Showing 216001 words to 219000 words out of 242549 words

Chapter 73 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3354

Uncle dinnan ya kaini na ganshi. Kuma har ya daukoni zai kawoni gida. Sai Uncle dinnan ya buga masa kai da bango ya yi jini. Sai ya bani ya ce ka kira Daddy dinsa a zo a dauke shi."

Tiryan tiryan ta fada kowa yana ji. Cikin kuka Zakiyya ta roki Abbati da ya fada mata tsakani da Allah me yake faruwa. Ita tunda basu mayar da Qibdiyya gida ba ta san akwai matsala.

Kansa sake daukar chaji yayi. Ya waiga babu Munzali a wajen. Ya dubi su Mami wadanda sai yanzu da hankalinsa ya daidaita ya tuna gamuwarsa da Alh. Tahir. Yawu ya hadiya ya fadi iya abin da zai iya.

"Abokinmu Shazali ne ya dauketa jiya domin ya yi mana barazana ni da Munzali. Daga inda na karbota nake shi yasa ma ku ka ganni haka" ya nuna suturarsa wadda bai san tuni kowa yake tunanin inda yaje aka yamutsasu haka harda yagewa ta wuya ba "Sauran bayanin sai na dawo. Da alama ba ita kadai ya dauka ba."

Wayar da tunda ya katse take faman ruri ya dauka tare da bayar da hakuri.

"Na tsaya neman bayani ne game da mai wayar don ban san shi ba. Ka fada min inda zamu hadu domin zancen ba na waya bane"

"Dole ka ce ba na waya bane mana don kada ayi tracing dinku. Idan kudi ne ka fadi ko nawa kuke so a wuce wurin." Alh. Sadisu ya kare magana cikin fushi yana bubbuga kafarsa daya a kasa. Babu nutsuwa ko kusa a tare dashi. Duk sakan guda gani yake kamar zai rasa dansa har abada.

Shi kuwa Abbati da ya tuna yadda yaji kafin ya dawo gida da Qibdiyya sai ya yi masa uzuri.

"Kayi hakuri. Idan na zo zan yi maka bayani gwargadon abin da na sani."

Wayar a speaker take dama saboda 'yan sanda da suke wurin. Saboda haka da rad'a da inkiya da komai na kwatance suka nunawa Alh. Sadisu abin da suke bukata ya yi. Ya kuwa fada yadda suke so din.

"Ka same ni a gate din makarantarsu Abdul."

"Ina ne?"

"Kada ka nemi ka raina min hankali mana.."

Wani dan sanda ya sake yi masa alama da hannu. Ba don ya so ba ya fadi sunan makarantar da unguwar da take.

Kallon iyayensa da duk wadanda suke wurin Abbati ya yi ya ce,

"Zan je na sami mahaifin yaron"

Mal. Sa'idu ya dube shi da damuwa a fuskarsa ya ce "anya ayi haka kuwa? Daga yanayin maganarku naga kamar kai yake zargi"

"Babu komai in sha Allahu. Bari na canja kaya na je"

Mami Khadija ya sake bawa hakuri da Lilu. Suka yi musabaha da shi da Suhaib sannan suka ce masa zasu koma gida.

"Za ku gane hanya kuwa? Ko za ki biyoni a baya na kai ku sai na wuce daga can?" Ya yi maganar yana duban Farha.

Mami tayi la'akari da halin da ake ciki ta ce "Kada mu wahalar da kai. Idan mun bace hanya zamu kira gidan. Allah Ya rufa asiri Ya kare gaba".

"Babu wata wahala. Makarantar a hanyar take. Sai ma mun wuceta kafin mu karasa gidan"

Baaba Mari ta saka baki ta ce su amince su bishi. Idan ya fadawa mutumin abin da ya sani sai su wuce. Bai kamata a barsu su tafi bayan abin da ya faru ba.

Haka kuwa aka yi. Cikin minti goma Abbati ya kimtsa ya sauko suka tafi. Bai nemi Munzali ba saboda ya san a yau zuciyarsa ko kusa babu dadi. Lilu ne yake jan motar. Farha na gaba su Mami da Suhaib na baya.

