Showing 27001 words to 30000 words out of 242549 words
yake faruwa. Ko a jikinsa don bai ma yarda ba. Ya dai ce Allah Ya bata lafiya tare da juyawa ya koma cikin gida. A zatonsa irin shirin da suka saba masa ne don tatsar kudi a jikinshi. Tuni ya riga ya dawo daga rakiyar su, auren ma ya fice masa rai don dai ba yadda zaiyi ya rabu da ita ne.
Da kunnuwan sa ya ji wani lokacin da Ladidi take cewa Nasiman akawo mata Mardiya yaye don su samu hanyar cin kudin gurinsa. Shi kuwa daga jin haka kafin su farga washegari ya dauke ta ya kaita wurin Yakumbo. Gashi har yanzu kusan satin ta biyu gurin bai ma karbo ta ba. Lokacin haihuwarta sun tatse shi son rai. Shi da ya saba mu'amala da mata a waje ya san duk wadannan karairayin na cin kudi. Sai dai kawai ya kyalesu suka zata wankarsa suke. Daga lokacin ne ya dinkewa Nasima da ta dawo.
"To sai ki tashi bakin naki ne. Daya daga cikin kannenki ni ba rike sunayensu nake ba."
Bai ko damu da fada mata me ya faru ba kamar bai ji sakon ba haka ya ja bargo ya koma baccin sa.
Da haushin kalamansa na rashin rike sunayen kannenta gami da tashinta daga bacci ta fita. Fitar tata ke da wuya sai gata ta dawo ta dan tattaba shi don ya tashi,
"Wai Ladidi ce ba lafiya"
"Tun a wajen na ce Allah ya bata lfy." Ya sake juyawa ya cigaba da baccinsa.
Ta danyi kwafa a ranta ta fita da niyyar shirin tafiya. Bayan tayi wanka ta shirya ne ta shigo ta same shi yadda ta barshi yana baccinsa hankali kwance. Bata ji dadin yadda ya nuna halin ko in kula ba amma dama itama ba daraja bane da uwar a idonta.
"Amma dai Diya yanzu fa nace maka Ladidi ba lafiya baka ce komai ba."
"To me kikeso na ce miki?" Ya ce da alamun kosawa.
"Kudin zuwa asibiti zaka bani mana."
"Bani dasu, dan Allah ki barni na samu bacci me dadi kar ki dame ni." Ya juya mata baya yana tunanin ko idan ya tashi ya je Zaria wurin Khadija.
Fuuuu ta fice tare da bugo masa kofa ta tafi gidan su. Halin da ta iske Ladidi ya wuce yadda tayi tsammani. Haka suka kwasa sukayi a asibiti ba yadda take. Allah dai ya taimaka akwai yan kudade hannun Nasiman dasu ta biya aka basu gado tare da saka mata ruwa.
Suna zaune asibiti har la'asar. Ladidi jiki ya dan lafa ta samu ta lallaba ta tashi zaune.
"Wash, Nasima me zamu samu ne na dan saka a ciki? Me kuka dafo ne a dan tarfa min naci."
Shekrke ta kalli uwar tare da sakin wata yar dariya.
"Amma dai wallahi Ladidi a gaishe ki. Ace kin kwana kina cikin wannan yanayi amma daga dan samun salama sai ki hau neman abinci."
Marairaice fuska tayi "To yar nan ya za ayi? Kinga ko fa magungunan nan da ake narka ma ba za suyi aiki ba in babu abinci. Ni a bar zancen nan dan Allah ku zuba min na ci. Allah ma yasa dai ba mai da yaji ba ne. Nafi son harkar miya kun san akwai gina jiki."
Rai a bace Nasima ta yarfe hannuwa "To ni dai babu wani abinci anan. Tun safe da muka kawo ki ko tashi ban daga nan ba balle wani zancen abinci."
Tuni fuskan Ladidi ya rikide tai kicin kicin ta hade rai.
"Yanzu kina nufin haka zan wuni na kwana ban ci abinci ba fisabilillahi. In zawon da na kwan inayi be kar ni ba ai sai yunwa tayi sanadi na."
Nasima ta juya ta kalli Jiddo a wulakance.
"To kinji dai sai ki tashi kije ki dafo ki kawo ko."
