Showing 192001 words to 195000 words out of 242549 words

Chapter 65 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3384

suke samu. Munzali bai taso da akidar karatu daga wurin uwa da uba ba shi yasa baya ma mararin karanta irin litattafan Abbati. Ashe zasu yi musu rana. Ashe abotar irin wadda ake fatan ta kai ma'abotanta karkashin inuwar al'arshi ce.

Da ya shafa addu'arsa bacci Abbati ya tilasta masa yi. Yana son jin bayani game da fyaden da aka yiwa Qibdiyya sai dai dan saukin da Munzali ya samu yana bukatar a tattala shi. Tambayar damuwa za ta dawo masa da ita. Haka ya hakura sai dai har gari ya waye bai rintsa ba. Yana ta faman tufka da warwara akan yadda ya kamata ya fuskanci Shazali.

***

Alh. Rabi'u ya dawo gida daga wurin da suke buga karta da abokansa shadaya da rabi na dare. Innayo dama ba kwana gareta ba. Babbar rigarsa ya cire ya nufi bangaren Asabe. Kudi yake so a wurin Munzali ya kasa samunsa a waya. Ba za a rasa wani abu a hannun Asabe ba ko yaya ne. Shi ne ya taho da dan kunshin tsirensa ya kai mata. Ko kallo ledar bata isheta ba har ya ajiye. Rashin kulawarta ya bashi mamaki domin ko mage bata fita jin kamshin nama ba. Ledar ya kama ya shiga kwancewa yana 'yar dariya.

"Hala mura kike baki ji yadda kamshin tsiren nan ya cika dakinki ba. Nace wai ina Munzali ne kwana biyu"

A hautsine ta kalle shi da jajayen idanunta tana kada kai.

"Ga mayya ba. Ai dole in juyo tunda maigida ya kawo nama"

Ledar ya dire ya kare mata kallo a tsorace sannan ya ce "wani abin Innayo tayi miki?"

Asabe bata amsa ba sai ma juya masa baya da tayi. Da ya san yadda zuciyarta take a jagule da ya fita ya bar mata dakin. Shi kuma a wautarsa sai ya zata da gaske Innayo din ce.

"Ai kuwa yau daga ita har wadancan zaurawan da ta tara a dakinta ba za su kwana lafiya ba."

Hanyar fita yabi Asabe ta tashi tayi saurin dakatar dashi da taji ya fara kiran sunan Innayo.

"Dakata min Malam don wannan hargagin naka ba zai burgeni ba. Innayo kuma da kake magana da taron zaurawan dakinta a yini guda sun yi min abin da baka taba yi min ba a iya tsayin shekarun aurenmu. Duk wanda ya damu da naka ba don abin hannu ba shi ne cikakken masoyi."

Kirjinsa ya shiga nunawa cike da kokonto yana cewa "dani kike Asabe?"

Dama can zuciyarta tana wuya. Wannan borin kunyar nasa sai ya kara tunzurata. Da yatsa ta nuna shi tamkar dan cikinta.

"Da kai nake Rabi'u. Da kai nake sako tumaki ballo jakai."

Tas ya dauke fuskarta da wawan mari yana huci.
"Ni kike zagi a cikin gidana?"

Ita kuwa rike kumatu tayi tana kuka ta ce,
"An zageka din. Wannan ginin kuma billahillazi ba gida bane. Gida ai inda miji da mata suke tattalin 'ya'yansu ne. Nan kuwa bashi da maraba da bariki gidan ka zo na zo. Gara ma Innayo tana yiwa 'ya'yanta. Amma da yake jini baya karya ai bata fara jindadinsu ba sai da duniya ta koya musu hankali. Sun so gadon bakin hali a jikinka ba don Allah Ya tarfawa garinsu nono ba."

"Wai Asabe ko kin fara shaye shaye ne?"

"Zancen kake so kuma zan yi maka shi filla-filla. Munzali yana kwance a gadon asibiti. Jiya ya yi min wasu zantuka da na kasa fahimtarsu amma sun yi matukar razana ni. Sannan wani dan iska ya yiwa Mariya fyade kuma an saceta ma amma duk halin da muke ciki babu wanda yaji a ransa wai ya kamata a sanar da kai. Saboda me?" ta sake nuna shi da dan allinta "saboda kai da babu sammakal. Amfaninka daya a gidan nan shi ne ka yiwa mace ciki ta haihu..."

