Showing 3001 words to 6000 words out of 242549 words

Chapter 2 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3339

cije lebe jin kafarta tana rikewa ta zaga bayan gidan tana kwalawa Nasima kira.

Nasima tayi matukar razana da jin muryar uwardakin nata a kurkusa da inda take kwance. Hannuwan mutumin da suke bin jikinta ta doke da sauri tana mikewa tsaye. A razane shi ma ya dauki jakar da ya dawo da ita daga office yana gyara zaman necktie dinsa. Gaba ya yi yana yiwa Nasima inkiya da ta dakata kada ta biyo bayansa. Bata bari ya tafi ba ta bishi da sauri ta ware hannuwanta a gabansa. Mamakin karfin halinta ya yi a wannan yanayin da matarsa take gab da kamasu ya yi saurin zaro kudin da ya san su take nufi ya dora mata.

"Yaya Tahir?" Khadija ta kira shi da mamakin rashin sanin dawowarsa.

Da saurinsa ya tareta ya kama fadan borin kunya. "Me ya fito dake kina jan kafa ke da likita ya ce kina bukatar absolute bed rest? Meye amfanin Nasima a gidan da ba zaki huta ba?"

Murmushi tayi tana yabon irin kulawar da yake bata a ranta.
"Nasima nazo kira."

Hararar Nasiman ya yi "idan kin gaji da aikin ne sai a nemi wata."

Hakuri ta bawa Khadija kai a kasa cikin sassanyar muryarta ta makiran yara. Duka duka da kadan ta haura shekara sha shida, amma fitinarta a boye tafi ta wata 'yar arba'in din. Tamkar hawainiya haka ta kware wurin boye halayenta. Sumumu kasau, macijin sari ka noke shi ne tashenta a wurin saurayinta na farko wani Alhaji a kasan layin.

Sai da suka shiga daki yake cewa Khadija wai yau yaji wa'azin da ake cewa kayi kyauta da dama hagu ba sai ta sani ba.

"Shi ne fa ina shigowa na hango wannan kazamar 'yar aikin taki tayi baya. Da yake kanta kamar dusa aka zuba maimakon kwakwalwa inata kiranta na bata sadaka bata ji ba. Ni kuma na riga nayi niyar yi da fatan Allah Ya saukeki lafiya. Shi yasa na bita bayan."

Kwalla taji ta sauko mata ta farinciki. Tana alfahari da mijinta domin ta san sai an tona ake samun irinsa. A da kam ta wahala akan 'yan matansa amma da dabara ya nuna mata ya bari. Baya son ta wahala kuma baya son damuwarta. Tana cewa wash zai bar duk abinda yake yi yazo gareta. Ga saurin bata hakuri idan ya bata mata rai. Kulawa sosai yake bata duk da mai aikin da ta dauko 'yar makotansu tun tana laulayi. Da zarar ya dawo gida bayan yara sun tafi Islamiyya yake turata daki tayi bacci. Wai nan so yake ta huta da kyau kafin su dawo. A wannan lokacin yake samun kebewa da Nasima ba tare da saninta ba. Nuna mata yake ya tsani yarinyar domin kada ya bar kofar zargi a tsakaninsu.

"Nagode Yayana amma don Allah ka rage hantarar Nasima. Kaga amana take a hannunmu."

Ruwa ya tashi watsawa jikinsa ya nuna mata kamar baya son zancen. Yana bandaki shi kadai yake tsakin zuwanta bayan gidan dazu. Bin mata sana'arsa ce tun yana matashi. Khadija 'yar kanwar babansa ce aka hadasu wai ana ganin idan ya yi aure zai rage. Babu wanda ya bata zabi kawai aka ce ta auri dan uwanta don ya shiryu. Ya kuwa nuna musu shiriyar tasa kamar gaske saboda yana son Khadijan. Da yake kwararren dan duniya ne babu wanda ya san ya cigaba da harkokinsa a waje.

Dawowarsu unguwar nan abin nasa ya kara baci tunda ya ga Nasima komai ya kwance masa. A zahiri yake nuna mata kyama amma a badini tafi kowa. Ita ce kawai a gabansa kuma bashi da burin da ya wuce ganin lokutan da suke samun kebewa a gidan ko a wuraren da ya saba kai 'yan matansa.