Ba musu Jiddo ta ta mike har zata fita ta juyo ta nema kudin mota, Nasima ta ciro a wulakance ta dangwara mata a hannu tana cewa "saura in kinje ki dade".
Jiddo bata ce komi ba ta fice abunta tana fatan Allah dai ya kai damo ga harawa Ya bata ikon cikar burinta dan tsaf sai ta rama duk wannan wulakanci da ake mata.
Tana sauka daga bus a bakin layinsu maimakon ta wuce gida sai ta tsaya kofar gidan Nasima. Ta gaishe da Malam Ado tace masa Nasima ce ta aikota. Bsi hanata shiga ba tunda ya san kanwar matar gida ce.
Ganin motar Tahir a farfajiyar gidan ba karami dadi yayi mata ba har da sakin dan murmushinta.
Yadda duk aka kai aka kawo aka yi auren Nasima da Tahir din ai babu abun da basu sani ba. In dai kura na maganin zawo to shakka babu yau zan wa kaina magani ta fada a ranta tare da cusa kai cikin gidan
A falo ta iske Tahir ta gaishe shi a ladabce tare da fada masa Nasima ce ta aiko ta yin girkin asibiti. Bai ce mata komai ba sai tunanin irin wannan karfin hali nasu, dan me ba za suyi a nasu gidan ba sai a nashi. Hanyar kitchen ya nuna mata ya kau da kai ya cigaba da abun da yakeyi.
Kafin ta wuce sai ta cire mayafi ta aje kan kujera, ta wani hau yarfe gumi daga su wuya da kirjinta. Jujjuya jiki ta dinga yi na daukar hankali. Tahir kamar baisan tana gun ba, ita ko bata fasa ba har sai da ta tabbatar ya waigo ya kallo inda take nan ta juya masa baya ta wuce kitchen din.
Bata jima da shiga ba ta saki wata kara har sai da Tahir ya dan firgita ya taho da azama zuwa kitchen din dan ganin me ya faru. Tsalle ya sameta tana yi tana direwa ita nan a dole hannun ta ya kone.
Sai ya tuna da lokacin da Nasima ta fara rungumar sa a cikin gidan da irin wannan sigar. Sabanin Nasima, ita Jiddo bata nufo shi ba. Yayi dan murmushi a ransa tare da yi mata sannu ya juya zai fice kawai ta saka kuka. Hakan ya sashi dawowa.
"Naga hannun" ya umarceta.
Kamar jira take ta mika masa. Yasa hannu ya riko hannun nata ba kunya ba tsoron Allah. Daman yaya lafiyar kura balle yaga abin da rai ya biya. Ya hau hura mata yana kallon cikin idonta, ita kuma tana wani sussune kai.
"Ko muje daki na shafa miki magani ne."
Ta sunkuyar da kanta tana matse ido wasu hawayen na zuba "A'a ka barshi ma ba zafi."
"To kukan na meye?" Ya tambaya hannunsa a bayanta yana shafawa. Suna hada ido ya kanne mata nasa yana murmushin 'yan duniya.
"Babu komai" ta ce baki na rawa.
Dakinsa ya ja ta tana binsa kamar bata sani ba tana kuka. Rarrashinta ya yi ya sake tambayar dalilin kukan.
"Hannuna zugi yake yi min da wuya na iya girkin. Idan na koma haka kuma Nasima da Laraba ba kyaleni zasu yi ba."
"Kar ki damu. Muje na saya musu sai ki kai."
"To ai za ta yi min fada idan taji kai ka saya." Ta ce a shageabe.
"Zan yi mata bayani."
Godiya ta dinga yi masa har suka bar gidan. Da dai bai yi niyyar zuwa asibitin ba amma tunda yana son samun kan Jiddo sai ya bi a sannu. Da suka isa asibitin shi ya dauko ledojin abincin tana biye dashi a baya. Ta bude masa kofar kafin ya shigo Nasima ta soma zaginta.
"Uban me ya tsayar dake daga zuwa girki bayan babu nisa."
Hawaye ta sake tarawa a idon tana rawar murya ta bata hakuri. Tahir kuma yaji ransa ya baci. Ita da Ladidi suna ganinsa suka fara murna.
Duk da Nasima taga abinci ya kawo amma sai da ta tambayi Jiddo ina wanda ta dafa.
