Showing 51001 words to 54000 words out of 242549 words
Ita dai taji ya ce 'asibitin nasarawa' sai kuma 'idan ciniki ya fada nima zan zo d'ani '.
Danliti ya yi matukar murnar samun biyan bukata wato samun damar ganawa da Ayaah. Motar da tafi kowacce kyau a garejinsu ya dauka ya canja kaya zuwa jampa da wando da ya aro a wurin wanki. Ogansa bai san ya fita da mota ba sabòda girman garejin.
Sun kusa zuwa junction din Dan agundi direban ya dinga taka burki da gangan kamar adaidaita sahun yana da matsala. Ayaah son bati maimakon ta fita ta tari wani sai tayi zamanta. Direban ya fita yana ta 'yan kwale kwalensa nan kuwa Danliti yake jira. Haushi ya fara kama Ayaah saboda wayar Honorable yana tambayar ko ta sami su Hasiya. Mata duk tabi ta asirce musu uba ya tada hankalin kamar tashi babar ce babu lafiya.
Gajiya tayi ta fito bayan kamar minti ashirin daidai da dosowar wata mota da ta dauke mata ido da hankali. Danliti ya rage motar ya tsaya a gefensu ya sauke gilas. Kansa babu hula amma ya taje sumar da ya dan tara ta kwanta. Ta bi fuskarsa da kallo taji gabanta ya doka. Wannan yafi Rabeel kyau. A nutse ta gangara jikinsa da ido ta karewa yadin da ya saka kallo.
"Malam don Allah kwanar Wanzamai nake nema a sabuwar kofa." Danliti ya yi kamar bai ganta ba ya tambayi direban.
Da baki ya yi masa kwatancen karya saboda babu wata kwanar Wanzamai ya ce bai gane ba.
"Ni kuma mashin din nawa ya sami matsala ga fasinja ma ban san yadda zan yi da ita ba."
Sai a lokacin Danliti ya kalli Ayaah. Da gaske ta hadu yadda yake son ganin mace. Kawar da kai ya yi ya ce tazo ya rage mata hanya idan hanyarsu daya.
"Malam ita fa wannan asibitin nasarawa za ta je."
"Sai na sami lada ko 'yan mata?"
Sai a lokacin ya kalli idonta kuma ya yi mata murmushi. Ayaah ta nemi hankalinta ta rasa. Gabadaya zuciyarta ta tafi wurin Danliti har tana hango 'yan dagwai dagwai dinsu suna wasan tsere a idanunta.
Ta manta da Anti Hasiya bare jakarta da ta bari a adaidaita sahun. Jiki na rawa ta shiga gaban motar ta zauna.
***
Su hudu ne a falon kowa da abin da ya saka a gaba. Mami Khadija ta dinga bin su daidai da kallo tana rayawa a ranta daga yau sai yau anyi an gama. Tunda Mamanta ta amince da kudurinta ba za ta taba yarda shawarar zaman hakuri tayi tasiri a kanta ba.
Alh. Tahir ne ya tara matansa a gabansa amma tunda suka shigo yake danna waya yana doka murmushi. Mami Khadija za ta iya rantsuwa da wata budurwar yake chatting.
Nasima da waya ta shigo a kunne har yanzu bata gama ba. Zancen shiga da fitar kaya ne sai kudaden da suka shafi kasuwancinta.
Jiddo ma selfie take ta kashewa tana dariya idan ta tura. Ko wa take turawa Allah Masani.
Mami Khadija ta girgiza kai. Wannan ba gidan aure bane. Za dai ta zauna har ya gama ya yi musu maganar da yasa ya tarasu.I just published "12" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/w5mYwrfiGab
UWA UWACE...12
Batul Mamman 💖
Godiya ta musamman ga duk masu comment a kafafen da nake dora labarin nan. Allah Yasa mu cigaba da karuwa da alkhairin dake cikin labarin Ya yafe mana kurakuran dake ciki. Amin
***
Abin ba na kare bane. Awa guda cur ta kusa rufuwa amma har yanzu Alh. Tahir bai yiwa matansa da ya tara a falonsa maganar da ta sanya ya tarasu ba. Mami Khadija ta gaji da kallon fuskokinsu ta mike tsaye. Hanyar kofa da ta nufa ne ya dawo dashi daga duniyar jindadin zafafan kalaman da yarinyar da suke chatting take aiko masa.
