Showing 156001 words to 159000 words out of 242549 words
kanwarki kya bayar. Zumuncin da kike wulakantawa Uwani shi ne gatanki. Ba don kinsa kafa kin tattaka shi ba da bamu ga rana irin ta yau ba akan aurenki."
Kunyar rashin tunaninta taji da kanta.
"Kiyi hakuri Innayo. Ku gaisheta kafin na zo."
Murmushin takaici Innayo din tayi ta fita tana cewa "da girmanki baki san gatse ba. A yadda Hasiya ta dade tana neman haihuwa na zata kiran mijinki zaki yi ki nemi izinin zuwa dubota. Komai girman farincikin da zai gilma a gidan nan indai ba ke ya raba ba wato ba za kiyi murna ba..."
Har tayi waje Uwani tana jiyota. Abin ma sai ya sata murmushin da bata yi niyya ba. Autar Innayo da ciki kuma bata je dubiya ba. Ta san ba makawa yau sai ta kwana tana jin mitar mahaifiyarta. Sai dai kuma abin da yake damunta yafi karfin samun cikin Hasiya a yanzu dai. Hakuri ta sake bayarwa da sakon gaisuwar ta koma ciki. Suna fita ta fito ita ma ta shiga dakin Asabe. Daga bakin kofa ta tsaya cikin shiri don har mayafi ta yafa. Abin da ya kaita ta fada ba tare da kwana kwana ba.
"Gidan Munzali za ki kwatanta min ko ki rakani."
Da tsananin mamaki Asabe tayi mata duba irin na wanda ake tsammanin ya yi makuwa "gidan Munzali kuma?"
Uwani sai ta dauko waya ta mika hannu gareta don bata ga dalilin mamakin da Asabe ta nuna ba. Ta rasa gane me yasa kowa yake ganin kamar bata son zumunci. Waye cikinsu yake zumuncin da ita?
"Bani nambarsa idan kwatancen ba zai samo ba"
Asabe sai ta sabi mayafi. Yau din gani take kamar duniya tana hajijiya da ita. Ba kuma don abin da ta gani a tattare da Qibdiyya ba kadai. Harda maganganun Munzali. Tunaninta ya kasa hasko mata inda zantukansa suka dosa.
Da yake mai hali ba ya fasawa suna samun adaidaita sahu Asabe sai cewa tayi "amma dai ke za ki biya min ko? Tunda dai ke zan raka."
Uwani ta hade girar sama "Munzalin ba danki bane? To nima ba kudi gareni ba. In ba za ki biya ba ki kwatanta min."
Asabe tayi azamar gyara zama tana kallon idanun Uwani "Idan baki nuna min halinki ba ai bana ce ke din tsatson Alh. Rabi'u bace."
Direban da yaji irin maganganunsu sai ya tsaya cak a tsakar titi.
"Hajiyoyi ku sauka don Allah kafin mu isa mu soma rigima daku akan kudi."
"Muje zan biya" cewar Uwani tana hararar Asabe da gefen ido.
"Wai ma me zaki je yi a gidan Munzali?"
"Abin da yasa kika biyoni maimakon yi min kwatance ne zai kaini."
Asabe ta hangame baki "kema ya fada miki?"
"Labe nayi muku duk da dai hargaginki ne ya sani zuwa ba wai nayi niyya bane." Uwani ta bata amsa kai tsaye.
"Nice nake hargagin? Lallai Uwani baki da mutumci. Koda yake ki ka yiwa gyatumarki ma wace ni?" Cewar Asabe tana kara kulewa.
Uwani bata kulata ba. Hankalinta ya yi gaba cikin tunanin nawa zata caji Munzali idan ta duba 'yarsa. Ko babu komai yadda ake labarin arzikinsa da son da yakewa 'yar dole ya mata hasafi. Kila ma ya hada da toshiyar baki.
***
Banda 'ya'yan cikinta da jikoki babu wanda ya yi saura a bangaren Baaba Mari. Jama'ar gidan manya suna asibitin da Mal. Inuwa ya jagoranci kai Mal. Sa'adu. Sauran kuwa musamman mata suna bangarensu a tsorace. Labari yazo musu cewa Baaba Mari da kanta ta aika kiran Mal Sa'adu. Gashi daga shigarsa bai fito da kafarsa ba sai gadon asibiti.
A asibitin kuwa tunda Mal. Sa'adu ya dan farfado ya soma cewa a kai shi gida yana son ganin Baaba Mari.