"Konewa nayi Nasima. Shi ne Abban Mardiya ya ce na barshi zai siyo."
Mantawa tayi da yadda take ladabin kura a gabansa ta hau zazzaga mata bala'i.
"Wani salon karuwancin ne wannan ko me? Gidana na tura ki? Me ki ka je yi?"
Ai sai Jiddo ta fashe da kuka
"Naji kin ce naje gida nayi girki. Na zata gidanki ki ke nufi."
Sake bude baki tayi Tahir ya mike a fusace sai tayi shiru tana taune lebe saboda bacin rai. Ta fi Jiddo iya bariki. Idan ta ce za ta shiga huruminta sai ta kwashi kashinta a hannu.
Daga ranar ta ja mata kunne akan kada ta sake zuwa gidanta ko da wasa. Ladidi ta sake matsa mata. Ba don tana morarta da aiki ba da ta korata inda ta fito. Jiddo ta amsa da to. Aka kwashi kwanaki Tahir baya ganinta. Sai rannan bayan ta gama fakonsa ya hangota a gefen gidansa tana share hawaye. Da sauri ya taka burki ya fita wurinta.
"Ke lafiya?" Bai rike sunanta ba.
Fashewa tayi kuka ta rike ciki tana matsawa.
"Don Allah ka taimakeni. Cikina, cikina."
"Muje ciki wurin Nasima. Ko kuma shiga mota bari na kira ta mu kai ki asibiti."
Hannunsa ta kamo da sauri tana zubewa a kasa "ni dai la taimaka min ka mayar dani garinmu." Kallon rashin fahimta ya yi mata ta ce masa tun ranar da ya kaita asibiti da abinci Nasima ta hanata shiga gidanta. A can gidansu kuma Ladidi ta matsanta mata. Abinci ma sai da kyar ake bata. Yanzu haka ma ciwon na yunwa ne.
Da yake idanunsa sun rufe sai yaga kamar da gaske ta fada. Ransa ya mugun baci ya shiga da ita gidan. Nasima bata nan bai san inda taje ba. Khadija kuma ta zo hutu da yara saboda bikin kanwarta bai san suna ciki ba. Akan idon Suhaib ya shigar da ita dakinsa. Ya koma ya hada mata abincin da Nasima ta ajiye masa ya kai mata. Ta ci ta koshi sannan ya ce ta taso zai kaita hotel ta kwana gobe sai ya kaita gidansu.
Khadija ta gama yiwa Sauda wanka kenan Suhaib ya fada mata Abbansu ya dawo.
"Amma Mami naga ya shiga dakinsa da bakuwa maimakon ta zauna a falo ta jira ki fito."
Gabanta taji ya fadi. Ba abin mamaki bane daga halayyar Tahir amma tayi zaton ya yi hankalin da zai daina kawo tarkacensa gidan aurensa. Yadda fuskarta ta sauya a idon Suhaib ya gane akwai matsala. Da ta ce ya zauna ya kular mata da Sauda tana zuwa sai yabi bayanta ba tare da ta sani ba.
Batun zuwa hotel kadai taji a kofar dakin ta kwankwasa. Ya zata Nasima ce saboda haka kai tsaye ya bude. Ganin Khadija a tsaye sai yaji kunya ta lullube shi.
"Ko don lafiyarka idan ma baka tsoron Allah Ya kamata ka yiwa kanka fada."
Da sauri ya ce "ba fa abin da kike zato bane. Taimakonta kawai nayi."
"Hmmm, taimako a uwar daka? Ina jiye maka ranar nadama domin wallahi hakkin duka matan da ka ke lalata dasu ba zai barka ba."
Haushi yaji tunda bai yi din ba kuma take gaya masa magana. Kafin ya ce wani abu Nasima da ta dawo ta shigo wurin. Bata san me yake faruwa ba ta taho da gadara da tsiwarta.
"Duk jarabar mutum dai yau girkina ne tunda ban san zaki zo ba. Sai ki koma sai gobe."
"Ke miji ya dama Nasima. Idan kin shiga kya yi maganar girki da ta ciki ba ni ba."
Ai kamar ta watsawa Tahir wuta ya ji takaicin abin da ta ce. Hannu yasa ya janyota za ta bar wurin ya kwasheta da mari.
