Showing 189001 words to 192000 words out of 242549 words
ya karbi nambarta kafin su tafi bisa umarnin Abbati. A wurinta ya sami kwatancen da ya yi masa. Babu bata lokaci ya nufi asibitin cikin gaggawa. Sai da ya kusa shiga ya dinga kiran Abbati amma ba a dauka. Ya san za a rina saboda abubuwan da suka shiga tsakaninsu. Bai damu ba ya shiga da niyyar yi musu barazana. Da shigarsa kuma ya hadu da Asabe shi ne ya canja shawara ya gudu da Qibdiyya. Sai da ya yi tafiyar minti goma sha biyar ya tabbatar ya yi nisa da asibitin sosai sannan ya turawa Abbati message.
(Idan kana son sake ganin Qibdiyya ka zo ka same ni a Guest house din Comared gobe.)
*
Kiran Shazali a wayar Abbati yafi goma amma yana sane yaki dauka. To me ya rage a tsakaninsu ma da zai sa shi yawan kiransa? Kunnuwan da yafi tsoron su ji irin gurbatacciyar sana'arsa sun riga sun ji. A tunaninsa babu wata sauran barazana da Shazali zai zo da ita wadda tafi tashin hankalin da ya gani a cikin 'yan kwanakin nan. Shi yasa yaki dauka domin alkawari ne sun bar shi har abada. Ba don son sanin halin da Munzali yake ciki ba ma da tuni ya kashe wayar tasa. Suna shigowa gari ya sami adaidaita sahun da zai kai shi gida. A gurguje ya shiga ciki ya fada bangarensa da sallama.
Hanne ya gani tayi daidai a falo tana kallo. Sanye take da kayan bacci wadanda bashi da masaniya yau ta saka su ko tun na jiya ne. Kai ta dago ta ce masa sannu da zuwa ta cigaba da kallonta. A yau sai bai ga laifinta ba. Mutum irinsa ta yaya ma zai yi zaton cewa komai na rayuwarsa zai zo da sauki? In zai yi mata adalci ma a ganinsa ita din abar tausayi ce. Yana dai sauke hakkokinta dake wuyansa amma daga nan babu wata shakuwa ko soyayya. Laifina ne ya ce a hankali yayinda a zahiri ya tambayeta ya gida.
"Lafiya lau" ita ce amsar da ta bashi ta mayar da kai ga tv.
Bai tsaya a wurin ba ya karasa sama. Mukullin mota kawai ya dauko ya dawo ya ce mata zai tafi asibiti wurin Munzali.
"A dawo lafiya"
Daga nan bata kara cewa komai ba ta kuma mayar da hankalinta ga talabijin.
Zamansa ke da wuya a mota Shazali ya sake kira. Da yaga sunan tsaki ya yi. Sai kuma ya kula da shigowar text da sunan Shazalin. Budewa ya yi yana mamakin bakin naci irin na wannan mutumi.
Maigadi gani ya yi motar ta yo kansa gadan-gadan. Ihunsa ya dawo da Abbati hayyacinsa. Bai san ya saki hand break ba sai a lokacin. Cikin sauri ya tsayar da motar sannan ya leka da kansa ta taga.
"Bude min gate da sauri"
"Yallabai kamar bai dace kayi tuki a yanayin..."
"Na ce ka bude min!" Ya fada da tsawa. Gumi kawai yake yi yana kiran Shazali wanda a lokacin banda kyakyata dariya babu abin da yake yi.
"Shege ashe yana da hannun daukar waya"
Kafin yaje nasa gidan Abbati ya kira sau ashirin da 'yan kai. Ya tura text yafi goma. Shazali dai dariya kawai yake yi kamar mahaukaci. Ba gidansa da su Abbati suka sani ya nufa ba. Wani dan karamin gida yaje a wata unguwa da bata gama cika ba. Kafin ya fita daga motar ya turawa Abbati sako ya kuma kashe wayarsa a take.
(Aiki ne ya samu wanda yinsa ne kadai zai fanshi 'yarku. Idan kuma ka ki to ka kwana da sanin cewa ni Shazali zan sayar da ita ga duk wanda yake da bukata.)