Tunda suka fara rigimarsu Innayo, Salima, Zara da Uwani suka yi shiru suna sauraronsu. Kalmar Asabe ta karshe ta janyowa Zara da Salima harma da Innayo muguwar kunya. Su biyun suka tashi suka shige daki da dimbin mamakin fyaden Qibdiyya. Uwani kuwa ko gezau ta cigaba da zama tana kallon yadda Innayo ta takura. Kofar dakin da su Salima suka shiga tabi da ido ta ce,

"Ai ba karya tayi ba duk suka wani watse don munafunci."

Innayo ta kada kai ta ce "Uwani kenan"

Ta kuwa yi kicin kicin da fuska "to banda sunansa da muke karawa a gaban namu akwai wata riba ne?"

Kafin ta dauko abin da zai karasa kunyata ta sai ta tambayeta ko tana da masaniya game da abin da Asabe ta ce ya sami Qibdiyya.

Nan da nan fuskarta ta canja kuwa. Al'amarin da ya faru tun zuwanta gidan na farko ta labartawa Innayo. Bayan ta gama gani tayi Innayo din tayi ajiyar zuciya amma bata ce komai ba.

"Kin san wani abu ne akan abin da ya same shi?"

Da hanzarinta ta girgiza kai "ko kusa. Kawai dai ina rokon Allah da Ya kawo mana komai cikin sauki ne"

Uwani bata gamsu ba ta ce "amma na fada miki cewa ya dinga yi ta yafe masa wai laifinsa ne"

"Duk iyayen da suke kaunar 'ya'yansu suna dorawa kansu laifi ne idan wani abu mara dadi ya faru dasu." Ita ce amsar da Innayo ta bata. A fuska kuwa kana iya gane zancen ya tayar mata da hankali fiye da yadda take son nunawa.

Mikewa Uwani tayi ta dan bata rai "da yake ba su Hasiya bane sai nema kike ki katse 'yar hirar da na samu kina yi dani." Tayi hanyar daki "Bari naje na mike bayana yau na sha tsayuwar aikin lada. Allah Yayi mana albarka."

Innayo bata san lokacin da ta tuntsire da dariya ba. Uwani tayi kasake tana kallonta. Abin sai ya taba mata zuciya fiye da zatonta. Ji tayi kamar an tsikareta a kahon zuci. Bata san tayi kewar fara'ar mahaifiyarta ba sai yau. Yaushe rabon da taga ko murmushi ne daga Innayo akanta?

Bayan ta gama dariyar ta ce "Allah Ya bada lada Yayi albarka".

Kafin Uwani ta sami damar magana ta tashi ta shige bandaki. A ciki ta share wata kwalla ta bata ma san ta taru a idanunta ba sai yanzu. Da a wuri mai tsarki take tabbas babu abin da zai hanata sujjadar godiya ga Allah. Bayan shekaru masu yawa ace wai ita ce take hango yunwar mahaifiya a idanun Uwani. 'Yar da tasa kafa ta take duk wani kusanci dake tsakanin uwa da 'yarta. Uwanin da take nuna mata kyama kirikiri saboda ta sami abin duniya. Kaico! Duniya abar banza. Dan adam ya yi ta daga kafada yana nuna izza a doron kasa. Lokaci guda Allah Yana nuna masa iko sai ya yi lakwas. Tana son furtawa Uwani kalmar yafiya sai dai tana tsoron kada a koma gidan jiya idan duniyarta ta sake zukar iskar wadata.

Wanka tayi amma har ta fito tunanin rayuwa bai barta ba. Munzali da Qibdiyya ne a ranta fiye da komai. Bata son fadawa kowa ne amma ta dade da dora alamar zargi akan sa. Yaron da bai yi boko ko islamiyya ba sai yawo cikin unguwa ace lokaci guda ya yi kazamin kudi. Tabbas da dan cikinta ne da ta jima da kwankwasarsa akan sana'arsa. Shi kuwa yanayin gidansu yasa ta kame bakinta. Tun da ta taba magana Asabe ta ce ta saka masa ido ta janye jikinta. Banda Allah Ya taimaka da kansa ya sake waiwayo ahalinsa da yanzu haka zai shiga halin nan shi kadai. Dalili mai karfi ne zai sa ya ambaci fyaden Qibdiyya a matsayin laifinsa. Kamar Baaba Mari sai gashi ita ma tana tunanin ko sata yake yi.