Kafin su isa Alh. Sadisu ya kira Abbati yafi a kirga. Wani ya dauka ya ce su yi hakuri yana hanya, wani zubin ya share saboda ransa ya fara baci. Suna isa ya hango motocin 'yan sanda fal a gate din makarantar. A ransa ya ce dan wani babba ne Shazali ya tabo. Wuri ya samu ya yi parking su Lilu ma suka yi a bayansa a waje.

Yana fitowa aka sake kira. Ya kara wayar kenan a kunnensa daga bakin gate din kawai yaga 'yan sanda sun yi masa da'ira. Kafin ya gama sanin me yake faruwa sun fara dukansa. Cikin abin da bai wuce kifta ido da budewa ba suka tura shi cikin motarsu.

Farha bata san lokacin da ta fito daga tasu motar ba da aka fara dukan shi. Lilu ma ya biyota. Haka Mami Suhaib daga baya. Mami ta rasa da wane suna za ta yiwa wannan rana lakabi. Kafin su iso motar da aka saka Abbati tuni tayi gaba. Sauran ne a baya. Farha kuka kawai ta fashe dashi. Lilu ya tsayar da daya daga cikin motocin yana yi musu bayani cewa ba Abbati ne ya dauke yaron ba.

"Yaro ka kama bakinka ko kai ma a tafi da kai wallahi." Wanda ya bashi amsa ya kallo gate din ya ce da direbansu "ga Alhajin nan ya fito muje"

Su Mami suka juya a tare. Alh. Sadisu ne ya fito yana tafiya da sauri kamar zai tashi sama. Ga 'yan kazanginsa da securities da malaman makarantar suna biye dashi a baya.

Kwakkwaran kallo guda Mami tayi masa ta kara sauri tun kafin ya shige motar da aka riga aka bude masa.

"Alh. Sadisu?"

"Don Allah ku rabu dani" ya amsa a fusace don ya gaji da amsa mutane. Burinsa ya gan shi a station din da aka kai mutumin da ya kira shi a waya.

Da ta fahimci da wuya idan zai juyo balle ya kalleta ne ta kara da cewa "Alhaji Khadija ce, Maman Suhaib"

Ai kuwa da saurinsa ya leko kansa ta taga.
"Hajiya Khadija me kike yi a nan?" Ya yi wa direbansa alama da su tafi yana cewa da ita "Za dai mu yi magana daga baya, yanzu ina cikin tashin hankali ne wallahi"

Da sauri ta ce "na sani.Abdul aka dauke ko? Manemin 'yarka ne aka kama yanzu. Ba shi ne ya dauke shi ba"

Kallonta ya yi a tsanake sannan sautin Innalillahi da Farha take ta ambato cikin hawaye ya soma shiga kunnens.

"A mota kuke?"

"Eh"

"To ku biyo mu don Allah."

Suna shiga mota tasa Suhaib ya kira mata Munzali. Ita da kanta tayi masa magana ta kuma umarce shi da ya boyewa su Baaba Mari kafin a san me yake faruwa. Sai dai tuni hankulan iyayen ya tashi tunda ya amsa wayar ne a gabansu. Suna gama wayar suka nemi jin ba'asi. A dole ya sanar dasu. Haka suka tashi babu wanda ko ruwa ya shiga bakinsa tun zuwansu suka bishi.

A hanya ya kira Alh. Tahir. Yana can gidan Comared har lokacin bai tafi ba. Ya yi bakincikin rashin zuwa da direba gidan saboda har yanzu babu kuzarin tuka mota a tare dashi. Kansa ya rufe ruf ya rasa zaren kamawa tun tafiyar Abbati.

Da yaji kira kamar ba zai dauka ba yadda ya yiwa sauran kiran da suke ta shigo masa. Sunan mai kiran da ya gani ne ya sauya masa tunani. Abokinsa ne da suka hadu ta dalilin ayyukan kwangila. Duk zafin zuciya da kwarjinin da Alh. Sadisu yake yiwa mutane sai tasu tazo daya dashi. Har ta kai suna ziyartar juna a gida.

"Alhaji kaji labarin na shigo Kano ne?" Ya ce da kokarin kawo raha tsakaninsu.

