Showing 33001 words to 36000 words out of 242549 words

Chapter 12 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3351

da a gaba saboda hassada da bakinciki. 'Yar fitar nan da yake yana roro min abin arziki a wurin mutanensa kina neman saka masa hannu."

Dariyar da Innayo tayi kafin ta bata amsa sai da ta bata haushi.
"Asabe kenan. Yau kuma rigimar dani kike ji? Da nice ke gyale zan dauka na bazama nemansa ba zaman karyar son 'ya'ya amma ban san halin da suke ciki ba."

Gyalen kuwa ta janyo akan kyauren dakinta tana mai cigaba da kumfar baka da borin kunya ta kare da cewa,
"Dama fitar zanyi." Kugu ta kama tana karkada hannu daya kamar 'yan mata a wurin gaďa "Kuma ki gaggauta fadawa bokanki ya yi karya don bashi da rabo akan ahalina ehe."

Har ta kusa rijiyar dake daf da kofar gidan taja tunga ta tsaya. Tuno wani abin karin haushin tayi ta kuwa kalli Innayo ta kwashe da dariya.
"Su 'ya'yan so din wai uwar me suka tsinanawa wahalalliya? Ai in fada miki dadin haihuwa bai wuce ki haifa ki mora ba. Amma ka haifa kuma a more kuruciya da lafiyarka a gujeka wai....uhumm bari nayi gaba."

Daskarewa Innayo tayi tana jiyo sautin Asabe tana rangada ahayye nanaye da salon wulakanci. Zafafan hawaye ta goge ta duka ta cigaba da tatar gero.

"Wata rana zan huta. Balle ma indai sun huta basu yi irin rayuwata ba ni bani da sauran damuwa." Ta fadi da dan karfi tana baiwa kanta kwarin gwiwar cigaba da aikin gabanta.

Munzali yana dakinsu ya gama jin zantukansu. Bai jidadin kalaman Asabe ga Innayo ba. A ransa yake jin inama ita ta haife shi. Ya tabbata da zai ga gata mara misaltuwa kamar su Hasiya.

Sai da yaji tsakar gidan shiru ya lallaba ya fita. Murmushi ya karade ramammiyar fuskarsa ta kwana biyu da ya yi tozali da Abbati ya rakube a dakalin gidan. Shi ma yana ganinsa ya taso da saurinsa.

"Ya jikin? Ga abinci na samo maka. Akwai sauran kudi in siyo maka lemon kwalba? Ko kunun zaki? Kafi son lamurje ko?"

Dariya ce ta subucewa Munzali ganin Abbati duk ya rude. Kwana biyu da yake ciwon sai Asabe ta fita yake fitowa. A wurinsa yake wuni yana jinyarsa. Don kokari har kemis yaje ya siyo magungunan mura don a zatonsa mura ce da zazzabi ke damun Munzalin.

Wannan kadan daga irin abubuwan da suka kara masa kaunar Abbati kenan. Kulawa yake so kuma babu ta inda Abbatin ya gaza nuna masa ita. Abbati has always been there. Babu mai yi masa fada ko gyara masa wani abu sai shi. Tasgaron da ya mamayi wannan kyakkyawar alaka ba komai bane illa alfashar luwadi. Saboda sakar masa ragamar rayuwar da iyayensa suka yi da kananun shekara daga Asabe har baban nasa babu wanda yake gani da mutumci har ya girma. Sai dai ya kawo kudi su karba babu bincike ko damuwa. Tunda ya ce kasuwanci yake magana ta kare.

Yunwa, bala'i ce wadda mutum zai iya komai domin kawar da ita idan ba ya kai zuciya nesa ba. Munzali ne ya mikowa Abbati hannun taimako a lokacin da take neman kassara shi. Halinsa na tsoro da rashin son rigima sauran daliban suke dogara dashi suna cutar dashi. Shi ma Munzali da baya makarantar ya tsaya masa. Sai da ta kai hatta manyansu suna shakkar taba shi saboda fadan Munzali. Duk kulawa da soyayyar Mari gare shi bai hana shi jin zafin barinsa da suka yi zuwa bara ba ita da mahaifin shi. A lokacin da ta so ya zauna a gida bayan rasuwar Sani ya riga ya saba da abin da suke yi. Amma ba shi ne makasudin kin zamansa ba. Bai ga yadda zai iya rayuwa babu Munzali a cikinta ba.

