Showing 60001 words to 63000 words out of 242549 words
take ganin Mamin tayi. Kafin tayi marin Alh. Tahir ya taso da sauri ya rike hannun.
"Kiyi hakuri Mama don Allah. Ban nemeku domin haka ta faru ba. Hakuri kawai nake so ku bata sannan ta san cewa na janye."
"Wallahi ba za ka janye ba. Wannan aure kamar anyi an gama kuma ni zan maka waliccinsa ma. Idan an daura ta mutu tunda bata da tawakkali" cewar Baba.
Nan fa gaban Alh. Tahir ya fadi. Shi da ya yiwa kansa garkuwa da auren karya wannan tsohon (wato Baban Mami Khadija) yana neman ballo masa ruwa. Da aminansa na shashanci su biyu wadanda ke zaune a falon suka kulla komai.
*
Daren Jiya (Dakin Nasima)
"Zabi ya rage naki. Ko dai ki goyi bayana ki ce auren yarinyar na nema Khadija ta tubure ko kuma na rantse miki zan SHEGANTA Mardiyya."
Dif taji kunnuwanta sun daina daukar kowane sauti sai gudun jininta a cikin jijiyoyin jikinta.
"Me...me? Me kake nufi Diya?"
Ta fara zuwa hannu ya fada a ransa sannan ya murtuke fuska "an fada miki ni sauna ne ban san me nake ba? Daga aurenki ko wata taran cif bamu yi ba ki ka haifeta. Na san tawa ce dai amma..."
Dankwalinta ta cire ta daure kugu dashi jikinta na rawa kamar ana yi mata allurai. Gabadaya ta haukace masa ta soma masifa ido rufe tana zufa.
"Wallahi kayi mugun kadan Tahir. Kambu..ni zaka yiwa haka?...to bari kaji in gaya maka. Zan jure komai banda wannan. Wallahi Mardiyya 'yar sunna ce. Ba a waje nayi cikinta ba" sai kuka ya kwace mata. Iyakar abin da Mardiyya zata tsira dashi na mutumci kenan a duniya. Shi ne kawai abin arzikin da ta san ta yiwa 'yarta da bata sami cikinta a waje ba. Nata dangin babu wani asali na bugawa a misali. Ga miji bashi da maraba da bunsuru. Ai ita ba mahaukaciya bace. Ta dade da sanin barin Mardiyya cikin 'yan uwanta gata ne gareta. Duk wannan hargagin na son ta rabasu ba komai bane sai barazana da kishi.
Kukanta kuwa ya faranta ran Alh. Tahir
"Za ki iya bani hadin kai na ceci aurena da Khadija ta hanyar karyata ta gobe ko kuma ki fadi gaskiyar abin da ya faru 'yarki ta shiga sahun marasa asali...that is bayan mutuwar naki auren da karbe shagona dake hannunki."
Bata daina kukan ba ta ce "Ka karba. Ko yanzu ka ke son zan baka amma idan ka taba mutumcin Mardiyya sai na nuna maka haukan da har ka mutu idan kaji sunan Nasima sai zuciyarka ta girgiza."
"Nasima kenan. Bakinki ba ya mutuwa. To ni dai kin amince ko kuwa?"
"Na yarda."
(Ai na fada muku komai lalacewa Nasima ma uwa ce. Duk barazanarsa babu abin da ya dameta illa asalin 'yarta da zai lalace. Babu wani abu komai dadinsa a gareta da zai sa ta yarda hakan ta faru. Saboda Mardiyya ta amince da wannan shiri.)
*
Daren Jiya (dakin Jiddo)
"Ina magana kin yi shiru. Idan ba za ki bani hadin kai ba ki fara hada kayanki domin dama zamanki bashi da amfani sai karin nauyi. Ke ko barin nan da mata keyi baki taba yi ba."
Shekeke ta kalle shi "kaga ni babu ruwana da sabgarka. Yawon tambada ai ba yanzu ka fara ba..."
Marinta ya so yi ta kauce kafin hannun ya iso kuncinta.
"Kaga Malam kar ka taba lafiyata. Idan kana so ma ka aurota da gaske ba matsalata bace"
Hankali kwance ya fice daga dakin. Dogon tsaki Jiddo ta bishi dashi kafin ta mike ta saka mukulli ta kulle dakinta. Ruwa ta watsa ta saka wata figigiyar rigar bacci sannan ta bi fuskarta da heavy make up. Selfies ta kashe sun fi ashirin. Ta zabi biyar da suka fi kyau da nuna jiki ta tura whatsapp dinta.