A motar ma ya kulle wayar da Abbati yake da layin ya dauki sauran biyun ya watsa a aljihu. Ya fito ya zagaya inda Qibdiyya take bacci ya dagota yaga ta jike sharkaf da fitsari. Sau biyu kafin tayi baccin tana sake tuna masa fitsari take ji. Daga baya ta soma kukan kiran Paapa da Daddy da Asabe har bacci ya dauketa. Tsaki ya dinga yi da kananun zage-zage. Baya son harkar yara ko kadan. Ba don kada ta mutu a motar ba da a ciki zai kulleta ta kwana.
Haka nan ya sabata a kafada ya yi amfani da nasa mukullin ya bude gidan. Wani yaro matashi da bai fi shekara goma sha shida zuwa sha bakwai ba ya fito sanye da gajeren wando da fara'arsa zai tarbe shi. Ganin yarinya a hannunsa yaja tunga ya tsaya.
"Zo ka karbeta mana" Shazali ya ce dashi da dan fada-fada.
Yaro ya noke kafada harda buga kafa.
"Wallahi ba zan karbeta ba sai na tabbatar ba 'yarka bace"
Shazali ya yi dariyar jindadi ya mika hannu guda ya rungumo yaron a jikinsa yana bubbuga masa baya.
"Da mace da buhun siminti duk abu daya ne a wurina. Basu taba burgeni ba balle a kai ga sha'awa..." Ya kashewa yaron ido.
A falo ya kwantar da Qibdiyya suka shige daki shi da yaron suna dariya.
(Mai karatu wannan yaron dan wata makarantar kwana ne ta maza. Shazali ya jima kwarai da daina mu'amala da idon sani. Ya kuma fi son yaran da suke ganiyar tasawa. Bisa shawarar wani abokinsa a irin wannan harkar suke zuwa makarantun kwana suna biyan masu gadi ko malamai sai a fito musu da yara. Wani zubin washegari yake mayar dasu da sassafe. Wasu ma basa kwana. Amma wannan yaron tun haduwarsu gabanin hutun makaranta ya kasa rabuwa dashi. Dubu hamsin ya biya ya dauko shi ranar da aka koma hutu wato lahadi. Yana so ya kai wata lahadin sannan ya mayar dashi. A cewarsa ya yi kewar yaron.)
*
Wani irin ciwon kai ne ya kama Abbati yayinda ya fahimci da gaske Shazali ya dauke Qibdiyya. Ga Asabe a gefe ta soma kuka tunda taga halin da ya shiga ta san babu lafiya.
"Shi yaron ba abokinku bane?"
Amsar da zai bayar yafi kowa sanin cewa karya ce. Sai dai karyar ita ce cigaban rufin asirinsu. Yana bayar da amsa yana mai Allah wadai da sana'a ko dabi'ar da muninta zai sa mutum ya dinga karya da gangan.
"Abokinmu ne a baya. Rigimar kasuwanci ce ta hadomu. Ya cinye mana kudi ya kuma ki yarda mu hadu balle ya yi mana gamsashen bayani game da kudin. Shi ne muka yi masa barazana da zuwa kotu. Saboda yana so mu janye karar da zamu kai shi ne ya dauketa."
"Amma anyi lalataccen yaro. Na rasa gane inda duniyar nan take dosa damu" cewar Innayo ita ma tana share kwallar tausayin dauke 'yar karamar yarinya.
Salihi ya dafa kafadar Abbati ya ce "Zama bai kama mu ba. Muje a kai raport ofishin 'yan sanda"
A razane ya dubi Salihi. Shigowar 'yan sanda cikin lamarin nan a yanzu ba komai bane zai faru illa allura da za ta tono garma.
"Ya ce gobe naje na same shi tare da takarda mai sa hannu cewa mun yafe masa kudin. Idan ba haka ba zai sayar da ita. Ka bari naje tukunna mu gani. Idan ya saba alkawari sai mu nemi 'yan sandan. Yanzu ya kashe waya ne kawai saboda ya tayar mana da hankali sannan ba gidansa ya tafi ba."
Zukatansu ba duka suka yi na'am da shawarar Abbati ba. Sai dai kuma sun san cewa a yanzu ko masu satar mutane suna gaggauta cutar dasu ne idan suka fuskanci hukuma za ta damkesu.