Shekaru suna gaba yana dan yin karatun addini sama-sama. Bai jima ba ya gane muni da girman abin da suke yi. Lokacin da ya kai shekara ashirin abin ya dame shi matuka. Shazali yana kaisu wurin manyan mutane ana amfani dasu a basu kudi sosai. Tuni Shazalin ya bar makarantar ya zama kawalin almajirai mai gidan kansa.

Wannan sana'a tasu ta dami zuciyar Abbati. Ya yi nufin ya fadawa Munzali su daina su nemi sana'a ko ta wankin mota ce. Kullum abin yana ransa amma ya rasa yadda zai fito masa da maganar. Tsoronsa kada yaji haushi ya nemi rabuwa dashi.

Wata rana yana zaune jiran isowar Munzali su je su sami Shazali tunani ya dame shi. Bai ji zuwan Munzalin ba sai da ya taba masa kafada.

"Allah Yasa ban barka jira ba. Matar nan (Asabe) ce wai na ranta mata dubu biyu."

"Ka bata ko?" Abbati ya tambaye shi yana tashi tsaye.

"Kudin da muka samo a gidan nan ne fa na shekaranjiya ta gani ta saka min ido. Ni kuma na riga nayi amfani dasu."

Idanu Abbati ya zaro. Dubu biyar biyar aka basu shi ko dari biyar bai cinye ba. Zai tambaye shi me ya yi da kudin ya miko masa leda. Atamfa ce guda daya da lesuka biyu.

Kallon tuhuma Abbati ya yi masa
"Na meye wannan?"

"Kayan sallar da ka ce zaka sayawa Baaba dasu Atine (kannen Abbatin)"

Zuciyarsa yaji tayi nauyi ya kasa magana. Abu daya ya sani. Munzali yana matukar kaunarsa. Ko kyamar almajirai bai taba yi masa ba.

"Kai da ka ce baka da kudi duk ka kashe naka?"

Murmushi Munzali ya yi. Shi ba maraya ba amma yana da wanda yafi uwa da uba a zuciyarsa saboda sakacinsu.
"Ka fini bukata kai da zaka je gida gobe. Na hannunka sai kayi kudin mota da wanda zaka bawa Baaba ta rike. Kafin ka dawo kullum zan dinga fita in tara mana."

Abbati yaje gida da tsaraba. Baaba Mari tana gidan kawunta a Maigatari. Ta kasa gaba ta kasa baya sai tunani. Duk sanda yazo hutu yaje ganinta sai ta tuna masa kada ya kusanci zina. Kar ya manta abin da ya faru shekarun baya. Idan 'yan matan sun zo su ma maganar kenan. A wahale suke rayuwa ana gasa su a gaban mahaifinsu. Da Abbati ya fara girma ne idan yazo ake daga musu kafa tunda da 'yan canjinsa a hannu.

Ya je gaishe ta wannan karon ma ya bata kayan ta tsatstsare shi da ido.

"Sana'ar me kake yi ne?"

"Jiran shago nake hadawa da karatun" Ya amsa mata kai tsaye "Wannan ma ubangidana ne ya baki." Ya mayar da hannunsa da ya riko kudin da yake niyar bata ya dunkule.

"A kula dai. Banda daukar kayan mutane. Banda ha'inci ko cuta."

"To Baaba."

Kwanansa biyar a garin ya koma Kirikasamma. Da isarsa gida da Gwaggonsu Deluwa ya fara cin karo a zaure. Guda ta saki tana ganinsa ta fara habaicin da ta saba wanda ya saka shi dakata karfi da yaji.

"Ango manya, na Hanne ka sha kamhi. Da Malan har iya cewa a bika Maigatarin ai...hummm, su Mari idan aka ga d'a sai ayi bulunbukwi a manta da an tsani almajiranci. Ledar da ka tafi da ita can ka barota kenan?"