(Danliti Makanike) shi ne sunan da ya bayyana. Tura masa hotunan tayi ta kwanta tana jiran waya ko amsarsa ta nan.
A lokacin Danliti yana zaune tsakiyar abokansa su Rabilu da direban adaidaita sahun da ya dauki Ayaah. Jakar Anti Hasiya suka zazzage suna shirin raba kudin dake cike Danlitin ya hanasu.
"Ni da zan yi amfani da jakar na koma gareta ai zaku zubar min da girma idan aka taba kudin.."
Ihun basu yarda ba suka fara yaji shigar sakwanni a wayarsa. Budewa ya yi ya doka uban tsalle sannan ya cillawa Rabilu wayar.
"Wayyo Bobo ina ka samo wannan kayan dadin?"
"Wohooho...kai kaga wata dakakkiyar haja. Shegen ina ka samota?" cewar direban.
"Matar da nace muku motarsu ta lalace a wurin Ciromawa (Zaria road) aka daukoni na gyara musu. Daga hira fa tana ce min biki suka zo za su koma Kaduna sai gani da lambar wayarta. Sai ma kun ji irin hirar da muke yi." Ya kare da lumshe ido yana mantawa da batun Ayaah.
"Bobo kawai kaje asha shagali. Wannan fa katin gayyata take turo maka da hotunan nan."
Kada kai Danliti ya yi "inaaa, matar aure ce. Haka kawai azal ta kaini asiri ya tono a batar dani ban gama morar duniya ba."
"Banza dan bakinciki. Ni ka hadamu kawai" cewar Rabilu.
Basu tashi ba sai da kowannensu ya tura hotunan a wayarsa suna ta fasalta ta tare da amfani da kazaman kalamai akan mummunar alakar da suke son kullawa da ita.
(Komai mutumci, girma da kimar mutum tsirara yake komawa da zarar ya kulla abota da zina. Ya Allah ka nesantamu da zuri'armu daga wannan kazamar alfasha. Amin)
*
Bakin Mami Khadija kasa rufuwa ya yi a lokacin da Anti Jiddo da Mama Nasima suka hada baki wurin bada shaidar zur. Su biyun sun ce rigimar ta faru ne lokacin da Alh. Tahir ya fada musu zai auri kawar Farha idan sun tare a sabon gida.
Sai da iyayenta suka gama yi mata tatas sannan ta iya cira baki ta ce "Allah Ya sanya alkhairi a tsakaninsu. Bari naje mu cigaba da parking kafin goben."
Ficewa tayi ba tare da ta sake kallon kowa a falon ba. Jikin Mamanta sai ya yi sanyi ta soma tunanin ko akwai wata a kasa. Ta san halin Khadijanta amma jiya fa Tahir din da abokansa yazo gidansu kamar zai zubar da hawaye. Yayinda zuciyarta take wannan tunanin sai wani sashe ya tunatar da ita cewa idan aurenta ya mutu yanzu tamkar ta bata rawarta da tsalle ne. Mata kowacce fa hakuri take a gidan aurenta. Me zasu ce da 'yan uwansu ya raba auren shekara da shekaru?
Jikin Yakumbo yafi nata sanyaya. Tafi kowa sanin halin dan nata. Kafafu babu kwari haka ta tashi ta dogara zuwa dakin Mamin. Kofar a rufe take. Daga ciki taji an ce,
"Ko waye ku fadawa sauran bana son damu. Kar wanda ya shigo sai na nemeku."
"Ni ce" cewar Yakumbo a raunane.
Da sauri Mami Khadija ta taso ta bude mata kofar duk da dama ba mukulli ta saka mata ba. Sai da suka zauna sannan Yakumbo ta soma magana.
"Khadija fada min tsakani da Allah me ya faru."
Sai da ta hada da roko sosai sannan ta sami amsar da tazo nema. Hawaye ne ya balle mata ita kuwa Mami dama nata ya kare.
