Showing 54001 words to 57000 words out of 242549 words

Chapter 19 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3359

da bai yi niyya ba. Tana tsaye a gabansa tana rangwada kai gefe da gefe. Duk wanda ya san Qibdiyya zai shaida manyance da tsantsar wayonta. Idan ma akwai tashi a hannun kaka wato Gwaggo Lami kanwar Asabe harda halinta. Wani abin idan tayi shekara goma ko ma fi za ka bata.

"Daddyna please fa nake ta cewa" ta dan turo baki alamar gajiyawa.

Daukota ya yi ya dorata a cinyarsa "ki zo na baki don Allah ki ci mu je mu kwanta."

Ita ma hakurinta ya kare tana ganin ba za ta sami abin da take so ba. Tafi son kwana a gidan Abbati amma tun bayan ya tura Hanne Kirikasamma sai ya ce ta dinga kwana a gidan Munzali tare da Iya Kande.

"Ni Papa. Papanaaaa"

Tun Munzali da Iya na rarrashi har ya koma fada. Bata yi shiru ba sai ciwon kai da ta kara masa. Wayarsa ya tashi ya dauko ya kira Abbati ba shiri.

*
Tun farkon kwanciyarsa har bayan asuba da ya koma bacci mafarkin Farha yake yi. Sunanta kuwa ya ambata a mafarkin da kuma a farke yafi a kirga. Wayar Munzali ce ta tashe shi ya yi guntun tsaki.

"Idan na shigo sai ranka ya baci. Ka san me ka katse min da wannan wayar kuwa?"

"Ba matsala duk abin da zaka yi na shirya in dai za ka dauki 'yarka. Yadda ka san in yi bacci a zaune amma kamar da gangan ta isheni da rigima."

Murmushi ne ya mamaye fuskar Abbati yayinda yasa kafa ya shure katon duvet din da ya lulluba dashi. Sanyin dakin ya sauka a jikinsa ya mike da gaggawa ya dora riga mai madauri akan dogon wandon baccin jikinsa.

Girarsa ta tattare da fushin da ya maye gurbin fara'arsa "me yasa ka tasheta da sassafe haka? Ko takwas fa bata yi ba. Yara suna bukatar isasshen hutu. Asabar din ma yaro ba zai huta ba to sai yaushe?"

"Sannu mai 'ya. Dadin abin dai nima ba daga bishiya aka tsinkoni ba. Haka kawai ta hana mutane bacci ka zo kana yi min fada..."

Dariyar da bai yi niyya ba ce ta kama shi. Wani zubin ya kan rasa gane da Munzali da Qibdiyya waye 'ya waye uba. Munzali har kishi yake da ita idan ya ga yaki kula shi. Ba don komai ba kuwa sai don ya tashi da yunwar kulawa irin ta iyaye. Shi ne komai na aminin nasa shi yasa yake ganin lokaci ya yi da zai yi amfani da wannan damar su saita rayuwarsu. A nasa bangaren dole sai ya je gida gobe. Munzali kuwa tunda iyayensa suna gari yanzu zai fara yi masa maganar abin da ya kamata ace ya yi tuntuni.

Wannan rayuwar ta ishe shi. Suna bukatar iyali na kurkusa wanda zasu rayu tare. Farincikinsa daya yaki da jahilcin da suka dage sosai suka yi. A lokacin sun yi ne domin samun kasuwarsu ta daga a idon manya. Yanzu zai musu amfani wurin yin kasuwanci a ilimance. Wayewa dai irin wadda mutum zai je ko'ina kai tsaye ya saje sun samu. Haka nan manyan kasa ke biya musu su je kasashen waje domin idan sun iso su amfana dasu. A haka suka sami wayewa sosai idanunsu suka bude.

*
"Papaaa"

Qibdiyya ta ce tana yin tsalle. Abbati ya dagata sama ya juya suna kyalkyala dariya. Munzali na ganin haka ya tashi zai gudu daki.

"Malam dawo magana zamu yi fa. Me Audu ya dafa ne?" Ya yi maganar lokacin da ya dire Qibdiyya.

A marairaice Munzali ya kalle shi "kayi min rai dan Mariya uban Mariya. Kaina wani yammm yake yi irin na mai shirin zarewa saboda rashin bacci."

