Showing 135001 words to 138000 words out of 242549 words
kamaku shi ne na zauna ina ta fifita don ku samu da wuri."
Wasa take son shigarwa tsakaninsu. Basu sace mata gwiwa ba kuwa suka dinga dariya suna cewa ko dai akwai sauran bebi a cikinta.
"Ku barta dani take tunda ni na ce a dora."
Zara sai idanu suka raina fata. Gabanta ya fadi. A tsorace ita dasu Mqimuna suka kalli Innayo ta fara cewa
"Wallahi, wallahi..."
Innayo sai tayi dariyar da ta bawa 'ya'yan nata mamaki.
"Lallai ma Zara. Ke ki tsokani 'yan uwanki amma ni ba zan tsokaneki ba?"
Ajiyar zuciya Zara ta sauke su Hasiya ma duk sai suka saki rai. Sun san yadda Innayo ta dauki zafi da ita. A gaban ido da baya duk suna bata hakuri da son ganin ta sakarwa Zara.
"Tsoron bata miki rai nake Innayo." Ta ce a sanyaye wanda ya soki zuciyar mahaifiyar da bata da tamkarta.
Harararta tayi cikin wasa ta ce "Ai kuwa dai ya soma baci tunda kin bar min jika da yunwa."
A gaggauce Zara ta gyara zama ta rungume 'yar a jikinta sosai. Ta kalli su Salima kowa murmushi yake mata. Innayo ta sake shayar da ita mamaki da ta ce,
"Komai ya wuce Zara ki daina saka damuwa a ranki. Allah shaida na yafe miki duniya da lahira. Rashin zuwan maigidanki da yara duk ba wani abu bane indai kin sami lafiya. Muna nan da yardar Allah zaki ganshi dasu."
Allah Sarki, Zara sai hawaye "na gode Innayo. Salima kuma ku yafe min. Don bakin halina yarinyar nan ko suna bai saka mata ba har yau."
"Allah Ya san sunan da Ya halittota dashi. Kada ki sake tambayarsa." Cewar Innayo ta sake sako wasa don ta kawar da damuwarsu "ni dai a dafa min masara in mayar da mugun yawu."
Kusan tare yaran nata da ita kanta suka saka dariya. A zuciyarta tana jin wani irin farinciki wanda yafi kudi da duk abin da kudi zai saya.
Dariyarsu ce ta kawo Asabe wadda take mamakin ko Alh. Rabi'u bai yi musu yadda ta ce ba. Zuwanta ya yi daidai da tambayar da Hasiya ta yiwa Innayo akan dalilinta na cewa a dafa masara bayan abin da babansu ya yi mata. Su duka sun kasa gane dalilin rashin nuna fushinta da abin da ya yi. Asabe ta kasa kunne da kyau domin kwasar gulma ta kara hada fada.
"Allah ne fa Ya ce kada mu zata don mun ce munyi imani ba zai jarabcemu game da 'ya'ya da dukiyoyinmu ba. Da rayuwa tana tafiya da burin dan Adam da babu wanda zai yi kuka da komai. To amma yawan jarabawa da hakuri da ita karin daraja ne a aljannah. Tunda Allah bai bani kudin yin sadaka ba ba zan butulce don Ya dora min wannan rayuwa ba."
Hawaye ta sanya 'ya'yan nata. Suka kara ganin kima da darajar mahaifiyarsu. Ana haka Salihi ya iso. Bai jira isowar Uwani ba ya ce da Innayo idan ta zo ta ce mata ta zauna.
Abin da ya fadi ya tabata sai dai dama ta san dole akwai ranar da tura zata kai bango. Ya yi hakuri na ban mamaki a zamansa da Uwani.
"Wani abin ta sake yi?"
Murmushin bacin rai ya yi "ta dai zauna. Idan zuciyata ta sanyaya zan zo ki mana hukunci. Mubashir zai kawo mata kayanta."
Bata taba ganin suruki irin Salihi ba. Nauyinsa ta kara ji. Yana da iyaye da 'yan uwa amma har kullum bai gazawa wurin kokarin rufa asirin matarsa. Ta rasa wace irin zuciya ce a kirjinsa mai matukar hakuri da zurfin tunani. Ba shi ta haifa ba amma ya iya zuwa debe mata kewar 'yarta yana kuma bata hakuri akan halayyarta. Yau kam ta tabbatar Uwani bata yi masa da wasa ba wajen bata masa rai. Za ta bashi hakuri ya ce don Allah ta bari. Uwani ce mai laifi don ta haifeta ba za ta dauki nauyin laifinta ba. Bai jima da fita ba uwar gayyar ta iso.