"Mami ina zuwa?" ya yi maganar da kokarin saita hankalinsa gareta.
Amsarta takaitacciya ce gareshi don bata son fallasa kanta a gaban matansa.
"Dakina."
Ya dan ji kunyar abin da ya yi da ya kula da lokaci.
"Ayi hakuri Mamin yara yanzu zan sallameku, dawo ki zauna."
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta dawo inda ta tashi ta kuma zama. Alh. Tahir mai neman hanyar kawar da fushin da ya san kokarin dannewa take yi sai ya tambayeta uzurin da zai mayar da ita daki da wuri.
"Hada kaya muke yi ni da yara."
Da murmushi ya ce "Ina mamakin yadda ake wani lokacin tunaninmu ke zuwa daya. Nima zancen da nake son yi muku kenan. Ga wannan kowa ta dauki daya."
Ya karashe maganarsa tare da zube mukullai guda uku akan teburin gabansa.
Anti Jiddo da Mama Nasima ne kadai suka dauka. Mama Nasiman tana kai hannu tana magana kasa kasa amma yadda ta san kowa zai ji.
"Ba dole ku dinga tunani iri daya ba tunda bokanta ya buga ya sanar da ita."
"Ke Nasima!" Alh. Tahir ya yi mata tsawar da tasa ta sakin mukullin da ta dauka "Khadija sa'arki ce ko me? Wato wuyanki ya yi kauri ko? Ki bar ganin ina kyaleki wallahi ba zan zuba ido ki rainata ba."
Ta baya ta rago shi ne abin da kalamansa suka sanya Mami Khadija fadi a zuci. Waye ya bayar da wannan kofar sama da shi? Shi yake nunawa matansa cewa wadanda suka tarar a gidan basu da kima a idanunsa ta hanyar nemansu a waje. Bata taba kulasu dai saboda babu sa'ar yinta a shekaru, ilimi da wayewa. Jiya ma fada sosai ta yiwa su Farha akan rashin kunyar da suka yiwa Mama Nasiman a shagonta.
"Idan baku raga mata don darajar tana auren mahaifinku ba ai kwa kyautata mata a matsayin mahaifiyar Mardiyya. Har abada bana fatan abin da zai zo ya raba kawunanku da kanwarku. Ta taso da kaunarku da girmamani shi ne ku kuma don rashin kunya zaku dinga fadawa mahaifiyarta magana akan idonta? Uwa uwa ce fa. Baku san abin da kuke yi zai iya tunzurata ta koma bin umarninta ko da ya sabawa addini da dabi'a ba? Ku tashi ku je dakinta ku bata hakuri."
Lilu da Farha ta bawa wannan umarnin. Suka tashi suna kunkuni gami da hararar Suhaib da ya kawo kararsu.
Zuwan nasu da bada hakurin bai canja komai na tsanarsu a zuciyar Mama Nasima ba. Mardiyya kuwa sai ta kara kaunarsu a ranta har ta dinga doka murmushi. Farha sai taji dadi ita ma. Lilu kuwa tana biyo bayansu ya shiga tsokanarta domin ya kara wanke laifinsu. Da hannuwansa duka biyu yake wasa da kumatunta.
"An Mardiyya, Mardiyya. Kamota nan kamota nan."
Ai kuwa ta kwashe da dariya sannan suka taru shi da ita suna bin Farha tana gudu.
"Kamota nan, kamota nan.."
Da Alh. Tahir ya shigo ya gansu sun hade su hudu suna bin Suhaib har wata guntuwar kwallar farinciki ya yi. Yana son su, yana kaunarsu. Su ne mafi girman arzikinsa a duniya.
*
"Mukullan na meye ne?" Anti Jiddo ta katse fadan nasa saboda tana son tashi. Gasar tura hotuna da shigar kece raini ake yi a wani group dinsu na whatsapp. Gabadaya ta rikice tana gudun idan bata tura da wuri ba za a iya zargin bata kai matsayin zaman group din ba.
"Na dakunanku ne a sabon gidan. Kowacce bangaren da mukullinta ya bude shi ne nata. Ku fara shiri ranar Juma'a zamu tashi. Kuna da kwana uku na packing."