"Kana ina Alh. Tahir? Don Allah duk inda kake ka taho police station din Gadon K'aya. Akwai matsala an sace Abdul kuma muna tare da iyalinka Haj. Khadija."

Satar Abdul din da yaji ta firgita shi. Sai dai ko kusa bata kai kidimar da ya shiga da yaji sunan Mami ba. Ya nemi jin cikakken bayani amma shi ma Alh. Sadisun bashi da abin cewa.

Mukullin motarsa da waya kadai ya dauko ko hula da babbar rigar da ya cire bai tuna ba ya fito. A harabar gidan ya tarar da Comared da Shazali kowa rai a bace suna ta musayar yawu. Comared ya dora masa laifin duk abin da ya faru shi kuma Shazali yana cewa ba zai fita ba sai an bashi kudin da aka alkawarta masa ko ya baza sirrinsu a ahafukan sada zumunta.

"Kai karamin kwaro ne Shazali. Karyar rashin mutumci kake shi yasa har ka sami kwarin gwiwar mayar min da magana. Harma da barazana. Amma yanzu zan tuna maka waye ubangidan kuma waye bawa."

Kira ya kwala da karfi wasu garadan maza biyu suka fito ya umarcesu da su kulle masa Shazali a store din gidan. Da yake jikinsa ya riga ya yi tsami saboda dukan da Abbati ya yi masa sai ya kasa kwatar kansa. Alh. Tahir yana gani aka ciccibe shi aka yi ciki dashi. Da Comared ya nemi jin ina zai je da sauri haka kin fada ya so yi. Sai kuma ya tuna cewa ta dalilinsa ya hadu da Alh. Sadisu. A takaice ma dai yana cikin yaransa na hannun dama. Saboda haka babu bata lokaci ya zayyane masa iyakar abin da yaji daga bakin Alh. Sadisun. Comared ko cikin gidan bai koma ba ya kira direbansa suka tafi tare.

***

Kafin su Alh. Sadisu su iso har an fara dukan Abbati a cell. Lokacin ya daina kokarin kare kansa daga zargin da ake yi masa balle dukan. Irin tunanin Munzali wanda yake ta kwabarsa a kai ne ya shige shi. Kokwonto da tsoron ko tubansu bai karbu ba shi yasa da an toshe kofa daya sai wata daban ta bude ta bakin ciki.

Ba su suka sarara masa ba sai da wani ya leko ya yi musu magana.

"Kai Sergent, ku taho da shi ofishin DPO yanzun nan ana jira"

Suna jin haka sun san cewa Alh. Sadisu ma ya iso. Jiki na rawa saboda kwadayin samun wani abu suka fito. Dukan da suka yi masa ma dama don su burge shi ne in yaji dadi ya yi musu ihsani.

Hankada shi su ka yi har ciki. Tausayinsa ya sake tsirga zuciyar Farha da taga yadda ya koma cikin kankanin lokaci. Fita taji tana son yi daga office din saboda ba za ta iya jurar kallon sa a a cikin wannan yanayin ba. Tana share hawaye suka hada ido sai ya yi murmushi yana yi mata alama da ta bar kuka.

Bai ankara ba yaji an kai masa wata mahaukaciyar a wuya. Yana kici-kicin kwacewa sai saukar duka a gefen idonsa. Farha ta sake saka kuka yayimda Lilu da DPO suke kicikicin kwace Abbati daga hannun Alh. Sadisu wanda yake ta ihun a fito masa da dansa.

Da kyar bayan an rabasu DPO din ya ce da Abbati "Malam ina mai baka shawara da kada ka wahalar da kan ka da mu ka fada min yadda aka yi ka dauke dan Alh. Sadisu da dalilinka na daukarsa"

Zai fara bayar da amsa su Munzali suka shigo suka same su. Hankalinsa ya kara tashi da yaga yadda aka sab'a masa kamanni a lokacin. Wannan abu fa a dalilin dawo da 'yarsa ya same shi. Shi kadai yaga ribar zama da Abbati yayinda Abbatin yake shiga tarin matsaloli tun farkon haduwarsu. Baaba Mari da Mal. Inuwa suka rasa abin cewa saboda tsananin tashin hankali. Mal. Sa'idu ne ya hau bayanin cewa dansa ba zai taba cutar da wani ba balle a kai ga sace shi.