Innayo taji kamar ta rufeta da duka akan amsar da ta bayar bayan ta fada mata abin da Salihi ya ce.
"Ba zan yi mamakin duk wani abu da zai yi min ba yanzu tunda ya auro matsiya... "
"Rufe min baki shashashar banza. Kina girma halinki yana kara tabarbarewa. Akanki ni ba sai dai na ce banga ranar boko ba? Ke kadai kika same shi mai yawa a cikin 'yan uwanki amma banda hauka bai kareki da komai ba."
Haukan ta nuna ziryan inda ta kada baki tana hurawa kannenta hanci ta ce "ai kuwa boko ya min komai Innayo. Na sayi mota, nayi gini sannan na biya kujerar Hajji."
'Ikon Allah' Innayo ta sami kanta da cewa cikin wani irin yanayi a zuciyarta. Bata cikin iyaye masu saka ido akan kudin 'ya'yansu amma bata jin duk hakurinta zata so ace bata san cigaban yaranta ba. Babu abu daya da Uwani ta lissafa wanda zata yi mata shamaki da mallakarsa. To me ya hanata fada mata ko addua ta tayata da fatan alkhairi. Abin bai yi mata dadi ba ko kadan. Murmushin fatar baki tayi mata tare da fadin,
"Sai ki wuce gidan naki kafin mijin naki ya sakko."
"KNUPDA sun kwace" Uwani ta ce tana tura baki kafin kuma cikin sauri ta dora da yi musu bayanin cewa zata je a daidaita don kada suyi mata dariya.
Dariyar da ta guda ita Innayo tayi.
***
Bayan tafiyar kimanin awa daya da rabi sai ga wayar Suhaib. Munzali ya samu a lokacin. Ya jima yana kiran layukansu shi da Abbati amma duka sun ki shiga saboda raunin service na hanya. Da ya same su kuma aka rasa mai daukar wayar cikin su biyun. Gara ma Munzali tuki yake. Abbati kuwa ragowar karfin halinsa ne yaji yana neman kufce masa da yaga sunan mai kiran. Kira hudu ya musu a jere ta wayar kowa sau bibbiyu sannan ya hakura.
A gidan bikin iyayen nasu duk sun damu saboda an san cewa wayar da Abbati ya amsa ce ta tayar musu da hankali har suka tafi.
Yayinda Mardiyya take ta kiran Munzali saboda halin da ta shiga na taya shi jimamin damuwar da ake tsammanin suna da ita, Farha bata kira Abbati ba ko sau daya. Ko ma mene ne ta fahimci gagarumi ne tunda ya bar gidan ba tare da ya yiwa iyayensu da suke tare sallama ba. Za ta jira zuwa gobe idan ba a ji daga garesu ba ta bangarenta ko 'yan uwanta kafin ta kira. Addu'a kawai ta zauna tana yi don bikin ya fice mata a kai. Da Suhaib ya ce wayoyinsu na shiga ba a amsawa sai ta tura masa text.
(Allah baya dorawa bawa abin da yafi karfinsa. Wannan alkawari ne daga Mamallakin dukkan halitta. Ina fata Allah Ya kawo muku saukin abin da yake gabanku. Luv, Ya Farha)
Karar shigowar sakon ya kada duk wani abu dake yawo a jikin Abbati. Fargabar barnar da yake tunanin Shazali ya yi masa ta shafe komai a kwakwalwarsa. Wayar tana aljihunsa amma jikinsa ya bashi daga ina sakon yake. Jiki a sake ya dauki wayar ya bude sakon. Numfashi kawai ya dinga ja yana saukewa da sauri da sauri.
"Shazali ne? Me ya ce?"
Munzali ya tambaye shi da yaga yadda ya kara birkicewa.
"Farha ce."
"Nima tun dazu Mardiyya take kirana."
Shiru suka yi na lokaci har suka isa Gumel. Fadan irin tashin hankali da tsoron da suka sami kawunansu a tsukin lokacin ma bata baki ne. Gidan mai suka shiga suka kara mai tare da yin sallah. Sun kusa barin garin Abbati ya ce da Munzali ya yi parking. Gefe ya gangara ya fuskanci Abbati ba tare da kashe motar ba.