Da wannan aka samu suka bar maganar haka. Abbati ya fadawa Uwani shi ne zai kwana da Munzali. Ya kuma jaddada musu mahimmancin iame bakunansu daga zancen abin da ya faru. In ya nemeta ace masa tana wurin Asabe. Hankalin kowa sai ya kwanta suka tafi gida ana tararrabin me zai faru washegari.
A gaban gadon Munzali ya tsaya yana kare masa kallo. Ya zabge sosai kamar ba shi ba. Gashi dai bacci yake yi amma ana iya ganin yadda fuskarsa ta tattare kamar wanda ya fada tunani mai zurfi saboda damuwa. Tausayinsa ya sake kama shi da ya tuna abin da aka yi mata da dauketa da Shazali ya yi. Iska mai zafi ya fesar ya fita daga dakin ya koma mota. Ya dauko abin sallah sannan ya sayi ruwa ya dauro alwala ya koma. Tashin hankali ya hana shi jin yunwa. Da ya idar da sallar dorawa ya yi da nafilfili cikin kankantar da kai da cikakken tawali'u. Addu'oinsa basu da yawa sosai. Istigfari ce yake ta yi domin neman gafarar Ubangiji gare shi da amininsa. Idan sun samu rabauta ya yi imani komai zai zo da sauki. Asirinsu zai rufu, iyayensu zasu yafe musu. Sannan Allah zai tsare Qibdiyya a duk inda take. Yayi nisa cikin ibadarsa yaji muryar Munzali tana fitowa a hankali.
"Ka yafe min ko zan sami sassaucin kunar dake raina."
Dago kai ya yi suka hada ido. Abin da ya gani a idanun Munzali ya bashi tsoro. Irin yanayin nan ne da zaka ga mutum bashi da maraba da mutum-mutumi. Total hopelessness and helplessness. Mikewa ya yi ya ja kujerar gaban gadon nasa ya zauna suna kallon juna. Munzali ya zauna ya jingina bayansa da bango.
"Ni kake cewa in yafe maka Munzali?"
Murmushin karfin hali ya yi da yaga kamar ran Abbati ya sosu ya ce
"To ko sai na durkusa?"
"Ka ajiye wasanka muyi magana. Me zaisa ka ce na yafe maka bayan ni da kai muka yi laifin kuma Allah Ya kamata mu roka gafara?"
Kodaddun idanun Munzali sai suka ciko da kwalla. Yana so ya yi magana ba tare da ya nuna karayarsa ba amma ya kasa.
"Ina ta rokon Allah gafara kamar yadda ka ce amma zuciyata tana raya min tubana ba zai karbu ba. Ga nauyin zunubina ga na lalata maka taka rayuwar daga zuwa karatu."
Rai a bace Abbati ya ce "dakata haka"
Girgiza masa kai Munzali ya yi yana murmushi wanda ya koma kuka kafin ya kai karshen maganarsa
"ka barni na karasa magana. Laifinmu yana da girma. Abin da aka kifar da al'umma guda a dalilinsa. Shi ne nayi silar fadawarka gare shi har muka mayar dashi sana'a. Wallahi zuciyata har kokonto ta soma akan amintarmu. Shin Abbati amincin Allah da Annabi ne tsakaninmu ko kuwa kazamar soyayya nake yi maka? So nake a shafe babina a doron kasa domin ban san waye ni ba. Da wannan nauyin kana tunanin har ina da darajar dukawa gaban Allah in roki gafara? Baka ganin tun yanzu na soma ganin bala'i? Qibdiyya me ta sani a duniyar da har ..."
Abbati ma kwalla ya soma fitarwa yana ta girgiza masa kai don ya yi shiru.
"Ka daina irin wadannan maganganun Munzali kada kayi sabo."
"Sabawa Allah ai na riga nayi. Gashi yanzu ina jin kaina kamar mafi kaskanci a cikin halittun Sa. Idan na tuna kwanciyar kabari sai naji na karaya fiye da tunaninka. Abin da ya sami Qibdiyya bai min ciwo kamar tsoron mutuwata. Me zan ce da Allah?"
Wani irin kuka Munzali ya fashe dashi wanda ya janyo makotan gadonsa a dakin suka fara kallonsu. Abbati ya gama sauraron dukkan zantukansa sannan ya kama hannunsa na dama ya rike.
"Na rantse maka da wanda rayuwarmu take hannunsa gafarar Allah ta ninninka azabarSa. Sannan wadannan tunanin na banza da suke damunka ba komai bane illa wasiwasin shaidan. Idan ka bari rayuwarka ta kare a haka to tabbas zaka mutu cikin nadama..."
