Showing 30001 words to 33000 words out of 242549 words

Chapter 11 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3345

suka rage take take fatan ko za a samu wani abu na cigaba a rayuwarsu.

To matsalar Zara karya ce sama da kasa take dawainiya da ita. A dole ita sai tayi rayuwar da za'a ce ita 'yar wani ce, ita dai kar a rainata. Hasiya kuwa ba sawa ba fitarwa. Yadda bata son rigima haka take kin halayyar Uwani da Zara. Maimuna da Salima kuwa tausayi suke bata.

Zara ta gama sakandire da wata shida aka kawo kudin aurenta. Lokacin Hasiya tana aji shida ita kuma ita ma ta kusa gamawa. Saurayin nata da ne ga guda cikin mashahuran 'yan kasuwar da Kano take ji dasu a Singa. Alh. Rabi'u kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha. Yadda yake jindadi da mijin A'i haka yake fata daga mijin Zara. Asabe kuwa hadiyar zuciya ne kawai bata yi ba. Hankalinta in ya yi dubu ya tashi wurin nemarwa Ummakati miji na wuce sa'a. An sanya biki wata biyu masu zuwa.

Innayo ce zaune a daki da Uwani da Hasiya ga kayan amfanin gida irin su kuka da daddawa da ta siyo tana rabawa gida uku. Uwani dake kashingide akan gadonta ta dago kai.

"Ki dan kara min kukar Innayo kin san Usman bai ki kullum na kada masa ba."

Murmushi Innayo tayi ta debi cokali bibbiyu a sauran kaso biyun ta kara a daya. A zahiri ita ba da Uwani take rabon ba. Ta san tana da kudin saye. Nata ne da Maimuna da Salima. Ba yadda ta iya ta hakura da natan. 'Yan kudaden hannunta duk sun kare wurin siyayyar auren Zara. Wadannan din ma cikin nata ne ta dibar musu.

Dan gyaran murya tayi tana juyayin samun biyan bukata a wurin Uwanin.

"Uhmmn. Dama abin da yasa nace ki zo saboda maganar Zara ne."

Tashi tayi zaune tana hade fuska
"Wallahi indai harkar kudi ce sai dai kiyi hakuri. Na fada miki adashi nake yi kuma sai nan da wata hudu zan dauka."

"Yanzu ba za ki iya rokon arziki a baki daukar watan nan ba? Kinga bikin ya matso ko bamu sayi kujeru ba."

Tashi Uwani tayi. Da ta san dalilin kiran ma da ta kirkiri dalilin kin zuwa.

"Ki nema a wurin Baba ko a rokesu a daga bikin. Ni wallahi yanzu dubu ashirin ma ba zance za a samu a jikina ba. Gobe nake shirin ranto talatin a asibiti. Sai na raba muku ke da Baba kuyi hidimar bikin."

Muryar Innayo kamar za ta yi kuka ta ce "iya gudunwamarki kenan a bikin kanwarki? Uwani idan baki tausaya min ba waye kuma zai min? Sauran 'yan uwanki duka abin a tausayawa ne a gidajen mazajensu amma ban taba cewa ki kawo wani abu na basu ba. Na zata kina da hankalin duba yanayin da suke ciki ki ..."

Yanzu taji magana. Ta rasa dalilin da yasa Innayo ta kawo ido ta saka akan albashinta. Lokacin da take hana idanunta bacci tana kwana karatu me Maimunan da Saliman suke yi? Basu tsaya sun gina rayuwarsu ba kowace tayi aure. Sai kuma ake tunanin ita za ta dauki dawainiyarsu saboda bata san zafin nema ba. Muryarta a sama ta soma magana.

"To ni dai ba zan dauki nauyin kowacce katuwa ba wallahi. Dubu talatin kuma ita kadai zan iya fitarwa saboda nima bani dashi. In don nace ki kara min kuka ne to ki bar abarki. Haba! Ba damar nazo gidan nan kin dinga tasowa da bukatun kudi..."

Tasss...taji saukar gigitaccen mari. Da kyar ta bude idonta da ya kanne saboda zafin shigar marin tana neman wanda ya yi mata wannan aikin. Hasiya da Innayo ne a gabanta. Kalaman autar tasu ne ya nuna mata hannun waye ya sauka a kuncinta.

