Showing 219001 words to 222000 words out of 242549 words

Chapter 74 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3390

da yake faruwa kuwa shi ne da Comared ya koma gida sawa ya yi aka fito da Shazali. Ya kare masa kallo a ransa yana tausaya masa. Indai ta tabbata dan Alh. Sadisu yana gidansa to kashinsa ya gama bushewa. Ta wani fannin ma sune da riba domin duk abin da yake takama dashi na sirrinsu bai isa ta fito dashi ba idan yaje hannu.

"Kayi hakuri. Bai kamata na bari bacin rai ya sani tsare ka ba. Sai dai kana sane da matsayina. Ba zan so duk wani abu da zai shafi mutumcina ba"

"Ina iya tafiya?" Kawai Shazali ya iya tambayarsa saboda ransa ya riga ya gama baci. A gefe guda yana ta tunanin Abdul da ya hada da bango kafin ya fito. Ya rasa dalilin da yasa yake ta fado masa a rai tunda aka rufe shi a daki. Bai sani ba ko don son da yake masa ne har ransa.

Da dingishi ya karasa motarsa ya fice daga gidan. Yana tuki ana biye dashi a baya ba tare da ya sani ba. Motar amittacen yaron Comared ce wanda yasa bin Shazali gida. Shi a nasa zaton ma a can ainihin gidansa da kowa ya sani ne ya ajiye shi. Sai da yaron ya kira ya fada masa suna hanyar wata unguwa mai cikowar mutane da yawan gidajen gargajiya.

"Bishi kawai. Gamu nan a bayanku. Ka kwatanta min inda ku ka bi"

Bai yi mamaki ba don kuwa Shazali ya taba fada masa cewa yana da gida a unguwar inda yake shagalinsa. Suna hanya ya kira Alh. Tahir. Shi kuma ya sanar da DPO da Alh. Sadisu. Nan da nan aka yi ayari aka bisu.

Shazali bai san me yake jiransa a waje ba ya shiga gidansa kai tsaye.

"Abdul na dawo"

Shiru babu amsa. Ya murmusa a ransa yana tunanin ko har yanzu fushi yake saboda yanayin rabuwarsu da zai fita da Qibdiyya.

Yana sanya kafarsa a karshen soron ya hango shi kwance cikin jini a inda ya barshi da zai fita. Rawa jikinsa ya dauka tamkar mazari a yayinda ya duka a kansa yana kiran sunansa cikin sarkewar murya.

"Abbbbbduuu...llll?"

Shiru mai hargitsa tunani ne kadai ya bakunci kunnuwansa. A take duk wani ciwon jiki da yake ji sakamakon dukan da yasha ya kau. Ya dago kan Abdul wanda kasansa babu komai sai jini ya jijjiga shi. Jikinsa gabadaya a sake yake. Fuska tayi fayau saboda rashin jini. 'Na shiga uku' ya dinga ambata a ransa don ko sau daya bai tuna da sunan Sarkin da ke warware dukkan matsala ba.

"Mutuwa kayi?"

Ya yi tambayar da bai sa ran samun amsarta ba. Jinin wajen ya sake kallo wani ya bushe ma. A lissafinsa ya yi wajen awa hudu da barin gida. Cikin sauri-sauri ya tashi ya shiga daki ya dauko duk wani abu da zai iya tunawa wanda zai iya tona masa asiri ya saka a wata jaka. Dama ba wasu kayan kirki yake ajiyewa ba tunda lalatarsa kadai yake yi da kananun yara a wurin. Yaran da ko da zata kwabe a gaba iyakarsu nan gidan wanda ya saya da sunan wani dan uwansa na kauye. Kallo daya ya sake yiwa Abdul ya bude kofar gidan da niyar idan ya tafi ya tafi kenan har abada.

Sai dai me???

Ko minti goma bai yi da shiga gidan ba Comared da motocin 'yan sanda wadanda aka ki kunnawa jiniya suka iso tare da Alh. Sadisu. Ba don an rirrike shi ba ma da tuni ya afka gidan.

Idanun kowa akan kofa. Ga wasu 'yan sandan sun tokare kofar gidan ta yadda ko jinjiri ba zai iya wucewa ta tsakaninsu ba.