"Kiyi hakuri shi ne kadai abin da zan iya cewa. Wallahi ba don kun tara zuri'a ba da da kaina zan karbar miki takardarki. To amma yanzu kina fita me zaki fadawa 'ya'yanki ya rabaki da mahaifinsu? Dukkansu fa aqilai ne babu karamin yaro a ciki. Ko kin boye da sannu magana za ta fito. Yaya zasu ji ace uban da basu da madadinsa ne da wannan halayyar? Da girmansa ya zube a idonsu ace ya nemu kanwar 'yarsa a waje ai gara ace aurenta ya yi. Kina kallon halin da Suhaib ya shiga. Tahir din da kansa ya fada min da na matsa da tambaya. Ki daure ku karasa rayuwarku tare don Allah."
Ga mamakinta sai ji tayi Mami Khadija ta ce "Yakumbo zan zauna. Wannan shawarar na san ita ce dai zaki bawa Amina ko Asama'u ( ya da kanwa ga Tahir). Kamar yadda nake tsammanin zasu yi miki biyayya nima zanyi. Zan zauna har Allah Ya kawo masa shiriya."
Kalamanta sai suka bar Yakumbo da bude baki da rufewa. Ta rasa me za ta cewa Mami. Ba abin ta ce tayi mata rashin kunya ba ta san cewa gaskiya ce ta fada kuma dama wanzami baya son jarfa. Fita tayi Mami Khadija ko kofar daki bata rakata ba. Irin ciwon da zuciyarta take yi a lokacin tana tsammanin zai iya kwanyar da ita. Wannan wace irin duniya ce muke ciki mai cike da son zuciya da son kai. Sab'o ya tashi daga abin kunya ya koma abin rarrabewa tsakanin mata da maza. Jinsi mafi rauni idan ya aikata shi ne laifi.
Bayan tafiyar iyayen nasu Alh. Tahir ya kai gwauro ya kai mari yana ta safa da marwa a falonsa. Baba ya ballo masa teku ba ma ruwa ba. Yakumbo tayi rantsuwar idan bai auri Yumna ba sai ta tsine masa kafin ta tafi.
"Me zan ce da yaran nan? Me zan cewa Farha?"
***
Da safiyar wannan ranar ne kuma 'ya'ya da jikoki harma da tattaba kunnen Marigayi Mal. Auwalu Sarkin Dori suka tashi da shirye shiryen isowar Farinwatan (Zahra Tabi'u) gidan. Kwai da kwarkwatansu babu wanda baya ci daga arzikin Auwal wato Abbati. Kafatanin danginsa na uwa da uba babu mai arzikinsa gashi babu rowa balle nuna kyashi. Washe garin ranar ne za ayi masa nadin sarautar da ayyukan alherinsa a garin suka saya masa. Sardaunan Matasan Kirikasamma. Da yake ba wasu abokai gareshi ba daga shi sai Munzali, Shazali wanda ba a son ransu ya biyosu ba, Iya Kande da Audu kukunsu sai shalelensu Qibdiyya.
Katafaren ginin da ya yi a jikin katangar ainihin gidansu nan Hanne take zaune tun bayan ya maidota da kansa. Zama suke wanda babu soyayya ko kadan sai bakaken halayen da take nuna masa. Shi ma kuma yana sane da nasa mummunan aikin da ya shallake 'yan sace sacen da take yi masan. Nesanta da juna a tunaninsa shi zai raga musu yawan fadan da suke yi. Da ya dawo da ita Gwaggo Jummai gidan tazo ta sha kukanta akan lallai ya mayar da ita. Mal. Sa'adu ya shafawa idanunsa toka kamar ba ciki daya suka kwanta da ita ba ya ce maganar Abbati ce abar dubawa. Idan Hanne ba za ta kwantar da kai taci arziki duk da rashin haihuwa ba zasu bashi wata. Tana jin haka ta gane autarsu suke son bashi. Lokacin halin Deluwa ya fito musu zahiri. Rigima sosai aka yi wadda har yanzu da burbushinta domin gaba lamarin ya haddasa. 'Yan fadar Deluwa suna goyon bayan asa Abbati ya auri 'Yashshafa. Masu amana na hannun daman Gwaggo Jummai suna tuna mafarin hadin auren Hanne da Abbati suna sukar abin. Mal. Sa'adu bai ce komai ba saboda shi ma ransa yana so. Baaba Mari abin duniya ya isheta. Tayi ta kiransa ya zo a sulhunta yaki zuwa. Kowacce kamar za ta kwanta mata a kasa. Hanne da 'Yashshafa su wuni suna girki da zuwa yi mata shara da duk wani aikin bangarenta wanda ya koma aljannar Kirikasamma.