Wannan abu ya harzuka Deluwa musamman taga ko sannun da take ta ce masa bai amsa ba.
"Jama'a ku kawo min dauki. Mari ta fito da maitarta fili ta lashe kurwar Malam."
'Yan koranta da na Mal. Sa'adu suka dinga jinjina kai alamun amincewa. Shi kuwa wanda ake yi dominsa ransa sai ya baci. Abu ne da bai taba zato zai ji a ransa ba sai gashi a yau duk kalmar batanci da za a fada akan matar kaninsa sai yaji tamkar an loda masa kaya ne a kansa. Tuntuni ya fahimci illolin da take son nuna masa game da bara. Sai ya zabi ya take gaskiya saboda bata kai matsayin da zai dauki shawararta ba. Kuma sauran yaransu masu zuwa ai kowa ya dawo lafiya. Gabansa ya fadi da wani tunanin ya mamaye kwanyarsa. Shi ganau ne ba jiyau ba akan canjin da aka samu cikin 'ya'yansu da na makota.
Akwai uban da yake zuwa wurinsa yana yiwa dansa rubutu domin neman a raba shi da dauke dauke. Ya gallabi gidansu da makota babu damar mutum ya yi ajiya.
Wani kuma dan ya addabesu da haurawa matan aure cikin dare yana musu fyade.
Ga kwararren malamin tsibbu wanda matan aure suke tarawa arzikinsu akan mallakar miji da korar kishiya.
Suna da dan kwaya wanda har a kwata ana tsinto shi.
Akwai wanda ya koyo mugunta da tsantsar cin zali. Sau biyu yana zubarwa matarsa ciki da duka sannan ya karya mata cinya.
Wani ma dan damfara ya zama. Yana can Dubai ana damawa dashi
Wasu sun bata har yau babu su babu labarinsu.
A karshe akwai wadanda suka rasu sai dai a kawo gawa. Wani ma sai dai labari ya riski iyayensa bayan an binne shi.
Wadannan halaye hatta a makaratun boko na kwana ba baki bane saboda wahalar dake cikin tarbiyya. A can safe, rana, yamma da dare duka akwai ido akan yaran. Amma basu tsira ba. Idanun masu kular sun yiwa daliban kadan. Dalibai sama da arba'in a karkashin kulawar mutum daya na wani lokaci. Dole a sami masu kangarewa ba tare da sani ba. To ina ga makarantar allo wadda idon bai wuce na malami ba? Yaran kuma suna fita a duk lokutan cin abinci neman na kansu?
Duk da haka akwai wadanda suka yi dacen samun alkhairi daga zuwa karatu. 'DACE suka yi' Mal. Sa'adu ya tunatar da kansa. Irin dacen da wadanda suka fadawa halaka basu yi ba. Karatu ba zai taba tafiya babu tarbiyya ba. Tarbiyya kuwa tana samun kwakkwaran tubali ne a inda ake bayar da kulawa. Ita kuwa kulawa sai an jure an daure domin bayar da tarbiyar akwai wuya. Zamanin baya ido kadai d'a zai hada da mahaifiyarsa ya fahimci sakon dake cikinsa kuma ya yi aiki dashi. Yanzu kuwa sai ka zare idon shi ma ya bude maka nasa kirikiri yana dariya. Ka dake shi cikin sakan talatin ya manta ya sake maimaita laifin. Akwai wuya...ke uwa kina yi ma ya aka kare balle an kai dan nesa babu mai kwabarsa.
Mari ta ce ba za ta yafe masa ba.
Abbati ya zama dan luwadi...Wa Iyazu Billah.
Da me zai ji? Tsatson gidansu da yake alfahari da kyawunsa shi ne aka sami reshe guda ya lalace. Bayan sadaukar da rayuwarsa wurin ganin gidansu ya cigaba da amsa sunan gidan Malamai yanzu wannan masifa ta bullo. Zuciyarsa bata son karba amma kwakwalwarsa ta san gaskiya. Idan ma yaki neman gyara shi ne babban mai kwana ciki. Ba don ya so ba ya yiwa Deluwa magana akan kalamanta.
"Ba zan lamunci wannan shirmen ba Deluwa. Idan ba za ki iya kama bakinki daga barin aibata Mari ba ki wuce gida.
Kirji ta dafe ba shiri kamar tana gudun faduwarsa. Ta dube shi idanu a waje.