DPO ya tambayi matsayinsu tare da yiwa Sergent din da ya shigo dasu fadan cika mutane a wurin. Jin cewa iyayen wanda suke tuhuma ne sai ya ce lallai a ragu. Office din ya rage daga Alh. Sadisu sai Mal. Inuwa, Munzali (a matsayin mahaifin yarinyar da ta kawo waya) da Abbati. Su Baaba Mari, Hanne da Mami Khadija da su Asabe duka suka koma reception. Mal. Sa'idu kuwa jinjina kai ya dinga yi. Duk takamarsa akan 'ya'yan 'yan uwansa yana ji yana gani DPO ya ce ainihin mahaifin Abbati kadai ake bukata. Wannan ya kara karya lagonsa da yaga ko kara babu Mal. Inuwa ya ce shi ne uban.

Shi Abbati Allah kadai Ya san irin ciwon da kansa, jiki da ruhi suke yi masa a wannan lokacin. Idonsa daya har ya tara jini don ya kasa bude shi sosai. Ya daure ya fada musu iya abin da ya sani

DPO ya bubbuga kan bironsa akan tebur ya sake yi masa wata tambayar.

"To kai me yasa ya dauki taka 'yar? Sannan ina ya kaita har ta hadu da Abdul?"

"Ban san inda ya kaisu ba. Kamar yadda na fada maka ya yi amfani ne da abotarmu ya tafi da ita daga hannun kakarta a asibiti." Abbati ya amsa masa cikin wani irin yanayi na kosawa da komai.

"Wannan bayanin naka bana jin ko alkali ka fadawa zai karbi uzurinka balle ni."

Munzali ya galla wa DPO din harara ya ce "Karya kake so ya yi maka ko me?"

"Kaga DPO a mayar dashi cell mana a dauko Shazali din" Alh. Sadisu ya fada ganin lokaci na tafiya an kasa cimma matsaya guda "idan wani abu ya sami d'ana ku ma da kuke ta jan kafa ba tsira zaku yi ba" ya kare magana yana tashi tsaye. Fita ya yi da waya a hannu yana waya wadda da alama da wani babba cikin 'yan sanda.

DPO din da kansa ya taso Abbati a gaba zai mayar dashi cell. Suna fitowa duka jama'ar da ya zata sun fita waje suka taso lokaci guda. Kowannensu da irin tambayar da yake jefowa domin son jin ko ya kubuta ne.

"Naga alama kana da tarin masoya" cewar DPO ya mayar da hankalinsa garesu "ku bashi shawara ya fadi gaskiya. Wallahi akan yaron nan case din yafi karfin tunaninku. Komishinanmu ma yana hanya kuma ko shi bai isa ya ja da umarnin Alh. Sadisu Nakano ba."

Jiki sam babu kwari Abbati ya dubi DPO din ya ce "iyakar gaskiyata na fada muku. Bani da zabi idan baku yarda ba sama da na cigaba da addu'ar neman taimakon Allah. A cikin kwanakin nan ina cikin jarabawar Ubangiji. Abubuwa suna ta tasowa wadanda suke barazanar rabani da duk wani abu da nake so. Babban burina bai wuce in rufe ido ko da na minti biyar bane idan na farka in ga ashe duka kwanakin nan mafarkinsu nayi."

Sai ga Mami Khadija da Asabe suna share kwalla. Farha ta fita ta sami wani dan dandamali ta zauna tana kuka. Ana dawowa daga rufe shi Alh. Sadisu ya dawo. Munzali ya tari gabansa ya ce shi ya san gidan Shazali.

"Me yasa baka fada ba tuntuni? Officer a hada shi da mutane mu tafi"

Basu bar wurin ba Alh. Tahir da Comared suka shigo reception din.
Mami Khadija da 'ya'yanta suka fara kallon kofa da tarin mamakin me ya kawo shi nan. Tana yin ido hudu da Comared taji zuciyarta ta tsinke. Babu ko tantama abin da suka saba na tara 'yan mata a guest house a kwana ana sharholiya ne take jin ya hadasu. Takaici ya sake kama ta da ta tuna cewa duba dansu fa suka zo yi amma ya kare da zuwa wurin Comared.