*
KWAYAYE ZASU FASHE...tabbas dole su fashe ko sakon da nake burin isarwa a karshen labarin da yardar Allah zai sami damar bayyana kansa. Ku dakaci shafukan karshe masu zuwa gareku soon in sha Allahu. Jazakumullahu khaira






I just published "40" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221353320?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=NYezbORxrG%2Bh%2BigXx3DygdDpPU0OhBETkTnfRmjQZewRsbUh%2F0BZd4OGN8VCL3tmlLZfj4%2BWNmhHzFlgcXZlsN7%2FqVYIdxEMPJ4W3EGm5KsQVuVFxQaVt%2BcUvr%2FAdNp%2B



UWA UWACE...40



Batul Mamman💖



EID MUBARAK~Kullu amin wa antum bikhair.


An sha jira. Ayi hakuri ba da niyya bane. Yanayin chanjin rayuwa ne wanda ya zama silar birkita yadda mafi yawanmu muke sarrafa lokutanmu. Fatanmu Allah Yasa mu rabauta duniya da lahira.

Littafin UWA UWACE tukwici ne ga dukkan masu karatun da suka sha jiran kammaluwarsa. Musamman masu kira da turo sakonni ta whatsapp, wattpad da instagram. Kun yi min halacci. Nagode

H2H
The Queens
KDM Sisters
The Sparkle
Antina Prof. Asabe
Habiba (Mantis kitchen)
Lubabatu S. Shayi
Maman Fatima
Aisha Lagos
Mamin Fadil
Pherty BB
Anti Fauziyya Bindawa
Anti Binta DB
Anti Samira DB
Da sauran da ban sami damar ambata ba duka nagode.




***Safiyar Talata***



~A gidan Innayo ita da 'ya'yanta sun yi sammakon tashi domin hada abincin asibiti. Gabadayansu 'yan dakin babu wadda tayi baccin kirki saboda batan Qibdiyya. Duk sun matsu da son ganin an dawo da ita lafiya a yau kamar yadda Abbati ya sanar dasu. Asabe da Alh. Rabi'u kuwa tun rigimar da ta barke tsakaninsu da daddare babu wanda ya kara jin duriyarsu.

~Gidan Mami Khadija kuwa ita da Lilu tare da Farha ne a mota suke shirin tafiya Kano. Sai da gari ya waye su Sauda na shirin tafiya makaranta sannan Mami ta ce da Farha ta shirya. Basu da niyar kwana sai dai ita tafiya ta Allah ce. Shi yasa suka dauki kaya na kwana dai-dai koda bukatar hakan zata taso.

~Baaba Mari ta tashi da karfin jiki a yau har taji zama ba nata bane alhalin Abbati da Munzali suna cikin wannan yanayi. Bata ma da labarin dauke Qibdiyya amma taji zancen kwanciyar Munzalin a asibiti. Garin Allah na wayewa ta nemi izinin Mal. Inuwa. Da ya so hanata saboda yanayin jiki sai ta dage ba za ta iya zama ba. Muryar Munzali a lokacin da ya fada mata abin da aka yiwa takwararta da ma rokon gafararta da yayi suna ranta. Tare suka shirya domin lokacin sakar mata ragamar 'ya'ya ita kadai ya riga ya wuce. Makauniyar biyayyar da yake yiwa Mal. Sa'idu bata yi masa rana ba. To kuma sai Mal. Sa'idun ma ya ce zai je. Haka aka fito dashi ba yadda yake ya zauna a gaba da yar sandarsa.


*****

Damuwa ce karara a fuskar Zakiyya lokacin da ta tashi daga bacci. Irin baccin nan rabi da rabi wanda kusan duk abin da ake yi a kusa da mutum zai ji tayi. Ba komai ya haddasa mata wannan rashin kwanciyar hankali ba sai rashin dawo da Qibdiyya da Munzali ya yi. Indai ba lokacin hutu ba a ka'ida bata wuce lahadi idan tana wurinsa. Hutun da ya wuce da bai zauna a gari sosai ba da kansa ya maidota kafin a koma makaranta. Sai kuma daukarta da Abbati ya yi ranar Juma'a. Tunda kowa ya san litinin za a koma makarantu ta zata zai yi aiki da hankali. Daren lahadi tunda aka yi isha take kiransa shiru baya dauka. Litinin ma haka. Yau gashi talata. Me yake nufi?