"Malam Mari ka ke karewa? Mari dai wadda muke raba dare muna kwashewa albarka ni da kai? Kaiiii..." Ta fada da karfi tana girgiza kai "Yasin da wata a kasa. Mari ta karawa bokanta kudi aiki ya ci."
Mal. Sa'adu da ya san shiru sosai yake bukata domin samun nutsuwar tunani da neman mafita tamke fuska ya yi. Bai bata damar roko ba ya ce lallai ta koma gida baya son zamanta a asibitin. Bata yi masa musu ba ta tafi gidan. Amma tana zuwa dakin Baaba Mari ta nufa tana danna ashariya.
***
Yamma tayi, gari ya soma duhun da dakuna suke bukatar haske. Lokacin da Asabe da Uwani suka yi sallama a falon gidan Munzali basa ganin kofofi da matattalar dake wurin. Ko ina dund'um an saki labulaye. Kwada sallama suka dinga yi da karfi tunda Maigadi ya tabbatar musu cewa ya shigo sannan ga motar da ya fita da ita a wurin parking. Uwani ta so shagala da kallon tsala tsalan motocin dake zube a wurin. Ga gidajen daga waje ma sun hadu. Tsarin fuskantar juna da suke yi dana Abbati ya sake burgeta.
Shigowar Kande ce ta kawo karshen sallamar tasu. Da yake ta san Asabe sai ta gaishesu da girmamawa.
"Alhamdulillahi kun zo Hajiya. Yanzu nake fakon idan aka yi Magriba Alh. Munzali bai fito ba zan taho gidan naki."
"Me ya faru kuma?" Cewar Asabe da saurinta.
Kande ta labarta musu yanayin da Munzali ya shigo gidan yana harhada hanya. Da ganinsa baya cikin nutsuwa ko kadan. Qibdiyya tana kafadarsa tayi bacci. Da ta nemi karbarta har wata tsawa ya daka mata. Dole taja baya ta zuba masa ido. Hawaye ne tabbas taga saukowarsu daga idanunsa. Sai dai kafin ta gama janyo tunanin da ya dace tayi, ya haye sama sai karar buga kofa taji.
"Ki hau ki kira min shi da Qibdiyyan" inji Uwani ga Asabe tana ajiye dan akwatin tafi da gidanka na kayan asibiti.
Hantar cikinta sai da ta dan kada don bata manta maganganunsa na dazu ba.
"Ban gane in hau ba? Don rashin tausayi tsofai-tsofai dani zaki sani hawan bene."
Uwani ta tabe baki. Abin kirki tazo yi amma halinta kam ya zanu akan dutse.
"Gidan danki ne fa kuma ni ban taba zuwa ba. Ke ya dace ki hau."
"Sai an magana ku dinga cewa ubanku daya. Da su Maimuna ne ai ba za ki ce yau kika fara..."
Sauran maganar makalewa tayi don tuni Uwani ta kusa kure benen.
Kankanin lokaci ya sadata da wani katafaren falo wanda yake cike da ababen more rayuwa. Kofofin dake cikinsa ta dinga kallo tana neman kofar dakinsa. Cikin sa a sai ta hango takalmin Qibdiyya a bakin kofar daya daga ciki. Duk yadda aka yi nan suke. Bata ji ko dar ba don dakakkiyar zuciya gareta ta karasa kofar dakin tana kwankwasawa gami da yin sallama.
Munzali yana zaune a gaban gadonsa inda ya shimfide Qibdiyya ya hada kai da gwiwa yaji sallamarta. Yayi matukar mamaki duk da ya san taji komai bayan haduwarsu ta dazu. Bai motsa daga inda yake ba kawai ya dago kai.
"Shigo."
***
I just published "34" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1095387462?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=Y6Whd7vibxZO3ov2%2FPsLYwHTGqHbwm%2FcSizoY4fzcwOV0cAQganfcuU6IofLueJEMdtJpryQscJyFE6EhHul9y%2FCQlLqNPPExesSATjzSneThshj7TIDLT4mdnC%2FGc82
UWA UWACE...34
Batul Mamman💖
Yan uwa muna barar adduarku ga mahaifin 'yar uwa Massouda Moulaye. Wanda Allah Ya yiwa rasuwa ranar larabar da ta gabata. Allah Ya jikanshi Ya gafarta masa. Allah Ya kyautata makwancinsa. Ya bamu ikon tarar dasu cikin aminci. Amin
******
Wata sallamar tayi ta kutsa kai cikin dakin da sanyinsa ya busa har kasusuwanta. A take taji kwarin gwiwarta ya dadu. Sai da ta shiga daga inda yake zaune ya danna remote kwayayen fitilu uku suka kama. Haske ya gauraye dakin da zaka rantse ba namiji ke gyara kayansa ba. Komai tsaf ga kamshi ga kyau.
