da bai taka kara ta karya ba. Shin namiji ba mijin mace hudu bane? Menene aibu don ya nemi auren kawar Farha? Ba sunna ya dabbak'a ba? Ko baki da masaniyar cewa 'ya'yan Nana Khadija (RA) su Sayyada Zainab da Ruqayya sun girmi Nana Aisha Allah Ya kara yarda dasu baki daya."

Maganganun sai suka daure mata kai. Ido ta sake kaiwa ga Alh. Tahir wannan karon bai yarda ya kalleta ba. Ita kuwa bata yi shiru ba ta ce,

"Baba me ya ce nayi ne?"

Ran Mama ya sake baci kuwa ta kalleta a harzuke "Khadija ko dai da gaske kin fara kawance da matan da basu san girman na gaba dasu ba? Mijinki ya kwana yana fushi dake amma don kokari a gabanmu ki ke son shashantar da zance."

"Ku kyaleta don Allah da fadan nan. Kishi dole ne. Khadija matso nan.." Mami ta matsa kusa da surukarta kuma yayar mahaifinta "kiyi hakuri tunda dai auren ba haramun bane. Abin da yake haramtacce shi ne mace ta dinga neman mijinta ya saketa ba da dalilin da shari'a ta yarda dashi ba. Na san irin auren nan babu dadi amma kar ki manta ba haram bane."

Ta soma hasashen abin da ya faru amma duk da haka shi ta kalla kai tsaye. Zai kawar da kansa ta daga murya rai a matukar bace.

"Kar ka kuma kawar da kanka ka kalleni ka fada min abin da ka sanar da iyayenmu."

Tana kare maganar Mama ta tashi za ta mareta cike da takaicin zubar mata da mutumci da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login