"Ayiririiiiii. Kai jama'a, mai hanci ta buga mana gud'a mai doguwar gunna mana. Ga Shafa'atu ikon Allah. Kainuwa dashen Allah. Zinariyar gidan Alh. Sa'adu mai kyauta bata kirgawa. An buga an barki an sake bugawa an kuma barinki. Sannu uwa ga jikokin Haj. Mariya ta Alh. Inuwa gatan marasa galihu. Muna nan muna jira badi war haka sai an saki guda kala hudu a jere na saukar irin da zaki dasa a gidan Alh. Abbati. Na ce ina gaisuwa da babbar murya ga Alh. Abbati Sardaunan Matasan Kirikasamma..."
Ta tagar wani falo dake saman nasu gidan Hanne ta leko cikin gidan iyayen nasu. Su ma basu fara ba sai da suka daidaici jikin katanga inda suka san ana yi zata jiyo. Tana lekowa kuwa 'Yashshafa da kawarta mai wannan kirarin suka kwashe da dariya gami da tafawa.
Ta kule iyakar kulewa ta koma kasa inda kannenta ke tayata girke girke da gyaran gida na tarbar mijinta da bakinsa.
"Ki barmu kawai Hanne muje ayita ta kare wallahi." Cewar wata kanwarta tana yanka ganyen salad din da ko wanke shi ba ayi ba. A tasu fahimtar sai an gama yankawa ake wankewa (datti da kwari idan akwai ba lallai su fita duka ba)
"Ni fa jikina har tsuma yake Yasin. So nake kawai wata ta dan bangajeni ko da bisa kuskure ne inyi mata zugar zogale."
Murmushi Hanne tayi ta kada kai "kar wacce ta kuskura ta taba kowa. Ina da maganin wannan rawar kan kuma zaku ce na fada muku. Su gama haukansu su hakura domin ni na tabbata ba zai taba kara aure ba."
(Mutumin da take tunanin ba don rabon cikin da ta dinga samu a baya ana samun matsala ba da tayi rantsuwar bashi da lafiya. Duk wani abu da zata yi na daukar hankali sai ta ga kamar baya gani. Ta jima da sakawa ranta akwai matsalar da ta shafi lafiya a tare dashi.)
Ana gama aikin 'yan matan suka yi wanka suka koma can gidan aka barta ita kadai. 'Yan kulle kullen magungunan mallaka da Gwaggo Jummai ta karbo mata ta zauna ta zuzzuba na abinci da na abin sha. Cikin irin juice din da yake girke mata a gidan ta bude daya ta tsiyaya ruwan maganin. Za ta kula ta tabbatar shi ya sha. 'Ba don mayen nan ba (Munzali) ai da kana gama ci zan saka ka zuwa yiwa Baba Sa'adu rashin mutumci' take zancen zuci ita kadai tana murmushi.
Sai yamma likis taji dirin motoci wanda ya yi daidai da iface-iface daga bangaren iyayensu. Ta katanga ta leka ta hango kannenta mata da wasu cikin 'ya'yan Mal. Sa'adu ciki harda 'Yasshafa suna dambe. 'Yashshafa na kwance a kasa ana tumurmursata ko hannu bata daga ba. Wannan shiri ne na Deluwa akan suna isowa ta bari ya ga abin da ake mata. Fadan ma su suka takala.
Motarsu na tsayuwa yaga 'yar wani kawun nasa kuma aminiya ga 'Yashshafa tana ihu tana tumami a kasa.
Da sauri ya fito "ke Baito lafiya?"
"Ina fa lafiya? Gashi can Anti (kalmar da bata taba fada ba) Hanne tasa kannenta suna nema kashe 'Yashshafa."
Dogon tsaki ya ja ya juya yana cewa su Munzali su fara shiga gidansa yanzu zai fito. Bayan Baito yabi suna shiga katuwar tsakar gidan 'Yashshafa ta soma zunduma ihu. A guje ta ture 'yan matan da suke dukanta ta yi kansa da gudu kowa yana kallo.
Saura kadan ta fada jikinsa ya dan ja baya tare da zaro idanu.
"Ki ka tabani sai na wanka miki mari"
Turus ta ja tunga ta tsaya. Deluwa taji wata irin muzanta da bata taba jiba. Da sauri ta bar wurin. Sauran iyayen nasu mata 'yan kallo ma kowacce ta sulale aka bar 'yan mata da kananan samari.