"Ke da waye?" Ya tambayeta yayinda ta kai ido inda Qibdiyya take bacci.
"Asabe. Tana kasa."
Shiru suka yi na dan lokaci suna yiwa juna kallon kallo. Ita tana ganin wautarta na rashin kusantar kanin nata tun da dewa. Shi kuwa abubuwa da dama ne suka cunkushe kirjinsa. Zazzabi yake ji da matsanancin ciwon kai.
"Na san abin da ya kawoki Uwani zan kuma baki domin ki taimaki Qibdiyya. Sai dai abu daya ne ba zan miki ba..."
Idanunsu suka sarke da juna. Magana yake yi mata ba da wasa ba. Bata jin ma banda gaisuwa sun taba yin wata doguwar magana dashi banda yanzu. Idanun nasa sai suka zame mata tamkar masu wadanda ke huda sassan jikinta. Gabadaya sai ta tsargu ta kasa sakewa. Don ma tana da baki ne ta ce,
"Ban gane ka san me ya kawoni ba? Daga zuwa taimako sai ka soma fada min magana saboda raini."
Dan murmushi ya yi cikin son nuna burgarta bata je masa ko ina ba. Ya dora maganarsa ba tare da ya damu da bata amsar maganarta ba.
"Kamar yadda na ce zan biya ki dubata amma ko kwandala ba zan baki ba domin ki bar maganar nan a matsayin sirri."
"Me yasa?" Ta fara cewa tana zaro ido sai kuma tayi saurin gyara zancen "yaushe na ce maka idan baka biya ba zan tona maka asiri?"
Mikewa ya yi kansa na cigaba da sarawa ya matso da Qibdiyya bakin gadon yana cewa,
"Baki fi kowa so da damuwa dani ba Uwani amma sai gaki ke kadai a gidana a wannan lokacin. Ina Innayo ina su Zara? Me yasa baki fada musu kun fito tare ba?"
Hade rai tayi na borin kunya ta saka safar hannu.
"Saboda irin wannan abin ba abu bane da ake so ayi ta yamadidi dashi ba."
Wani dan murmushi ya yi mai sauti
"Qibdiyya dai 'yarki ce, tonon asirinta naki ne. Kuma magana dole zata fito idan aka tsinci tsinannen da ya yi mata wannan abin da rai ko babu."
Fita ya yi yaja kofar dakin ya barta da tunanin kalamansa. Taji zafin maganganun duk da gaskiya ce ziryan bai mata sharri ba.
Qibdiyyan ta tasa a hankali don kada yarinyar ta firgita idan taji ana tabata cikin bacci.
Cikin yan uwan mahaifinta Uwani tana sahun gaba na wadanda bata saba dasu ba kuma suke bata tsoro. A firgice take kallonta amma Uwani bata fahimta ba saboda sabgar yara ba tata bace.
A hankali dai take yi mata magana domin ta kwantar da hankalinta.
"Yi kwanciyarki dubaki zanyi."
Tana kai hannu zata cire mata pant, Qibdiyya ta runtse ido yadda ta yiwa Asabe.
"Kema hannu zaki saka min a nan? Idan an saka wannan safar ba zai min zafi ba?"
Hannuwan Uwani sai suka fara rawa ta kasa cire pant din. Wannan wadanne irin maganganu ne suke fita daga bakin karamar yarinya irin wannan?
Tana can tana tunani caraf idanun Qibdiyya akan alluran dake cikin first aid box din. Jikinta ya kama rawa ta soma kuka.
Munzali yana jin kukan ya bude kofar. Sai dai yaci karo da abinda yasa shi jin ina ma bai zo duniya ba. Qibdiyya ce take cewa,
"Don Allah kada kiyi min allura wallahi ba zan fadawa Daddy ba. Abin nan ne bana so ki tura min da karfi yana min ciwo kinji" kallon da taga tana yi mata ta kasa cewa uffan ne ya bata damar tashi zaune don ko kadan bata so ayi mata "Kwanta ni inyi miki. Nima na iya."
