Showing 9001 words to 12000 words out of 242549 words

Chapter 4 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3336

komai ba. Innayo na fita kamun bikin 'yar kanwarta da yamma ta turawa Hasiya aikin da jan kunnen kada ta sake ta ce ita tayi.

Bayan Hasiya ta gama ta fita waje kiran almajirin da yake kai musu bakin hanyar wata makarantar dare tayi. A kofar gidansu yake zama da an yi magariba. Tana jiran karasowarsa daga daya tsallaken layinsu a-kori-kurar da ta dauko su Abbati ta zo ta wucesu zuwa makarantar dake cikin unguwar.

"Kai ina Munzali?" Suka ji muryar Asabe daga bayansu. Rabonta da shi tun kafin ta sauke abincin rana. Shi ne babban danta namiji.

"Ban gan shi ba" yaron ya bata amsa.

"An ce min tare ku ke zuwa filin kwallo."

"Bai je ba yau. Su Shazali ya bi yawo."

Da ta bi ba'asi sai ta gane su Shazalin wasu matasa ne almajirai kamar yaron Innayo din. Hankalinta ne ya soma tashi saboda an kusa Isha'i.

***
"Cire wandonka na ce" Shazali ya ce da fada saboda bata masa lokaci da Munzali ke neman yi.

Idanu a waje cike da tsoro Munzali ya sake kama wandonsa ya kankame.
"Na ce maka bana jin komai. Ni gida zani Asabe za ta dakeni idan ban koma ba."

"Kai ma ka tsaya sai wani lallaba shi kake yi. Dalla bani wuri na nuna maka yadda ake yiwa sababbin shiga." Cewar wani dan kwaya abokin Shazalin.

Matsawa ya yi ya turo masa Munzalin da ya fara turjiya gabansa. Shi ya rike hannuwan abokinsa kuma ya dauke Munzali da mari kafin ya zare wandon ya yi wurgi dashi.

Dariyarsu ce ta fara karade kangon kafin ihun azaba da Munzali ya saka yana kiran AsabI just published "3" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/jlkjBC37l8




UWA UWA CE...3

Batul Mamman💖


Duk duniya babu mai rufa maka asiri sama da mahaifiyarka. Komai lalacewar da sai ta kure sai kuma ta jure za ta iya fadawa duniya. Da mai kyakkyawar zuciya da ma mai akasinta duka suna yi ne domin kada rayuwar dansu ta lalace a wani mataki. Amfani ko kuskuren yin hakan ga dan da akayi dominsa kuwa gaba ce kadai za ta nuna.


***
Tsohuwar naira biyar da ta gama shan wahala tsakanin kwandastoci da direbobin tasi ta yayyage Shazali ya dauko daga aljihunsa.

"Ungo ka tafi gida." Ya sakawa Munzali a aljihun gaban rigarsa.

Yaron da kyar yake tsayuwa saboda bakar azabar da ya sha a hannunsu. Da ya tashi tsaye ma kafafunsa duka rawa suke yi.

Warce kudin abokin nasa da suka tafka ta'asar tare ya yi yana magana irin ta takadiran 'yan kwaya.

"Kai da talo-talo ne wani sa'in. Banda hauka ya za ka ce ya tafi gida bamu yanka masa wainin (warning) ba" kwalar Munzali ya ci ya fizgo shi gabansa ta karfin tsiya sai da ya yi kara "idan ka sake ka fadawa wani abin da muka yi maka sai na yanka uwarka. Ka san dai na santa ko? Ko ba Asabe Gantali ba ce gyatumar taka?" Ya karashe da yi masa tsawa.

"Ita ce" Munzali ya amsa da sauri jikinsa na bari. Ga ciwo ga tsoro.

Sai da suka tabbarar ya gama tsorata sannan suka kama gabansu. Tsoro bai bari ya zauna a wurin da sunan ciwo ba. Ga duhu ga kukan kwari da kananan dabbobin da suka mamaye kangon. Da jan kafa ya fito yana cije baki tare da runtse idanu. Idan hawaye ya taho sai ya sharesu da sauri saboda ya rike kashedin da aka yi masa. Tafiyar minti shabiyar zuwa gidansu sai da ya rubanya ta.