Khadija bata san wainar da ake toyawa ba. Da zuciya daya take zaune da kowa. Gidansu Nasima a can kasan layinsu yake kuma sun fi kowa karamin karfi. Abinci a rana bai fi su ci sau daya ba idan an sami faraga. Shi ne fa ta nemi Nasima ta dinga tayata aiki suna biyanta karshen wata.

A ranar da daddare ta sake yi masa maganar dauko kanwarta ko tasa su tayata zama ko da zuwa tayi arba'in ne idan ta haihu.

"Na fada miki ba zuwansu ne bana so ba amma a gani na me zai hana ki dauko waccan yarinyar?" Ya ce da sigar laluma.

Dan jim tayi tana tunani kafin ta fada masa dalilinta na neman ta gida.
"Na fara tunanin sallamarta ne kawai." Gabansa ne ya fadi zai yi magana ta dora da cewa "ka san ko Lilu da yake dana muna fada akan rashin kunya balle Nasima. 'Yan kwanakin nan sai tayi zamanta a baya taki aikin. Idan na kirata a murya sai ka ji lafiya amma a fuska sai in ga kamar tana hararata."

Dariya ya kwashe da ita duk kuwa da fargabarsa ta cikas da korar Nasiman zai kawo masa.
"Shi yasa nifa bana sonta. Ke kuwa da anyi magana sai ki ce marainiya ce. To kema dai naga alama kin gaji da aikin ladan kenan."

"Ba gajiya nayi ba." Ta amsa masa ganin kamar yana ganin asarar kudi yake da biyanta bayan aikin nata babu yawa.
"Zan yiwa mamanta magana ta fara kwana. Idan ta cigaba da halinta sai mu rabu."

Zuciyarsa kamar an zuba ruwan sanyi don farinciki. Nasima tana gara shi a 'yar haduwarsu ta bayan gida. Minti biyar idan tayi sai ya biyata. Idan ta fara kwanan zai fi samun lokaci tare da ita.

Bayan ya tafi aiki washegari Khadija ta je gidansu Nasima da misalin shabiyun rana. Lokacin yara suna makaranta ta barota ita kadai tana wanke-wanke. Tarba ta girmamawa ta samu daga wurin mahaifiyar Nasima. Bayan sun gaisa ta fada mata abinda ya kawota.

Ladidi ta dan bata rai "haba Mamin Suhaib? Yanzu don kina son Nasima ta dinga kwana
har sai kin fito a wannan yanayin da kike? Ai cewa za ki yi kawai ta fada min magana ta zauna."

Dan murmushi Khadija tayi tare da girgiza kai. Don tana taimaka musu ba shi ne dalilin da zai sa su juyata son rai ba.
"A'a gara dai na zo da kaina. Ban fada mata ba ma na ce sai naji amsarki."

"Allah Sarki Mamin Suhaib. Yasin shi yasa nake kara ganin girmanki. Kina da mutumci kuma kin san mutumci. Allah na tuba banda ma kin dage ai da ko kwandalarku ba zan karba a matsayin albashinta ba. Ciyarwar da kuke mata damu kanmu ta wadace mu."

A zatonta sai washegari ko nan da kwana biyu Nasima za ta taho sai gata ta dawo da kaya niki-niki kafin magariba. Lokacin ko cikakkun mintuna talatin bata yi ba da tafiya. Da mamaki Khadija take kallonta tana turo katuwar jaka da wata karama sai ghana must-go.

"Ashe da shirinki."

Tabe baki tayi Nasima tayi ta ce "uhm".

Khadija ta daure zuciyarta daga take taken fitsarar da take gani a wurin Nasima. Shirin nata cikin kankanin lokaci ya bata mamaki ganin bata san da zuwan ba sai da ta gama aiki za ta tafi ta fada mata. Ita kuwa tuni sun gama shirinsu da Tahir.

Mamakin Khadija ninkuwa ya yi da taga Nasima ta nufi dakin baki da kofarsa take a cikin falon da kayanta. Idan tayi tunanin ko mamanta ce ta hada mata kaya kafin ta koma gida to da ya akayi ta san dakin da za ta zauna bayan ko su Suhaib basu sani ba. Kama bakinta dai tayi tana kallon ikon Allah.