Yana tsayawa Abbati ya kama kofar ya bude. Kafarsa daya a waje ya juyo ya kalli Munzali mai binsa da ido da alamun tambaya.
"Ka koma Kano zan wuce ni kadai."
A razane Munzali ya dube shi maganar tana dukansa ta ko ina.
"Me ka ke nufi?"
Kadaici yake bukata? Tsoron haduwarsa da Baaba Mari? Tabbacin rasa Farha na har abada? Hasashen girman tashin hankalin da zai wanzu a gida da garinsu? Babu abin da ahi kadai bai isa ya haukata tunanin shi ba. Sai gashi su duka da ma wasu suna jiransa. Bai san ta ina zai fara ba, amma gara ko meye ya tunkareshi shi kadai tukunna.
"Don Allah Munzali ka koma. Tunda kaji na ce ka barni ni kadai ka san bani da zabi ne."
Yawu mai daci ne ya wuce ta makoshin Munzali. Ko ba a fada ba ya san cewa Abbati ya gama sarewa da komai. Yau din rana ce da za ta zama mafarin wani abu da bashi da suna a rayuwarsu. Kuma har ga Allah Yafi kowa sanin cewa tonowar asirin Abbati ba kamar nasa bane. Abbati ya tashi cikin dangi da iyaye. Duk wani rikicin cikin gida bai raba kan iyayensa ba. Shi kuwa ko yau iyayensa suka ji bashi da abin da ya wuce dora musu alhakin komai. Darajar Qibdiyya da kuma 'yan uwansa da ya fara sabunta zumunci dasu ne ababen dubawa. Sai kuma masoyiyarsa Mardiyya wadda ko kadan baya son abin da zai shata layi tsakaninsu. Mafi girman damuwarsa kuwa tana tattare da bakincikin shi ya batawa Abbati rayuwa. Numfasawa ya yi bayan ya dan yi nazari.
"Kana nufin za ka je ka tonawa kanka asiri ne ni kuma na zauna? Waye silar shigarka wannan rayuwa."
Hannu Abbati ya nuna masa "kada muje nan wajen."
Rai ya soma baci Munzali ya ce "to ina zamu je? Ba ni bane? Ba don ka hadu dani ba da yanzu kana rayuwarka cikin kwanciyar hankali."
Kafin ya gama maganar idanunsa sun yi jajir. Zuciyarsa a kuntacce take yana jin yadda take zafi. Ya sake bude baki zai yi magana Abbati ya dakatar dashi da cewa,
"Don Allah kayi tuki a hankali."
Duk yadda Munzali yake son yi masa musu haka ya hakura ya tafi bayan shigar Abbatin motar haya.
***
Mummunan faduwar gaba ne ya sami Baaba Mari har ta saki butar hannunta da taji muryar yaran gidan suna yiwa Abbati barka da zuwa. Sake dibar ruwa tayi cikin rawar jiki duk tana zuzzubarwa ma ta kuma cika botar ta zauna za tayi alwalar Isha'i. Jikinta har wani karkawa yake saboda tashin hankali. Tunda ya iya biyo dare ya taho garin a yau da basu kwana da shirin zuwansa ba ta san babu lafiya. Tabbas babu ko tantama Abbatinta bashi da gaskiya. Da babu wata a kasa tun dazu zai kirata ya karyata zantukan da taji sunyi a waya da Shazali. A yadda zuciyarta take dakan lugude a kirjinta kuwa a lokacin ko me ya fada a waya zata amince. Yardar ta zame mata wajibi ko don kada bakincikin jin gaskiya ya kwantar da ita.
Shi kuwa a bakin kofar da zata sada shi da sashen mahaifinsa ya tsaya tun shigowarsa. Idanunsa da suke cike da kwalla suka sauka akan Baaba Mari tana alwala. Ya gama karanta da fahimtar duk wani motsinta. A firgice take! Alwala take yi amma sam hankalinta baya jikinta. Shafar kai kadai wadda da wuya ake kuskure adadinta saboda sau daya ce sai da tayi biyar akan idonsa. Ya lura duk gabar da ta kama sai ta dawo hayyacinta take tafiya ta gabanta. Bai san kuka yake ba sai da yaji ruwan da zafinsa yafi wuta a zuciyarsa yana bin kumatunsa. Asalin kunci da damuwa ne suka rufe shi ya juya a hankali ya fita daga gidan.