Kafe shi da ido Abbati ya yi wanda ya nuna masa zaman nasa dole ne. Sai da ya harare shi ya koma ya zauna.

"Ka dai ci sa a ina tsoron masifarka wallahi da ba zan zauna ba."

Iya Kande ta dube su tayi dariya. Abokan suna matukar burgeta. Tana fatan kowanne ya sami matar da zasu yi zaman lafiya tare. Ta san wani abu cikin zaman Abbati da Hanne mara dadi. Wauta take ganin ta yiwa Hannen yawa tunda duk kokarin Abbatin na son kyautata mata ta 'buge da yi masa sace sace a gida.

"Mutum ma yaki zama mana idan ya isa." Cewar Abbatin bayan ya zauna a kujerar kusa dashi.

Iya Kande sai ta ja hannun Qibdiyya da dabara suka bar falon. Bread da kwai Audu ya kawo musu domin bai kammala suyar doya da farfesun da yake ba. Ka'idarsu sai wuraren sha daya suke karyawa shi yasa bai fara da wuri ba.

"Ni wallahi jikina duk ya yi sanyi. Ka sanni idan an ce za ayi magana amma don mugunta ka tayar min da hankali kafin na ci abinci."

"Idan baka ci ba ma maganar sai jibi."

Munzali na jin haka ya shiga tuttura abinci yana kurbar tea. Yana gamawa ya ture harda na gaban Abbati dake cin nasa a nutse.

"Yauwa fadi don Allah."

"Ban koshi ba"

"Ba kyau abin da kake yi min." Sai kuma ya dan muskuta tare da rage murya "ko dai ya shafi maganarmu ta jiya? A shirye nake mu daina da gaske."

Wannan yanayin na zance mai mahimmanci Abbati ya yi da fuska sannan ya ce "Wannan maganar zamu yi ta sosai amma kafin nan Munzali gidanku kai ne namiji babba ko ba haka ba? Duk yawan yayyenka mata ka fisu iko saboda kasancewarka namiji. Saboda haka alhakin gyara zumuncinku yana wuyanka. Ka nemi 'yan uwanka ka san su sani na jini da jini. Kaga ni dasu Atine bamu da shamaki. Babu wadda ban san halin da take ciki ba duk da suna gidan miji."

"Ummakati ce babba kuma tayi aure mijinta yana da abin hannunsa."

"Ina ruwan zumunci da abin hannun mijinta? Kuma fa muna tare fa babbar yar ku ta rasu kuma ka ce min akwai wasu."

"Wadanda ba dakinmu daya ba su tara ne duka mata."

"Sai kuma aka ce sun sauya suna daga matsayin 'yan uwanka don baku fito daki daya ba? Nima muna da 'yan uba kuma duk na hadesu. Magana ta gaskiya Qibdiyya ba mu kadai take bukata a rayuwarta ba. Banda 'yan gidan su Zakiyya bata saba da kowa ba."

Kallo sosai na nutsuwa da fahimtar mutum Munzali ya yi masa. Kullum shi ne mai hango masa matsala kuma ya taya shi gyarata. Shi kam ko yau ya bar duniya ya yarda da soyayyar dake tsakaninsu ya san Qibdiyyansa ba za ta taba maraicin uba ba.

"Naji zan kokarta. Amma sai ka tayani don ka san Asabe ita kudi kawai take so. Su kuma wallahi idan na bi wata ta gayan bak'a sai na rama."

"Ka kwana biyu baka yi muryar 'yan tasha ba ai."

"Kut...ni ne dan tashar?"

Munzali ya tashi ya yo kansa a guje shi ma ya mike yana neman tsira. Idan ya zauna karshenta sai ya nemi panadol. Gajiya Munzalin zai tara masa don a jikinsa yake fanshe wasan kokawarsa da bai yi ba da kuruciya.

"Ka dawo kawai mu gwabza mutumina ko na goge nambar yarinyar nan ta Diamond plaza."

"Da gaske ka karbo?"

Farinciki mara misaltuwa ya bayyana a fuskar Abbati lokacin da Munzali ya gyada kai. Bai jira komai ba ya je ya riko shi suka fara gwada kwanji. Yau dai Munzali ne ya ji jiki don bai san me Abbati ya sha ba har yake jin karfi irin haka.

