Showing 12001 words to 15000 words out of 242549 words
sun ce idan na fada zasu kaini gidan 'yan yankan kai."
Jiki a sabule Abbati ya koma ya zauna murnarsa ta koma ciki. Wani tunani Munzali ya yi ya ce masa "kasan me? Ni suna bani kudi ko abinci. Idan naje aka yi dani kai ma sai nazo nayi maka sai na sammaka kudin ko abinci. Ka yarda?"
Wata dariya Abbati ya saka ya washe bakin da ya bayyana gibin turamensa biyu.
"Na yarda."
Munzali ya mike tsaye yana cewa "amma fa idan ka fada zasu yankamu har babarka da babanka."
"Ba zan fada ba." Abbati ya nanata yadda zai amince masa.
"To tashi ka cire wandonka."
A cikin soron da babu wadatar haske Abbati ya zaro idanu "cire kuma? Iskanci ne fa. Wai ma ya sunanka?"
"Munzali."
"Ni kuma Abbati. In fada maka Baaba ta ce duk wanda yake cewa a cire wando wuta zai je ba zai ga Annabi Muhammadu (SAW) ba."
Dariya ce ta kama Munzali ya ce "kai nima haka na zata. Ashe wai idan aka yi da mace da namiji ne mutum zai shiga wuta. Irin wannan kuwa dadi ake ji kuma a baka abinci."
"Baaba bata fada min namiji yana cewa namiji ya cire wandi ba. Kila da gaskiyarka shi ba na 'yan wuta bane."
A wannan daren Abbati mai shekaru goma sha biyu amma babu wayo da idon uwa ya fara koyon wannan mummunar dabi'a saboda yunwa da rashin gata a wurin Munzali.
Munzali da ya koya masa bai san muni da zunubin dake cikin wannan alfasha ba saboda rashin saka ido na uwa da uba.
Daga wannan ranar abotarsu tayi karfi. Munzali zai jure ko mutum nawa Shazali yazo dasu ayi a bashi abin da za'a bashi saboda Abbati ya ci abinci. Ana fitowa barar dare Abbati zai zo suyi shima ya biya shi. Abincin tare suke ci sannan ya raba musu kudin daidai. Zuciyarsa bata taba raya masa ya cuci Abbati kada ya bashi kudin da ya samo ba.
Abin taysayi. Abin kuka. An kulla abotar kuruciya da aka so ginawa bisa alkhairi amma mummunar alfasha ta zamo jigonsa.
Kaico! Allah kadai Ya san Abbati da Munzali nawa ne a tare damu cikin wannan masifa bamu sani ba. Wasu suna mu'amala da 'ya'yanmu wasu da kannenmu.
*****
"Ke kuwa Khadija kamar me haihuwar fari me ya fito dake yawon arba'in? Ko har kin gama warkewa?"
Yakumbo ke wannan fadan tana karbar jaririya Sauda daga hannun Khadijan. Su Lilu kowa da murnarsa ya je jikinta suna tambayar ta ire iren cimar da take ajiyewa a dakin domin jikoki.
Sai da ta sallamesu suka fita daga dakin sannan ta zauna suka sake gaisawa da Khadija.
"Jiki ya yi kyau. Allah Ya kara miki lafiya. Naji dadi sosai da yadda ki ka karbi kaddararki. In sha Allahu wadannan yara zasu zame miki sanyin idaniya. Allah Ya muku albarka."
"Amin"
Khadija ta amsa tana kokawa da hawayen dake son zubowa. Ita kadai ta san irin bacin rai da bakincikin da take kunsa a wurin Tahir a kwanakin nan. Nasima bata kara zuwa gidan ba tunda ta koma. Sai dai ya fito mata da salon wulakanci irin na namijin da ya fahimci karin aure a matsayin lokacin cin zarafin ta gida. Bata yi sati da komawa ba ta canja shawara ta ce ya saketa.
"Kin san abin da zai faru idan muka rabu. Kowa zai san me nake yi kuma kan 'ya'yanki zai koma."
"Na sani Tahir amma duk da haka ina so ka sakeni kafin zuciyata ta buga. Kayi min adalci albarkacin zaman da muka yi a baya da yaran nan."
"Zan miki. Ke ki je ma na sake ki saki daya. Amma ki sani nayi miki rantsuwa ko Yakumbo bata isa ta sakani baki yaran nan ba. Zan daukesu mu koma Lagos tare da Nasima."