Asabe sai kai gwauro da mari take yi wurin neman Munzali. Ta shiga duka makota gidajen da yake da abokai bata same shi ba. Nemansa take yi saboda nutsuwar kanta ba wai don Alh Rabi'u zai yi mata fada ba. Tarbiyar yaran a wuyan uwar da ta kawosu duniya ya rataya a nasa tunanin. Ummakati yayarsa ta gama karantawa wasu gidajen da za ta je ta fita ita ma ta sake daukar mayafi.

Tana isa soro Munzali na shigowa. Basu da wutar nepa amma akwai hasken farin wata saboda wurin babu rufi. Kunnensa ta jawo iya karfinta sai da ta durkusar dashi a gabanta sannan ta hau shi da fada tana jibgarsa. Bata taba yarda hukunya 'ya'yanta a gaban Innayo. Kullum nunawa take nata 'ya'yan basa laifi.

Munzali bai yi kuka ba ko ya roketa tayi hakuri kamar yadda ya saba idan ya yi mata laifi. Zazzabi yake ji ga ciwo babu wani sauran kuzari ko da na kuka ne a tare dashi.

"Shegen yawon tsiya kamar wanda makiya suka sako a gaba. Ban hanaka yin dare a waje ba? So ka ke babanku ya sani ya daina baka kudin makaranta?"

Naira biyar din da Shazali ya bashi ce ta fado ta kyalla ido ta gani ta dauka ta karkade. A kirjinta ta soke kudin sannan ta cigaba da yi masa fada kunnensa a tsakanin yatsunta tana ja.

"Ki yi hakuri Asabe."

Ya iya cewa da kyar yana jan jiki. Bayansa ta bi tana cewa gara ma ya saki jikinsa domin bata yi masa dukan da zai saka shi irin wannan tafiya ba. Ko kadan tunaninta bai bata ta binciki inda ya sami kudin ba. Ita bata ma son tayi zancensu bare ta ji cewa ba wadanda za ta iya ci bane. Inda ya je ma ba laifi bane indai zai dawo kafin duhun dare.

Innayo ya wuce bai gaisheta ba kamar kullum. An koyar dasu kiyayyar kishiya da 'ya'yanta tun kafin su gama wayo. Yana shiga bandaki ya fashe da wani sabon kukan. Bai taba jin ciwo makamancin abin da yake ji yanzu ba. Ga cikinsa ya kulle amma yana tsoron yi ya tadowa kansa sabon ciwo. Kukansa ya sha ya dauki wandonsa da ya baci da jini ya jefa cikin shaddar (masan kasa) ya fito. Rigarsa ta wuce gwiwarsa ma saboda haka babu mai gani.

"Munzali ina wandonka?"
Muryar Alh Rabi'u ta karade tsakar gidan.

Kafin ya bada amsa Asabe tayi saurin amshewa ta ce wai don ya ga babu wuta ne ba mai ganinsa shi yasa ya fito.
"Zai gyara Alhaji. Da kaina zan yi masa fada." Ta ja hannunsa "Bashi hakuri ka wuce muje ka ci abinci."

Da dassashiyar murya ya ce da Alh Rabi'u ba zai kara ba. Shi kuma jin muryarsa a haka ya tambaye shi me ya same shi. Nan ma Asabe bata bari ya yi magana ba saboda kada wani ma ya ji cewa tayi masa fada ya yi kuka.

"Mura ce. Murar zafi ce Alhaji. Ka san ta da bakin naci."

Gyaran murya ya yi abinsa ya wuce ba tare da ya sake kulasu ba. Da yaje daki ya tarar da abincinsa wanda Innayo ta kai ta ajiye kafin ya shiga dakin. Da kafa ya ture farantin da ta jera langar tuwo da miya a kai ya zauna yana sassauta daurin tazugen wandonsa. Daga gidan wata sananniyar mai danwake yake ya ciko ciki. A kasuwarsu magidanta kalilan ne basa sayen danwakenta. Ga tsire da ya saya ya hada dashi da lemon kwalba. Wata uwar gyatsa ma ya yi ya kwanta zai yi bacci.

***

"Mungode fa da ka saukemu Malam har kwana biyu. Ba don kai ba da sai dai nayi kwanan tasha." Cewar Inuwa yana mikawa Mal Alto hannu.