Nasima kuwa tana shiga dakin ta buga wani uban tsaki. Ta lura Khadijan sai wani fiffika take yi ita mai miji. Mijin da yake a tafin hannunta matarsa har wani daga kai za ta yi mata? Sake yin tsaki tayi da ta kula tsohuwar katifarsu Lilu ce aka ajiye mata a dakin da wankakken bedsheet da pillow.

"Kut! Ai wallahi gado za ka zo ka saka min a dakin nan ko na kama gabana. Lallai ma Khadijan nan kin rainani."

Shu'umin murmushi tayi da ta tuna tuggun da ta shirya mata. Lokaci ya yi da Tahir zai bata nata 'yancin ko ta kwata ta karfi. Ba zai yiwu bane ya cigaba da raina mata wayo. A gaban matarsa ya fada mata magana a bayan idonta kuma ya dinga lallabata. Da Tahir ya dawo Nasima tana daki ta ji hayaniyar yaran.
Da saurinta ta mike ta gyara kwalliyarta ta fesa turare ta fito.

Shirt dinsa ce a jikinta ta hada da zani da dankwali iri daya.

"Daddy oyoyo" ta ce da karamar murya kai a kasa.

Kallonta ya yi sama da kasa wani abu na fizgarsa gareta. Ba don idon yara ba da sai ya biya ladan wannan ado. Gwalo tayi masa karaf a idon Khadija wadda ta fito daga kitchen da tray a hannu. Nasima sai ta wayance ta kuma yin gwalon.

"Nima na rama Lilu." A zuwan wasa suke yi dashi.

Tahir sai ya karbe da cewa "anya Khadija ba rainon mutum hudu ki ke ba? Ita da ta zo taimaka miki ta buge da wasan yara."

Bai bawa Khadija damar yin magana ba ya bukaci ta tara masa ruwan wanka. Daki ta nufa zuciyarta cike da wasi-wasin abin da ba ta son zargi. Abincin ma daki ta kai masa a ranar. Sai da suka kwanta ta sako zancen shirt din.

"Ni fa kamar shirt dinnan taka da nayita nema wancan wankin na gani a jikin Nasima dazu."

'Jaraba sai da ta gane' ya ce a zuciyarsa.
"Oh ashe bamu yi maganar ba. Rannan na tsinceta a bayan mota tayi datti. Ina jin daga kayan wankin ta fado. Na dauko zan yar shi ne da ta gani ta ce tana so."

"Ka dai san ina bata kaya. Idan kari take bukata ai da sai kayi min magana. Rigarka ai ba abin sawarta bace."

Da bacin rai take magana ya soma bata hakuri. Zuciyarta sam babu dadi har wani zazzabi taji yana neman kamata. Abubuwan da take ta son turewa game da Nasima sun sami wuri sun manne mata a rai.

Bayan kamar minti arba'in tana fama da guntun ciwon marar dake tsungulinta taji kamar hannun Tahir a saman fuskarta. Da alama karkada hannun yake ya gani ko tayi bacci. Da gangan tayi motsi ai kuwa ya dauke hannu ya kwanta da sauri. Juya mata baya ya yi ta bude ido ta tabbatar baccin karya yake yi. A hankali tayi kwafa ta sake rufe ido. Ba afi minti goma ba ya sake kada hannun. Wannan karon luf tayi takaici na nukurkusarta. Akwai abin da yake boye mata. Fatanta Allah Yasa ba Nasima bace. Tana jinsa ya tashi ya shiga bandaki. A cikin kunnuwanta taji ana bude dakinsu shi ma ya bude bandakin. Sannu a hankali ta bude ido kadan don kada a san ta farka ta hango Nasima a bakin kofar. Abin ya daina bata mamaki ma tunda har take da karfin gwiwar zuwa dakin. Da yatsa Nasima take yafito Tahir da ya fito daga bandaki, shi kuma yana nuna mata Khadija wadda duhun dakin yasa basu gane ta bude ido ba. Barazanar shigowa Nasima tayi masa ya yi murmushi yana yi mata inkiya ta karaso mana. Ba kunya ta sako kafa a kofar dakin ya yi saurin karasawa ya dagata a kafadarsa suka yi gaba. Kememe Nasima taki yarda a koma dakinta wai ita a gadonsa za ta kwanta. Sanin rigimarta yasa ya ce da Khadija su kwana a nata dakin.