Kofar gidansa yaje tun daga dan nesa yake hango hasken tocilan din wayoyi guda uku a wurin. Bai yi mamakin ganin 'Yashshafa da wasu 'yan mata sa'o'inta biyu ba. Su ma duka kannensa ne kowcce da tsintsiya a hannu.
"Gwaggo Deluwa ce ta aikomu muyi maka shara kafin a kawo abinci."
Guda cikinsu ta fada bayan ta gaishe shi. Mukullin kawai ya mika musu ya juya masallaci. 'Yashshafa bata manta gargadin Deluwa ba tayi saurin cewa a dawo lafiya.
"Ki kwantar da kai ki kyautata masa domin mu sami biyan bukata."
Cewar Deluwa mintuna kalilan da sallamar Abbati cikin gidan.
'Yashshafa tana dirzar kafarta da dutsen goge kaushi ta daga kai tana zumburo baki.
"To wai ni Inna haka za kiyi ta min ne? Yau ki ce in daina sakar masa fuska gobe in saki? Yaushe zai soni a haka?"
Deluwa ta murmusa tana wani jijjiga kai
"Yaro man kaza. Banda abin ki 'Yashshafa idan baki kwantar da kan ba ta yaya zamu samu ya baki lambar shi Sha'aib din cikin sauki?"
Cigaba da dirzar kafarta tayi cikin yanayin ko in kula ta ce "Inna ki bar batunsa don a ranar ko kallo ban ishe shi ba."
Harara mai kyau ta samu kuwa sannan cikin fushi Deluwa ta ce mata,
"Ta yaya zaki san me yake faruwa a lokacin nan kina can kina kukan shanu? Kar ma ki zata dominki na damu. Tausayin yaron da mutumcin uwar tasa ne yasa nake ta kokari. Ni kadai na san me na gano a kwayar idanunsa game dake. Jikina ya bani suna ta nemanki ta wurin Abbati. Amma don mugunta yaki hadaku. Su kuma 'yan birni ba wuya ciwon zuciya ya kwantar dasu saboda da gaske suke soyayya."
Tabe baki 'Yashshafa tayi bayan tafiyarsa tabi 'yan uwanta cikin gidan. Daga Abbatin har Suhaib ta san bata gabansu. Ita din ma ta turesu daga gabanta. Kwanakin nan mutum daya take yawan tunawa tana jin ina ma zasu hadu ta rama dariyar da ya yi mata.
Da Abbati ya dawo bai koma gidansu ba. A waje ya gaisa da sauran iyayensa maza ya ce kansa ne yake ciwo zai kwanta. Harda nanatawa Mal. Inuwa ya sanar da Baaba bashi da lafiya kada ta ji shi shiru. Nan kuwa karfin gwiwar hada ido da ita a daren ne bashi dashi. Abinci kala biyu ya gani a falonsa. Wanda ya tabbata daga wurin Baaba Mari aka turo ya tsakura kadan ya yi shirin bacci. Sun dan taba shawarwari da Munzali a waya sannan ya kwanta.
***
Tafiyarsu Munzali ta gaggawa ta dagawa iyaye da 'yan uwan Alh Tahir wadanda Allah Yasa suka gamu dasu jiya hankali. Saboda haka suka dinga kiransa ana tambayar ko yaji daga garesu. Shi ma ya damu haka Mami Khadija da Mama Nasima. Wuraren tara na safe yaci sa'a Munzali ya dauki waya.
I just published "29" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1069890147?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=HEUJmsOYglY3kZgRbXSElahoP5O7Gz9YEvViSnSSKsmjyDvaje5RtEr7HvxDXafaYphpjZJAgd0Hp1y2h4lNwKgQgH4AuufTWYBhuc3haYtNjFvXB3eIrX9CBO7iJXay
UWA UWACE...29
Batul Mamman💖
Tafiyarsu Munzali ta gaggawa ta dagawa iyaye da 'yan uwan Alh Tahir wadanda Allah Yasa suka gamu dasu jiya hankali. Saboda haka suka dinga kiran Alhajin ana tambayar ko yaji daga garesu. Shi ma ya damu haka Mami Khadija da Mama Nasima. Wuraren tara na safe yaci sa'a Munzali ya dauki waya. Munzalin kwanan zaune yayi inda yake ta tufka da warwara. An wayi gari kansa yana wani irin ciwo saboda rashin bacci da alhinin me zai faru tsakanin Abbati da Baaba Mari. Irin wannan lokacin sallah da kankantar da kai a gaban Allah SWT shi ne yafi dacewa da bawa. Sai aka yi rashin sa a munin dabi'ar da suka rayu cikinta ya danne tunaninsu daga shi har Abbati. Asalin kalmar da bature yake kira despire ita ce ta wanzu a kawunansu. Suna jin tamkar basu da sauran rabo. A duniyar sai sun ji kunya sannan a lahira da wuya su sami dacewa da rahama. Wannan shi ne tunanin kowannensu. Shi ne fargabar da suke da yakinin ganin ranar faruwarsa.