"Ina Abbatin yake?" Ya fara tambayar Munzali.

"Kai kuma waye?" DPO ya tambaya ganin shima nasa hankalin a tashe yake.

Alh. Sadisu ya bashi amsa da cewa abokinsa ne.

Shi kuma Alh. Tahir ya ce da DPO su shiga office dinsa yana da magana.

Alh. Sadisu ya yi saurin cewa "A'a ka bari tukunna. Gidan wani Shazali zamu je Abbati din ya ce wai 'yarsa a can ta hadu da Abdul."

Comared ya ce "Shazali kuma?"

"Ka san shi ne?" DPO da Alh. Sadisu suka yi masa tambayar a jere.

"Kwarai kuwa. Yallabai muje office din naka"

"Comared wallahi ba zan iya sake bata lokaci ba. Ka fadi ko ma mene ne a nan bani da damuwa." Alh. Sadisu ya furta a kagauce.

Alh. Tahir da Comared suka hada ido. Munzali kansa ya tsorata don bai san me zasu ce ba. Jikinsa ya gama sanyi yana jiran a farke musu laya.

"Shazalin nan da ake magana gagarumin kawali ne mai fada a wurin manyan mutane. Yana kai maza da mata duk inda ake da bukata. Bana fata amma indai shi ya dauke Abdul akwai yiwuwar ..."

A hargitse Alh. Sadisu ya ce "kai dakata min nan kada ka karasa wannan maganar banzan da ka dauko."

Baaba Mari, Mal. Inuwa da Mal. Sa'idu sun san waye Shazali da rawar da ya taka a rayuwarsu Abbati. Shi yasa furucin wannan mutumin bai basu mamaki ba. Sun dai kara shiga rudani ne akan dalilin da yasa Shazalin ya dauke Qibdiyya tunda basu sami zama anyi maganar ba.

Cikin lumana DPO ya lallaba Alh. Sadisu da cewa "Yallabai kada muyi saurin katse masa hanzari. Irin wannan abin yana cikin manya manyan matsalolin da muke fuskanta daga makarantun kwana. Lallai zamu je gidan shi Shazali din. Kuma yanzu zan tura mota a taho min da Principal, masu gadi da malaman makarantar tasu."

Gyaran murya Comared ya sake yi ya ce "ina da magana"

"Ina jinka" Alh Sadisu ya bashi amsa rai a bace kamar shi ne Shazalin.

"Ku bani kimanin rabin awa zan kawo muku Shazali har nan."

Alh. Sadisu ya nisa ya ce " kowane sakan guda yana da mahimmanci a gareni. Ni dai na fi son mu rankaya gidan nasa in ga halin da dana yake ciki"

"Ka sanni ba tun yau ba. Abin da ya shafi jininka nima ya shafeni. Ka bani lokacin da na bukata kawai. Komai zai zo karshe in sha Allah. Shazali shu'umi ne. Na rantse maka zai gwammace a kulle shi akan ya fadi gaskiya idan muguntarsa ta tashi."

"To meye alakarku da Abbati da shi wannan Shazalin da ake ta fada?" DPO ya jefawa Comared tambayar da take cin zuciyar kowa.

Alh. Tahir ne ya bashi amsa da cewa "Ni zan baka amsar tambayar nan idan komai ya lafa."

***

Babu wani abu da zai sami bawa face da sanin Mahaliccinsa. A wannan rana taimako ya zo wa Abbati da Munzali a yanayin da basu taba zato ko tsammani ba. Waye zai taba kawowa a ransa cikinsu cewa duk ranar da asirinsu ya tasarma tonowa Alh. Tahir zai zame musu garkuwa? Sai gashi ya zama wata katanga wadda ta tokare bayyanar sirrinsu da tozarcinsu a idon duniya ba tare shi kansa ya shirya hakan ba.

Kamar yadda DPO ya fada, ya tura motoci biyu an taho da duk wani mai kusanci da aji ko hostel din su Abdul daga makarantarsu. Masu gadi ma sai police aka zuba aka taho da su.

Jigum-jigum aka zauna jiran dawowar Comared. Alh. Sadisu kamar zai zare a tsokin lokacin saboda rabin awa ta gota.

Abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login