***

Sai da ta kusa isa dakinta wani tunani da ya karasa dagula mata lissafi ya darsu a ranta.

"Yumna. Yumna aminiyar Farhata?"

A guje ta shiga dakin 'yan matan har tana tuntube saboda sauri.

"Farha bani wayarki"

Ta umarceta fuskarta babu wasa. Bakinciki da taraddadin dake kai kawo a kirjinta kuwa baki ba zai iya kwatanta shi ba. Wani irin sauti kamar bugun kararrawa take ji a kunnuwanta. A tsaye take tana haki amma cike da dauriya ta kai hannunta dake rawa bangaren hotunan wayar. Bata ga komai ba saboda haka ta mika mata

"Baki isa ki ha'inceni ba wallahi. Ungo ki budo min wadanda ki ke tura masa."

"Shi wa?" Lilu ya tambaya suna shigowa dakin shi da Sauda da Suhaib.

Akwati ta kira shi ya zo ya sauko musu dashi daga kan wardrobe. Tun a hanya ya ce ta san ba tsayi gareshi ba kawai ta kira shi don suyi dariya. Da kansa ya kira Suhaib suka taho tare.

Mami Khadija ta kallesu ta ce "duk ku jirani zan zo gareku daya bayan daya." Ta mayar da hankalinta ga Farha "idan ba za ki bude ba bani nambarsa ko waye shi in kira."

Farha ta karasa rudewa sai kuka take yi tana juya wayarta a hannu. Ran Mami Khadija ya sake baci ta daka mata tsawa nata jikin yana 'bari da tsoro.

"Har kin isa ki yaudareni? Ina ta kaffa kaffa daku ashe ni aka mayar shashasha. Kuna can kuna turawa mutanen banza tsiraicinku."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

Su duka yaran abin da suka ambata kenan amma sautin muryar Farha tafi ta kowa. Kuka take yi iyakar karfinta Sauda tana tayata. Mamin tasu ta hargitse basu san musabbabin hakan ba. Kirjinta ta shiga nunawa wasu sababbin hawayen suna wanke mata fuska.

"Mami ni? Ni din? Wallahi, wallahi karya yake ko waye shi. Saboda gudun fadawa halaka da tsoron bata miki Mami watana biyu bana kula Yumna."

Da kyar Mami ta dan saita kanta ta nuna bata san komai ba "ina magana akanki me ya kawo zancen Yumna. Me tayi?"

" 'Yar kawunta ce tazo hutu gidansu ta koya mata bin sugar daddies. Nayi ta mata nasiha taki ji shine na rabu da ita bayan ta ce za ta hadani da wani."

"Ta hadaki da wani don mugunta? Me yasa ma baki sanar dani ba?"

Farha ta share kwalla "ce mata nayi zan fada miki ki gayawa Ummanta sai ta ce min wai in na fada miki sai me? Shi ne naji haushi na kyaleta."

A zuci Mami Khadija ta iya cewa 'Ba dole ta ce miki sai me ba tunda mahaifinki ya zubar mana da mutumci?'

"Naji kuma na yarda amma na rantse duk ranar da ki ka afkawa irin wannan sharin ki kuka da kanki."

Sauda ta nuno da hannu tana labe bayan Suhaib duk ta tsure.

"Wallahi Mami bana komai ni. Masu zuwan ma nace su rabu dani sun ki."

"Ki daina kokarsu tunda lokaci ne da Allah Ya kawo miki. Na baki kwana uku kiyi shawara da zuciyarki da 'yan uwanki ki fidda wanda ya kwanta miki. Kina gama secondary zan miki aure."

Da yake bata ga fuskar musu ba ko tari bata yi ba sai aukin gyada kai.

"Kai kuma Lilu idan na sake jin an ce kana bibiyar mata sai na saba maka. Yaro tun baka tafasa ba kana neman konewa. Kar kayi tunanin cututtukan zamani ne kadai sharrin dake cikin yawon banza. Lahirar mutum ce kacokan take gurbacewa. Duniyar ma kuma duk kudinka ba za ka taba samun nutsuwa da jindadin da kamilalle zai samu ba. Wadannan abokan banzan naka ku raba jaha kowa ya kama gabansa. Sai kun fi jindadin shiryuwa."