Ya tashi zai fita saboda karar text da ya shigo wayarsa yana saurin zuwa ya bude yaji saukar mukulli akan centre table din. Dan wigowa ya yi sai yaga Mami Khadija ce ta ajiye nata.
"Ina son magana da kai."
Yadda Anti Jiddo da Mama Nasima suka ci burki sai ka rantse cewa tayi ina son magana daku. Alh. Tahir ya mayar da wayar da har ya zaro daga aljihu ya bude sakon.
Baya son rigima shi yasa ya zube musu mukullai amma indai wani bangare take so a ranta zai bata dama. Ta cancanci fiye da haka ma.
"Ku kawo mukullan. Idan munje sai a zaba. A fara ta kan babba."
"Bar musu kayansu."
Tsayuwa ya yi da kyau yana kallonta "to ki dauki naki mana."
"Ba zan dauka ba. Maganar da ta kawoni kenan. Na gama gini kayi min izini na koma can tare da yara ko kuma ka sauwake min. Duk wanda ka zaba dai a ciki zan koma gidana ne." Ta ce a hasale ganin ya sake kai hannu ya shafo wayarsa da wani sakon ya sake shigowa. 'Yan mintuna kalilan din da take nema ma ba zai iya bata ba saboda matan titi.
Kalamanta sun saukar masa kamar dirar aradu ne. Ba shiri ya mayar da wayar. Hajiyoyin gulma suka dawo abinsu kowacce tana ayyana idan Mami Khadija ta fita zata jidadin korar 'yar uwarta.
"Wace irin magana ce wannan Khadija? Kina cikin hankalinki kuwa."
Bata zauna ba. Zuciyarta ke tunkudarta akan ta amayar da bacin ranta a yau ko zata ji sauki. Abubuwan da suka yi ta faruwa shekara da shekaru suka dinga dawo mata. Mafi muni a cikinsu bai wuce yadda mijinta ya shafawa idanunsa toka yake tozarta addinin musulunci ba. Haram haram ce babu ruwanta da jinsi. To akan me za a dinga yiwa maza uzuri akan zina? Sabon Allah ne fa!
"Duk abin da ka dauka game da hankalina daidai ne. Zaman gidanka ne na gama."
Ya kankace idanu da mugun bacin rai "saboda ke butulu ce? Sai yau, washe garin ranar da ki ke ganin kin sami duniya za ki fito da wannan maganar? Me ma aka yi miki?"
Rashin kunyarsa bata bata mamaki ba tunda ance zina tana daukewa dan Adam kunya.
"Wanda ka yi min na yafe amma bari na tuna maka kadan a cikinsu. Ka ha'inceni. Ka cutar da lafiyata. Kaci amanata. Lalura ta sameni a rasa mai zabar min abin da ya dace sai wadda na kama ka akan gado da ita? Wannan wulakancin yafi komai yi min ciwo. Ni Nasima tasa aka cirewa mahaifa." Idanu jazur ta kalli Mama Nasiman "da yake Ubangijina adalin sarki ne sai ya barki da taki mahaifar Ya kuma hana wani dan kwanciya a ciki. Gashi nan da bakinsa yake fada min asibitoci da kudaden da ku ke kashewa wurin neman haihuwa."
A haukace Mama Nasima ta kalli Alh. Tahir ranta a bace. Ta yaya zai dinga fallasa sirrinta a wurin matarsa. Ga wata shewa da Anti Jiddo tayi tana tafa hannaye. Ita kam a bangarenta komai zam. Duk su bar mata gidan ta ci karenta ba babbaka.
Tashin masifar Mama Nasima ko dis bai shiga kunnuwan Alh. Tahir ba. Zantukan Mami Khadija ne suke kai kawo a kowanne sassa na jikinsa. Don yana bin mata sai me? Mata nawa ne zaune da maza irinsa? Wasu ma kannensu ciki daya mazajensu suke bi kuma ayi sulhu a zauna lafiya.
"Meye ban miki ba Khadija? Wace irin kyautatawa ce ban yi miki ba a tsayin rayuwar aurenmu? Karatun da kike son fara yi min takama dashi waye sila?"
Ba taso ya ga rauninta ba amma hawaye ne suka balle mata. Yau daya ta daga muryarta sama da ta mijinta. Ta gaji da hakurin gaibu. Babu abin da kokarinta a kansa ya haifar na canji sai kara tabarbarewa.