Munzali ya galla masa harara ya ce "a dinga tauna harshe idan za ayi nasiha don likita ya ce jinina ya mugun hawa"
Shi ma Abbatin harararsa ya yi yana jin kamar ya mangare shi ya ce,
"Gara ka tsorata kada kayi min sanadin rashin samun wuri a karkashin inuwar al'arshi"
Munzali sai ya yi kasake yana sauraronsa. Wannan ya bashi damar yi masa bayani gamsashshe.
"Tsahon lokacin da muke tare cikin sabon Allah kai shaida ne ina yawan karatu. Karatun ne ya taimaka min wurin kara fahimtar munin abin da tuntuni muka san haramun ne. Shi yasa na damu da son mu tuba. Amma kafin na cigaba da magana zan yi maka tambaya guda daya. Kana jin da bamu tuba ba za ka iya yin mu'amala dani Munzali?"
Wata irin zabura ya yi ya ce "A'uzubillah minash shaidanir rajim"
Abbati ya ce "to Shaidan sai a nemi wani gaulan wannan dai ya tsira"
Dole Munzali ya yi dariya. Abbati ya yi murmushi ya dora da cewa "Masha Allah. Abotarmu ta Allah ce ba ta shaidanci ba. Da ace zukatanmu suna marmarin haka a tsakaninmu to ina mai tabbatar maka tubanmu ba zai cika ba sai mun nesanta da juna kamar yadda Baaba ta fara bamu shawara domin samun nutsuwar zuciya"
Munzali ya hau ambaton "Alhamdulillah" da yaji wannan bayani mara wahala.
"Abu na biyu kuma mafi mahimmanci shi ne ka daina raina rahamar Allah. Ta yaya ma za ka dinga tunanin ba zai yafe maka ba bayan ya yi alkawarin gafara ga bawa idan ya tuba. Inda na karanta fa cewa aka yi zunubi ko ya kai kumfar kogi Allah zai yafe idan aka tuba."
Cikin rauni Munzali ya sake cewa "Amma gafarar ba sai ga wanda yaso ba? Idan bana ciki fa? Alfarmar wa zana hau a cikin mutane wanda zanci albarkacinsa har a yafe min?"
Abbati ya dauke duk wani burbushin fara'a a fuskarsa ya ce "in ka sake magana wallahi sai na bata maka rai. Ta yaya ina fada maka girman Allah kana dawo da hannun agogo baya? Tudun da za ka ci ya wuce na kasancewarka daya daga cikin halittun Allah? Ko kana tunanin akwai wanda Allah zai yafewa zunubai a dalilin aikin wani ahalinsa alhalin shi bai mika wuya da gaskiya ba? Tsarki ya tabbata ga Sarkin da yake yafewa bayi a kan kowane zunubi indai sun tuba. Munzali da za ka tuba yau gobe ka komawa zunubi ka sake tuba zai yafe maka (hakan ba yana nufin bawa ya yi ta wasa da damar tuba bisa izgilanci da tunanin gobe ma za a yafe masa ba. Idan mutuwa ta wafce mutum a cikin halin sabo kafin ya tuba shikenan!). Kai..."
Ya tabo kafadar Munzali domin ya sami cikakken hankalinsa a tare dashi "akwai wani sahabi kuma surikin Annabi SAW mai suna Abu Sufyan. Ko ka san irin taskun da suka sanya musulmi kuwa? Yana cikin jagororin yakin musulunci na farko wato Badar. Matarsa kuma a yaki na biyu (Uhud) ta hayi wani ya kashe mata kawun Manzon Allah SAW. Kawunsa fa wanda yake matukar so. Sunansa Hamza. Kuma bayan an kashe shi aka ciro mata hantarsa ta tauna. Sannan ta lalata gawar ta hanyar yayyanka sassan jikinsa. Da Allah baya yafe laifuka da bai basu damar karbar musulunci ba duk su ukun."
Zaro idanu Munzali ya yi "sun musulunta?"