Rufe kofar da ya yi a hankali ya yi daidai da matsanancin bugun zuciyar Khadija. Hawaye take yi ba tare da ta sani ba ta tashi da kyar ta bude kofar ta fita. Dakin Nasima ta nufa bata same su ba sai ta nufi na Tahir. Daga bakin kofa take jin dariyar Nasiman tana rokonsa ya daina yi mata cakulkuli. Shi kuma yana cewa ta rage murya.

Sai da ta tsaya ta hadiyi wani yawu mai daci sannan ta murda kofar da karfinta. Ganin da tayi musu yasa komai na jikinta tsayawa cak. Murdawar cikinta ce ta dawo da ita duniyar mutane ta rike ciki tana salati.Wattpad: https://my.w.tt/Fae5U4oHh8


UWA UWACE...2

Batul Mamman💖



Duk hukuncin da uwa za ta yanke akan 'ya'yanta tana yi ne da tunanin hakan shi ne maslaha a rayuwarsu ko da kuwa a gaba shi zai zamto mafarin kukansu.

***
Kwakwalwarta babu abin da take hasko mata sai yanayin da ta ganshi tare da Nasima lokacin da ta farfado. Idanunta a rufe amma hawaye yana sintiri daga kwarmin idanun zuwa kunne ya sauka akan pillow. Daga kamshin da take ji na dakin kadai ta fahimci a gadon asibiti take. Sakayau take jin jikinta babu wani nauyi sai na zuciyarta da ta koma tamkar dashen dutse. Cikinta ta shafo a hankali taji babu tokarewar nan ta dan da ya kusa zuwa duniya. A firgice ta tashi wani irin radadi na ban mamaki ya soki mararta.

"Bar garaje Khadija jikinki da danyen ciwo." Cewar Yakumbo mahaifiyar Tahir.

Da yake bata san da ciwon ba tashin bai wahalar da ita ba kamar komawa ta kwanta. Ita ba a kwance ba ita kuma ba a zaune ba haka ta saka hannuwanta ta dafe gefen gadon don kada ta fada da karfi. Yakumbo ce ta taimaka mata ta koma ta kwanta tana rarraba idanu. Tambayoyi ne akan harshenta ta kasa amayar dasu saboda sabon al'amarin da take ji a jikinta.

Yakumbo ta sake cewa "Bari na fadawa nos kin farfado" har ta kusa kofa ta dawo ta dafa mata kai "sannu kin ji. Allah Ya baki lafiya."

Khadija ta kula da hawayen da Yakumbon ta dauke daga gefen idonta kafin ya sauko. Jikinta sai ya kara yin sanyi da tunanin ko me yake faruwa ba alkhairi bane.

Yakumbo bata jima da fita ba Mamanta ta shigo tare da kannenta da su Farha. Kowa sannu yake yi mata tana amsawa da ka. Sallamar Tahir taji ta dawo mata da duk wasu lokuta da sai a yanzu take fahimtar raina mata wayo suka yi shi da Nasima. Runtse idanu tayi tana jin Mamanta tana tambayarta ko cikin ke mata ciwo ta girgiza kai. Shi kan shi Tahir din ganin idonta biyu sai da yaji kamar ya koma saboda firgici. Saukinsa daya yaransa da suke wurin Mama jikinsu a sanyaye da yanayin Maminsu. Yana da tabbacin ba za ta yi wani abu a gaban 'ya'yanta ba.

"Ku bashi wuri mana ya zauna kun yi ďare-ďare akan gadon." Mama ta furta tana nunawa kannen Khadija hanyar fita daga dakin.

Mutum biyu ne dama suka zauna a gefe sai suka tashi amma basu fita ba. Tahir ya kalli Khadija ba shiri yau shi ne da sauke kai kasa. Tsoronta ne ya mamaye masa zuciya saboda irin kallon da take yi masa babu komai a cikinsa sai tsana da disappointment.

Mama kuma ta kara masa zafi da cewa "Ina mai-aikin taku yau? Kodayake ya kamata yau ta huta."