"Kai har kana da bakin goranta min akan abin da kayi min? Ni da aka datsewa farinciki aka rabani da masoyina saboda ana neman shiriyarka in ce me? Kamar yadda mahaifiyata ta yiwa Baba biyayya ta amince da aurenmu haka nima na dinga yi maka. Ni ce shan banza da hofi duk domin ka sami gamsuwar da za ta rabaka da matan titi. Wani abin na sha na kwana na wuni gudawa, wani ya kulle min ciki, wani ya sani jiri amma duk a banza. Har yau ban dace da maganin infection ba saboda zama da kai. Ban gajiya da zuwa kunshi da gyaran kai saboda ance idan na dage da kwalliya zan karkato da kanka. Kai kanka ka sani babu irin kwalliyar da bana yi maka. Ka tara min abokanka nayi ta dora tukunya ina saukewa bana nuna maka gajiyata. Ladabi da biyayya har bayan na kama ka da mai aikina ban daina ba. WALLAHI MAZA IRINKA SUNA DAGA CIKIN MASU KAI MATANSU WUTA. Ba don kariyar Allah ba da tuni na dade da fara gurfana gaban malaman tsibbu ina karbo asiri. Kuma duk da na dade da kudurin barinka amma wallahi inata kyautata maka zato. Fatana ka shiryu mu cigaba da rayuwa da 'ya'yanmu har karshen rayuwarmu. Haba TAHIR! Idan ka tsarkake kan ka daga dattin zina ba Khadija ka yiwa ba. Bani da wuta da aljanna. Kanka kadai za ka taimaka da 'ya'yan da kake ikirarin so. Su ne nake jiyewa kada hakkin alfasharka ya fara bibiya."
Zuwa yanzu fuskar Alh. Tahir a tamke take baya ma gani da kyau. Wai shi matar da yake kokarin ganin ta tsallake kowa a matsayi da mukami ce take gasawa maganganu haka. Da ya rasa abin cewa sai ya yi mata tambayar da yayi nadamar yi saboda amsar da ta soma bashi.
"Duk wata nasara ta rayuwarki ba a jikina ki ka samu ba?"
Shekeke ta kalle shi har lokacin idanunta suna zubar da hawaye "nasara? Dama akwai nasara a auren wanda baya tsoron Allah? In dai auren irinka nasara ce ga mata to ina fata Allah Ya hada 'ya'yanka da maza irin..."
"Kina hauka ne?"
Ya ce da dukkan karfinsa. Sannan ya dauketa da mari, wani abu da bai taba shiga tsakaninsu ba. Idanunta sun rine da bakinciki shi kuma da bacin rai. Da ya barta ko kadan bata da niyyar karasa addu'ar ita ma. Ko ba ita ta haifesu ba ba za ta musu wannan addu'ar ba. Marin bai sakata kuka ba sai dariya.
"Ashe dai kana sane ka ke take sanin. Da na dauka kallon waliyyai ka ke yiwa masu halinka shi ne zan rokawa zuri'arka"
Da dan allinsa ya nunata cikin fushi yana kumfar baka "ya isheki haka nan. Kuma babu inda zaki je. Ki hada kayanki jibi zan turo mota." Ya karashe a kufule.
"Idan ta kama na kaika kotu ne zan kai ka. Babu wani dalili na shari'a da ya ce wajibi ne zama da kai."
Nan yaji zuciyarsa ta dan girgiza. Dama ta fada ne don ta tayar masa da hankali. A daidai lokacin kuma waya ta shigo masa a wadda tun dazu ake turo masa sako. Wayar taki tsahirtawa duk da anji bai dauka ba. A kira na hudu yana faman babatun nuna mata wajibcin bin sa tunda shi ne namiji ya amsa kiran da sauri.
"Zan kira ki...ka anjima"
Bai ankara ba Mami Khadija ta warce wayar daga hannunsa. Katse kiran tayi da rawar hannu duk jikinta yana tsuma. Ace har a wannan matakin akwai wata tsagera a waje da ba zai iya hakura da bacin ranta ya shawo kan iyalinsa ba.
Ta sake jin alamun shigar sako a lokacin da ya hayayyako mata da fadan ta bashi wayarsa. Daga Anti Jiddo har Mama Nasima sun kula da yanayin tsoratar da ya yi.