Shazali yana bude kofa ya yi ido hurhudu dasu. Cikin dimaucewar tunani ya koma ciki da sauri zai rufo kofar. Sai dai tuni mutum biyu sun riga sun sanya hannuwa sun dannota ciki. Na ukunsu ya tura da kafa. Na karshen kuma ya zura hancin bindiga.

"Idan ka sake yunkurin rufe kofar nan sai na fasa maka kai da harsashi"

Baya ya yi ya daga hannuwansa sama. Ya nemi yawu zai hadiya yaji bakin a bushe. Tunaninsa ya dauke sai hanya da ya bayar domin 'yan sandan su wuce. Abu daya yake takama dashi. Manyan mutanensa ba za su bari ya rayu a kulle ba.

"Ku bani hanya, ku bani hanya."

Abin da yaji ana fada kenan daga kofar gidan. Ya zuba ido domin ganin mai shigowa sai yaga Comared da Alh. Tahir. Budar bakinsa zai yi musu tambayar abin da ya kawosu nan sai ya hada ido da mutumin da ko baka taba haduwa dashi ba a zahiri to lallai an sha gamuwa a TV ko kafafen sada zumunta. Kai hatta muryarsa ba bakuwa bace.

Wani irin sanyi mai hade da zafi a tare suka fara binsa daga tsakar kansa har tafin kafa. Me ya kawo Alh. Sadisu Nakano gidansa?

Shi Alh. Sadisu ba tsayawa ya yi ba. Ciki ya bi 'yan sandan. Yana zuwa ya gansu akan Abdul suna salati. Kirjinsa yaji ya takure. Gumi ya wanke masa jiki. Gwiwa a sake ya durkusa a gaban Abdul ya janyo shi jikinsa. A daidai nan Shazali ya juyo domin ganin me ake yi. Hoton da idonsa ya dauka da kalaman Alh. Sadisu suka kusa sanya shi hadiyar zuciya. Duk da cewa ko uffan bai ce masa ba saboda rayuwar dansa ce a gabansa tukunna.

"Abdul tashi domin Allah kada ka mutu ka barni. Me zan fadawa mahaifiyarka? Me zan fadawa uwayenka? Wace rayuwa ce kuma za ta rage min idan na rasaka? Kai kadai na mallaka. Abdul ka tashi Baba ne da kansa ya zo"

Da kyar da sudin goshi kwakwalwar Shazali ta bude har yaji a ransa cewa muddin ya cigaba da tsayuwa babu abin da zai hana a dauki tasa gawar. Duk fadin kasar nan babu mai tsaya masa ya bar Alh. Sadisu. Mutumin da shugaban kasar dake kan kujera ma babban yaronsa ne a siyasa.

Kofa ya kalla babu ko tunani ya nufeta a guje ya fita. Kafarsa na fita yaji hanya ta kare. 'yan sanda sunfi biyar da suka cafke shi.

Ana kokarin daukar Abdul a ciki Alh. Sadisu ya ce su bari. Da kansa ya dago shi ya saba shi a kafada. Idanuwansa suna zubar da kwallar da rabonsa da yin irinta tun ranar haihuwar Abdul din ya yi ta farinciki. Hanya aka bashi ya fita da shi ya sanya shi a bayan mota. Ya juya da niyar fadawa DPO cewa gida zai wuce sai yaji an kamo hannunsa. Rikon dai babu karfi saboda rashin kuzari.

"Baba.." Abdul ya furta a hankali.

"Alhamdulillah. Ya Allah Ka bani ikon aikata alkhairin da za Ka yi farinciki dani albarkacin raya min Abdul da kayi"

Wannan shi ne furucin Alh. Sadisu kafin cikin gaggawa su bar wurin zuwa asibiti.

'Yan unguwa suna kallo aka jefa Shazali a bayan mota. Wadanda idanuwansu suka taba ganin lokutan da yake kawo yara sannan bakinsu ya bude suka dinga bada shaida.

Sai da aka gama bawa Abdul taimakon da ya dace kafin ayi maganar 'yan sanda. Alh. Sadisu yasa aka duba masa kuma likita ya tabbatar cewa lallai ana amfani da dansa don har ya dauko hanyar gamuwa da cuta. Kansa kuma ya bugu sannan ya zubar da jini. An matukar auna arziki da rayuwarsa bata salwanta ba.