Tana can duniyar tunani bata ji shigowar Ummansu ba sai da ta kai mata duka a kafada.

"Raba kanki da yawan tunani tun da kananun shekaru ba alkhairi bane" ta sami wuri kusa da ita akan gadon ta zauna sannan ta cigaba da magana "wai akan rashin dawowar Qibdiyya ne kika kasa baccin safen naki na jaraba?"

Kwabe fuskarta tayi ta ce "Umma daga cewa zata kwana biyu sai in ji shiru sannan yaki daukar waya?"

Maganar haushi ta bawa Umman ta ce "tunda dawa ta tafi ai dole ki tada hankali."

A sanyaye Zakiyya ta ce "ba haka bane. Kinsan makarantarsu da tsauri. Yanzu sai kiji ana cewa za a maye gurbinta da wani dalibin idan bata dawo ba."

"Na dauka don Allah kika damu da ita ashe don tijarar makarantarsu ne. To Allah Ya kyauta. Kin bi kin sakwarkwace daga haihuwa daya. Babu wani kulawa sai aukin hada lanci bus (lunch box) a kai yarinya makaranta." Ta mike tana tabe haki "Sai ki sake kiransa ko ita Yaya Asaben don ni dai babu wanda zan nema."

"Umma na sakwarkwace fa kika ce?" Zakiyya ta ce a shagwabe.

Da fada Umman ta karanto mata abin da yake damunta wanda a karshe ta kai ta daga murya sosai.
"Yo sakwarkwacewa mana. Da kina da kula sosai akan abubuwa amma yanzu idan kika fara danna waya da kyar kike tashi sallah. Kin bari ta namaye miki rayuwa baki da katabus kan lamuran rayuwarki. Yarinya daya ba don ina gidan ba ni ban san yaya zaki yi da ita ba. Maganar gaskiya ko yau Munzali ya yi aure ya bukaci 'yarsa wallahi ko ba kya so sai na bashi. Kulawar da take samu in taje hutu ta ninka taki kuma kema kin sani. Shi ne zaki wani dami mutane don ta kara kwanaki don wawanci? Mtsewww"

Fadan Umman bai karawa Zakiyya komai ba face sake shiga rudani. Tabbas tafi kowa sanin yadda taja baya wurin kula da 'yarta. Mafarkinta na jiya ya sake dagula mata lissafi. Ganin Qibdiyya tayi a yanayi mara dadi har tana neman taimakonta. Anya idan ta cigaba da zama ba za ta amsa sunan sakarai bayan wawiya da Ummanta ta kirata a cikin fada ba? Da wannan tunanin ta mike a gurguje tayi wanka ta shirya.

"Sai ina kuma?" Cewar Umma ba tare da ta sakar mata fuska ba.

"Gidan zanje in daukota"

"Yanzu ba za ki bari ya dawo da ita don kansa ba?"

"Umma gara inje dai. Daddy zai kaini"

Cikin minti goma sha biyar Daddy da Zakiyya suka dauki hanyar gidan Munzali.

***

Alh. Sadisu Nakano rikakken dan bangar siyasa ne wanda ya iya takunsa a wajen iyayen gidansa. Da abin da ya dinga tarawa a jikinsu ya hada jarin da ake yi masa kasuwanci kala kala. Duk fadin Kano babu wanda zai ce bai taba jin sunansa ko labarinsa ba. Yana da baki kamar reza. Idan ya sako mutum a gaba to kashinsa ya bushe. Idan yana yi da kai kuma da wuya ka fadi takara ma. Da karfin cin tuwo ya mayar da kansa uban 'yan siyasa da 'yan jagaliyarsu a Kano. Mutum ne shi wanda baya yafiya, komai daren dadewa sai ya fanshe idan aka yi masa laifi. An alakanta shi da muggan laifuka iri iri wadanda suka hada da safarar hodar ibilis da yankan kai saboda kudinsa da k'aurin suna. Gashi bashi da tsoro ko digo. Kai har cewa aka yi ya taba sawa an dauko masa gwamna cikin dare ya yanka masa warning akan wani kuduri da ya sabawa aikinsa. Jita jita mara dadi kullum cikinta yake. Wata gaskiya ce wata kuma ana kara gishiri. Duniyarsa dai tana garawa yadda yake so ta kowane fanni illa lamarin zuri'a. Dansa daya mai suna Abdul. Yana ji dashi kamar rai. Matansa hudu amma ta biyun ce ta haife shi. Sai dai wani abu na ban mamaki shi ne duk irin kishin gidan gabadaya matan suna kaunar Abdul. Kowacce tana kokarin faranta masa ko don gyara fadarta a zuciyar maigida.