"Idan su Yaya A'i sun wulakanta rikon da Innayo tayi musu basa dubanta yanzu ke kina da wata uwar ne bayan ita?" Cewar Hasiya lokaci guda tana fashewa da kuka. Muryarta ta dinga yin sama-sama saboda taki yin shiru.
"Kullum ki ka zo gidannan kin dinga kiran babu kenan saboda kada ki taimakawa uwar da ta biya miki kudin makaranta. To Allah Ya hadaki da babun nan da kike kira don girman..."

"Hasiya kama gabanki. Fita kada ranki ya baci. A gidan wa ki ka koyi rashin kunya haka?" Innayo ta furta da kwalla a idonta.

Kwallar ta sake tunzara zuciyar Hasiya. Rainin wayon yayarta ta ya kaita makura. Idan bata amayar da ranta ba tana jin zuciyarta sai ta buga.

"Innayo ki barni don Allah. Dubi dakinki don Allah." Ta nuna kowacce kusurwa da hannunta "Dakin da Yaya Uwani ta mayar kemis a gidanta fanka biyu ce da ta bango da ta tsaye. Ke kuwa fankar tsayen ma da kyar take juyawa. Nima tashi nayi na ganta a gidan nan."

Bakincikin marin da Hasiya tayi mata yasa ta kasa cewa komai. Duk abin da ta fada gaske ne to amma gaskiya tana tsoron talauci. Idan tana bada kudin sai su koma matsayin da ta tashi a ciki. Innayo ce ta kama hannun Hasiya ta fita da ita daga dakin. Tana juyowa taga Uwani ta saba jakarta tana gyara mayafi.

"Uwani."

Ta kira ta a sanyaye. Banda kudin bikin Zara da take nema harda na zuwa asibiti. Kwanakin nan sam bata jindadin jikinta daurewa kawai take yi. Dan abin da take dashi idan ta taba a zuwa asibiti dame za ta aurar da Zara? Danginta suna kauye a haka ta fi da yawa rufin asiri. Shi kuwa Alh. Rabi'u bakin hali ya raba shi da nasa sai jefi-jefi.

"Innayo sai naci mutumcin Hasiya. Dani take zancen. Kar ma ki bani hakuri don wallahi ba zan hakura ba."

"Zan yi mata fada. Yanzu dai ki taimaka min da ko dubu biyu ne in je asibiti gobe. Bani da kudi a hannu duk nayi sayayya dasu."

'Innayo ba dai naci ba' Uwani ta fada a zuciyarta. A ganinta duk abubuwan da take yi sun isa su sa tayi fushi ta daina tambayarta komai. Ba dole su A'i suka gujeta ba. Kila su ma roko ta damesu dashi. Dubu daya da dari biyar ta bata tasa kai ta fita.
"Nima ba kudin gareni ba."

Hasiya tayi kukan bakinciki a ranar. Bata ga me Innayo tayi da ya cancanci wannan wulakancin daga 'yar cikinta ba.

Washegari ta rakata asibiti. Hawan jininta ne ya tashi tana daf da samun stroke idan bata huta ba. Sannan likita ya bada shawarar ta rage damuwa daga ranta. Da ta fadawa su Maimuna babu abin da suka iya zuwa dashi dubiya sai sannu da fatar baki. Innayo din ce ma ta ce ta basu kullin kayan da ta ajiye musu. Zara kuwa bata zama ana ta shirin biki da kawayenta 'yan karya.

Da daddare ne ma da ta dawo daga rabon kati ta saka Innayo a gaba da kuka.

"Wancan gadon na soro ne gadon da ki ka saya? Dangin Unais raina ni zasu yi. Kuma har yau ban ga kujerun ba. Idan auren ba zai yiwu ba kawai zan ce masa na fasa."

Tana jin motsin Hasiya tayi shiru. Tunda Uwani ta dawo ta fadawa Alh. Rabi'u marin da tayi mata itama take shakkarta. Shi kuwa har uwar daka ya kirata ya zazzageta tunda Uwani ta bashi dubu shabiyar tayi mutumci a idonsa.

Da maganganun Zara Innayo ta kwana a ranta. Gari na wayewa taje gidan A'i. Tangamemen gida ne na zamani. A wani karamin falo aka ajiyeta har A'in ta sakko bayan kusan minti arba'in.