"Ku kuma tunda karfi kuke ji kowaccenku ta samo tsintsiya ku share gidan nan tas. Ina nufin a shiga bangaren kowa da kowa har soron waje. Zani gida nayi wanka. Don Allah idan na fito ace min ga wadda bata yi ba taga yadda zanyi da ita."
A gurguje suka dinga watsewa ya saki guntun murmushi. Wai 'Yashshafan da bata dade da daina yawo da majina bace aka koyawa irin wannan abin. Babu abin da bai ji ba a wurin Baaba Mari. Zai saitasu ne su duka su fita hanyarsa.
Bangaren iyayensa ya wuce yana mai fadada murmushinsa. Babu kowa a falon ya shiga da sallama. Daga cikin daki Baaba Mari ta amsa ya bita can. Yana sallama ko amsawa bata yi ba ta soma fada.
"Kaga abin da ka haddasa a gidan nan ko? Nayi nayi kazo sai yau kaga damar zuwa don ra'ayin kanka. To ka fadawa Hanne ta shirya ku koma tare zaman ya isa haka. Su Deluwa ma ka san yadda zaka yi dasu amma na gaji."
"Ayi hakuri Baaba komai zai daidaita in sha Allahu."
Kallonsa tayi ta danyi murmushi "haka nake so. Idan ka huta kazo ina da magana da kai."
Tatsuniyar gizo bata wuce ta koki. Zancen Baaba Mari baya taba wuce kwakkwafinta akan silar arzikinsa. Ita dai burinta ta san me yake yi ko taji sukuni a zuciyarta.
"Nima na taho miki da albishir. Ni da Munzali zamu bar kamfanin da muke yiwa aiki mu bude namu a Kano."
"Cewa zaka yi an daina bani labarin gaibu. Zan ga kamfanin da idona kenan." Ta ce tana washe baki.
"Kwanan nan kuwa da yardar Allah" ya amsa mata yana murmushi.
"Kai Madalla..."
Addu'a ta dinga binsa da ita kamar ba za ta daina ba. A can kasan ranta tana jin kamar an sauke mata nauyi. Tana son danta kuma babu abin farinciki sama da ganin dan cikinka ya zama gatan wasu ba ma kai kadai ba. Amma sabanin wasu iyayen ita sanin silar kudin shi ne kwanciyar hankalinta. Fargabarta kullum idan baya gari shi ne kada azo ace mata an kama shi tare da 'yan fashi ko barayi. Da wannan zulumi take kwana ta tashi. Ta sani cewa shi ma yana sane da rashin gaskata shi da tayi. Shi yasa tana dauko zancen yake nemo abin zillewa. Iyayensa maza kuma ko a jikinsu. Babansa ma da yake tayata damuwa ya sallamawa Ma. Sa'adu. Tunda ya ce a kyale shi ya san jininsu duk inda ya shiga ba zai yi abin assha ba.
*
Ya shiga gidansa ya sami bakinsa a zaune a falo su kadai.
"Ina Hannen?"
"Gani nan Yaya. Barka da zuwa. Ina kitchen na shiga hado abinci ne."
"Amma ko ruwa da ba sai basu ba"
"Ayya, ban ji shigowarsu ba."
Zai sake magana Munzali ya kada masa kai sai ya fasa. Abinci ta fara kawowa Abbati ya ce ta bari suyi wanka. Dakunan da ya ce ta gyara ya leka babu wanda aka share. Da kyar ya hadiye fushinsa ya dauki jakar Qibdiyya.
"Iya Kande muje bangaren Baaba ku kwana a can. Nan takura zaki yi. Qibdiyya ma za ta fi sakewa don akwai 'ya'yan kannena."
Iya Kande ba musu ta mike. Ta kula da irin kallon da matar tasa take jifansu dashi na rashin maraba da zuwansu.
Tare suka fita su duka sauran ma sun ce zasu gaishe da Baaba Mari. Sai da suka zazzauna a falonta tana ta haba-haba dasu sannan Abbati ya fita ya kira Hanne. Ransa a bace ya ce ya bata minti talatin ta gyara dakunan. Kuma ta aika musu abincin suci a can.
Hada komai tayi ta kalli juice din da ta zubawa magani kamar tayi kuka. Malamin