Sauran surutan nata ba shigarsa suke ba. Kalmar 'na Hanne ka sha kamhi' ke kai wa da komowa a kwanyarsa. Me hakan yake nufi? Bai furta tambayar ba ya shige ciki da sauri. Kafin ya kai bangarensu tuni gudar Deluwa ta sanar da Mal. Sa'adu dawowarsa. Yana ajiye jaka dan aike na fada masa sakon kira. Gabansa ne ya fadi. Bai manta ba! Ta ina zai taba manta dalilin mutuwar auren Baaba Mari?

"Wa ka fadawa za ka je Maigatari?" Cewar Mal. Sa'adu fuska a daure bayan Abbati ya amsa kiran nasa.

A dakile ya bashi amsa da cewa "Babu kowa." A ganinsa baya neman izinin kowa musamman na wan mahaifinsa kafin yaje wurin mahaifiyarsa.

"To ba zan dauki raini ba. Sai kazo ko kwana biyu baka iyawa a gidan ubanka amma ka iya tafiya dangin dangiro ka kai musu dan abin da ka tara. Ita kuma ko kunya babu ta karbe bayan ta gama aibatamu da karatun da aka tura ka."

"Baaba ce Dangin dangiro din? Baaba Marin da ta haifeni?"

Yadda ya fadi maganar da bacin rai muraran a idanunsa sai yasa Mal. Sa'adu yin lakwas. Tabarmar kunya ya nade da hauka ya sako bakunan kannensa cikin maganar yana cewa su taya shi gani Mari ta zugo danta ya raina shi. Da kyar aka bashi hakuri sai da Baba Inuwa ya zazzagi Abbati a gabansa.

Baki Mal. Sa'adu ya turo gaba shi a dole ransa ya baci ya ce "sai ka shirya gobe ka je kaga amaryarka. Da baka dawo ba munje an daura aurenka da Hanne jiya. Ai baka manta alkawarin da muka yiwa shi uban nata ba hekarun baya."

Dif Abbati yaji kamar an sara masa guduma a ka. Aure?! Shi kuwa me zai yi da mace yanzu? Macen ma wadda rabon da ya sanyata a ido tun tana shekara hudu. Tunaninsa ya tsaya a inda ya auno shekarunta na yanzu. Shadaya shi ne har an aurar da ita kamar zai gudu.

Lokacin da mallam Saidu yace masa sai bayan shekara biyu zata tare bai damu ba. Sai kuma wani tunani ya darsu a zuciyarsa wanda yasa shi sakin guntun murmushi. Ko ba komai ya sami hanyar da zai fadawa Munzali aibun abin da suke aikatawa tunda dalilin bari ya samu. Abu ne da babu ko sabanin fahimtar malamai game da haramcinsa saboda haka bari ya zama wajibi.

Washe gari suka shirya tare da dan Mal. Sa'adu don zuwa ganin Hanne. Haka ta fito tana ta sussune kai wai ita nan amarya a gaban angonta, bakin nan ya sha jan baki ga fuska da dige digen jagira. Yarinya karama amma wai ta san shi mijinta ne, abin ma dariya ya bashi.

Bayan ya koma da yan kwanaki kadan ya shirya dawo Kano da farinciki zai ga Munzali dan yi masa fada da fatan kubutar dashi shi ma amma nan ya tarar da mummunan labari. An kama Munzali yana police station.

Sanadin rufe shin ba komai bane kamar yadda ya ji daga bakin wani dan makarantarsu da ya san abotarsu illa sumamen 'yan kwaya da aka kawo unguwar. Hankalin Abbati in ya yi dubu ya tashi. Munzali ko taba baya sha. Shan kayan maye bai kasance cikin dabi'unsu ba.

Jin kwanansa hudu a can ya daďa jefa shi cikin tararrabin halin da yake ciki yanzu. Bai yi kasa a gwiwa ba ya nufi gidansu. Ya dai san ba a maraba dashi domin Asabe ta gargade shi da rabar danta tunda ta gane almajiri ne. So yake yaje ya tabbatar ba a sake shi ba sai ya nemi station din da yake.

Ya dade yana sallama kafin yaji wata murya ta amsa a fusace. Da azamarsa ya shiga soron gidan ya tsaya turus sakamakon maganganun dake tashi a tsakar gidan.

Muryar da ta amsa sallamar shi ya gane ta Alh. Rabi'u ce saboda hango shi da yake yi a tsaye yana sababi.