Bayan komai ya daidaita ya bar Abdul tare da matansa ya koma police station. Abin mamaki babu mutum ko daya da ya tafi cikin wadanda suka zo domin Abbati. Ga kwamishinan yan sanda shi ma ya zo. Alh. Sadisu ya fada masa yana so a gaggauta shigar da makarantarsu Abdul da Shazali kotu.

"Ina gudun daukar mataki a hannuna. Ku yi abin da ya dace da wuri kafin a kira ku daukar gawar da hukuma bata bada umarnin kashewa ba"

Office daban aka ware domin sauraron wannan batu. DPO yasa aka fito da Abbati. A reception din Alh. Sadisu ya taresu ya rike masa hannu tare da raba shi a jikinsa.

"Ka yafe min. Da taimakon Allah da jajircewarka akan wanda baka sani ba dana ya kubuta."

Abbati bai ce komai ba. Alh. Sadisu ya juya ya ce idan yana da uwa a wurin nan a nuna masa ita. Mami Khadija tayi murmushi ta nuna masa Baaba Mari. Akan idon kowa ya karasa gabanta ya sauke gwiwarsa daya a kasa.

"Duk wanda ya sanni zai shaida duk zafina bani da girman kai. Ina rokon gafararki akan tozarcin da aka yiwa danki. Wallahi babu mai gane halin da na shiga dazu da wanda nake ciki yanzu sai wanda ya dandana shi. Don Allah ki roka min yafiyar Abbati. Dalilinsa Allah Ya raya min Abdul. Da ya jinkirta ko bai ma kira ba da karshenta bayana ya yanke kenan har abada"

Duk dauriyarta sai da kwalla ta zubo mata.
"Ya yafe maka har abada ba zai kara kallonka da laifin yau ba"

Tunda uwa ta yafe waye d'a da ba zai yafe ba? Tana fada zuciyarsa ta wanke fushinsa zuwa ga fatan kaffara. Munzali ya riko shi domin bashi madogara. Hanne tayi gaba tana kuka zasu tafi. Alh. Sadisu ya dakatar dasu.

"Ina neman alfarma. Don Allah kafin ku tafi ina son ganinka Abbati tare da baban yarinyar nan da Shazali ya dauka"

"Nima ina da magana dasu game da alakarsu da Shazali da satar diyarsu da aka yi." In ji DPO

A wannan lokacin ne kuma Alh. Tahir ya taka rawar da ta shafe tunanin kowa akan laifinsu na baya.

Office din DPO dai aka koma. Alh. Tahir da Comared, Munzali da Abbati sai kuma Alh. Sadisu da DPO din.

"Dazu Alh. Tahir kayi mana alkawarin warware abin da ya hada samarin nan da wancan matsiyacin. Na dawo da tambayar nan ne saboda ina son a hukunta shi akan Abdul da yarinyar wajenku."

"Wani labarin sirri ne wanda jinsa zai iya cutar da mai shi"

Alh. Tahir ne ya yi magana . DPO kuma ya bashi amsa da cewa rashin sanin gaskiya a hukumance zai mayar da Abbati sahun wadanda ake zargi. Wanda a karshe dole shi ma a kai shi kotu.

Basu da zabi. Kofofi sun toshe. Dole su fadi komai da bakunansu yau. Bisa wannan dalilin suka nemi a shigo da iyayensu. Abbati ya ce a hado da Mal. Sa'idu.

Abbati ne ya fara magana yana duban amininsa.
"Ranar wanka ce yau fa Munzali."

"Na sani. Ba a boyon cibi idan ta zo"

"Wadannan sune iyayena" Abbati ya nuna su Baaba Mari, ya dora da cewa "daga Kirikasamma aka turo ni Kano almajiranci. Da karancin shekaru da rashin wayo na zamewa kaina uwa da uba a dalilin haka."

"Ga nawa iyayen. A gabansu na tashi. A cikin gidanmu. Amma daidai banda wurin kwanciya babu abin da zanyi tinkaho dashi a matsayin kulawar uwa da uba."

Shiru akayi. Hankula da kawuna suka karkata garesu a yayin da kowannensu ya bayar da labarin yadda rayuwarsu ta wanzu tun farkon haduwarsu. Baaba Mari tana kuka, Asabe tana tumami. Alh. Rabi'u kuwa kunya tamkar kasa ta tsage ya fada ciki.