Duk maganganun nan tana yinsu ne cikin haki da kunar zuciya. Suhaib yaji duniyar tayi masa zafi. Kusa da ita ya karaso ya dora hannayensa akan kafadunta ya sallami kannensa.

"Ki kwantar ta hankalinki Mami in sha Allahu komai zai daidaita"

"Komai zai daidaita a ina? Shaye shayen da kake ka shirya dainawa? Idan kana tunanin kana sha domin batawa mahaifinka rai ne to ka sake tunani. Bai san kana yi ba. Ko ma ya sani babu mai dora masa zunubanka tunda ba shi ya kama hannunka ya kai gaban 'yan kwaya ba"

Idanunsa a kanta yana kara samun tabbacin Abban nasu ya yi wani abu mai girma ya ce "In Allah Ya yarda ba za ki kuma yi min maganar nan ba."

Farha, Lilu da Sauda sai suka ji kansu ya kulle. Kalaman Mami na karshe ga Suhaib sun hasko musu wata kofa da basu san akwai ba. Kofar sirri tsakanin mahaifiyarsu da babban wansu. Kofar da suka kwadaitu su bude don ganin me aka rufe a cikinta.

***

"Kayi hakuri don Allah. Zan yi mata magana da kaina."
Anti Hasiya ta furta da sauri domin ceton Ayaah daga fushin Honorable. Ba don tayi magana ba daf yake da kai hannunsa jikinta. Amma duk da haka wani kallon kasa-kasa na raini Ayaah ta bata tukwici.

"Hakuri kamar yaya? Kina ji fa jiya da na tambayeta a ina ta manta jakar cewa tayi a daidaita sahu. Daga baya kuma ta ce motar wanda ya rage mata hanya."

"Zan mata magana don Allah ka sassautawa zuciyarka." Ta rarrashe shi. Tafi kowa sanin yawan hidindimun gabansa da rashin kudi. Ga matsalar Abbas.

Takalmansa ya zura ya nufi kofar dakin zai fita "ki yi mata magana Hasiya. Zan dauki komai na halayyar da take mana a gidan nan, amma wallahi banda yawo. Idan ta ce yawo zata yi babu wanda ya isa ya kwaceta a hannuna."

Sai da ya fita Ayaah ta taso tana kumbura baki zata fita daga dakin.

"Dawo ki zauna."

Murguda baki tayi ta juya idanu sannan ta ce "a zaunar dani mana idan an isa."

Maganar ta daki Anti Hasiya sosai. Fuskarta ta hade da bacin rai ta daka mata tsawar da ta zaunar da ita ba shiri. Wani gululun abu ya tsayawa Ayaah a rai saboda tana son bijirewa amma a tsorace take sai kawai ta soma hawaye.

"Kar ki soma yi min wannan kukan gulmar taki."

Dan shiru tayi ta jira Ayaah ta share hawayenta da bayan hannu sannan ta cigaba da yi mata fada. Sam babu alamun lallabawa ko rarrashi a yadda kalamanta ke fita.

"Ni ba kishiyar babarki bace da zaki zauna kina kishi dani Hajara. Da Yaya A'i tana doron kasa ko sama da kasa za ta hade ba zan auri mahaifinki ba tunda jininmu daya. Saboda haka ki ajiye makaman da ake baki na kishi dani a gefe. Ko kina so ko ba kya so, da auren babanku a kaina ko babu ni Hasiya uwa ce a gareki. Sannan ko babu alaka tsakanina da Yaya A'i bani da dalilin cutar daku domin mahaifinku bai cuceni ba. Na san kina da hankali ko da ba kya tunani sai abin da aka ce kiyi. To a cikin hankalinki ki zauna ki fada min me na taba yi muku a gidan nan na rashin kyautawa. Idan kuma jira kike bayan duk fadi tashin da nake a gidan nan in dawo na kwanta ki takani ba za ki ganin wannan ranar ba in sha Allahu. Idan ban ci darajar komai ba a wurinki in ci ta uba da na hada da wadda ki ke ganin zuwana gidan nan cin amana ne a gareta. Karshe ina so ki san cewa ba soyayya bace kike yiwa Yaya A'i da wannan halayyar. Kina tozarta tarbiyarta ne wadda Allah zai muku shari'a ranar lahira, ai kin sani idan abin da ki ke yi daidai ne ko akasinsa. Tashi ki bani wuri."