Cak ta tsaya tana kallonsa idanunta cike da hawaye.
"Yaya dama haka kake ko duka son Nasiman ne ya mayar da kai haka?"
"Ki dauki duk wanda yayi miki bani da damuwa. Na ce ki zauna mu rufawa juna asiri sai dawo da hannun agogo baya ki ke yi. To ga sakin nan kin samu ki tafi da Sauda idan kin yayeta zan zo na karbi abata."
Da kyar ta lallaba ta zauna a bakin gado bayan ya fita. Ta kasa gaskata abubuwan da suke faruwa yanzu musamman sakin da ya furta mata. Halayensa ba bakinta bane a da amma ko a wancan lokacin da yake tashen akuyancinsa yana shakkar ta sani. Yanzu kuwa akan kankanuwar yarinya ya yanke igiyar auren shekara tara.
Abin da basu sani ba daga shi har ita shi ne Nasima da Ladidi mahaifiyarta suna kauye ana yi musu aiki akan Tahir. Duk yadda za'ayi ya aureta ko babu izinin iyayensa suke so. Sannan ya fifita ta akan kowa. Shi ya bayar da wannan kofa daga ranar da ya fara nemanta. Ladidi ta san komai game da halayyar 'yarta amma tunda ta zame mata jari shi kenan.
Fuskarta ta wanke ta fito falo ta sami kanwarta ta gama girki ta zubawa yaran. Dakinta inda Gwaggo kanwar mahaifiyarta mai kulawa da ita tayi masauki ta shiga. Kuka ta saka mata ta sanar da ita sakin da ya yi mata. Hankali a tashe ta zari mayafi ta tafi gidansu ta sanar da Mama. Tare suka dawo ta kora musu jawabin abin da ya faru.
"Khadija na san Tahir bai kyauta ba amma shi ne rufin asirinki. Idan kin fito waye zai auri mace mara mahaifa?"
Kai ta girgiza tana karyata cewa mahaifiyarta ce take fadin wannan magana bayan ta fada mata matsalarta.
"Dena yi min wannan kallon na fiki sanin halin maza. Kwansu da kwarkwata ban dauke miki uban da ya kawoki duniya ba duk jirginsu daya."
Kiris ya rage ta saki Sauda saboda firgici "Baba ma yana neman mata?"
Mama tayi murmushin takaici "ban fada miki don ki daina ganin girmansa ba amma babu irin cin kashin da ban gani ba lokacin da yake manajan banki. Ni da yake kawosu har cikin gida ya ce abokan aikinsa ne in yi musu girki."
"Me?"
Zantukan sun kadata sun yi matukar bata mamaki.
"Rayuwarku da tsoron kada ku tagayyara yasa na zauna. Kema kuma ina shawartarki da ki rungumi kaddararki kiyi zaman 'ya'ya."
"Yanzu Mama saboda 'ya'ya sai mata su dinga zama da fasikai?"
"Idan kin fita kin san gidan wa zaki fada? In kuma baki yi aure ba ina zaki kai wadannan yaran ke ba sana'a ba kuma babu aiki. Babanku ya yi ritaya kannenki ma da kyar ake biya musu kudin makaranta. Ga zumunci da zai lalace kuma karshenta a bar miki 'ya'ya a hannun kishiya ta gallaza musu. Shawara daya zan baki. Idan ya dawo ki roke shi ya mayar dake kafin kowa ma yaji. Dama can an san halinsa ai aka aura miki. Lokacin ba yadda banyi ba aka ce zan raba zumunci."
Khadija na kuka Mama ta cigaba da tausarta akan tayi hakuri. Al'adarmu ta fifita farincikin namiji akan mace. Ko mun sani ko bamu sani ba mun nunawa maza zamu nemo dalilin zama dasu duk lalacewarsu saboda gudun zawarci. Babu uwar dake son 'yarta ta fito daga gidan aure amma addini ma ya halarta fitar domin a zauna lafiya.
Tahir bai yi mamakin ganinta ba da ya dawo da yamma. Dauke kai ya yi ya shige dakinsa. Zuciyarta na kuna ta tashi ta bishi dakin.
"Na amince zan zauna."
"Ya dai fiye miki. Ki turo min kofar idan kin fita." Ya ce daga kwance.