"Namiji ya nemi dan uwansa alfasha ce wadda Allah Ya la'anci ma'abotanta. Ya yi fushi da wadanda suka fara ta. Ya kuma gargademu akan koyi da su." Muryar Abbati ta karade kunnuwansu da kaifi.

Munzali ya cigaba da cewa "Mu kuma da ita muka rayu, muka inganta rayuwarmu. Muka yi hajji da umra harma muka kai iyayenmu. Muka yi aure sannan muke kara neman aure. Kuma a ciki muke rainon 'yarmu"

"Da ace iyayena basu turoni almajiranci ba, da ban hadu da Munzali ba. Rashin haduwarmu ina sa rai zai tsameni daga cikin mutanen da Allah Ya tsinewa tun a duniya" wannan karon da kuka Abbati ya karashe maganarsa.

Kafadarsa Munzali ya dafa yana duban iyayensa " da na sami kulawar da ta dace da 'ya'ya bisa koyarwa shari'a, da ban hadu da Shazali ba. Nima da na tsira daga cikin mutane marasa rabo"

Banda hawayen da Asabe da Baaba Mari suke yi, dukkan mazan wurin babu wanda hankalinsa bai tashi ba. Tsigar jikinsu ta tashi.

Abbati ya dubi Alh. Sadisu "kune masu fada a ji a kasar nan. Idan kun kafa doka ina tsammanin za tayi tasiri."

"Doka akan me?"

"Almajiranci. Da farko dai duk musulmi ya san cewa neman ilimi wajibi ne ga mata da maza. To amma duk duniya a arewacin Nigeria ne kadai ake musulunci? Me yasa mu ne kadai muke wulakanta zuri'armu da sunan neman ilimi? Wane irin tunani ne yake shige wa iyaye har su iya turo dan da bai shekara biyar ba ya zamewa kansa gata? A ina yake kwanciya iyaye basu sani ba. Me yake ci? Wadanne ranaku ne ba shi da lafiya? Su waye abokan huldarsa? Mene ne hali da dabi'arsa marasa kyau wadanda ya kamata iyaye su tsawatar? Babu guda da aka sani!"

Munzali ya tausayawa Abbati sai dai shi ma ba wani cikakken bambanci bane a tsakaninsu. Shi yasa yana shiru shi kuma ya karbe ragamar zancen.

"Almajiranci ba shi ne silar lalacewarmu ko ta ragowar dalibai ba. RASHIN MAFADI shi ne yake jagorantar duk wata barna. Yadda almajiri zai iya tashi da gurbatacciyar rayuwa saboda rashin gata haka dan dake gaban iyayensa idan basu kula dashi ba. A suna ne Abbati yake almajiri amma ni da shi bamu da bambanci sai na wurin kwana. A gidanmu idan ka cire ginin gidan babu wani abu da mahaifinmu yake yi mana na tsakanin uba da da. Hatta abinci sai mun nema. Karatu sai mai ra'ayi ko wanda mahaifiyarsa ta tsaya masa. Kafin na shekara sha biyu mahaifiyata ta fara karbar kudin icce, maggi da mai a wurina. Ina nake samowa ba damuwarta bane." Ya dan numfasa kafin ya cigaba da cewa "da ace makarantun allo anyi su a killace, yaran kamar kowanne dalibi su sami kulawa. Abinci kuma duk malamin da ya bude tsangaya sai ya tabbatar cewa yana da masu girki da wurin kwana. A killace yaran nan daga yawo cikin unguwa da tituna. Da tabbas makarantun allo sun amsa sunansu na cibiyar karantar da Al'Qur'ani da samun nagartacciyar tarbiya. Duk dan da ba a tsarewa cikinsa da lafiyarsa ba muddin iyayensa suna da rai komai talaucinsu sun zalunce shi. Domin duka wadannan abubuwan idon iyaye kadai yana rage radadinsu a zuciyar 'ya'ya."

"Ni duk zuwa da abinci ake turo ni. Almajirai da yawa iyayensu suna yi musu wannan kokarin. To amma waye zai dafa mana? Manyanmu a makaranta da su kansu malaman suna da bukata. Yawanci wanda ya kawoka yana tafiya za ka yi sallama da abincin harma da suturar sawarka. Kwace da rashin tausayin na k'asa ya zama ba komai ba saboda yanayin da muka tsinci kawunanmu." Abbati ya fada idanuwansa suna kan Mal. Sa'idu wanda ya dukar da kai.