" Dan iskan yaro kai, ni zai zubarwa da mutunci a unguwar nan? Ashe wai a wani kango aka same shi da talatainin dare. Kuma jama'a sun yi ittifaki akan yawan ganinsa a wurin kamar kangon ubansa."

'Shazali yake jira' Abbati ya ce a zuci. Babu abin da ke kaisu kangon nan yanzu sai jiran zuwan Shazali ya kaisu wurin mutanensa.

"To ni dai ka kawo kudin sai naje nayi belinsa" Asabe ta ce a sakalce. Ta riga ta gama bincike dakin Munzali tas babu kudi. Da ace ta samu dama rabonta za ta dauka sai ta fito dashi. Ta rasa uwar me yake boyo a dakin da ya kori kaninsa ma daga ciki.

"Nawa ne kudin?" Cewar Alh. Rabi'u a fusace kamar an ce ya bada ransa.

"Dubu ishirin da biyar ne. Ka bada ishirin sai na cike sauran."

Sake bata rai ya yi cike da fushi sai kuma ya fashe da wata irin dariya. Kudi irin wannan indai ba kodarsa take so ya sayar ba a ina zai samu.
"Kisan kai ya yi da zan biya talatin da biyar? To babu! Ya zauna su koya masa tarbiyar da ki ka kasa koya masa. Aikin banza. Baki da aiki sai yawon makota kina kwadayi. Ke dai kin shiga uku. Ko kishin yadda Innayo take tsaye kan nata 'ya'yan ba kya yi."

Habawa! Ran Asabe ya fi nasa baci saboda hadata da Innayo da ya yi akan kudi. Hannuwa ta tafa ta rike kugu tana sauke nata ruwan bala'in.

"Aikin 'bur in ji tusa. Kai dai anyi lusarin namiji. Ka haifi 'ya'yan ka bar mata da wahalar rayuwarsu. Kuma 'ya'yan Innayo din akwai wata ta dukan kirji a kai ne? Ba gara nawa ba akalla ko banza yana bani kudi."

Kanta ya yi kamar zai kai mata duka "ni kike fadawa wannan maganar?"

"An fada din lusari ko karya nayi?"

"To Yasin ba zan bada ko kwabo ba."

Hannu daya ta saka ta rufe bakinta tana masa ihu
"Wohhhhh, anji kunya. Lusari. Dama me zaka iya fitarwa bayan kayi gadon bakin hali."

Shi dai bai tanka ba tunda ya sabule ba zai bayar da kudin ba. Dakinsa ya shige ita kuma ta yi rantsuwar sai dai a barshi a kulle don bata da kadarar sayarwa akan dan da dama ba wani tausayinta yake ba. Mayafi ta dauko ta sanar da sauran yaranta wadanda a kunnuwansu aka gama bala'in zata je gidan Ummakati. A lokacin auren duka duka bai yi shekara ba. Hasiya ce ma take neman shekara ta biyu a nata gidan.

Innayo kuwa tun safe da take ganin take taken rigimar kudin belin ta fita. Uwani da Zara ko ba a hada da sauran kannen A'i ba zasu iya hada kudin belin dan uwansu. To amma ta san fakewa zasu yi da rashin halin Asabe su ki taimakawa. Wannan kenan.

Yau idanun Abbati sun gane masa abin da yasa Munzali baya kaunar iyayensa. Gabadaya son kai ya musu katutu babu mai cikakkiyar damuwa dashi. Kudin belin ne ma ya dame shi. Dubu ashirin da biyar da yawa. Bai je station din ba ya tafi gidan Shazali. Cikin sa'a ya same shi. Ko gaisawa basu yi ba ya ce,

"Rance nake nema don Allah na dubu ashirin da biyar."

Shazali ya kanne ido "babu sai dai akwai manya da suka shigo gari. Kayi sa a domin kuwa harda mataimakin wani gwamna cikinsu. Idan zaka iya aikin na tabbata nan da gobe ka tara dari ma ko sama da haka."

Bashi da zabin da ya wuce karbar wannan tayin. Munzali ne fa. A wuni da daren ranar sai da ya ziyarci mutum biyar. Kudi kuwa don ma sun san ba wayayye bane amma duk da haka dubu dari biyar ya saka a gabansa yana kallo. Jikinsa har bari ya dinga yi saboda kudaden sun bashi tsoro. Haka ya hau titi zuciyarsa na fat-fat da fargaba. Gani yake kowa ya kalle shi zai gano adadin kudaden.