Bata san daga gidan Yakumbo yake ba ya kai mata zancen auren Nasima ta fattako shi.
"Tunanin me kike yi ne Khadija? Inata magana kin yi shiru."
Dago kai tayi ta kalli Yakumbo tayi murmushin dole.
"Babu komai."
Ba yarda tayi ba tunda ta san Tahir yana neman aure. A wannan yanayin ba Khadija ba duk wanda yaji zai kira shi butulu ne. Ace daga cirewa matarsa mahaifa yana kiran sake aure. Nasiha ta dinga yi mata akan karbar kaddararta ta cire mahaifar amma bata sako zancen auren nasa ba. A gidan suka yi azahar sannan suka tafi gidansu Khadija a bayan layin da kafa.
Da yamma Tahir ya zo daukarsu ya fara biyawa ya gaishe da Yakumbo. Bai samu sakin fuska ba tunda ya ce mata zai yi aure.
" 'Yar waye yarinyar da kake nema ne wai?"
Sosa keya ya yi "ba fa bakuwa bace Yakumbo. Mai aikinmu ce Nasima..."
Kaf...Yakumbo ta kwade masa baki cikin fushi "mai aikinku fa kace. Kenan ma Khadija ta sani. Wannan wane irin cin fuska ne haka?" Alamun zai mata tijara ta gani sai ta zabi lallaba shi akan dai ta yarda da wannan danyen aiki "Idan auren kake so ka bari Saudatu ta shekara sai ka nemi wata"
"Nasima kadai nake so!"
"To ba za ka aureta ba duk abinka."
Tahir dagewa ya yi babu jin nauyi ya nunawa mahaifiyarsa fa bata isa ba.
"Akan mace nake fada kana fada Tahir?"
"Meye aibunta? Ba gara na auri wadda Khadijan ta sani ba."
Tsananin bacin rai yasa ta samun wuri ta zauna tana rike kai. Wani tunani ne ya darsu a zuciyarta ta kalle shi a razane.
"Wannan bakin naci da kake kafa min akan yarinyar nan anya wani abu bai shiga tsakaninku ba?"
Kai ya sunkuyar yana wasa da mukulli bai musanta zarginta ba. Hawaye tuni ya balle mata ta nuna shi hannu na rawa "Khadija ta san ita kake neman aure ko?"
Da ka ya amsa mata.
"Ko dai ta kamaku ne?"
Nan ma da ka ya amsa. Yakumbo taji kamar ya soka mata kaya a kahon zuciya. Tashi tayi tana kaiwa duk inda ta samu a jikinsa duka.
"Bana so in yi maka baki Tahir, tun kuruciyarka kake gasa min zuciya. Allah Ya sani ban zubar da mutuncina a waje ba amma akanka meye banyi ba. Saboda ka shiryu na tursasa kanina ya baka 'ya. Mahaifiyarta har yaji tayi amma na dage ko ayi ko in saka shi ya saketa. Tahir duk kai na yiwa wannan" kuka ne yaci karfin Yakumbo ta kifa kai a cinyarta.
Jikin Tahir ya dan yi sanyi amma a ganinsa akan me zata hana shi auren da addini bai shata masa layi a kai ba.
"Idan nayi auren nan ba zan sake bin wasu ba."
"Iya abin da za ka iya cewa kenan? Akwai hakkina, da na matarka da na zuri'arka mai zuwa a gaba ma da na gabanka ba a wuyanka. Tahir. Tahir. Tahir kaji tsoron Allah idan kayi auren nan."
Da murnarsa ya tashi zai fita ta dakatar dashi "ban amince don kafi karfina ba. Nayi ne kawai saboda kada ka cigaba da cusgunawa Khadija. Ina jin kunyar iyayenta. Ina nadamar kafewa su baka ita. Kada ka bari Allah Ya sakawa fushina a kanka ko da ban kai kararka gareShi ba." Zuciyarta kamar ta ballo kirjinta take ji.
Kalaman mahaifiyarsa sun dan tsaya masa a rai amma biyan bukatarsa ya zarce kwabar da zuciya take yi masa. Ko babu komai akwai zalunci mai girma tursasawa Khadija zaman kishi da Nasima bayan ta gansu ra'ayil aini. Bai san dalilin Nasima na son ya cigaba da zama da Khadija ba amma ba ya son bata mata rai.