"Babu komai. Ni ke da godiya da ku ka kawo danku wannan makaranta mai tarin albarka."
Tsamurarren malamin ya bashi amsa idanunsa akan buhu da kullin ledojin dake gaban Inuwa.

Kamar Inuwan ya gane ma'anar kallon kuwa ya fada masa cewa kayan abinci ne ya kawo masa. Ya turo mafi girman buhun wanda shi ma ledoji ne a kukkule a ciki da murmushinsa.

"Wannan kuma kayan abincin Abbati ne. Akwai kanzo da hatsi harda shinkafa. Da yake yana da 'yar matsalar shiririta shiyasa uwar ta ce don Allah kada a barshi ya je bara. Ko rana da dare ne kadai idan anyi girki daga cikin gidan a zuba masa. Wallahi ba ma shi da ci sosai." Wani irin kallo yaga Mal Alto yana binsa dashi ya yi maza ya kara da cewa "kuna iya saka shi wanki, shara ko aike. Fatanmu ya samu ilimi mai amfani kamar 'yan uwansa ba sai ya hada da barar ba."

"Ba damuwa. Bara ce dai kadai baka so ko? Iyalina zasu dinga girki dashi. Kar ka damu."

Haka nan zuciyar Inuwa bata aminta da kalaman Mal Alto ba amma bashi da zabin da ya wuce barin dansa a nan. Idan ya mayar dashi gida Mal Sa'adu ba zai masa ta dadi ba. Har ransa shi ma ba ya ra'ayin yaransa suyi barar amma bashi da zabin cewa a'a. Zuciyarsa ta kwankwashe shi akan ya tafi da dansa sau ba adadi amma ya ki ji. Nan gaba kadan yana sa ran a kira Abbatinsa da Gwani. Haka nan ya fice ya barshi kamar yadda ya baro Sani a Zaria ya kama hanyar tasha zai koma gida.

Abbati kuwa ya yi kuka sosai. Bayan kimanin rabin awa da fitar Inuwa lokacin Mal Alto ya tabbatar duk inda yake yana hanyar Kirikasamma. Dorinarsa wani babban dalibinsa ya dauka ya zubawa Abbati a baya shi kuma bai ce komai ba. Dalibin da yake yin abin daya san malamin nasu ya yi na'am dashi ya ce,

"Tashi shagwababbe. Ni ban san akwai sangartattu a kauye ba sai yau. Wai kada a bari kayi bara. To uban me ya kawoka birni idan ba shinkafa da miya ba? Babban naka ya raina Malam ma."

A firgice Abbati ya tashi yana kuka hannuwansa na susar inda bulalar ta same shi.

"Ku je a bashi roba ya bi 'yan uwansa bara idan an fito daga karatu shabiyun rana. Sannan ka fada masa duka tsare-tsaren tafiya barar don kada a sami matsala." Cewar Mal Alto kai a kasa yana jan wani katon carbi kamar ba shi yake maganar ba.

Ba kowa ya san halin Mal Alto ba saboda iya kankantar da murya da nuna shi na kwarai ne. Ya goge sosai wurin ci da addini. Mutane suyi ta kawo masa yaransu yana bautar dasu. Idan an tashi komawa gida kuwa sai an yi dogon gargadi akan iya rike baki kada a fadi me yake faruwa a makarantar. Da yake yana taba tsibbu a boye har rubutun kafe yaran yake yi. Duk wanda yaje ganin gida sai ya dawo. Wadanda wahala ta zamewa jiki har suka rika suka fara yawo irinsu Shazali kuma suyi ta dauko masa magana. Akwai 'yan daba, 'yan kwaya, masu haura katanga da duk wani nau'in gagararren mutum a gidan. Karatu ne suke yi babu ikilasi ko kankani. Idan mutum yayi magana cikin 'yan unguwa ace yana kalubalantar karatun addini.

Ana fitowa shabiyun rana aka bashi wata kodaddiyar roba. Kayansa kaf dinsu har na jikinsa an dauka an kai cikin gidan Malam. Akwai wadanda girmansu ya zo daya a cikin 'ya'yansa. Jakar kayansa ta koma babu komai sai wasu tsummukaran kaya da aka fito dasu daga cikin gidan.

"Kafin karfe uku ka tabbatar ka dawo."