"Innayo kece a gidan namu? Nima ina son zuwa kawo gudunmawata ta bikin Zara." Juyawa tayi ta koma sama. Bata dade ba ta dawo da leda mai baka da yalo ta bata.

Godiya tayi tun kafin ta bude sannan ta fadi abin da ya kawota.

"Don Allah rance nake so A'i. Kujeru zan sayawa kanwar taki da sauran kayayyakin da basu samu ba."

Kallon tausayi ta bita dashi kamar gaske "banda abinki Innayo kiyi mata komai daidai karfinki mana. Kodayake naji ance dan masu kudi ne. Zara da rawar kai maimakon ta kawo tsaranta shi ne ta dauko wanda yafi karfinta."

Daurewa tayi bata ce komai ba tunda nema take. Wai A'i ce take yi mata haka? Lallai duniya baka shaidar da ko da naka ne bare na wani.

Ta sami bashin tayi ta murna ta karba ta tafi gandun albasa inda kafintoci ke kware basirarsu. Ta sayi kujeru aka biyota dasu hae gida.

Zara na gani ta tabe baki alamun basu yi mata ba. Innayo sai ta shige daki kawai ta fashe da kuka.

"Allah kar kasa 'ya'yana su maye gurbin mahaifinsu wurin wulakantani. Idan nayi kuskuren tarbiyarsu Allah Ka shirya min su. Ya Allah na yafe musu. Da wanda suka yi da wanda zasu yi a gaba."

(Haka rayuwa ta kan zo wa bayin Allah. Sai mu wahala akan wani abu da tunanin samun jindadi a tare dashi nan gaba. Idan lokacin girbar dadin ya zo lokuta da dama sai mutum ya kare da shan mamaki. Babu abin da Innayo bata yiwa 'ya'yanta ba na kyautatawa amma har yanzu bata ga wani abin buga kirji game da cigaban da ta jima tana yi musu fata. Duk da su din jininta ne to amma kar mu manta jinin Alh. Rabi'u ne. Basu tashi sun ga mahaifiyarsu tana da kima ba. Wannan zai iya rage mata daraja a idanunsu. A wahale suka ganta kuma dabi'ar dan Adam ce gudun wahala da talauci. Sai mai hankali, hangen nesa, tuna baya da tsoron Allah ne yake jajircewa wurin sakawa iyaye musamman uwa da alkhairi.)

Anyi bikin Zara ba yadda take so ba amma dai ta bar gidan kamar yadda ta jima tana buri. Sai jifa jifa take zuwa gidan nasu saboda tana kunyar a ce Innayo mahaifiyarta ce. Ga talauci ga rashin wayewa. Mijinta ko a jikinsa. Bata nuna masa tana ganin girman mahaifiyarta ba shi ma bai ga dalilin girmamata ba.

Abu na karshe da ya karasa kashewa Innayo jiki ta fitar da rai daga samun saukin rayuwa shi ne auren Hasiya. Wata uku bayan bikin Zara aka aiko musu da mummunan labari. A'i tayi hatsari ta rasu. Shi kuma babban danta da suke tare ya sami rauni a kansa.

Wannan labari ya gigita Innayo ya kusa zarar da Laraba mahaifiyar A'in. An sha koke-koke an hakura. Ranar da aka yi sadakar uku Innayo ta sayar da filin da shi kadai ya rage mata kadara ta biya bashin da A'i take binta na kudin kujerun Zara. Mijinta Hon. Habu ya ce ya yafe, idan ma adadinsu ya shiga gadon 'ya'yansu zai biya a madadinta. Kafin ta isa gida Laraba har ta je ta ce ta bata kudin. Ba musu ta dauko ta bata.

Kafin ayi bakwai ashe Alh. Rabi'u yana can yana kulle-kullen yadda zai cigaba da ci daga jikin Hon. Habu.

"Ga kanwarta Hasiya ba sai ta maye gurbinta ba. 'Ya'yanka suna bukatar uwa da za ta kula dasu tsakani da Allah."

Da mahaifiyarsa ya yi shawara ta ce ya amince. Dama ta kula a 'ya'yan Innayo din Hasiya ta fita daban.

Basu san hawa ba basu san sauka ba sai sadaki aka miko musu ranar da A'i tayi arba'in. Da uwa da 'ya aka rasa mai rarrashin juna. Asabe ta dinga habaici da zage-zage wai wa ya san me suka kulla har haka ta faru? Sai da Allah Ya kawowa Ummakati miji mai rufin asiri bayan shekara guda sannan ta daina zaginsu.