Asiri ke cin Tahir amma idan bera da sata to daddawa ma da wari. Da bai bawa Nasima kofar ganin tana da matsayin da zai ci amanar matarsa akanta ba da ba za ta taba tunanin mallakarsa ta wannan siga ba.
Yakumbo kmar kowacce uwa ita ma ta haifi Tahir tana mai tattalinsa. Tayi fadi tashi dashi har ya zama mutum. Idan yana ciwo tayi kuka ko ta shiga damuwa. Murmushinsa daya tamkar mukullin aljanna yake a gareta. Soyayyarta gareshi bata bari ta sangarta shi ba. Yau fari gobe tsumma haka ta rayu da duka 'ya'yanta. Bata sani ba kuma ba da son ranta ba an wayi gari daya daga cikinsu ya zama mazinaci kuma mara jin magana.
Duk da ko 'yar da ya tashi da wannan dabi'a har duniya ta tsane shi ya taba rayuwa a tsumma ana sambarka. Anyi wani zamani da ake mika shi daga wannan hannu zuwa wancan ana cewa 'Allah Ya raya.' Uwa tana ta murna bata san kaddarar da aka rubutowa rayuwarsa. Idan da adalci ba kowane lalataccen da bane za'a zargi mahaifiyarsa. Indai Uwa ce, to burinta yafi kowa shiryuwa ko da bata bada gudunmawar da ta dace wurin yiwuwar hakan ba.
Sai mun hadu bayan sallah in sha Allah. Allah Yasa mu amfana da wadannan kwanaki masu daraja da albarka.
#StaysafecoronaiWattpad: https://my.w.tt/rNemE3YfS8
UWA UWACE...4
Batul Mamman💖
***
Kwanaki sun zo sun wuce kamar kiftawar ido ya rage saura kwana shida Nasima ta tare. Abin kamar a mafarki haka ya zo wa Khadija. Rayuwarta, iyalinta, mafarkinta da komai nata lokaci guda ya sauya. Mata da yawa a irin wannan lokacin da mazajensu zasu kara aure suna shiga wani hali. Kalmar kishiyar kadai basa so amma idan akwai ilimi, tawakkali da hangen nesa sai mace ta karbi kaddararta har ma ta mori alkhairin da yake ciki. Wadda za'a aurowa mai-aikinta kamar Nasima nata bakincikin yana karuwa ne da tunanin cin fuska da miji ya yi mata. Shi ma da anyi auren an kwana biyu zuciya tana iya samun salama radadin ya gushe tare da shudewar lokaci. To amma idan amaryar ta kasance matar da ta gida ta kama kuru-kuru ce tare da maigidan fa?! Ta ina za ta fara kuma wane bangon za ta dafa domin jin sassauci? Tambayar da ta addabi zuciyar Khadija kenan a yau da Tahir ya fada mata za'a zo jeren Nasima.
"Dakina yafi girma saboda haka shi Nasima ta zaba. Ki kwashe kayanki daga naki dakin kafin azahar don za'a jera min nawa kayan a ciki."
Magana ce yake yi mata da sigar nuna isa don kada ma tayi tunanin kawo nata korafin. Wato dakinsa Nasima ta zaba. Kodayake babu mamaki tunda ta gama sanin dakunan gidan. Bayanin karshe da ya yi mata na rainin hankali murmushi tayi masa ta amsa shi da 'to'.
"Kinga ke za ki tashi da dakuna biyu harda falo." Da hannu ya nuna mata bangaren dakunan yaransu wanda hanyar zuwansa take a gefen hagu na karamin falon gidan.
Tsarin ginin na mai karamin iyali ne dama. Idan ka shigo babban falon ne a farko. A cikinsa akwai kofar karamin falon da Khadija kan shiga da bankinta idan Tahir yana da baki a lokacin. Shi sai ya zauna a babban. Dan korido ne a cikin falon da kofa uku. Dakuna biyu sun saka bandaki a tsakiya. Daki daya gadajen yaran ne irin siraran nan. Daya mai hawa biyu, Suhaib a sama Lilu a kasa. Mai hawa dayan kuma na Farha. Daya dakin kuwa karami ne sosai. Nan Tahir ya tsara idan sun kara datawa Farha za ta koma da kansa a da. Idan an koma falon akwai wani korido din mai zuwa dakin Tahir da na Khadija. Ga bandakin baki a falon da kofar kitchen duka a cikinsa. Manyan dakuna ne daidai iyayen gida da bandakunansu. Yanzu ya ce ta kwashe kaya. Bata ma san ta ina za ta fara ba balle yadda za ta yi dasu.