Da farko bai yi niyar amsa wayar kowa ba sai ta Abbati. Amma karar kiran da ya shigo tamkar ana kada kararrawa a cikin kansa ya saka shi mika hannu ya daukota a gefensa. Katse kiran yaso yi tunda bai san nambar ba, bisa kuskure sai ya zamana ya amsa ne.
"Alhamdulillahi ya dauka"
Shi ne abin da Munzali yaji an fada daga dayan bangaren. Bai sha wahalar gane mamallakin muryar ba. Hakan ya tilasta masa tattaro duk wata nutsuwarsa ya gyara murya suka gaisa sosai.
"Me ya faru jiya Munzali? Kun tafi kun barmu da fargaba. Ina shi Abbatin?"
Murmushin fatar baki Munzali ya yi da ya hasko tonuwar asirinsu da irin yadda zasu wulakanta bayan rabuwa da masoyansu. Karya ce kadai rufin asirinsu kuma ita ya gilla kamar yadda suka saba domin kare kai.
"Ku yi hakuri. Wan Baban Abbati ne aka kira babu lafiya ...."
Alh. Tahir ya katse shi tun kafin ya gama da cewa "Subhanallahi, ciwon ya yi tsanani kenan duba da yadda ku ka tafi."
"Eh suma yake yi kamar ba zai tashi ba."
"Kuna ina ne yanzu?"
Munzali sai da ya dauke wuta na wucin gadi kafin ya iya bayar da gamsashiyar amsa. A yadda suke dai bai kamata ya ce Abbati ne kadai ya tafi ba. Sannan idan ya yi gaggawar binsa yanzu bai san me hakan zai janyo ba. A takaice ma dai dole ya zauna domin ya dakile yunkurin da yake hasashen Alh. Tahir ya fara.
"Muna Gumel nima aka kirani Qibdiyya ta fadi ana zaton karaya ce." (Da safe ranar ta fadi amma ko kuka bata yi ba)
"Sannunku kaji. Ya jikin nasu?"
"Kawu Sa'idu ya fara samun sauki. Qibdiyya kuwa mai kula da ita ce ta firgita. Buguwa ce kawai."
Nutsuwar da Alh. Tahir ya rasa tun jiya ce ta dawo masa. Ya sake jajantawa Munzalin sannan suka yi sallama.
Munzali har ya fara jin sanyi a ransa na rabuwa dashi lafiya sai ya sake kira. Bayan ya fada musu me yake faruwa ne Mama Nasima ta ce ayi musu kwatance zasu je dubiya. Ita a nufinta taje har gidan Munzali ta kara gane ina zata kai Mardiyya. Alh Tahir bai ki ba saboda shi ma baya son wadannan zaratan matasa su kufcewa zuri'arsa. Tunda Allah Yasa suna Kanon gara ma da aka yi haka. Sai suje domin a karfafa magana.
"Amma ya dace muje gidansa? Babu mace fa a ciki. Idan akwai ma kuma ai bai kyauta iyayen wadda yake son aure suje duba mata 'ya ba."
Mami Khadija ce taja hankulansu kan kuskuren zuwa gidansa. Mama Nasima sai ta hau borin kunya.
"Mutum kullum burinsa ya nuna yafi mu sani da iyawa. Da an fimu din kuma da bamu zo gidan ba. Ki kwantar da hankalinki bance sai kinje ba. Yanzu nake shirin cewa a fada masa ya kaita gidan iyayensa sai muje can."
Mami Khadija sai ta girgiza kai kawai. Ba don tayi magana ba tsaf gidansa zasu je. Yanzu kuwa ko don a bata kunya dole a canja salo.
Ba bata lokaci Alh. Tahir ya kuma kiransa ya fada masa shawararsu. Suna gama wayar Munzali ya tashi a gaggauce ya fada bandaki. Cikin mintuna biyar har kaya ya