Hasiya ta tare da bakincikin auren dole da katse mata karatu. Mahaifiyarsu bata da mataimaki a gidan ga yawan rashin lafiya. Kaddara ta mayar da ita uwar 'ya'ya hudu da kananun shekaru.

Bata taba zaton zama zai hadata inuwa guda da 'ya'yan da suka raina mahaifiyarta ba. Sai gashi Abbas, Ummi, Murja da 'yar karamarsu Hajara (Ayaah) sun koma karkashin iko da kulawarta. A wannan lokacin ne kuma Innayo ta tashi tsaye wurin son ganin ta kashe wannan aure. A idanunta Hasiya ta maye gurbinta ne tamkar tarihi yana neman maimaita kansa.

Asabe kuma ta canja sheka daga yawon makota ta zamar da mijin Ummakati injin tatsa. Munzali ya kawo karfi ya yi kudi amma iyakarta dashi ta ce danta ne a baki ko ya bata idan ya yi niyya.

***


2018


A yayin da uwa ta haifi danta bata san gobensa ba ko anjima ba amma tana gina kyakkyawan buri aka rayuwarsa. Idan so samu ne ya fi kowa nutsuwa, kyaun hali, kudi da kyaun halitta. Ita dai ace nata ya yi zarra akan duk wani abu da zuciya take muradin samu. Burika ba kasafai suke cika ba. Da dadi ko ba dadi koda da nakudar haihuwa ce kadai dole a jinjinawa gudunmawar uwa akan danta.

Tabbataccen abu ne cewa kaddara ita ce kashin bayan rayuwar kowanne dan Adam. Akwai mai dadi da mara dadi wanda sau tari tafiyar rayuwa daga ranar haihuwa ke kai mutum ga tasa. Waye yake tare da mutum a wadannan lokutan sama da UWA? Kokarinta wurin bada kyakkyawar tarbiya kadai ba shi zai kare mutum daga afkawa ga kaddarar cizon yatsa ba. Addu'a da taimakon Allah su ne jigo.

Wata za ta kokarta amma akasin mafarkinta ne zai faru.
Wata za ta shantake amma duk da haka kyakkyawan alkalami ya rinjayi mummuna akan zuri'arta.
Wata tayi mai kyau taga mai kyau.
Wata tayi mara kyau taga mara kyau.

A karshe dai ba a canjawa tuwo suna.
Mari uwa ce
Innayo uwa ce
Khadija uwa ce
Asabe da Nasima ma dukkanninsu uwaye ne.

Shekarar ta kama dubu biyu da sha takwas. An sha gwagwarmaya an yi fama. Iyaye, gari (society), abokai da ma ainihin halayyar da aka haifi mutum da ita sun kai manya da kananan taurarinmu ga matsI think you'd like this story: "UWA UWACE..." by BatulMamman17 on Wattpad https://my.w.tt/DwuHp8HW49





UWA UWACE...8

Batul Mamman💖


(Domin samun post da comment shiga wannan link din)
https://chat.whatsapp.com/G5l0oQUZAFi37K0TXGggd5



{Kamar yadda na nemi uzurinku a baya sai kun dinga hakuri da rashin samun post a kai a kai. Zan cigaba da kokari da zarar na sami hali zan yi typing. Nagode da kulawar masu kira da masu text da dukkan masoya labaran Batul.}


Thank you Maryam AD Baffa.
You know why
I know why
They know why
(A friend in need....)



***
LAGOS
2018


Mukullai da cheque bibbiyu mutumin ya ajiye akan hadadden teburin gilas din dake gabansa yana kallonsu. Dukkaninsu kyawawa ne ga cikar halitta da kwarewa a gayu. Haduwarsu ta hudu kenan amma bai taba ganinsu da sutura daban daban ba. Hatta safa wannan iri daya suke sakawa.

"Ga tukwicinku nan. Kun shigo da kafar dama domin na kwana biyu ban ji sun yabawa wani kamarku ba. Kudin kuma ku chanja wardrobe saboda akwai baki wata mai zuwa."