A wurin ya barta baki bude. Watanta uku da haihuwa taji sauki sosai. Ra'ayoyin dangi sun kasu biyu game da auren nan. Dadaddun masu bakincikin hadin Tahir da Khadija kamar su zuba ruwa a kasa su sha. Kowa taso ya auri 'yarta saboda matashi ne da ya soma kama naira daga gama jami'a. Mafi yawansu kuwa sun aibata Yakumbo sun ga laifinta wurin bashi goyon baya. Abin da tayi domin tsare auren Khadija ba sani suka yi ba. Zahirin suke gani wato ta fifita dan da aka cuci Khadija aka aura mata.
Unguwar Barnawa ma cikin kankanin lokaci ta dauki zancen wani magidanci da zai auri mai'aikin gidansa. Wanda suka san su kuwa sunayensu suke kamawa. Sun sha zagi da muggan fata a bakin mutane a dalilin auren cin amana da ake tunanin sun yi. Makota sun shaida Khadija ta kyautatawa gidansu Nasima sosai.
Lokacin da suka tare ta leka duka gidajen layin ta gaisa da kowa. A sannan ta fuskanci bakin talaucin da ya yiwa gidansu Nasima kawanya. Saboda tsabar babu ko tabarmar da za ta zauna basu da ita sai dankwalin kan Nasiman Ladidi babarta ta ciro ta shimfida mata. A take tausayinsu ya shigeta. Kullum da rana tana yin girki ya zarce bukatarsu. Idan ta gama sai ta tura Suhaib ya kira kanwar Nasima ta zuba musu. Tahir ya kan ce kada tasa rai da kwashe ladan saboda yana da nasa kason na mai siyowa. Sai su yi dariya su mayar da zancen wasa. Anyi haka na kamar wata biyu sannan Nasima da Ladidi suka zo godiya da neman aiki.
"Idan ya dawo zan sanar dashi sai na fada muku yadda muka yi." Ita ce amsar da ta basu a mutumce. Ba bukatar mai-aikin take yi ba saboda ita ba aiki take ba. Lilu ma shekararsa hudu lokacin. Tsakaninsa da yayyensa dai duka kwanika tayi. Daga kansa ne ta sami dogon hutu.
Godiya suka yi mata Ladidi harda hawayenta tana godiya. Cewa ma tayi ko babu albashi indai zasu dauke mata baki daya cikin wadanda take ciyarwa ta gode.
"Ni kuwa Nasima ba kya tsoron matan layin nan su tona miki asiri akan irin abin da ya faru a gidan Alhaji?" Cewar Ladidi bayan sun fito.
Juya idanu tayi tafiyarta tana canjawa gabadaya zuwa irin ta masu turo kirji gaba.
"Kafin su farga na gama dashi."
Da sauran rashin yarda babarta ta ce "uhm uhm fa. Kin tuna uban dukan da Hajiya tayi miki da rashin abincin da muke fuskanta saboda babu mai baki kudi yanzu?"
Yatsina fuska tayi irin na tantiran da basu ganin kimar iyayensu "wancan ma akasi aka samu kuma dai shi Alhaji matsoraci ne. Amma baban Suhaib dinnan...hmmm"
Ladidi ta kece da dariyar jindadi "labarta min. Ko dai har kun fara haduwa ne? Naga kina abu kai tsaye kamar anyi an gama."
Murmushi Nasima tayi. Bata son saurin sakawa Ladidi rai amma tabbas ita ta san irin kallon da Tahir yake yi mata duk ranar da suka ci karo a layin.
Bayan kwana hudu ta fara aiki. Ladidi jiki na rawa take karanta mata littafin rashin albarka.
"Ki bita da ladabi da biyayya. 'Ya'yanta ki jasu a jiki kamar naki. A bayan idonta kuma kada ki dagawa mijinta kafa. Na san indai surar mace na gigita namiji wannan mutumi ba zai gagara ba. Ki janyo hankalinsa sannan ki gara shi ta yadda zai rasa sukuni. Wannan karon gidan nake so ki shiga na