Saboda yanayi na sa ido daga abokan hamayya a dalilin karatowar zab'e da rashin tsaro Alh. Sadisu ya dauke Abdul daga makarantar da yake ya mayar dashi zuwa wata 'yar kadaran kadahan ta kwana. Masu matsayi irin nasa a jam'iyun gaba suna neman sako shi a gaba ta hanyar dansa. Duk wata yana bayar da kudi mai tsoka domin a kula masa da gudan jininsa. Burinsa ya kai shi waje da zarar ya gama sakandire.

A makarantar aka sami wadansu fitinannu suka koyawa Abdul mummunar dabi'ar luwadi. A nan ne kuma malamai marasa tsoron Allah da hadin bakin maigadi suke sana'ar tura kyawawan samari masu wannan hali wurin shaidanun mutane a waje. A takaice dai, Abdul Sadisu wanda aka boyewa inkiyar Nakano yana gidan Shazali!

A washegarin da Qibdiyya ta kwana a gidan shashancin Shazali ta tashi ne da kuka. Ta waiga hagu da dama bata gane inda take ba ga sanyi sanyin safiya sai ta fara kiran iyayenta.

A lokacin Abdul ya fito daga wanka kenan. Falon ya fito ya sameta a bakin kofa tana bubbugawa da karfinta. Sai ta bashi tausayi. Ya san ba huruminsa bane yin bincike akan duk wani abu da ya shafi personal rayuwar Shazali. Duk da haka sai yaji ba zai iya dauke kai daga yarinya karama irin wannan ba. Me ya hadata da Shazali har ya kawota gidansa?

Nufota ya yi da dan murmushi ya ce "Zo, ya sunanki?"

Ai tana juyawa da ta ganshi da tawul a kugu sai ta firgice fiye da ganin kanta a bakon wuri. Uncle Daddy ne ya fado mata a rai taji tsoron ko shi ma abin nan yake shirin yi mata. Da yaga yadda ta tsorata sai ya yi nufin tuntubar Shazali domin a bata koda shayi ne tasha. Yana kawo kai yaji wayar da shi kanshi ta kada masa ciki har ya kasa motsi.

*

Comared yana kwance tsakanin 'yan mata biyu yaji kiran Shazali. Rabonsa da gidansa yau kwana uku. Ya sanar da matansa ya tafi Lagos aikin sati daya. Basu san yana garin a guest house din da kalilan ne suka san da wanzuwarsa. Muryarsa a shake kamar basamuden kwad'o ya ce,

"Shazali ya ake ciki?"

"Comared an samu sai dai ina rokon idan da hali yazo ayi yau dinnan kawai. Da kyar na sami kan mutum daya daga cikinsu don sai da na hada da dauke musu yarinya"

"Dauke 'ya kuma Shazali? Nifa bana son abin da zai je ya dawo gareni."

Shazali ya yi dariya ya ce "kada ka damu. Akwai tamu dasu ne. Yarinyar ce kadai tikitin samun hadin kansu. Da azahar zamu zo."

Comared ya shafa kurcin cikinsa yana dariyar shakiyanci.
"Idan bai sami zuwa ba ni ka kawo min yarinyar na dana mana."

"Comared bata fi shekara shida ba fa"

"Irinsu sunfi...kai dai kawai nayi shiru. Ni dai ina so"

"An gama. Zan kawota indai bai zo ba. Amma sai dai daga wurinka a san inda za ayi da ita don babu hannuna kuma."

Jikin Abdul ya yi mugun sanyi da ya fuskanci girman abin da ke gaban Qibdiyya. Kafafu babu kwari ya koma da baya da sauri ba tare da ya shiga dakin ba. Bai san tun tsayuwarsa Shazali ya ankare dashi ba. Da ya fito ya kusa dariya ganin Abdul ya firgice a kokarinsa na son basarwa, shi a dole bai ji komai ba. Duk yadda yake son yaron dole ne ya dauki mataki a kansa tunda har ya san gidansa. Da niyarsa yace masa tsintota yayi kawai a bar maganar a haka.

***

Bayan Alh. Tahir ya gama waya da Comared bashi da zabin da ya wuce bin hanyar Kano a yau dinnan. Bayani daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login