Abbati ji yake kamar mafarki yake yi. Babu abin da ya fahimta a karatun har suka fito saboda fargaba. Ya dauki kwano ya bi bayan wasu yara da ya zauna kusa dasu da ana karatu. Wani lungu suka shiga ya daga kafa da saurinsa ya cimmusu.

Babban cikinsu ya saka dariyar muguntap suka cigaba da tafiya har karshen lungun ashe bayan gidaje ne. Tarfa shi suka yi babban ya tattale masa keya.

"Ba kaine aka ce ba za ka yi bara ba? Ya muka ganka da kwano?"

Sauran suka sa dariya.

Hannuwansa duka biyun a keyarsa yana kare dukan da suke yi masa na cin zali ya ce "Don Allah ku bari na biku."

"Ai baka isa ba. Ka nemi hanyar da za ka dinga bi saboda gidajen nan wurin namu ne. Idan muka kara yawa abincin ba isarmu zai yi ba."

Wasu na duka da kafa wasu da hannu a haka suka kore shi daga lungun jikinsa duk ya yi futu-futu da kasa. Gefen hanya ya samu da ya gaji da yawon ya zauna gashi ko wakar barar bai iya ba. A nan bacci ya yi awon gaba dashi kudaje suna ta kai kawo a jikinsa.

Munzali ne ya fito daga gidansu da jan kafa ya hango Abbati yana bacci a karkashin bishiyar kofar gidansu. Yau kwana biyu kenan da gamonsa dasu Shazali. Rashin kula na Asabe yasa ta yarda da ya ce mata a wurin bal ya turgude kafa shi yasa baya tafiya da kyau.

Da kafa ya shuri Abbati ya tashi a tsorace yana rarraba idanu. Kansa ne ya juye ya manta a ina yake sai da ya ga robar bararsa.

Munzali ya kankance ido ya ce "kai dan makarantar Mal Alto ne?"

"Eh."

"Shi ne kayi kwanciyarka kana bacci gashi har anyi la'asar sun kusa fitowa. Tabdi. Wallahi duka ake yiwa marasa komawa da wuri."

Ba a makarantar yake ba amma layin bayansu take. Yawancin abokan buga kwallonsa daliban can ne. Duk wanda ya makara wurin komawa ba karamin duka yake sha ba. Kwal-kwal idanun Abbati suka yi da hawaye sai ya bashi tausayi da ya ce masa ba zai gane hanya ba.

"Muje na raka ka amma ba zan shiga layin ba." Ya ce don yana gudun sake haduwa dasu Shazali.

Har farkon layin ya kai Abbati ya juya zai tafi ya hada ido da Shazali. Fitsari ne ya subuce masa tsabar fargaba ya fara ja da baya. Jan hannun Munzali da Shazali ya yi daidai da waigowar Abbati. Yana kallo har suka bacewa ganinsa. Bai san meye tsakaninsu ba kuma ba ihu Munzali yake yi ba shi yasa bai yi tunanin komai ba.

Kangon suka koma babu mutane ko hayaniya a wurin. Hannu Shazali yasa ya toshe masa baki sannan ya kuma maimaita masa rashin imanin nan.

Sai da ya gama ya lura da hawayen dake fuskar Munzali shabe-shabe da majina.

"Allah Ya isa. Mugu. Azzalumi. Dan wuta."

Cikin bacin rai Shazali ya riko habarsa ya matse "Ni kake zagi Munzali? Don ma ka samu ina sonka. Idan ka ce zaka yi min rashi kunya tattaka ka zanyi in taka banza a wurin nan."

Da kafa ya shura masa daurin bakar ledar da ya riko tun kafin su zo wurin. Munzali ya bude yaga langa ce cike da shinkafa da miya harda nama yanka biyu. Ga salad an yanka da tumatir da albasa. Duk wannan bakar wahalar da ya sha sai ya nemeta ya rasa a lokacin. Ga zobo kullin naira bibbiyu guda biyu da sauran kankararsu. Hannu baka hannu kwarya yake danna shinkafar nan. Ba shi ya daga kai ba sai da ya sude kwanon tas. Rabonsa da shinkafa da miya tun sallah karama da A'i ta aiko gidansu. Wata hudu kenan. Wanda ake ci a dakin Innayo kuma Asabe ta ce ta tsine idan suka karba. Wai guba za ta saka musu saboda bata da maza. Tafi ganewa girka musu wulakantaccen abincin da Alh Rabi'u ke kawowa.