(Iyaye mata mu sani cewa 'ya'yanmu komai kankantarsu suna lura da abubuwan da muke yi. Mu daure muyi namu kokarin wurin koyawa musu kyawawan dabi'un da zamu wanke kanmu a kai ko a gaban Allah. Abin da wuya kyma ba iyawarmu bace amma mu yi iya yinmu. Ayaah bata da wani wayo ta rasa mahaifiyarta. Amma bata manta cewa babu alaka mai kyau tsakaninta da Innayo da 'ya'yanta ba. Yau babu A'i amma tarbiyarta bata bar autarta ba. Sannan a gefe ga Laraba da sauran kannen A'i suna ingizata. Su Ummi da suka fara wayo sun rigata fahimtar wace Hasiya a tare dasu. Ita kuwa da akidar kiyayya suka raineta a gefe. Allah Yasa 'ya'yanmu su zama silar samun rahamarmu ba kishiyarta ba. Amin)

Jiki a sanyaye Ayaah ta tashi ta bar dakin. Tana shiga dakinsu Murja da Ummi suka fice suka barta bayan tsakin da kowaccensu ta buga. Ai sai taji kuncin zuciyarta ya karu. Kukan gaske ta kama yi ba ji ba gani. Tabbas bata kyautawa ta sani. Tun jiya ake zancen jakar Anti Hasiya da ta manta a adaidaita sahu amma ita mai jakar bata ce komai ba. Sannan ga tunanin mai motar da ya kaita asibitin Nasarawa ya isheta. Komai nasa ya burgeta amma ko sunanta bai tambaya ba har suka rabu.

Ko babu komai zuciyarta ta cika da shakkar Anti Hasiya. Bata taba yi mata fada kamar na yau ba. Lallabawa za ta yi ta nuna musu ta shiryu zuwa ta samu tayi aurenta ta bar gidan ta huta. Yadda kowa ya tsaneta (a tunaninta) barin gidan shi ne mafi a'ala.

A bangaren Anti Hasiya kuwa duk yadda take son zuwa duba Innayo yau hakan ba zai samu ba sai can yamma ko dare idan ta gama lalle. Musamman saboda tun safe Uwani ta rangado mata kira.

"Idan na taso daga aiki zan biya duba Innayo. Dama kira nayi in tuna miki kada ki manta da sakona."

Da azahar ta sake kira shi ne musabbabin fadan da Honorable ya sake yiwa Ayaah.

"Karfe uku zan fito Hasiya. Idan ba da wuri zaki je wurin Innayo ba sai na biyo gidanki na karba."

Taji zafin kalaman amma ta daure bata mayar mata ba saboda nata kudin sun bata. Duk 'yar ajiyarta ce a ciki Ayaah ta salwantar. Wai akan kudin da ba a cikinta ta ci ba Uwanin ke kiranta bayan rabon da su gaisa a waya ta manta. Wani irin nauyi zuciyarta tayi saboda damuwa da hanyar da Uwani ta dage sai ta bi ta sabawa iyaye. Inda suke lallen ta koma ta cigaba da sakawa matan. Ana kiraye kirayen Isha ta sami shiga gidansu da abincin da ta dafowa Innayo.

"Ki yi hakuri. Wallahi jakata ce ta bata babu ko sisi a jikina."

Innayo ta murmusa da kyar. Idanunta duk sun zurma ciki saboda tsabar wahalar da tasha kwana biyu
"A waya ma fa na ce miki kar ki damu. Uwani ta zo kuma sai da aka yi magariba kamar Salima ta bar gidan nan. Fuskarta dai duk a kumbure ko kadan ban ji dadin ganinta ba."

"In Allah Ya yarda cikin satin nan zan ziyarceta. Mutumin nan baya tsoron Allah. Ko albarkacin 'ya'ya yaci ace yana raga mata wannan rashin mutumci."

"Hmmm" Innayo ta iya cewa kawai.

Anti Hasiya sai tayi shiru saboda ta san cewa cigaba da maganar zai kara bata ran Innayo ne. Salima bata taba sanar dasu mijinta yana dukanta ba amma sun dade da sani. Wahala kawai take sha amma Alh. Rabi'u ya ce ba zai iya riketa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login