"Wato ban dameki ba? To idan kin isa ki saki kanki."
Hannuwa yaji daidai kugunsa aka dage aka hankada shi sai da ya daki kofar dakin ya fadi. Yana tashi yaga Suhaib yana huci kamar maciji.
"Ni ka ture Suhaib?" Ya ce da tsantsar mamaki.
"Me yasa ka mari Mami?" Yaron ya bashi amsa kai tsaye. Bakinsa Khadija ta doke da sauri tana cewa ya bawa babansa hakuri.
"Khadija halayyar da ki ke koya musu kenan?"
Za ta yi magana suka ji sautin ihun Jiddo ya fada dakin yayin da Khadija taja hannun Suhaib. Amma kunnuwansa sun jiyo masa kalmar 'karuwa' da Nasima ke kiran Jiddo.
Lokacin da Khadija ta ce suyi magana da ta ciki ta fada dakin da sauri. Jiddo dama tana jin muryarta ta kwanta akan gado ta kwaye zani har cinya. Bata ma gane ko wace ce ba saboda azabar kishi sai da ta finciko wuyanta.
"Jiddo?" Ta ce da rawar baki "ni za ki yiwa haka? Mijin nawa zaki nema saboda ke 'karuwa ce'."
"Nasima kiyi hakuri babu abin da muka yi." Ta ce tana kukan munafurci. Idanunta sun rufe ta shiga dukanta ba ji ba gani.
Da kyar Tahir ya kwaceta ya kuma tsinkawa Nasiman mari.
"Ki je gida sai na nemeki. Zan zo na karbi Mardiya don ba za ta zauna a gidanku na marasa tarbiyya ba."
Hauka ne kadai Nasima bata yi ba. Tana ta kokarin sake kamo Jiddo ya shiga tsakani. Da kuka ta bar gidan da alwashin sai taga bayan Jiddo. Ita kuma tana ganin fitarta ta soma kukan rayuwarta ta kare domin ba ita ba hatta mahaifiyarta sai Ladidi ta ciwa mutumci.
"Zan baki matsayin da basu isa su tabaki ba."
Ya kuwa aikata abin da ya ce! Sati hudu a tsakani sai ga Jiddo ta dawo gidan a matsayin amarya. Dakinsa ya zama nata.
Nasima da Ladidi suka haukace wurin bin bokaye da malaman tsibbu. Zumuncinsu da 'yan uwa da yawa ya lalace. Da kyar da sudin goshi bayan wata biyar ya yarda ta dawo gidansa. Kazamin kishi suke bugawa ita da Jiddo kamar zasu ga hanjin juna.
Tun daga kan Mardiya bata sake haihuwa ba. Jiddo ta zubar da ciki yafi a kirga a kauye har ya taba mahaifarta. Ita ko haihuwar bata yi ba. Khadija ba ta shiga sabgarsu daga su har mijin da suke rigima a kansa. Tana gama karatu kamfanin da tayi bautar kasa suka riketa. Albashinta ta shiga tarawa har ya isa sayen fili. A hankali ta soma gina kayanta saboda ta matsu ta raba 'ya'yanta da kazamin gida irin na mahaifinsu. Duk da haka tana kokari sosai wurin shanye abubuwa da rufawa Tahir asiri don kada su san halinsa. Kusan babban burinta a rayuwa bai wuce nesanta su daga sanin halinsa da kwatanta aikatawa ba.
Sai dai tunda kudi suka sake zama a hannunsa rashin mutumcinsa ga duka matan ma ya karu. Ita da yake ragawa darajar 'ya'ya ma ya daina. Nasima da Jiddo dama basu da wanban darajar. Gida ne tambadadde wanda mai shi ya lalata da hannunsa. Abu daya suka tsira dashi wato makauniyar soyayyarsa ga 'ya'yansa. Su biyar dinnan bashi da na biyunsu. Don ma Suhaib ba ya sakin jiki dashi ko kadan.