Abbati ya gyada kai "da Abu Sufyan din, da matarsa (Hind bint Utbah) da wanda ya yi kisan (Wahshi ibn Harb) na dai manta sunayensu. Amma wallahi duk sun shiga inuwar musulunci kafin su bar duniya. Sahabbai ma suka zama tunda sun rayu da Annabi SAW. Duk sahabi daya kuwa darajarsa ta ketare tamu akan kowane aikin ibada."
"Allahu Akbar" cewar Munzali da wani irin shaukin fahimtar addininsa.
"Dalla can. Sau nawa ina kawo mana littafin tarihi kana kin karantawa sai aukin danna waya?"
"To ai dai na daina. Ni islamiyya ma zan shiga wallahi."
"Zamu shiga dai. Kaga irin wannan kambana girman zunubin da jin kamar baka da rabo ba komai bane illa aikin shaidan. So yake mu dauwama a zunubi. Idan muka tashi tuba kuma ya nuna mana kamar laifinmu yafi karfin a yafe mana. Kaga imani sai ya sami rauni. Muje lahira ..."
"A tutar babu" Munzali ya karasa masa.
Maimakon su kwanta sai suka koma tattauna abubuwan da suka danganci laifi da tuba. A nan ne Abbati ya sake fayyace masa kowane bawa da aikinsa zai dogara ba kusancinsa da waliyyi ko asharari ba. Ya bashi misali da tarayyar Fir'auna da Asiya Allah Ya kara yarda da ita. Ga Annabi Nuhu AS da Annabi Lud' AS da matansu wadanda Qur'ani ya tabbatar mana cewa 'yan wuta ne.
"Duk da haka amma fa musulmi masu imani suna cin darajar juna indai kowannensu ya yarda Allah da zuciya daya. Misali wanda dansa ya mutu kafin shekarun balaga indai yayi hakuri akwai sa ran dan zai cece shi (ina kara mika ta'aziyya ga Ummu Sadiq da Ummu Abdurrahman na Sparkling, Sanah Matazu Fikra da Halima Siyama H2H da duk wadanda suka rasa 'ya'ya. Allah Yasa rashin da muka yi masu ceto ne a garemu) , ko idan kana da d'a hafizin al-Qur'ani zai daga darajarka a aljannah. Sannan Allah zai bawa wasu ceto ranar lahira"
Bakin Munzali a bude har Abbati ya gama magana sannan ya ce "to wai ni ina ina ka tara wannan ilimin? Wallahi ganinka nake kamar wani shaihin malami."
Dariya babu shiri ta kama Abbati ya ce masa "Allah Ya shiryeka. Babu bashin salloli akan ka ko?"
"Akwai wallahi" ya amsa yana mai jin kunyar kansa.
Da taimakon Abbatin ya shiga bandaki ya yi alwala. A zaune ya gabatar da sallolinsa ya jima yana neman gafarar Allah. Sa'annan ya hada da godiya da Ya hada shi da Abbati. Lallai a cikin abota akwai riba idan an dace. Kuma masu cewa zama da madaukin kanwa yana kawo farin kai basu yi kuskure ba. Halin da ya tsinci rayuwarsa ya yi jirwaye a rayuwar Abbati. Yanzu kuma an zo wakafin da halin rayuwar Abbatin zai wanke musu duka jirwayen.
Karatu ne ya kawo Abbati Kano kuma cikin kudurar Allah Ya samu ya yi. Babbar illar da ya samu ita ce ta rashin idon mafadi da rashin kulawar iyaye a shekarun da ake bukatarsu. Allah Ya hada shi da mutum mai saukin kai da tausayi irin Munzali. Da ace Munzali ya tashi da kulawar iyaye tabbas da an yi bawa mai yawan kyautatawa na kasa dashi. A cikin halin kuruciya da rashin ilimin da iyaye suka barshi ya iya janyo almajiri jikinsa. Ya nuna masa sana'ar da yake yi domin yaci abinci. Sannan bai taba yi masa hassada ko kyashi ba. Wannan rayuwar bata hana Abbati cigaba da karatunsa ba wanda zamu iya alakanta shi da yawan addu'ar da mahaifiyarsa take yi masa da nasiha. Shi ne yaja hannun Munzali zuwa makarantar yaki da jahilci. A gefe guda yana ta bibiyar duk wani littafin da ya danganci addini wanda zai iya karantawa. Zuciyarsa bata nutsu da sana'arsu ba sai dai kuma a lokacin bashi da karsashin son su barta ko don kudin da