Tsigar jikinsa har tashi take yaji kansa kamar k'wari suna yawo. Da dan allinsa ya nunata yana daga murya ba tare da ya sani ba.
"Me kika iya? Me zaki yi? Qibidiyya waye ya koya miki wannan abin?"
Baiwar Allah a gigice ta tashi idanunta suna zubar da hawaye. Idan da abin da yafi komai daga mata hankali bai wuce shi ko Abbati su sani ba. Uncle Daddy alkawarin kisa ya yi musu. Zai yanka mata su irin yadda aka yi a bidiyon da ya nuna mata.
A zafafe Munzali ya sake cewa "nace waye ya koya miki? Da wa kuke yi? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ya rike kansa "Uwani kin ji abin da tace kuwa?"
Qibdiyya dai ba abin da take sai kuka. Haka ma Munzali wanda ya dubkule hannu yana dukan bango. Yatsunsa har kara suke amma bai daina ba. Uwani kanta ta kidime. Sai a lokacin taji wani girma ya sauko mata. Idan bata tari abin da yake faruwa ba da uban da 'yarsa duka zasu shiga wani hali. Hannunta ta kama ta zaunar da ita a kan cinyarta.
"Daina kuka Qibdiyya ki fada min waye yake saka miki hannu a cikin pant."
Cikin faduwar gaba Qibdiyya ta kalli Daddy dinta ta girgiza kai.
Wata irin tsawa ya yi mata wadda har Uwanin sai da taji cikinta ya kada. Kaiwa da kawowa kawai yake a dakin jikinsa na tsuma. So yake ya samu wani abu ya matse ko ya yi ta duka har sai kuzarinsa ya kare.
A lokacin azal ta fada kan wanda bai ji ba bai gani ba. Hakika Allah ba azzalumin Sarki bane. Sai dai kuma Yana nuna ishara ko aya akan wasu domin ya zama gargadi ga majibintansu.
"Uncle Lilu"
Amon muryarta ya fito lokaci guda da kiran sallan da Ladanin masallacin kusa dasu ya soma na Magariba.
Yawun bakinsa kafewa ya yi ya kasa hada harufan da zai kira sunan Lilu. Ga wani abu mai daci yana bin busasshen wuyansa yana saukar masa a ciki. Zuciyarsa kuwa tamkar farantin tangaran haka yaji tayi rugu rugu.
A karamar kwakwalwar Mariyatul Qibdiyya kuwa, tayi tunanin kama sunan Lilu tsira ne gareta da iyayenta. Shi yana da kirki ba zai yanka su ba. Uncle Daddy da yace yana ganinta duk inda take yanzu ba zai mata komai ba.
(Ba da niyya Munzali ya taka muhimmiyar rawa wurin janyowa Lilu laifin da ba nasa ba. Yarinya ce wadda aka tsorata tun lokacin da ake batawa rayuwa. Yanzu kuma an sake firgita ta da fada da tsawa. Wannan kadai ya isheta dalilin yin shiru ko ta kira sunan wani daban. Da wane mataki aka fi saurin samun bayyanar gaskiya a irin wannan yanayin da ba a fata? Rarrashi da laluma musamman ga kananun yara. Idan sun kama suna iyaye a bincika a sake bincikawa. Yara ma suna karya! Wani domin kwatar kai, wani kuma domin maslahar da yake ganin canja gaskiyar zai kawo.)
***
Washegari bakwai a hanya ta yiwa iyalan Alh. Tahir. Ana sallame sallar Asuba suka shirya. Lilu da Mardiyya ma ko wanka basu yi ba saboda iyayen sun matsu su tafi. Awa biyu ta kaisu gida. Shi Alh. Tahir kai tsaye office ya wuce. Yana shiga ya shiga dube dube yana daga abubuwa. Wannan wayar da yake kiran 'yan matansa yake nema ido rufe. Fatansa kada ta fada hannun da asirinsa zai tono. Da ya gaji da neman sai ya kira direbansa da masinja.
Shi direban umarnin kai mota wanki ya bashi. Ya ce a cire duka kujerun a duba masa wayar. Masinja kuma ya kira masu shara a fitar da komai na cikin office din a duba masa. Amma fa koda ya bayar da wannan aikin yana da tabbaci dari bisa dari bai barta a office ba. Motar yafi zargi. Kawai dai ya yi amfani da karin maganar