Tun ranar da ya mari Khadija ya dauki karan tsana ya dorawa mahaifinsa. Da sannu yana kara wayo ya gane halinsa ciki da bai. Sai yake jin inama wani ne can Abbansa ba wannan manemin matan ba. Khadijan da yake yi dominta kuma kullum fada take masa akan ya bi mahaifinsa don neman rabauta ranar lahira. Sai yake ganin kamar cin kashin da ake mata baya damunta. Yana shekara goma sha biyar ya fara zukar tabar wiwi a boye saboda yawan damuwa da halin da iyayensa ke ciki. Lilu kuma ya zama mugun fitinanne mai yawan dauko magana. Duk kaffa-kaffa da Khadija take yi da rayuwar 'ya'yanta saboda mahaifinsu ba zai hana kaddara ta cimmusu ba wata rana.
Wannan kenan!
***Wattpad
https://my.w.tt/Fc8knjdAf9
UWA UWACE...7
(Da dadi ko ba dadi)
Batul Mamman💖
***
Kwance tashi ba wuya a wurin Allah, yaran Innayo duk sun girma amma har kawo yau sana'o'in da takeyi babu wanda ta daina.
Girma ya soma kama ta, ga wahalhalun ayyukan da takeyi domin ta rufawa kanta da ahalinta asiri. Sannu a hankali lafiyar idanunta ya soma tabuwa sakamakon yawan zama gaba murhun da takeyi. Amma haka nan take daurewa don samar wa yaranta ingattacciyar rayuwa. A kullum burinta
Yaranta manyan uku duk sunyi aure Uwani, Maimuna da Salima, saura Zara da Hasiya a gabanta. A yadda rayuwa take gara musu tsugunne bata karewa Innayo ba.
Uwani ta gama School of Nursing abinta har ma ta kama aiki a Abdullahi Wase Specialist Hospital Kano wanda ake yiwa lakabi da asibitin Nasarawa. Tana samun kudi sosai sai dai anyi rashin sa'a. Halinta yana neman zarta na mahaifinta. Mugun mako da kyashi gareta. Mijinta yana da rufin asiri daidai gwargwado. Lab Technician ne a asibitin nasu. Bai taba dora mata nauyin da ba nata ba na kula da gida ko 'ya'yansu guda uku. Tana da wadatar da za iya taimakawa mahaifiyarta musamman ta harkar lafiyarta amma kullum cikin kiran babu take. Don ma kada Innayo ta dinga tambayarta kudi sai wata ya raba ta kan leko gidan. Tana zama bata da zance sai na bukatunta wadanda kudin hannunta ba sa su isa ta biya ba.
Ita kuma Maimuna lokacin da Allah ya kawo mijin rimi-rimi ya amince za ta cigaba da karatun da take a Legal. Sai dai anayin aure ko wata biyu ba a rufa ba zance ya juye. Innayo tace indai don kudin ne zata cigaba da daukan nauyin 'yarta. Yace yaji ya amince dama kudin ne baya so ya biya. To kuma sai mahaifiyar sa ta ce bata yarda ba ko dai tayi zaman aure ko ta fita taje tayi karatun ta.
Nan kuwa yace to sai dai ra ajiye karatun. Maimuna shaukin soyayya na dawainiya da ita a lokacin tuni ta amince da bukatarsa. Innayo taji ciwon wannan abun amma ba yadda zatayi haka ta hakura. Haihuwa biyu duk ta tsufa ta lalace. Babu cima mai kyau ga tashin hankalin uwar miji da talauci. A hankali nauyinta ya sake komawa wuyan Innayo kuma bata yi mata komai da kyashi domin 'yarta ce.
Salima kuwa watarana suna zaune kwatsam Alh Rabiu yazo wai yayi mata miji kuma aure nan da nan zaayi ba bata lokaci. Nan fa innayo da Alh Rabiu suka hau suka duro ta dage tana so yar ta tayi karatu ko don gudun abin da ya sami Maimuna amma yaki yarda sam. Karshe dai haka wannan ma ta hakura akai auren. Ashe basu sani ba auren biyan bashi yayi mata ga mijin mashayi ne na bugawa a jarida. Yau duka gobe tsangwama haka dai itama Salima rayuwar ta kare babu wani cigaba.
Banda lalurar ido tsabar damuwa da halin da 'ya'yanta suke ciki sai hawan jini ya sarketa. Innayo bata fasa komai ba. Tashi karfe hudu na asuba har jikinta ya saba. Kwata-kwata bata san hutu ba. Zara da Hasiya da