Shazali ne ya fada masa wane station ne yaje da kudin belinsa a hannu. Sergent din da yake wurin ya fadawa sunan wanda yazo fitarwa.

"Kawo dubu goma saboda da daddare aka gan shi. Da da rana ne sai mu karbi biyar."

A haka shi Sergent din mugunta ya yi masa. Shi kuma muryar Asabe ce ta dawo masa. Kenan karya tayi da masifar da ta hau danta. Da gaske Munzali bashi da kowa sai shi. Wani irin tausayinsa ya sake mamayarsa.

Kwalla ya dinga zubarwa da aka turo keyar Munzalin. Ya yi dukun dukun ga dingishi yana yi.

"Dama na san zaka zo Abbati. Na san wallahi ba za ka barni a nan ba. Nagode..."

Rungume shi Abbati ya yi suka fashe da kuka. Sergent ya tabe baki yana tunanin shakuwa ce ta 'yan uwa.

Abbati~Munzali ya yi masa gata tun bai san me ake kira gatan ba. Ba zai taba iya barinsa ba bayan ya san shi kadai ne tsaye a rayuwarsa.

Munzali~Abbati ne kadai ya taba bashi daraja ta dan Adam. Shi kadai yake kaunarsa da zuciya daya ba don wani abu ba. Iyayensa basu damu da kowa ba sai kansu.

Fita suka yi Abbati ya tallafi nauyinsa. Asibiti suka fara zuwa ya biya kudin gado don ya ce a kwantar dashi ya huta. Wani karamin private ne da suka gani a hanya. A nan aka gyara targaden aka saka masa ruwa. Abinci mai rai da lafiya suka ci sannan bacci ya dauke Munzalin. Sai da safe Abbati ya nuna masa kudin da ya samo.

"Me ya kamata muyi dasu?" Abbati ya tambayi Munzali.

Munzali ba amsa. Bakincikin iyayensa ke damunsa. A gefe guda yana taya amininsa farincikin samun abin da zai iya raba shi da talauci. Ya jima yana tunani sai jin muryar Abbati ya yi.

"To ga naka nan. Kowa ya dauki dari biyu. Wannan kuma.." ya nuna chanjin darin da ya taba yana musu hidima ciki "sai mu dinga cin abinci da sauran bukatu."

"Kudinka ne Abbati. Ka dai bani na abincin ka san cikina babu juriya" ya kare da dariya.

Sun yi ta kai ruwa rana akan Munzali da yaki daukar kudin. Shi yana ganin Abbati ya fishi bukata tunda yana da iyaye a kauye.

Da dai ya tabbatar Munzali bazai dauki kudin ba duk abun da ya ce, kawai sai ya dauki jakar ya fice. Kai tsaye gidan Shazali ya nufa, ya ci sa a kuwa ya same shi. Nan ya shaida masa yazo neman alfarma gunsa dan Allah ya sama masa gidan haya wadda yake mara tsada sosai. Daki biyu da bandaki ko da daya ne. Shi bai ma yi tunanin kitchen ba ko wani yadda za a ci abinci shi dai gidan yake so a sama musu ko da ma daki daya ne kuma yana so ya zama nea da gidan unguwar da aka sansu.

Wani murmushin gefen baki Shazali ya saki
" dan gari, ashe ka gane abun da nake ta so ku fahimta tuntuni" nan ya amshe kudin ya kuma shaida masa in Allah ya yarda nan da sati daya gida ya samu.

Bai ma yi tunanin zai cutar shi ba ko raba daya biyu haka ya dunkule duka kudin Naira dubu dari hudu cus ya mika masa yayi gaba bayan yayi masa godia sosai.

Da ya koma asibiti Munzali yayi ta tambayarsa ina kudin, me yayi dasu? Ya ce masa ba komai.

Fita ya yi ya koma wurin likitan ya nemi alfarmar lallai a bar Munzali ya kara ko sati daya ne a asibitin dan yana so ya samu hutu sosai.

Shima likita dai yaga kudi, abinka da private hospital iya kudinka iya shagalinka. Muddin zasu biya to fa shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login