Shazali na kallonsa ya saki murmushi "nima kudi na samu a wurin Alhajin da yake min irin abin da nayi maka. Idan kana zuwa wurina kullum har kaza zan saya maka da tsire."

"Akwai ciwo don Allah kada ka sake."

"Kai dalla can baka san idan ana yi kullum zaka daina jin zafin ba? Da kan ka za ka nemeni wataran." Ya yi masa wata irin dariya.

Da wayo ya dinga hillatarsa har ya amince gobe zai zo kangon ya same shi. Da zai fita ya sake bashi naira biyar tare da gargadi.

"Muddin ka sanar da wani da kai da duka 'yan gidanku zan kai gidan yankan kai!"

Sai bayan kwana goma suka sake haduwa da Abbati da jikinsa duk tabo da sabbin ciwuka. Daga bara Abbatin yake bai samo komai ba zai koma makaranta. Ranar ta kama alhamis ba sa karatu.

"Don Allah muje gidanku ko kanzo ne ka kankaro min." Ya roki Munzali.

"Nima babata bata da abinci. Ka dawo anjima idan kun fito barar dare zan baka abinci Yasin harda nama."

Cikin Abbati har wata kara yake saboda yunwa ya amince a guje. Kayan abincin da yazo dasu Mal Alto ke ci. Gashi bashi da aboki ko daya cikin 'yan uwansa almajirai kamar ma sun tsane shi.

Hasashen Shazali ya zamo gaskiya. Kwana biyu Munzali yana riga shi zuwa kangon. Ya saba yanzu ko babu kudi so yake ayi. 'Yan biyar biyar da yake batarwa a sayen kayan kwadayi har yau Asabe bata tambayi inda yake samo 'yan canji ba. Ranar da ta tsinci naira goma a aljihunsa ma boyewa tayi da sauri tana murna.

"Masu 'ya'ya mata ne da fargaba idan an gansu da kudi. Da namiji kuwa indai ba barawo bane babu inda zai samu sai wurin abokan arziki." Ta murmusa ita kadai "Munzali ba dai jama'a ba. Duk inda ya gifta sai an kira shi."

Kamar yadda ya alkawartawa sabon abokinsa da ko sunan juna basu sani ba da kansa yau ma yaje kangon. Shazali da wannan abokin nasa yazo. Bayan sun gama aka mika masa langar abinci da naira goma. Dadi kamar ya kashe shi. Ya duka yana juye abincin a leda Shazali ya tambaye shi me yasa ba zai ci a nan kamar kullum ba.

"Aboki nayi wani sabon zuwa a makarantarku. Abin tausayi idan ya yi bara ba ya samun abinci."

Dan tsorata Shazali ya yi "ina fata baka fada masa me muke yi ba ko?"

"A'a." Yana kallon kofa ya ce "In tafi? Na ce ya jirani."

Sallamarsa suka yi ya tafi da murna. Bai shiga gida ba saboda ya san sai Asabe ta ci ko bata bawa 'yan uwansa ba. Bai jima ba kuwa ya hango Abbati yana layi kamar zai fadi saboda yunwa. Karancin shekarunsa basu hana shi tausaya masa ba. Zuciyarsa tana da saurin rauni wanda da ace ya sami kyakkyawar tarbiya da kulawa da anyi mutumin kirki abin alfahari. Shekarunsa goma amma ya san ya gane mabukaci kuma ya yi abin da zai sama masa mafita daga yunwar da yake ji.

Cikin soron gidan makotansu da ba kasafai ake bi ba ya ja shi suka shiga ya bude langar. Abbati yawu ya tsinke jikinsa yana rawa ya tsoma hannu a ciki. Tare suka ci amma Munzali bai fi loma uku ya yi ba. Abbati ya barwa abincin.

"Nagode. Nagode don Allah ka ce da mamanka nagode kaji."

"Ba Asabe ce ta bani ba. Wani abu nake yiwa wasu sai su bani abinci idan an gama."

Mamakin ashe akwai aikin dake kawo abinci irin wannan Abbati ya yi "zan yi. Don Allah kaje dani gobe."

Cike da kuruciya Munzali ya ce "kai wallahi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login