"Ki bani wayata na ce."
Bata saurare shi ba sai hannu da ta daga masa tana yi masa alamar ya dakata daga matsowa kusa da ita. Da daya hannun ta bude bangaren sakonnin whatsapp wanda ta tabbatar dashi suke hirar.
(Mr Rufus)
Ta gani a sama alamun shi ne wanda ya turo sako mafi kusa da lokacin da suke ciki. Da kyar ta mallaki nutsuwarta ta bude.
"Khadija, Manzon Allah SAW ya ce wata tajassasu" ya fada muryarsa na karyewa.
"Ya kuma isar da sakon Allah SWT da Ya ce Wala taqrabuzzina."
(Gasu nan su tayaka bacci yau. Idan kuma dattijan gidanka sun barka fitowa ka tsaya a bayan layinmu ka daukeni.) Shi ne abin da aka rubuta na karshe
Mami Khadija bata so bude hotonan da suka fara bata tsoro ba tun a haka ma sai dai biyun da ya bude a sama sun kadata. A guje ta bude daya ta dago kai ta kalle shi a sanyaye. She felt disappointed. Lalacewar tasa har ta kai nan? Me yasa maza masu wannan halayyar basa tsoron Allah ne? Ina hakki zai kai su?
Mika masa wayar tayi jikinta a sake
"Yumna? Yumna aminiyar Farha. Tahir ita ma baka bari ba? Ita kadai da iyayenta suka mallaka sai da ka lalata musu 'ya? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Fita tayi ko gabanta bata gani da kyau tana jiyo hayaniyarsa da amarensa.
***
"Daddy ni Papa ne zai bani."
Cewar wata karamar yarinya da bature ke yiwa lakabi da cute. Duka duka bata fi shekara biyar ba. Tana sanye da kayan bacci riga da wando na cotton. Kanta sabon kitso ne yiri-yiri anyi mata shuku biyu hagu da dama. Ko a haka ka kalleta sai ta shiga ranka balle idan surutunta ya hadaku. Bata da haske sosai kamar mahaifiyarta domin Munzali ya dan fi ta haske ma. Amma akwai idanu dara dara da dan karamin baki daidai fuskarta. Hancinta yana da dan tsini kamar na Munzali.
Rike take da plate din indomie da kwai wanda mai girkin gidan Audu ya dafa. Daga bakin kofar kawataccen wurin cin abincin (dinning area) a tsaye Iya Kande ce dattijuwar dake kula da ita.
"Daddy ka kira min Papa pleaseeee."
Munzali ya dora hannu a ka kamar ya yi ihu. Kwata kwata ta hana shi baccin safe ga gajiyar da suka kwaso jiya. Kuma suna isowa Kano suka wuce gidansu Zakiyya mahaifiyarta suka daukota. Dama ita ma ta sani indai Munzalin na gari a gidansa Qibdiyya take zama ko lokacin makaranta ne su suke kaita. Bai yarda rabuwar auren ta kawo gibi tsakaninsa da ita ba. Yanzu breakfast suka zo yi karfe bakwai da 'yan mintuna saboda sammakon tashin da tayi amma take yi masa rigimar sai ya kira Abbati.
"Papa bacci yake yi idan ya tashi zai shigo. Ki ci wannan sai a sake dafa miki wani abincin idan ya zo." Ya ce da sigar lallashi.
Noke kafada tayi "ni dai a'a. Iya ta bude min kofa naje wurinsa."
Ransa ya soma baci ya zaro mata ido "zan zaneki fa Qibdiyya. Ki zauna ki ci abincin nan nace kafin ya tashi."
Sai kawai ta fashe da kuka kamar dukanta ya yi "Daddy sorry. Daddy ka ce ka hakura. Daddy..."
"Na hakura" ya ce a kagauce da gajiyar magiyarta "zauna ki ci."
"Kayi dariya"
"Hihihi" ya yi yak'e kansa na sarawa. Gadonsa yake muradin hayewa ya nutse cikin lallausan bedsheet....
Murmushinta tayi masa jin ya hakura don ita bata son ana fushi da ita "yauwa Daddy to in dauko maka waya ka kira Papana? Pleaaasee"
Ido ya tsura mata ya saki murmushin