Dawowar Yakumbo da likita ce ta taimaka masa bai bayar da amsar da za ta zama zallar karya ba. Kukan jinjiri ne ya biyo bayan shigarsu dakin a hannun Matron. Da dan murmushinta ta nufi gadon bayan gaisawa da jama'ar dakin.

"Ina nan ni dai. Doctor ki gama dubata ta bawa bebina abincinta mun gaji da shan madara."

Kallon kunshin shawul din Khadija take yi a lokacin da likitar ke yi mata tambayoyi game da jikinta. Babu abin da take fahimta sai gyada kai da take yi idanunta fal hawaye akan dan da bata ganin fuskarsa.

Likitar sai ta kalli Yakumbo da alamar tambaya "Maman Khadija ya naga kamar bata san me ya faru da ita ba?"

"Farfadowarta kenan na taho kiran Nos sai na hadu dake."

Da ido Maman ta kalli kannenta suka fice tare da su Suhaib. Tahir kamar ya nutse ya kasa kallonta. Likitan ce ta karbi bebin ta dora mata a cinya.

"Khadija kin san cewa tun farkon cikin nan akwai matsala har kina yawan zubar da jini ko?"

Bata amsa ba sai bin fuskar yarinyar da har kunne an bula mata take da kallo.

"Yau kwana kenan..." da sauri ta daga kai ta kalli likitan jin cewa kwananta biyu bata hayyacinta "maigidanki da mai-aiki sun kawoki cikin dare kina ta zubar da jini a sume. Ta ce zamewa ki ka yi a toilet wurin faduwa cikin ya bugu da sink. Kafin ki farfado faya ta fashe ga jinin bai tsaya ba."

"Hummm" ta ce da guntun murmushi idanunta akan Tahir. Yakumbo tana kallonsu ta kuma ha yadda yaki daga kai ya kalli matarsa.

"Ba cs din bane kadai Khadija harda mahaifar muka cire."

Sautin da taji ya ziyarci kunnuwanta ga dukkan alamu shi ake kira saukar aradu a yanayin tashin hankali. Zabura tayi za ta tashi a karo na biyu tana fama dinkin kasan mararta.

"Kwanta don Allah kada ki yiwa kanki rauni. Kaddara bata wuce kowa. Gashi an ciro miki jaririyarki lafiya kalau."

'Yar ta rungume ta fashe da matsanancin kuka.

"Ki yi hakuri Khadija. Mun yi iya yinmu amma jinin yaki tsayawa. Taimakon Allah ne kawai muka sami baby din tunda sun ce basu san tun yaushe ki ka fada kan cikin ba." Likitar ta karasa yi mata bayani.

Kukanta bai tsaya ba kowa na dakin ya tausaya mata. Yakumbo kuwa haka kawai tun farkon labarin dama bata wani yarda ba. Yanayin Khadijan a yanzu sai ya karfafa mata zarginta. Don ta tabbatar sai cewa tayi da Tahir ya rarrasheta mana. Mugun kallon da Khadija ta watsa masa wanda ya dakatar dashi ya bata amsarta.

"Mijin naki ki ke yiwa wannan kallon don rashin hankali kamar shi ya dora miki lalurar." Mama ta ce da ita cikin fada.

"Allah sarki" inji Matron "kar ki ga laifinsa da kyar ya yarda yasa hannu. Yarinyar da suka zo tare ce ma ta dinga tausarsa akan ya amince a cire saboda kada a rasa ki."

Numfashinta neman daukewa ya yi a wannan lokaci. Wato duka karairayin zuwanta asibitin sai da Nasima ta ingiza shi ya yarda aka cire mata mahaifa. Bata san me za ta yi musu ta huce ba. Ya ci amanarta ya kuma cutar da ita.

Gani tayi su Mama na fita daga dakin tayi murmushin takaici. Ta san irin abin nan ne ace a basu wuri ita da mijinta. Ana rufo kofar ya taho gareta da sauri.

"Nasima don Allah kiyi hakuri ki rufa min asiri. Na san ban kyauta ba amma don Allah in ci darajar 'ya'yanmu."

Tahir ya cika babban munafuki har tana mamakin yadda akayi ta kasa daukan haske ko sau daya. Saboda nisan da ya yi shi yasa bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login