Abbati da Munzali suka yi murmushi kowannensu ya dauki check da mukullin da yafi kusa dashi suka fita tare kamar 'yan biyu. Wandon jikinsu baki ne 3-quarter. Suka dora yellow din (hooded vest) riga mai karamin hannu hade da hula. Kafarsu bakaken original nike slippers ne irin na shakatawa. Agogo da askin kansu komai iri daya. Kyawawan matasa ne da suke ji da duk wani abu da cikakken matashi zai yi tinkaho dashi a wannan zamani. Abbati yana da shekara talatin da biyar yayin da Munzali yake da talatin da hudu.

Suna zuwa farfajiyar gidan shakatawar suka ga an bude motocin da suka wuce a lullube lokacin shigarsu. Lexus ne RX 2015 biege iri daya guda biyu. Wani irin ihun murna suka saka tare da rungume juna suna tsalle.

"Mutumin, yau akwai shagali fa" cewar Munzali yana yiwa Abbati kallon bani da na biyunka.

"Ai dole. Ba don maganar nadin sarautar nan ba da munje Dubai." Abbati ya mayar masa yana kallon cheque din. Miliyan goma goma ne a jiki.

"Kai dai kawai ka ce za ka je ganin uwargida Hanne."

Wawan duka Abbati ya kai masa da muguwar harara.
"Uwar Hanne zan gani ba Hanne ba."

Munzali ya kwashe da dariyar jindadi. Baya hada kowa da Abbatinsa. Yana kuma kishinsa kamar yadda kowane masoyi ke kishin abin da yake so. Iya tsahon rayuwarsa wani mahaluki bai taba nuna masa soyayya kamar Abbati ba. Shi dai ya san cewa yana da uwa da uba. Suna raye har yau amma cikinsu babu wanda zai ce ya san shi sani na hakika. Haihuwarsa suka yi suka bar wa duniya tarbiyarsa.

Yadda Abbati yake ga Munzali shi ma haka ya dauke shi. Bambancinsu bai wuce Baaba Mari da matsayinta bai tawaya a zuciyar danta ba. Munzali tamkar tsani yake ko kuma madogara a gareshi. A lokacin da iyaye suka watso shi hannun duniya babu wanda ya kama shi ya rungume sai Munzali. Shi ne gatansa wanda bai taba bari ya yi kewar iyayensa ba tunda suka hadu. Ya ciyar dashi kuma ya hana rayuwarsa tagayyara kamar ta sauran almajirai. Indai halacci yana sa dan Adam ya riki wani ya so shi kamar kansa to hakika bai ga ta inda Munzalinsa ya cancanci juya baya ba.

Sau tari iyaye maza suna son kasancewa cikin rayuwar 'ya'yansu amma sai neman abincin da zasu ci ya dauke uba ya nesantasu dashi. Irin wannan uba za ka same shi mai yawan dokin lokutan zuwa gida domin ya saurari kuruciya, shirme da zallar soyayyarsu gareshi. Akwai kuma kishiyoyinsu irin su Alh. Rabi'u. Shi a gida daya suke kwana amma rabonsa da bada kudin sayawa dan cikinsa panadol ma ya manta. Bai san komai ba sai cikinsa da biyan bukatarsa.

Idan aka sami uba irinsa ko wanda dole ta raba shi da gida da wahala ace uwa bata nan. Ita ke kokarin maye gurbin uban kuma ta taka tata rawar. Asabe bata cikin wannan sahun! Burinta daya ne. Me za ta samu a jikin 'ya'yan da tayi wata tara tana dakonsu a cikinta. Indai za ta ci ta koshi ta saka mai kyau to komai nafila ne.

Munzali kamar sauran 'ya'yanmu yana bukatar kulawar majibintansa. Ayi tattalinsa a shagwaba shi. Ayi masa fada idan ya kuskure. A taka masa burki idan yana neman tsallake layin da dabi'ar dan Adam da addini suka shata masa. Bai sami wadannan ba sai a wurin Abbati. Tun kafin su gama gane rayuwa Abbati yake son sa da zuciya daya. Ba zai tuna lokaci na karshe da Asabe ta san bashi da lafiya ba musamman idan ciwonsa na namoniya ya tashi. Amma tun kafin ya daina kwana a gida Abbati ke jinyarsa. Wani lokaci da ya tashi sai da ya kwana biyu bata leka dakinsu ba inda yake kwana da kaninsa. A rana ta uku ne ma da lalitarta ta kone kurmus babu 'yan canji yaji muryarta tana yiwa Innayo bala'i.

"An sako min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login