"Ba wanda zai dauki nauyin zunubanmu muke nema ba. Kowa ya sayi rariya ya san zata zubar da ruwa. Amma komai yana da sila. Silar da muke fatan a kawar da ita ko masu tasowa a bayanmu zasu sami tsira daga mummunar kaddara. Kamar yadda muka fada, ba almajiranci bane kawai. Hasali ma almajiran suna cutuwa ne mafiya yawan lokuta ta hanyar 'ya'yan da suke gaban iyayensu irina."


(Mai karatu wannan ita ce matsayata game da tura yara almajiranci. Kowa yana da ra'ayinsa na sani. To amma illar dake cikin karatun da aka mayar addini ne ma yinsa tana neman fin alkhairin cikinta. Yaran da uwa take rainon cikinsu ta haifa a wahale ne ake saki suyi ta walagigi kamar ba a san ciwon samunsu ba. Wasu saboda kuruciya da rashin wayo ko sunan garinsu basa rikewa. Sai a shekara biyu yaro bai je gida ba. Duk kuma masu kare irin wannan karatu idan ka duba babu dansu ko daya da zasu iya turowa. Na tabbata iyaye mata da yawa zasu yarda dani akan son a dakile wannan tsohon system din da kullum yake kara tabarbarewa. Duk lokacin da muka yi ido hudu da almajiri sa'annin yaranmu kananu sai mun shiga damuwa. Saboda ya zama dandalin yada mumanan dabi'un da sai sun baci ake sani. Allah Ya kawo mana mafita ta alkhairi akan duk abin da ya damemu. Amin)

Last page shortly in sha Allah.





UWA UWACE...Karshe


Batul Mamman💖



Shiru ne ya ratsa office din na wani lokaci bayan su Abbati sun gama bayaninsu. Baka jin komai sai jan hancin Asabe da saukar numfashin mazan da karfi. Hakika wannan zama ya zama tamkar daukar darasi ne ga dukkanin wadanda Allah Yasa aka yi a gabansu. Kowa ya kalli labarin ta fuskar da ya shafe shi.

Baaba Mari fin karfi ne.

Mal. Inuwa makauniyar biyayya.

Mal. Sa'idu kasa bambance neman ilimi (almajiranci) da bara (rokon abinci, da kudin gabatar da bukatun rayuwa). (Jama'a da yawa sun jahilci kiyayyar da ake nunawa wannan na'u'in karatun domin sun hada shi wuri guda da littafi mai tsarki. Abin da basu gane ba shi ne da makaho, da gurgu, da kuturu da dan malam wato almajiri dukkaninsu mabarata ne. Gyaran da muke nema shi ne a gatancewa yaran da ake turowa karatu ta yadda karatun kadai zasu yi cikin aminci da kulawa. Ita kanta bara tana kashe zuciyar ma'abocinta ne. Kenan tana rage darajar ilimin da suke nema. Duk inda almajiri mai roko yake ba shi da wata kima a idon mutane saboda kullum shi ne hannun karba.)

Asabe sakarar uwa wadda ta biyewa sawun miji wurin banzatar da 'ya'ya.

Alh. Rabi'u irin uban da ake yiwa yawancin hausawa kudin goro da halayyarsa. A haifa a kasa rikewa saboda son zuciya da zalunci. Irinsu da yawa 'ya'yansu lalacewa suke yi kuma su zama silar lalacewar 'ya'yan wasu.

Alh. Tahir magidancin da ya dauka zai ci bulus a tattare da alfashar da ya rayu cikin biyewa zuciya wurin kosar da ita. A yau duk wani tunaninsa ya ruguje. Ashe ita zina ba a cin bulus. Ko ayi a inda zai maka radadi ko aje lahira a girbe shuka. Ko a hadawa bawa duka biyun. Sanin zahirin su Abbati ya firgita shi fiye da zato. Gashi kuma suma bashi da sauran kima a idons.

Alh. Sadisu masu madafan iko wadanda nasu kadai suka sani. Duka matsalolin yau zasu iya zama tarihi idan gwamnati ta saka hannu tayi abin da ya dace. Maimakon haka sai suka zabi amfani da gurbatattun cikin al'umma wurin cimma burikansu na siyasa. Sai gashi daya daga cikin baragurbin ya harbi tilon dansa har ma yana shirin rasa shi baki daya.

*
Da aka rasa mai fara tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login